Thursday, October 28, 2021

Labarine Wanda Sunnansa "Trillion Amaal"

 



Labarine Wanda Sunnansa "Trillion Amaal"



Suna ganin yafita suka shiga dakin harsuna rige rige shiga, kwance suka sameta a yashe mutsima da kyar take iyayi, kinkimar ta sukai sukai ta dakinta nan akayi mata gashin ruwan zafi duk fuska kunbure duk kamaninta ya sauya, suhumaira sai dariyar mugunta suke, tana fara watsakewa tace wlh bazan yarda ba akan Yar aiki zaimin duka wlh sai nadauki mataki wlh kuma saina kira mom dita zai san waya doka. 

Humaira na dariya kasa kasa tace ma'ta "to aikinsan bro bazai doku ba ko kingayawa Aunty Shaheeda babu wani mataki da zata dauka dan itama tsoransa ta keji dan Ke da ita sai yayiwa rashin mutunci dan ba kunyarta ya keji ba, tunda anriga an zubar da mutunci a club, wani bama gujen zagi Salma ta ma'ta, duk rashin kunkyar da zaki karki zagi mamana , kuma dakika cewa club taje shima yaje abinda take shiyake to wazaiyiwa wani mummunanna kallo , ai kowa na sanjin dadi to mene aciki" Babu humaira tace, aike ma Yayarki aka kama da kato a makaranta kuma ta harkar basa.

Kai ya isheku marasa tarbiya, ko dai Allah ya wadaran naku ya lalace kowane bangare na dangi na zaune lfy duk da abin kunkyar kowa amma basa wannan haukan na ku suna zaune lfy sun rufawa kansu asiri amma banda ku marasa kunkya banza, Big Mom itace ke ingizamu wallahi duk yaran suka hada baki, tsaki taja, kada kudaina dan Allah yan iskan yara in bada maganar dana miji da yadda zaku kwanta dashi babu abinda kuke fada dudu shekarunku nawa ke da kike lekewa Amaal kinger mesa da shekara shida kina yarsa kince kina sansa yaki tunda har kika basa kanki wane kuma mutunci zaki da, daraja ai babu Yarikya dole kisha hulakanci da namiji, dakin kama kanki yaganki akamile da duk bazaiga wannan shekarun naki ba zai aure ki,amma wlh banda yanzo dan gani yake bashi kika farabawa wayasani ko ba a buduwa yasame ki ba dama kina tambadewarki awaje, tana wannan masifar tana hawasa bene inda dakinta yake dan taga idan tatsaya bakin ciki zai kasheta.













Shiru sukai sunsan Big Mom ranta yabace, da hartafara fada, suma barin dakin Salma sukai dan suna jin aushinta sosai.

Bantashi farkawa ba sai wajan daya na rana , mikewa nayi ina mamaki ganina kangado Amaal nayi dai-dai ina bacci, gefe na nakalla inda yake kwance yana baccinsa hankalin sa kwance ,da sauri na sakko ina dafe kuguna dakina na maza na tafi dan na tsorata da ganina kan gadonsa, bakin gado na zauna ina baida numfashi huya, tunin abinda yafaru jiya nayi, ina cikin wannan tunanin na kalli jikina, inda naga ba kyanda nasaka bane, rigar Amaal ce fara mai dugan hannu, rigar na daga naga da wando ajikina shi yanan na kayan dana sakane, yanzo ogane yaciremin riga, na shiga uku yagane min jiki sintire na hauyi cikin daki, ina tunanin wannan lamari, da naga abindai tunda yafaru to yazanyi gwara nayi abinda ya fisheni bandaki nashiga na kunna ruwa cikin Bahun wanka tare da cire kayana, ina tsaye nayi zigidir dani ina tattare gashi na naji anbanko kofa, banma gama tattacewa ya shigowa bandakin ko abune yafado ina kokarin juyawa naji anjanyo ni, "ke doctor yace bazakiyi wanka ba sai nan da sati saboda dinkin da akai miki sai dai kidinga goge jikinki da towel, idona zare yake fuskata nayi dauke da bakin cikin wannan lamari kamar zanyi kuka haka nake kallosa, ai kingane ko, kamar zanyi kuka na amsa" cikin alamar tambaya yace lafiya kike neman kuka ko dinki na miki zafine? Aiko yanayi to yazanyi ballema bayayi.

Ya mutse fuskayayi bangane ba wannan banzan amsan dakika bani?Aiko bazaka gane ba, kokarin bena yake da kallo na maza na saka hannu biyu na rufe masa ido, bama sai ka kalle ni ba wanda ma kayima ya isa, 'ke wai mene haka kike rufe min ido mai kuma na kalla yana neman banbare hannu na? Hankada sa waje nayi daka cikin ban dakin rufe kofar da karfi.

Numfashi na mayar ni dai bansan abinda ke damun Amaal ba, "ke wai mene haka naga yamiki karki wanka gwarama ki fito tunkan na balla kofar na shigo yana fada haka na ma za na mayar da kayana dan nasan zai aikata, da sauri na fito" tsaki yaja dalla fito kina wani buye jiki abu babu komai a kirji amma ana buye shi, duk ashafe yake kamar bangon dakin nan, rai na mabata adole ne ninaji haushi," fuska ya yamutse to karya nake hannusa ya kai kirjin gashi bakomai ajiki ya shafu kima kitaba kiji kitabatar da hakan hannu ya kama yadora akai aikinji babu komai amma sai wani babbuye jiki kike , dalla huce kije ki tayani hada kayana a trolley.


















To nace danni Amaal ya huce tunani na, ina zaune gefan gado shi kuma yana tsaye yana waya da yaransu , ina ta shirya kaya, akala na hada masa trolley uku na kaya ta hutunci nake saka turaruka, yana gama wayar , yauwa tunda mugama karasa min wannan bari nayi wanka na shirya sai kiyiwa direbana magana ya diba karki dauka fa," to nace ya huce yabarni, ni ina saka turarukan nidai kwai ina saka turarukan ne amma duk hankali yana kan tafiyar da zaiyi duk na damu sai naji babu dadi,, ina gama hadawa na kira drive awayar gida yazo yakwashe inan zaune har yafito cikin shiri, inda yasa kanan kaya babake sai dai kwai takalminsa ne kawai white, yana waya yana daura agogo.

Alamu yayi min da hannu alamar nagama ankai, kai na daga masa almar Eh ankai, murmusawa yayi, yayi min nuni da na biyoshi, babu musu na biyoshi yana tafe ina binsa abaya har kuma fito daka cikin gida," motoci ne sunfi Ashirin duka bodyguards dinsa ne kijiransa gashi anbude masa bayan mota ana jiransa, wayar yazare,rare da danne ta akirjinsa.









 









Yajuyo ya fuskance ni" Aara yauwa tafiya zanyi na shekara biyu sannan nasaka a akawo wadda zata tayaki kwana kafin na dawo sannan kuma duk abinda kike bukata akwai cikin Secretlock dina kinsan kuma Ma budin, tunamin naji ko kin rike, karanto masa nayi tas 9182475 yauwa kin rike , sannan za akawo miki malamin da zai dinga koyamiki karatu agida kafin na dawo naga canji kin iya reding daka kanki, kada masa kai nayi ni duk jinsa nake danni duk na shiga tashin hankali da wannan tafiya ina gani ya shiga mota aka rufe sukaja sai dusuka fita naji wani kuka yazomin bansan dalilin kukan nawa ba.

