Friday, December 31, 2021

Zainabu Abu Daga Kauye Kashi 1 zuwa 3



HAUSA NOVEL NE WANDA MAI SUNA "ZAINABU ABU" DAGA KAUYE

Kashi Na Daya 1

Da sallama tashiga gidan hajiya domin tanada kokarin ziyara yaya aliyu tatarar a Palow zaune akan kujera dasauri ta isa dakin tayi masa barka da zuwa brother, yaushe kazo, yace mata "najima da zuwa, gashi har yanzu babu hajiya, kuma babu alamarta. 

Sai tayi kokarin tashi dan tayi masa girki cemata yayi Kew "sai yacemata ki hadamin  black tea" nan ta shiga kitchen ta dauko kayan kamshi ta haɗa mai takawo masa a cup? Sai ta tashi tana kokarun saboda gida zata wuce watau ma yayanta aliyu, sai yace "ki gaida umma nima ganinan zuwa sai tacemasa to.










Sai tayi kokarin zuwa bakin titi dan tasamu abin hawa bayan ta tafi. Sai taiso kofar da zata sauka, sai  yayi parking a kofar gidan nasu, sai ta ciremasa kudinshi a cikin Jakarta tabashi, sai tashiga gidan da sallama sai tace baba megadi, sai  yaketayimata sannu har durƙusawa tayi tana gaisheshi domin ita hafsat batada girman kai. 

Sai tawuce cikin dakinta domin wasa ruwa  sai ta cire kayanta, tashiga  cikin toilet amma tadaɗe tana wanka sannan tafito daure da tawul a jikinta sai tafara goge jikinta, sai ta nufi dressing a mirror ta janyo kujera ta zauna.

Sai tayi kwalliya mai sauki, sai tadau ko doguwar riga pink Wanda yake da adon black stone sai ta daura dankwalinta shima pink sai tawuce zuwa ɗakin umma domin faɗa mata yaya aliyu yazo. 

Sai tasame umma tana waya da mahaifinta, sai tace bari tajira, sai tayi ihu wa umma, sai  umma tace "hafsat meya faru ne? hafsat tace umma dama yaya aliyu ne yazo. Nan sai umma tafara murna tace mata "zomu shiga kitchen domin yimasa kayan tsara ba, umma tace wa hafsat tayi dambun nama, ita kuma umma sai tafara haɗamasa kunun aya da kayan kamshi domin umma akwaita da iya girki. 

Sai ta dauko dankali bayan ta markaɗa aya sai tasa kankara a ciki, kuma tafara fere dankalin kuma ta sarafa shi yadda zaici dan tasan shi bayacin abinci me nauyi, sungama haɗa komai, sai ga karar motarshi a kofar gida sai yayi parking, sannan yanufi cikin gidan.

Da sallama yashiga guda, inda yatarar da hafsat tana jera abinci a kan taburma, sai momy tafito damurna sukafara gaisawa inda take tambayarshi nasir da Fatima.

                  FARKON LABARI

Hajiya tana zaune a zariya sai mijinta alhaji aliyu yarasu tun bayan shekara biyar da suka wuce, tana da yara biyu, alhaji Ibrahim da hajiya salma, inda alhaji Ibrahim ya auri hajiya Hauwa, Allah ya albarkace su da aihuwar aliyu wato yaci sunan kakanshi inda yana shekara uku sai takara haifar nasir, suna ta murna kamar ba gobe, sai dai ban bancin ra'ayin aliyu yafi nasir son talakawa, shi nasir be damu da kowa ba, sai hajiya salma.

Kashi Na Biyu 2

Hajiya salma tayi aure a zariya kusada hajiya, amma tsakaninsu da rata, inda ta auri wani sha hararren Dan kasuwa watanta bakwai, Allah yabata cikin hafsat, suna ta kulawa da ita da wannan cikin nata har Allah yasauketa lafiya, ta haifi kyakyawar yarinya Wanda taci sunan HAFSAT.

Cigaba Da Labari

Hajiya taji wayarta yana yana ringing, sai ta  dauka tayi sallama, sai hafsat tafara fadin "wato hajiya haryanzu baki dena fita yawon bako" sai hajiya tace "to ina kan hanyar dawowa driver ya daukoni meya faru, yaya nasir ne yazo yada ɗe yana jiranki amma ya wuce gidanmu, sai tace ganinan zuwa". Sai hafsat takashe wayar nata.