Da sauri na bar wajan nashiga daki da gudu na fada kangado na fashe da kuka sosai, na yiya kuka sosai sannan na tashi nayi alwala na rama sallolina da ake bina, ina idarwa na tafi Bangaran sa, adakin na zauna ina kallo da ka intaba takalminsa sai na shafa rigunansa na cikin haddan duruwarsa wadda take cikin bandaki inda mutum zai shirya da komai da komai wato dai dirowa mai daki, abunawa kamar almara haka na yini adakin , badan nagaji da dakin bane na fito na tafi dakina ina budewa, na kusa kurma ihu tsabar tsoro da firgita da kuma mamaki da abinda nagani.

Najaa ce zaune akan gadona tayi dai-dai ita da wata suna sun batar juna, budewar kofata ne yasa suka juyo, murmshi ta sakarmin, Babbar yarikya shigo mana aini ce wadda aka zaba na tayaki kwana ni da mijina ta nunamin buduwar dake gabanta dan haka zaki iya shigowa ko kiko ma dan mijina zai.

Bama sai na karasaba tunda kin gane abinda nake nufi tunda shi mai lalatsiki din ya tafi idan kuma zakizo kishiga maraba kofa abude take, da sauri na girgixa mata kai naja kofar da sauri nayi Bangaran Amaal na koma da sauri na rufe ko ina tunda ka Falo harzuwa sauran dakuna, dakinsa na huce shima nasaka key na kulle ina mai da numfashi, nidai tunda nake bantaba gani ba bantaba jiba ance mace ta aure mace yar kuwarta sai yau abun sai yayi wani bankwarai babu dadinji, kirane ya shigo ta waya dakin Amaal cikin mamaki nake kallon wayar sai datayi kara sau uku tukuna na tafi na dauki wayar, "Hlo nace"Kai My man na takiran wayayoyinka akashe gani na sauka, sai da yagama zubarsa tukana nace bashi bane bayanan yayi tafiya yau, shiru yayi"okay to kewace, tsaki naja kajini da mutum da tamyar rainin hankali, murmusawa yayi kinyi shiru? Mai aikinsace ni na maza na ajeye wayar.
















Wacece ke na kwai kwayi muryarsa ko kunkya bayaji, bayan wasu seconds wayar takara kara tayi kara yafi sau goma da taishaneni na dauka cikin fada dalla kafa takuramin da shegen kira haba dalla zan ajeye naji yace to in kingama sai kitsaya kiji abinda zance, cikin inda inda nace kayi hakuri bansan kaine ba, baima bani amsa ba yace kije kibudewa abokina zai kwana biyu agidan, ya kashe wayar tashi, cikin rashin jindadi abin na ajeye wayar na fita, A korido naci karo da su tsaye da naja tana masa magana naga yana bata waya, ko meyake da wayar"Oh, cikin hade fuska na karasa, tsayiwata kawai suka gani kansa ya dago ya sauke su anawa, kara hade rainayi zamu iya tafiya, kada kansa yayi," ke bakiga magana muke bane zakizo ki tsayamana, kinga malama bansa dake ba ban kuma rabadake ba na juya ina jan tsaki banza kawai.

Bangaran baki na kaisa , zan fito yace min jimana, baki fadamin sunanki ba Ayatsene nace Aara, na fice na barsa tsaye baki bude, kai gaskiya kin hadu yariya zanyi maganin jijjida kanki , wayarsace tayi kara , ya dauka,aboki na samu sabon hot fa hands-free yasa kai aboki kace kayi kamu , sosai ma sai dai fa kwailace dan yanzo tafara kirgin dangi sai dai girman jiki dan kusan kammu daya da kadan na fita tana da tsawan kafa, amma zanyi kiwanta ne dan samun budulcinta dan gaskiya zatayi zaki wlh, dariya abokina yayi gaskiya baka da dafa, yanzo kasan kuwa zan iya shiga rayuwarta sosai sannan na samu wata ballagazar na dinga rage zafi da ita, ita kuma wannan zanyi kiwanta, amma zan dan shawala dan akawai jida kai, daka bayansa yaji ance bamai sai ka wahalar da kanka ni dakaina zan maka kiwonta.

Juyowa yayi cikin mamaki!, karkadamu in dai kana tare dani tawani shafushi, badai kanasan shan zumarta ba to kabani komai a hannu, kuma zancan kwailace karkadamu, nan da wata daya sai na zamar da ita cikarkiyar mace, daka kasanta harzuwa baya da gaba, da gaske kike, Naja, umm tace ni dai kawai naji ruwan kudi zakaga aiki, daka nan kai kuma sai kashiga rayuwarta idan taki sai amata takarfi, rumgumta yayi gaskiya naji dadi sosai, murmusawa tayi nima alasamin wannan zumar mana, kashe mata ido yayi to nan dai suka shiga watsewarsu.

Ina koma daki na kwanta kango Amaal ina shakar kamshi mai ratsa zuciya har bacci ya dauke ni. Saune nake wajan Garden bacin malamina ya tafi da yake fama dani sai ya koyamin yare biyu Chinese da English, dama shima dan Nigerian ne, haka muke rigama dashi tun bana ganewa har nafara dauka, inan zaune ne ina bita mai aikin datake abince takawo abincin ta ajeye ta koma, kyallan da tarufa na bude tare da jan tire din gabana, daya bowl din kazace mai irin wani kala ni dai bataba gani ba dayan kuma chips ne amma ansamai miyar hanta akai mai duhu, sai lemon kankana mai madara shima, kazar na faraci to kazar dai gata nan gatan ita babu tas babu kuma rashin dadi kuma abin mamaki kuma babu kashi ajikin kazar sai da aka gyrata sosai ni dai haka naci na dauka sabon sanfar din Chinese ne.

Haka kulluma anake cin kazar da wasu abubuwa dab bansan mene suba. Ina saka kaya na na kalli kaina jikin madubi yadda naga na kara kiba na kuma kara fari sosai, sai kirjina da wasu abu suka fito kan nono na yan kanana masu zafi tsiya, idan na taba kamar nayi kuka , haka nagama shiryawa na tattara gashi wanda daka wankewa shikenan babu taja danni bana iya tajewa shiyasa ya cukurkudi, kofa aka turo Naja ce tashigo," ke Asmeeta meyasa bakyasan gyara gashinki ne duk kin barshi cukurkudi, banza nayi da ita na cigaba da abinda nake, inda nake takaraso gashin tataba bazaki gyara ba gaki da gashi kamar Yar india banza na mata, oh tunda bazaki magana ba shikenan bangazata tayi akirji, Ashh nace saboda zafin da naji mai ratsa jiki, na dafe wajan cikin dariyar mugunta tace kai sannu Asmeeta wlh bangani bane mene yake miki ciwo, dagowa nayi a wahalarce, laaa kema yana miki ciwo ashe , dakin magana dana baki magani, bari na kawo miki, durawar mudubi ta bude ta dauko kamar manshafawa amma duk wani bakin abu aciki, jaki bandaki kishifa zuwa dare zakiji sauki, babu musu na karba na shiga bandaki.

Jingina tayi da mudubi, hmmm Asmeeta kenan yanzo zaki fara shiga tarkona idan shafa ba daina ciwo zasuyi ba fitowa zasuyi kamafara zama mace kema, yadda nake ballagaza kamar yadda maza suke kirana kema sai na mayar dake haka, dan bazan yarda kizama kamilaba.


contact-form


Labels:

Wednesday, October 27, 2021

Ki Aure Dattijo Dan Ki San Meke Faruwa bayan Kwana Biyu.......


Ki Aure Dattijo Dan Ki San Meke Faruwa  bayan Kwana Biyu.......

    Sirrin soyayyar aure da dattijon namiji shine mace ta san cewa zata yi kishi da matan da suka girmemata ne, wata kila kuma sun ma haifeta, irin wadannan mazan suna bukatar ganin mace da zasu aura tana mutunta matansa na gida musamman uwargidan kamin ta shiga da kuma bayan ta shiga. 

    Haka kuma duk da irin kaskantar da kansa da zai yi a gabanki ganin yana nemanki da aure kuma gashi zai iya kasancewa sa'an mahaifinki, yana da kyau ki mutuntashi kuma ki dauke shi da daraja ba wai kuma ki maidashi wani boyi-boyi ba saboda zai rufa miki asiri ya aureki a matsayinsa na tsoho. Hakan zai baki martaba da daraja wajen ya yansa da kuma abokansa dama wasu masu sanya idanuwa game da soyayyan naku.

    Irin wadannan mazan basu cika kawo sako da kansu ba, akasari suka samu wani da suka aminta da shi kokuma wani babba daga cikin yaran gidansu su rika aika ne wajen matan da suke so da aure. Anan sirrin maza irin wadannan dattijan shine ki tabbatar 'yan aikensu kina mutuntasu, haka kuma kada kiyi wani abu, ko ki fadi wata kalma ko aikata wata dabi'a da zai iya kawo shakku a idanuwan dan aiken ko cusa masa wani kokwanto a zuciya yadda zai yi tunanin cewa maigidansa, ko mahifinsa ko kakansa zai auro mace ballagaza. 

    Wanni sirrin irin wadannan mazan shine, suna da matukar yiwa macen da suke nema da aure hidima, hidimar da wani lokacin yana wuce hankali, koda suna da shi ko basu da shi, abunda irin wadannan mazan basu so shine suyi maki kyauta kike karba. Suna bukatar ganin duk wani kyautar da suka yiwa macen da suke nemanta da aure ta sa hannu biyu ta karba tare da da nuna farincikinta da annashuwa. 

    Sai dai kuma kada hakan ya baki damar yawan yi masa aike da bani-bani, ko kuma yawan gabatar masa da bukatunki dana kawaye ko iyayenki a duk lokacin daya zo wajenki. Duk da yake idan mai haline ba zai taba nuna miki gajiyawa ba ko kuma fushinsa a zahiri ba, sai dai kuma hakan yana iya zubar miki da mutunci a wajen na kusa da shi, shi kuma zai dauka cewa iyayenki ba dattawa bane, haka kuma irin wadannan mazan babu wanda yakaisu gori, kada kiyi mamakin idan watarana ya cemiki shi yake ciyar da gidanku.


    Da yake sun manyanta kuma sun saba da karabniya da 'ya'ya da jikoki, kuma dadewarsu a duniya yasa suka fahimce halaye na mata dai dai gwargwado, mazan da suka manyanta masu neman aure maza ne da suke sha'awan ganin macen da zasu aura kullum a cikin kwalliya, haka kuma suna son mace mai yawan shagwaba tabkar karamar yarinya ko kuma jika a gaban kakanta. 
    
Wani abun sha'awa da irin wadannan mazan shine yana da wuyar gaske su nemi macen da zasu aura da lalata koda kuwa suna da matsaniyar tsohuwar karuwace Kamar yadda kika yi hakuri a lokacin soyayyar neman aurenki da namijin daya manyanta haka zaki ci gaba da hakurin bayan kunyi auren. Munyi bayani a baya irin matsalolin dake tattarae da soyayya da namijin daya manyanta, hakama zaman aure dashi yake da nasa matsalolin.

    Akasarin dattijawan maza dai yana da matukar wahala a rasasu da mace a lokacin da suke neman wani auren, haka kuma ana iya samunsu da 'ya'ya manya wasu lokutanma har da jikoki. Don haka duk macen data zabawa kanta zaman aure da irin wadannan mazan dole ne sai ta hada da gagarumin hakuri ko tana gida daya da sauran matansa ko kuma kowacce da muhallinta.

    Mafi yawan irin wadannan mazan da suka manyanta kuma suke bukatar aure, ba rashin jin dadin zama da tsoffin matansu bane basa yi, sai dai wasu loluta kamar yadda bincike ya tabbatar matan nasu na iya tsofar da bazasu iya gamsar dasu ba a lokutan jima'i. Haka kuma wasu tsofin magidanta giyar kudi ne ke dibarsu suji ko ba komai ai gara su samo wata mace mai dan galmi-galmi su aura domin su burge abokansu. Wasulokutan kuma abokai ne a tsakankaninsu suke yiwa tayi 'ya'yansu ga junansu.

    Koma dai da wace hujja ko dalili mace ta yanke shawarar auren namiji daya manyanta, babban sirrin zama da shi shine ta tabbatar da cewa bat nunawa matansa, 'ya'yansa, jikokinsa, 'yan uwansa da abokansa gadara da iyayin da zata iya fiskantar matsala dasu ba. Kamar yadda muka yi bayani a baya, a lokacin da dattijon na miji ya yanke shawarar auren mace, bai cika canza ra'ayi ba koda kuwa ya fahimci wani illa da macen da yake sonta da auren ba, haka kuma lokacin daya aure mace bai cika barin wani matsala a tsakaninsu yana bata masa rai ba ganin cewa yana da kwarewar zama da mata da kuma sanin irin matsalolin mata da hanyar warwaresu ganin shima ana kawo irin wannan gabansa na 'ya'yansa ko jikokinsa yana magacesu.

    Sai dai babban matsalar da macen data aure dattijon namiji zata iya fiskanta a zaman aurenta da mijin nata shine idan har ta sake wata matsala ya shiga tsakaninta da matan wannan mijin nata, ko kuma 'ya'yansa. Wanda irin gallazamata na karkashin kasa dana zahiri yana iya sanyawa ta gudu ta bar ladanta. Babban sirrin zama da irin wadannan magidanta shine ki tabbatar da cewa babu raini a tsakaninki da matansa duk da yake yanzu abunda suke ji wajen dattijon kema kina danawa, haka kuma a wannan lokacin idan matansa marasa fahimta ne da tsoron Allah zaki ga abubuwa da dama da cusa bakin ciki da takaici tumma ba ace kuna gida daya ba ganin su sun tasanma tsofa kekuma yanzu kike more mijin nasu dasu ci kurunciyan aure tare amma gashi yanzu sun zama 'yan kallo.