Yaya nasir yacika cikinshi da abinci a gidan umma sannan yayi musu sallama ummace tami ƙa masa jakun kuna masu kyau guda biyu da na kanwarshi Fatima da na momy godiya yashiga yimata sannan yakira hafsat ta kwaso kaya a bayan motarshi takawowa umma. Sai yawuce cikin gidan sai yaga hajiya tana cin farfesun kifi sai yayi sallama yashiga ya gaidata, sai ta amsa masa tayi tana maraba da megidan kirki sai ya hada fuskansa yayi kamar wani iri, sai yace "ina kika je, nazo bansa meki ba, hajiya tace "wallahi dan makociyata ne bai da lafiya, shine nasa driver yakaini". Ok, amma nizan tafi sai tayimasa godiya, sannan ta bashi tsaraba nan take sai yace wa momy suna da biki a kauyen kano wato.

Aliyu ya isa gida lafiya, inda kowa ke tafaman yi masa  maraban dawowa sai nasir ya miƙawa momy kayan tsarabar da su umma sai yakra mika wa itama hajiya murna sukayi sosai inda Fatima ta hango kayan makeup ne aciki masu kyau nan take tayi zuwa bedroom dinta, sai yayi zuwa dakinshi domin watsa ruwa, sai ya tuna da sakon hajiya nantake yafara neman number momy sai yakirata yake faɗa mata sakon hajiya, Fatima na kusa da ita tanaji tafara murna dan tana son zuwa kauye, sai ya kashe wayar ya cigaba da uzurin gabanshi.

Fatima tashiga ɗakinta ta lalubi number hafsat nan take ta gayamata maganar biki saura kuwana ɗaya amma washegari zasu tafi ranar alhamis daurin aure, suna ta murna suke sosai inda hafsat sukayi sallama da fatima. 

Sai fatima ta haɗa kayanta da na amarya da turaruka acewarta shine shine gift da zata bayar,  itakuma hafsat ta dauki kayanta tazaɓo Wanda bata sawa, wato su hijab masu kyau domin baiwa amarya.

Washe gari fatima ta hango motar yaya nasir saboda dady yasashi ya kawo hajiya zuwa zaria, fushi yake sosai driven yake kamar zetashi sama, fatima yana yin chatting gudunshi ko ajikinta saboda yayannata sai a hankali, sun isa lafiya inda ta lalubi number hafsat take gayawa hafsat ta iso tsalle hafsat tadoka sannan tace my sister tafiyarmu ta tabbata masha Allah.

washe gari ummace da hafsat driver sai yakawosu, fatima na hangosu tafara murna inda taje ta rungume umma cikin gidan suka dunguma sunata hira da hajiya, nan take a ka shigar da kayansu bayan motor sukayiwa umma sallama suka shiga mota sai zuwa kauye.

sun sauka lafiya inda fatima tayi mamakin kauyen akwai wutar lantarki, nan sai kakansu ta karbesu domin gidan yafara cika da yan biki, wani ɗaki aka kaisu me taburma da gado da katifa a shinfiɗe a kai.












Sai kakansu takawo musu shinkafa da miya sai ita kakansu takira nasiba da zainabu, suzo su gaida hajiya, nasiba amarya sai yanga takeyi  "kaka munyi Bakine kamar turawa saboda naga kamar basajin yarenmu", hajiya tace wato uwata haryanzu baki dena yaranta bako.

Kashi Na Uku 3


Shirye shiye akeyi domin yau juma'a, fatima ce tasaka a kirawo mata amarya nasiba babu musu tazo sai Fatima ta fito da kayan sa jiki yayi laushi da haske irin na gargajiy, da turaruka, sai Nasiba ta zazzaro idanuwa ita dai batasan me wannan ba. 

Sai Fatima ta Kwaɓwa, sai ta umarceta akan tacire kayan jikinta tabar zani a daure a kirjinta, sai ita Fatima ta fara dirjeta, kuzo kuga amarya nasiba zaki rantse ba nnasiban kauye bace, sai kamshi take zubawa, fatima tace tunda ya bushe jeki kiyi wanka da soso ki tabbata mai me laushi tafita.