    Dole ki dauka cewa wannan matan da yanzu kike zaman kishiyoyi tare tamkar iyayen kine su, don haka duk wata bakar magana ko habaicin da zasu yada miki ki kauda kunnenki tamkar baki ji ba. Haka kuma kiyi kokakrin jawo wasu daga cikin 'ya'yansu ko kikokinsu da kika fahimci cewa masu saukin kaine da fahimta kusa dake domin kokarin nuna masu halin da kike ciki cikin hikima da dabara. Haka kuma ki tabbatar da cewa kin samu natsuwa sosai a duk lokacin da kika ga wani abu ba dai-dai ba a gidanki ganin zama da tsaffin mata a matsayin kishiyoyi, zama ne da mace take bukatr darasi a kansa ganin irin kissan da kisisina na gadar zare da irin wadannan matan zasu iya shirya mace ta fada idan bata yi hankali ba.

    Haka kuma wani sirrin da zaki iya dauke hankalin tsohon mijin nan naki dashi shine iya kwalliya da kuma tsaftace jiki da muhalli. Shi na miji ko kazami ne yana sha'awar ganin cewa yana zaune da mace mai tsaffta. Haka kuma irin wadannan mazan ko kura bai kaisu kwadayin nama ba idan masu lafiyan hakora ne, idan kuma ba masu shi bane kada a raba ki da shirya masa 'yar wata ferfesu na kaza ko na kifi a duk lokacin da zai shigo gidanki ko dakinki.

    Maza masu yawan shekaru sune mazan dasu kafi sha'awar ganin mace da manyan nonuwa ko kuma tsayayyun nonuwa, bincike ya tabbatar da cewa akasarin manyan maza masu shekaru da suke sha'awar kara aure babu abunda ke sasu hakan irin sha'awar ganin suna wasa da mikankun nonuwan budurwa ko karamar bazawara idan suka ga cewa matansu na gida sun tsufa.

    Don haka a duk lokacin da zaki yi kwalliyarki na jiran miji, ki tabbatar da cewa kin yi shigar da zasu fito da hantsarki sosai domin kwantar da hankalin dattijon mijinki. Haka kuma iya tafiyarki shi kansa wani sirri ne na zama da dattijon na miji, domin a lokacin daya kyalla idanuwa yaga cewa kina tafiya jikinki na kadawa nan take keji tsohuwar tsuminsa yana tashi.

    Haka kuma a duk lokacin daya shigo da abokansa wadanda suma watakila masu shekaru ne, to ki tabbatar da cewa kin karbesu hannu biyu-biyu, kuma ki nunawa mijin naki so a gaban wadannan abokan nasa har sai sun gamsu da cewa tabbas abokinsu yana cikin wani sabon rayuwa na zamantakewan aure, wanda hakan zai sasu suma suyi sha'awar idan suna da halin yi.

    Bafa ina nufin cewa ki kwanta a kansa ko ki sumbace shi a gabansu bafa, a'a, abun nufi shine ko ta hanyar hira ki tabbatar masu da cewa wannan mijin naki yafi saurayi dan shekaru 17 a wajenki. Da kuma nuna masu cewa baki bukatar jimawansa a waje da makamantar irin wadannan wasanni na baki wanda wasi sako ne da mai hankali yana iya fahimtar abunda ke dauke cikinsa.

    Sirrin zama da magidantan da suka tsofa shine, a kullum ki dauke shi tamkar kina auren saurayi ne, kada ki kyamace shi ganin akasarin manyan magidanta ana iya samunsu da wasu halaye irin na tsofa. Haka kuma ki tabbatar da cewa yadda zaki yi soyayyar zaman aure da na miji mai karancin shekaru haka shima zaki yi da shi. Haka kuma ki cire a ranki cewa kina zaman aure ne da dattijon daya yayi sa'ar mahaifinki, saki jiki ki wahala kiyi soyayayyar zaman aurenki da mijin naki.

    Sai dai kuma manyan matsalolin da mata suka fi fiskanta a lokacin zaman aure irin wannan shi ne na rashin samun haihuwa a wasu lokutan da kuma ishenshen kwaciya ta jima'i ga macen data ke da bukata da yawa.

MATAR DATTIJO:

A ranar baba ya tura aka aka kira masa dattijona, a soro nayi musu shimfida cike da ladabi ya samu guri ya zauna, kallona ya rika yi yana min murmushi tare da kashe min ido da alama dai so yake nayi masa magana, banza nayi da shi na wuce gida saboda ji nake gaba daya na tsane shi, tsakar gida na koma na barsu su yi magana da baba.

    Bayan sun gaisa baba ya fara yi masa bayanin makasudin haduwar su, gyara zama baba yayi sannan ya fara yimasa magana, nasan za kayi mamakin kiran da nayi maka Alhaji, kansa a sunkuye ya amsa kwarai kuwa baba, Allah yasa dai lafiya gyaran murya yayi sannan ya cigaba da cewa, zamu iya cewa lafiya amma ba lau ba.

    Cike da mamaki ya dago yana tambayar sa me kuma ya faru baba?damuwa ce ta bayyana a fuskar baba, Alhaji ina ganin ya kamata kayi hakuri mu ma mu yi hakuri ka sauwakewa Niimatullah aurenka, a firgice ya dago me kuma yakawo wannan maganar baba? girgiza kai yayi ba komai Alhaji kayi hakuri mu ma dole ce tasa zamu fasa amma mun san kana son yarinyar nan ita ma tana sonka, amma Niimatullah bata dace da kai ba, saboda kai mai kudi ne kuma mai ilimi kuma ka fito daga babban gida, ita kuwa yar talakawa ce kuma marainiya mara gata, ina jin tsoron barin Niimatullah ta aureka saboda furucin matarka a kanta kada ta hallaka mana ita wata rana saboda na fuskanci tana da kishi da yawa shi yasa na duba naga abinda ya fi alkhairi shi ne ta bar mata mijinta.

    Kaga a kullum karfin mukarewa yake kada a yi auren nan wani abu ya biyo baya, tunda Niimatullah yarinya ce karama har yanzu bata gama mallakar hankalin kanta ba gashi ba tada wayo ga rashin gata ko cutarta tayi ba mu da halin karbar mata hakkinta,dan haka nake rokonka dan girman Allah ka sauwake mata, saboda maganin a yi shi ne a bari, kusan zuwanta biyu gidan nan tana ci mana zarafi, har shake Niimatullah tayi har sai da ta kusa suma yanzu haka
wuyanta ciwo yake, don haka mu baza mu iya fada da abinda ya fi karfin mu ba don Allah ka saketa.

    Tunda dattijo ya sunkuya bai dago ba wani gumi ne ya rika yanko masa ta ko'ina,nan da nan idanunsa suka yi jawur saboda takaici, bai san ya xai yi ba idan aka ce ya rabu da Niimatullah ba, cikin rawar murya yake wa baba magana, kayi min arziki baba wlh bazan iya sakin Niimatullah ba, dan Allah a yi hakuri zan tsawatar mata wallahi ban san tana zuwa tayi muku haka ba, dafa kafadar shi baba yayi ka kwantar da hankalinka Alhaji wannan duk ba wani abin tayar da hankali bane, abu ne da muke so a yi maslaha saboda Allah ya sani amanar Niimatullah a hannuna take, duk wani abu da ya sameta muna da alhaki a kai kuma sai Allah ya tambaye mu wannan dalilin yasa dole a warware auren nan saboda gudun bacin rai.

    Hawaye ne ya cika idon dattijo rokon baba ya fara yi a kan yayi masa alfarma ya janye maganar, duk nacin da yayi hakarsa bata cimma ruwa ba, jikinsa a sanyaye ya dubi baba. dan Allah ina so xan yi magana da Niimatullah, cikin sakin fuska baba ya bashi amsa ba komai Alhaji ai bazan hanaka magana da iyalinka ba tunda har yanzu a karkashin ikonka take.

    kirana baba yayi cike da ladabi na tsugunnah tare da cewa gani baba, cikin kulawa yace mijinki ne yake son magana da ke yana gama fada ya bamu guri, kan shimfidar da aka yi masa na zauna, sunkuyar da kaina nayi saboda yadda na ganshi yana cikin tashin hankali da damuwa karasowa yayi ya zauna kusa da ni, fadawa jikina yayi yana Hawaye tare da tallafo fuskata Niimatullah me nayi miki kike neman yanke alaka da ni? me yasa kike son na sake ki alhalin kinsan zuciyata baza ta iya jure hakan ba, ke kika fadawa baba kina son na sake ki? sunkuyar da kaina nayi tare da cewa.

    Eh na zabi hakan ne saboda hankalina zai fi kwanciya dama na dade ina tunanin hakan saboda cin kashin da matarka take mana ya fara yawa, na yanke shawarar hakura da kai indai hakan zai yi sanadiyyar farin cikina dan allah ka sake ni ko zan huta da wulakancin da matarka take mana.

    Kallona yayi da jajayen idanunsa lallai baki san adadin yadda nake sonki ba Niimatullah, ke yanzu a tunaninki zan iya rabuwa da ke wallahi son rayuwata nake miki bazan iya hakura da ke ba saboda ina matukar sonki, a halin yanzu kawai kina ganin kaso ne mafi kankanta daga cikin irin son da nake maki, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna miki tsantsar soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure.  

    Ba zan taba mantawa da sadaukarwar da kika min ba, kina yarinya kika aure ni a matsayina na dattijo, kina tunanin zan manta da wannan sadaukarwar? don haka babu macen da zata samu gurbin soyayyar da kika samu a zuciyata, kisa a ranki bazan iya rabuwa da ke ba,ya zan yi da rayuwata idan na wayi gari bakya tare da ni, ki tuna a wajenki kawai nake samun farin ciki, yana karasa maganar ya fashe da kuka.

    Nima kukan na rika ni kaina nasan ina son dattijona amma hangen abinda xai je ya dawo nake yi, cikin kukan nake masa magana nasan kana sona amma dan allah ka duba halin da zan fada ka sake ni, matarka bata kaunata tana zagina ta zagi innata me zan je gidanka nayi, ni tuni na bawa xuciyata hakuri a kan rabuwa da kai kuma ta hakura da kai.

    Kamo ni yayi hada da kirjinsa yana rarrashina, me yasa zaki min haka Niimatullah, kin san irin kaunar da nake miki da zaki ce sai na sake ki, indai aka takura na sake ki wallahi nasan sai na rasa raina, saboda soyayyar ki ta gama yi min illah. Zame jikina nayi na nufi bakin kofar shiga gida ina share Hawaye, hada kansa yayi da bango yana ta kuka kamar karamin yaro, bazan iya jure ganin shi yana kuka ba wannan dalilin yasa na shige gida gudun kada zuciyata ta buga saboda bacin rai.

    A soron na barshi ya fi kusan minti talatin yana kuka cikin kukan yake kiran sunana, Niimatullah ki tausayawa rayuwata ki aure ni, ki tuna irin yadda nake sonki da kaunar Ki,tun lokacin da na fara ganinki, kika shiga raina kin samu gurin da baza ki taba fita ba har abada. ke ta daban ce Niimatullah, kina da wata baiwa wadda ba kowace mace Allah ya bawa ba, ina samun nutsuwa idan ina tare da ke,kada ki guje ni Niimatullah ki kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskar ki,zan yi kokarin wadata ki da jin dadi daga cikin nau’ikan ababen jin dadin rayuwar duniya. 

    Ina tsanin sonki babyna bazan iya barin ki ba ya karasa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani, cikin gida na shiga ina zuwa na fada gado ina kuka, ban san halin da zan tsinci kaina ba idan aka raba ni da shi, shine mutum na farko da ya fara koyar da ni soyayya, a kullum burinsa ya tarairayi jaririyar zuciyata wacce bata san komai ba sai soyayyarsa da karfi na rika fadar hakan ina cigaba da kukana, innata ce ta shigo inda nake saboda taji sambatun da nake yi dafa kafadata tayi tana rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah indai Alhaji rabonki ne zaki aure shi,mu dai fatan mu ya yiwa tufka hanci wannan matar tasa ta daina zuwa tana ci mana mutunci, nasan Malam zai sakko saboda yana son abinda kike so, a ranar cikin damuwa na wuni.

    A bangaren dattijo kuwa yana komawa ya tarar da gidansa ba kowa, kwafa yayi ya samu kujera ya zauna a falo yana jiran dawowar matarsa, tunanin Niimatullah ya shiga yi da yadda zai shawo kan baba ya kyale shi ya tare da matarsa, baya jin xai iya rabuwa da ita saboda duk wani farin cikinsa ya hango shi tare da ita, yana cikin tunanin yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa, hannu yasa ya share gani yayi an tsaya a kansa, a hankali ya dago, matarsa ya gani tsaye tana yi masa wani kallo a fusace ya mike yana nuna ta da hannu, ji yayi bakinsa na rawa saboda takaicin da ya cika zuciyarsa kasa ce mata komai yayi.

    Cike da gadara take masa magana, naje na lalata auren yar iskar yarinyar da kake so, saboda bazan taba iya sharing dinka da wannan kazamar yarinyar ba, kuma wallahi ka sani na rika yi maka haka kenan Har abada ba kai ba kara aure, duk inda kaje neman aure sai na rika zuwa ina ci musu nutunci a haka har su yi zuciya a fasa auren, mutumin banza kawai mara alkawari, a fusace ya dubeta. ni kike kira da mutumin banza Hajiya Maryam? tsare shi tayi da ido tana harararsa na fada duk abinda za kayi sai dai kayi, karya nayi maka ba mutumin banzan bane kana tsoho ka auro yar cikinka saboda son zuciya da kwadayi an girma ba a san an girma ba, lalata aure yanzu na fara idan zaka nemi yan mata dari ni kuma sai na lalata auren har sai ka hakura ka daina.

    Komawa yayi ya xauna saboda idan ya cigaba da tsayawa tsaf zai fadi wani bakin ciki ne ya cika zuciyarsa cike da fushi ya mayar mata da amsa wlh ba dan arzikin yayan da kika haifa ba da zamana ya kare da ke yau,a matsayina na uban yayanki kike kirana da mutumin banza saboda ba ki da hankali, auren Niimatullah ne bakya so kuma kisa aranki kamar amarya ta tare a dakinta ne, kuma ki shirya ganin wulakanci kala-kala Allah dai ya kawota da alkhairi, da sannu sai na ganar da ke kuskurenki sai kin yi nadamar kirana da mutumin banza shashasha mara amfani, sai kin zama tamkar shara a gidan nan dama ba ki da wani amfani a wajena banda bata min rai babu abinda kike yi mahaukaciya kawai, yana gama fada mata ya wuce dakinsa.