Sai zainabu tashigo da sauri tana kwalawa nasiba kira, sai ta shiga kallon nasiba, sai  zainabu tace " kin koma kalar turawa, sai ta zaro jajayen idanuwa tashigayi tana cewa kibari kawai na wahala amma dai koba komai haliru ya bani kudin yin hoto, zainabu tace "yanzu ma kinsan meke faruwa wallahi su uwani ne sukaje gonar da zamu hako dankali shine nazo muyi sauri mutafi dan wallahi bazan sha wuyar tarawaba.

Nasiba tafito daga wanka taje wajen buhun kayanta dan haliru beyimata zannuwa ba da sauri tashirya domin zuwa gona, tofa yau daurin aure ga maganar gona, kaya tagani acike guda masu kyau masu tsada atamfa taciro mata daga cikin kayan da hafsat takawo mata, mancewa tayi zainabu najiranta aka shiga yimata makeup amarya ta canja kala kamar ba ita ba, bayan biki kaka tasami hajja tace mata yakamata tatafi da zainabu tunda tana yawan dauko mata magana atakaice dai kaka bata kaunar zaman zainabu agabanta.

Umma tashigo dan gidan hajiya nan suka gaisa take musu sannu da zuwa zainabu ce ta gaisheta nan take ta roka hajia akan ta bata ita hajja ta kafe akan zainabu sai abuja, sunsha hira umma tayiwa hajja sallama nan suka tattara ita da hafsat suka wuce gida.

Washe gari su Fatima suka shirya zuwa abuja inda zainabu tace wai gurin hajiya zata zauna saboda shayin safe da burodi da wainar kwai acewarta wayasa ni ko intakoma can din gidan jiya ne, seda lallashi sannan suka tafi da it's, isarsu gidan sukaci karo da uban gaiyya wato nasir kallon up and dawn yamusu Fatima tace brother yakake, sai ya amsamata maida kallonshi ga zainabu yace "wannan yar aiki ki kasamosu, sai fatima tace "wallahi yarinyar kawuce na kauye sai yayi tsaki ya wuce waje sai suka karasawa cikin gida suka tarar da momy da big brother wato aliyu da suka fara murna suka karɓi zainabu sabanin nasir.






Momy tace kuwuce Ɗakin Fatima, ita fatimace tace zainab biyo ni muje, sai ta tashi tayi domin itafa bata kaunar sunannan. Da isarsu ɗakin Fatima sai da zainabu ta firgita saboda faɗin haɗuwar ɗakin, ashe Fatima harta shiga wanka tafito nan tararda ita a inda tabarta sai mazurai take, cemata tayi "sister tashi kishiga bathroom kiyi wanka, sai tafara murkushemata baki, wai danme zatace mata wait bathroom kuma a karshen taji wanka, sai tace a nan sai fatima tace mata eh kishiga kiyi wanka. Sai tashiga, ta kunna ruwa yafara zuwa da sanyi kalo, sai ta fara ihu ruwan yana jikata, tarasa yadda zata fita daga cikin bayan gidan.

Sai ga nasir a cikin  kananan kaya blue Jens da pink ɗin riga ajiki an rubuta am happy ya daura agogonshi mekyau yafito yana zuba kamshi sai yayi dakin momy yanufa inda yatarar da ita tana shirin tashi tafiya alwala takoma tazauna nan suka tattauna tsakanin ɗa da mahaifiya.

washe gari jirginsu yaɗa ga sai India, inda abba yayimai bayanin komai kuma ya fahimta a can gida zainabu na hango daga nesa bazakace itabace tasa uniform namakaranta wato  school uniform, masha Allah ammafa tayi kyau domin dama ba mumuna bace gata tasa farar riga da wando tasa school bag dinta data rataya, ayanzu kauyancin yafara raguwa zuwa tayi tayiwa momy da dady sallama suka wuce da it's, yaya aliyu inda acan makarantar akayi musu bayanin bata taɓa shiga makaranta ba amma akwai me lesson a gida sun gamsu sosai malaman kuma suna tunanin kamar baza tayi wuyar daukar karatu ba. kuɗi yaciro yaba naira dari biyar saboda makarantar ta yayan manyace, sai ta amsa masa tayi tamai godiya domin tasan Wanda takeyiwa rashin kunya.

contact-form






Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home