    Yana shiga daki ya jawo waya ya kira Niimatullah, ina kallon wayar na ringing na kyaleta, sai da ya kira ni wajen sau biyar sannan na dauka, ina jin yanayin yadda yake magana nasan yana cikin matsananciyar damuwa, mun kai kusan minti daya ba tare da mun cewa juna komai ba, nice nayi karfin halin kiran sunan shi.

    Dattijona! cike da damuwa ya amsa min da na'am my Niimatullah, cike da damuwa nake masa magana, idan har akwai wani abu da zan roka a wajenka bai wuce na rokeka a kan, ka amince mu kasance tare ba har abada, domin tabbatuwar mafarkin da ya jima yana bayyana a cikin baccina, ina sonka amma dole na barka tunda iyayena sun hango min matsala a tare da Kai.

    Cikin sanyin murya yake min magana yanzu baza ki tausayawa mijinki ba niima, ina cikin damuwa ko abinci na kasa ci, yanzu babu taimakon da zaki neman mana a wajen baba ya taimaka ya kyale mu muyi rayuwar farin ciki da juna,shikenan duk ginin da muka yi a baya ya rushe my Niimatullah, ki duba halin da zan shiga ki tallafi rayuwata, ji nayi hawaye sun fara zubo min hannu nasa na goge.

    Ina sonka dattijona amma bazan iya aurenka ba saboda mugun halin matarka saurin dakatar da ni yayi, tsaya Niimatullah bana son kina kawo tunanin wannan matar a ranki, babu abinda ta isa ta hana game da auren mu rayuwa mai dadi za kiyi da mijinki, ki tallafi rayuwata ki shawo min kan innah da baba su yarda da ni, a sanyaye na amsa da to zan yi insha Allah sallama muka yi da shi ya kashe wayar.

    Ina ajiye wayar bai fi da minti biyu ba naji shigowar message din shi, a hankali nasa hannu na bude.

Ina fatan zuwan ranar da zan kasance shinfide a saman kafadun ki na kwana a cikin dakin Ki, na kasance a tallafe bisa hannuwan ki,wato ranar da za a kirani da angon ki. Ki duba kaunar da nake miki ki shawo min kan baba, ina sonki ki huta abar alfaharina. Ina gama karantawa naji wani hawaye ya xubo min na tabbatar da cewa mijina yana sona idan na bar shi ban yimasa adalci ba.

    Wajen innata na koma fadawa nayi jikinta ina kuka, cike da tausayawa ta dube ni, me ke faruwa da ke Niimatullahcikin kuka na amsa mata da dattijona innah kada ya mutu ta sanadina na samu alhaki, yana cikin damuwa yace na roke ku, ku janye maganar nan dan Allah.

    Cikin kulawa inna ta dube ni tare da girgiza kanta, kiyi hakuri Niimatullah zan samu malam nayi masa magana nasan zai janye idan yaga halin da kuke ciki,ni kaina bana son auren nan ya tarwatse saboda Alhaji mutumin kirki ne kuma tsakani da Allah yake sonki kiyi hakuri Insha Allah zai sakko, rarrashina ta rika yi har sai da hankalina ya kwanta.

    Wayar da ke gefen mu ce tayi ringing, hannu innah tasa ta dauka,sallama tayi cikin kulawa aka amsa mata tare da cewa dan Allah ina neman Niimatullah ne, da sauri innah ta miko min wayar na kara a kunnena tare da yin sallama muryar matar da take min gyaran jiki naji cikin ladabi na gaida ta, tambayata dalilin da yasa kwana biyu banzo makaranta ba ta fara yi, muryata na hardewa na bata amsa saboda bakin cikin da ke cike a raina, an fasa auren shi yasa na daina zuwa.

    A razane ta tambaye ni me kike fada min haka Niimatullah bana son shirme fa, ina innar ki?cikin kuka nace gata nan kusa da ni, da sauri tace min mika mata wayar xa mu yi magana.

    Cikin girmamawa take wa innah magana, sannu baba ya gida ya yara, nice matar da nake gyarawa Niimatullah jiki naga kwana biyu bata zo ba shi yasa na kira nasan jiki da jini, sai kuma yanzu da na tambayeta dalilin rashin zuwanta naji tana min wata magana wai an fasa auren nata menene gaskiyar abinda take fada min baba? kana ganin Innata zaka gane tana cikin damuwa don damuwar har a maganarta ta bayyana, bayani ta fara yi mata ba karya Niimatullah ta fada miki ba gaskiya ne abinda ta fada, cike da mamaki take tambayar innata, to menene dalilin
hakan baba.

    Sauke numfashi Innah tayi mun fasa ne saboda muna ganin hakan shi ne abinda zai fi zama Alkhairi a gare mu dakuma ita, mijin Niimatullah yana sonta nasan kema kin san haka, amma kishiyarta ce ba tada kirki zuwanta biyu gidan nan tana ci mana mutunci har tana ikirarin zata hallaka Niimatullah wannan dalilin yasa muka fasa.

    Cikin nutsuwa malama ta fara yiwa Innah bayani, ina ganin ba haka ya kamata a yi ba baba, tufkar kawai za a yi hanci, amma batun a fasa ma bai taso ba, saboda za a cutar da zuciyoyi biyu da suka dade suna son juna, tunda matsalar nan ba daga wajen bawan Allahn take ba bai kamata a fasa ba, saboda idan aka fasa an ji tsoro kuma an bata damar ta cigaba da yin haka nan gaba, ita wacece da zata ce ita kadai xata rayu da mijinta,tunda Allah yabashi dama kuma yana da ra'ayin kara aure dole yayi, bazai yiwu a ce duk gyaran da muka yi ya tashi a banza ba baba, gobe insha Allah zan zo tare da Alhajin duk inda matsalar nan take sai an warwareta, godiya Innah tayi mata sannan suka yi sallama. 

    Ba karamin dadi naji ba da jin kalaman malama nasan tana zuwa komai ya zo karshe insha Allah. Baba na dawowa innata ta sanar da shi yadda suka yi da malama, shiru yayi na wani dan lokaci yana nazarin maganarta a hankali ya dago da kansa yana duban mu ni da innah, ni kuwa gabana sai faduwa yake saboda ban san irin amsar da zata fito daga bakin sa ba, cikin nutsuwa ya fara yi mana magana.

    Ina so ku fahimci wani abu ko kadan ban taba jin na tsani auren Niimatullah da Alhaji ba, hasali ma zan fi kowa farin ciki idan aka ce sun yi aure saboda nasan kyakkyawan hannu na kai ta, baza mu taba yin da na sani ba, amma abinda za a duba matsalar matar nan da irin furucin da take yi a kanta, nasan irin wadannan matan ba tun yanzu ba idan suka yi yaki da baki suka ga bai ci ba komawa suke su bi mutum ta kasa, shi yasa bana son abinda zai zo ya tayar mana da hankali muna cikin zaman mu lafiya.

    Ji nayi kamar nayi kuka wata sabuwar soyayyar Dattijona ce take dada bijiro min ban ki a ce na tashi na komagidansa da rayuwa ba, duk wata matsala da baba yake hango min ni a yanzu bana ganinta, saboda ko kadan Allah ya cire min tsoron matarsa kuma ina jin zan iya yin fito na fito da ita ba tare da wata fargaba ba, nasan nayi nisa a zuciyar mijina wanda bata isa ta kamo ko rabin son da yake min ba, kaina a kasa na fara yiwa baba magana.

    Ni dai baba idan da yadda za a yi dan Allah ka bari na aure shi wallahi ina son mijina, cike da mamaki innah ta dube ni, inye Niimatullahi har kin san dadin mijinki, lallai yaran zamani sai dai a barku kawai, shi kuwa baba kallona kawai yake y rike baki Innah ce take ta bayani.

    Malam tunda har Niimatullah ta furta mana tana son mijinta ina ganin ba mu da wani zabi wanda ya wuce mu tattara ta mu kai ta dakinsa, girgiza kai baba yayi, nima tunanin da nake yi kenan shi yasa kika ga na kasa magana, amma zan nemi Alhaji yazo ya tattara ta su tafi kuka na fara yi cike da shagwaba nake magana a tattara ni fa kace baba sai kace wata kayan wanki ni Allah sai ma na fasa auren, murmushi baba yayi ko kin fasa sai an kai ki tunda ina yi miki gata har kina cewa kina son mijinki ni ba ruwana dole sai kin tare, kuka na fara yi a kan ni bazan tare ba na fasa tashi baba yayi ya bar mana wajen, kan cinyar innah na fada ina cigaba da kukana.

    Washe gari Dattijo da malamar mu suka iso gidan mu a tsakar gida suka same ni ina hada kwanuka, sauri nayi na sanya hijabina saboda bazan iya jure kallon da yake bina da shi ba, a dakin innah nayi musu shimfida, shiga malama tayi ta zauna shi kuwa dattijona a tsakar gida ya tsaya yana cigaba da kare min kallo, cike da tsiwa nake masa magana.

    Menene ka tsura min ido kamar baka saba ganina ba, murmushi yayi tare da matsowa daf da ni riko hannuna yayi cikin sigar shagwaba yake min magana shi ne don kin ganni kike wani saka hijabi ko,naga dai komai na jikin ki mallakina ne to me zaki boye min.

    Harar shi nayi tabdi wallahi ba mallakinka bane nawa ne ko innah za a tambaya tasan da haka, murmushi yayi gami da jan kumatuna kina da dabaru na sanya ni murmushi my Niimatullah ko da a ce ina cikin fushi idan kika yi magana sai naji wni snyi a raina,kin zamo wata ta daban a gare ni, shi yasa ina ganin ki dukkan shaukina yake tashi,bana gane cewa ni namiji ne sai ina tare da ke, don haka ki daina tuhumata idan ina kallon ki, tunda kina sona ko matar dattijo. 

    hankali na gyada kaina alamar eh, murmushi yayi sannan ya cigaba da magana nasan da cewa tunanin ki a kullum bai wuce neman hanyar da zaki inganta rayuwata ba ki bani farin ciki mara misaltuwa,wannan dalilin yasa na sadaukar miki da soyayyata kuma nake fatan kasancewa da ke har abada my Ni'ima, bazan iya daina kallonki da begenki ba har sai ranar da numfashina ya kare duk maganganun nan da yake yi kaina na kasa saboda kunyarsa gaba daya ta kama ni,maganar da innah tayi masa ne yasa ya dawo hankalinsa, a sanyaye ya cika ni tare da sumbatar hannuna, sai na fito my Niimatullah na sake ki ne ba dan na koshi da ke ba,sai dan zuwa na samo mana mafitar yadda zamu rayu da juna har abada, sakina yayi na koma gefe na zauna.

    Tattaunawa suka fara yi a kan maganar tarewa ta a gidan dattijo, kwala min kira innah tayi da hanzari na karasa dakin cikin ladabi na tsugunna tare da cewa gani innah, cike da kulawa ta dube ni kira mana malam a waje, takalmana na saka ina fita naci sa'a na same shi, yana shigowa malama ta fara magana.

    Mun xo ne baba a kan maganar tarewar yarinyar nan, naji ana cewa kun fasa shi ne nazo na baku hakuri a kan bai dace a yi saurin yanke hukunci haka ba,tunda dai suna son junansu, kuma maganar kishiya baza ta tsoratar da mu ba tunda yarinyar nan mijinta na sonta duk wani abu da zai cutar da ita zai yi kokarin kawar mata da shi.

    Gyara zama baba yayi, ni dama ban zafafa ba Hajiya fatana dama yazo ya fada mana irin matakin dazai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda zai je ya dawo ko ba haka ba. Gyara xama baba yayi, ni dama ban zafafa ba Hajiya fatana dama yazo ya fada mana irin matakin da zai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda xai je ya dawo ko ba haka ba.

    Cike da zumudi dattijo ya fara magana, wallahi baba babu wata matsala da za a samu duk wani matakin da ya kamata na dauka naje na dauka, na yi mata magana a kan ba ita ba Niimatullah idan kuma ta cigaba xa tayi a bakin aurenta.

    Saurin dakatar da shi baba yayi, a'a ba a haka Alhaji kada auren nan yayi sanadin rabuwar ka da uwar yayanka idan kayi haka baka yi adalci ba sannan duniya zata zage ka mu ma zata zage ma, a zaci don ka auri jikar mu ne kayi mata wannan wulakancin, baza a duba girman laifin da tayi ba namu za a gani, don haka kada ka fara aikata haka, kawai kai dai kayi niyyar tsayar da adalci a gidanka sai kaga Allah ya taimake ka amma batun kace zaka saketa ma bai taso ba.

    Cike da ladabi dattijo ya amsa da insha Allah zan kokarta baba, na gode da wannan shawarar da ka bani, haka suka cigaba da tattaunawa daga karshe aka tsayar da lokacin tarewar mu nan da sati biyu masu zuwa, ba karamin dadi dattijo yaji ba, nima farin cikin ne ya kama ni saboda duk kusan hirar da suke yi a kunnena ake yinta.

    Tashi suka yi zasu tafi, a tsakar gida dai suka kara tarar da ni, kirana malama tayi ta fara yi min nasiha. Kinga yanzu tarewar ki ta matso don haka gyaran jiki zamu rika yinsa ba dare ba rana idan kuma baki tsaya an gyara ki ba kin zauna kina gaddama kishiya ta raina ki,ni ba ruwana don haka yanzu duk abubuwan da na baki ki mayar da hankali ki shanye, idan kin zo gobe zan baki wasu ki kara sha,so nake ki rikita mijin nan naki ya kasa gane hanyar garin su, dariya muka yi gaba daya har mun yi sallama ta tafi ta dawo ta kira ni, kije mijinki na son magana da ke, makale kafada nayi ni Allah bana son zuwa, hararata tayi kinga irin abinda yake hada ni da ke ko wuce mu je nace miki.

    Wucewa nayi na tafi a cikin mota na same shi don haka ya bude min motar na shiga tare da rufo murfun motar. Wannan kenan.


contact-form




Labels:

Tuesday, October 26, 2021

Meyasa Ana Samun Mutuwar Aure A Cikin Lokuta Kadan

 



Mekesa Ana Samun Mutuwar Aure Da Wuri

Assallamu alaiku yan uwa jama'a, muna so ne muyi bayani game da yadda mutane suke magana game da, meyasa mata aurensu yakan mutuwa da wuri. Wasu matan sunce mazan ne basu da hakuri, ta wani wajen kuma mazan sunce matan ne basu da hakuri, to bari mugani ta wane bangare ne aka fisamun matsala kota wajen matane ko ta wajen mazane da kuma tayaya zamu magance wannan matsalar.

Zakaga masoya suna yin soyaiyarsu kamar har idan rana daya nasu hadu sunga juna ba sai kaga kamar zasu mutu, zakaga za a wuni ana ta yin chatting ko ta facebook ko ta whatsapp, in allah yakawo dare kuma sai a hadu ido da ido a cigaba da hira kuma kowa baya so yarabu da juna dan zunzurutun son da kowa yake wa junansu har lokacinda zakaga anyi aure, bayan aure kuma kowa yagaji da ganin juna bayan lokaci kadan kuma sai kaga anfara samun matsala da kadan kadan sai kaga abin yayi zafi in har ba a sa hakuri a ciki ba sai kaga saki yashiga aure ko wata biyar baiyiba aure yamutu.

To wannan al'ammarin bamusan ko me yake faruwa ba, yadda yanzu mata zawara suka yawa a yanzu, sai kaga mace taje gidan rediyo tana magana dan ita bazawara sai kaga kunya yafita a idanunta tana gaya wa duniya akan duk wanda yana sonta da gaske tafito yanuna kansa har idan dagaskiya yake yi sai suyi aure. Ita kuma bata tunane akan zuwanda tayi gidan rediyo za a fasarata ta hanya da dama.

A yadda mukayi bincike namu game da yadda aure yake mutuwa bawai yana da ga bangare daya kawai ba, ko wanne yana da na shi a ciki.

Wasu da ga cikin abubuwanda yakan iya jawo aure ya mutu shine, zaka namiji yana neman yarinya dan wani abinda yaga kamar tana da shi, sai kaga sonta yashiga ransa amma wannan son da yake yimata ba wai son na allah da annabi bane kokuma zance bai gina wannan auren dan allah ba kawai yana duban tana da wani abune wanda yaso kuma yashiga ransa, bayan anyi wannan auren yazo yagani abin kuma ba haka ba, sai kaga yafara wasu hallinda ita matar baza ta gane metayi masa ba, zata ta fara ganin wulakanci da dama iri iri sai kaga yana allah allah tayi wani abinda zai sa ya saketa.

Wani dalilain kuma zakaga mace bata son wani, amma iyayenta suna sonshi badan komai ba dan arzikin da yake hannunsa, sai kaga yarinyar tace bata so amma iayen sai sufi karfinta sai ta aureshi dan suma sudinga lasa abida yake dashi. Sai kaga bayan anyi aure yasanu abinda yakeso daga nan zata fara ganin abubuwa masu banhaushi dan yasan ta aureshi ne dan abin hannunsa a shiyasa zai fara yimata abinda har zai jawo dalilinda har idan ta nuna bacin ranta sai yasamu hanyar da zai saketa.

Zakagani wani lokaci namiji yana son yarinya amaimakon yafito mata a yadda yake da kuma yadda allah ya ajiyeshi, sai yafito mata da karya dan kawai yasamu yadda zai jayo hankalinta, bayan yasameta yayi nasaran aureta, sai kaga bata gani abinda take zaton za ta samu ba. Da ga nan ne sai idan basu sa hakuri a cikin zuciyarsu ba, sai saki ya shiga tsakaninsu dan auren karya bai da amfani fadin gaskiya shine mafin'alheri ga masoya in ana so ayi zaman lafiya.

wani dalilain shi ne rashin kulawa da juna ko ta wajen mace ko ta wajen namiji, dalilin da yasa nace haka, zaka ga mace bayan tayi aure ko bayan sun samu yara sai kaga ta fara yimasa rashin kulawa kamar misali bazata ta na kulawa dashiba dan tana gani sunriga sunyi aure kuma sunsamu yara a tsakaninsu ko tafara rashi tsafta wani lokaci zakaga idan kazo gida kamar da yamma sai katarar kwanon da aka ci abinci har zuwa yamma bata wanke ba ko sharan gidan ma zakaga batayiba, da kuma rashi kwalliya da sauransu. Ko kuma yakan faruwa daga shi namijin ta wajen rashin kulawa da ita bayan sun dauki lokaci ko shekaru bayan tafita akansa duk abinda yakeso yayi da ita sai kaga yafara mata wulakanci daga nan kuma wani namijin sai yafara neman matan banza a waje to kagani baza ta yarda ba dole ne tafara nuna rashin jindadin abinda kake yi har idan baka dena ba dolene har idan tagaji zata nuna maka abubuwa da dama na bacinrai har wanda zai kawo sanadiyar saki a tsakaninku.

Sha'anin aure abune wanda yakamata mu dinga kulawa, kuma abune wanda har idan munbi yada allah yafada abune wanda yakesa mutum yasamu aljannah har idan ma'auratan biyu kowa yabi abinda ubangiji yace game da aure. Kuma Allah (SAT) yana maicewa, har idan ka sake matarka Al'arshin Ubangiji yana kadawa, shi saki a musulunci hallal ne amma ba ace a rika yinsa wanda ba bisa ka'ida ba, sakin aure ana yinsa ne bisa yadda addinin musulnci yace ba wai kawai dan wani karamar matsala yashi ga a tsakaninku ba sai kace mata na sake a'a bahakabane, dan wasu mallaman addini sunce har idan wata matsala yashiga tsakaninka da matarka wanda har yakawo kun samu tsappani, kayi kokari kafita ko kaje kasamu wani abokinka kuyi hira nan da lokaci kadan zaka ga hankalinka ya kwanta itama sai kaga tayi sauki wani lokacinma in har kadawo gida sai kayi mamaki yadda zata karbeka.

wannan shine abubuwanda suke jawo aure yakan mutuwa da sauri dan idan za abi yadda shari'a yafada to akan samu sauki sosai ba wai yadda a yanzu muke sakin mata kamar yadda muke yin nunfashi ba, ko da kake so ka sake matarka kabi yadda addini yace to zaka samu sauki har idan ita matarka din taki tayi hakuri a sasanta to sakin yafi alheri amma kawai kwasam ka sake mace ba wai tayi maka na kirkiba dan kunjima kuna zaman uare ta ita ka gaji da ita sai ka nemi abinda zai kawo muku matsala dan ka saketa.

A wani lokaci kuma mata susuke kawo matsala gameda wasu matan bayan anyi aure an samu dan shekaru ana zama, sai kaga anfara yin kawance da wasu matan da ba na kirkiba sai kaga sun sata cikin wani rayuwa wanda har zata fara raina mijinta sai tana ganinsa kamar ba mutum bane halayenta zai canja dan tahadu da matanda sun bude mata idanunta wanda sun fi karfin mijinsu sai abinda suka ce a gidansu, to kagani wannan ma har idan mijinta yayi daidain karfinsa har idan abin yagagara dolene kaga saki yashiga tsakaninsu.

Yawancin matsalar da ake samu cikin kashi (100) ana samun kashi (70) na laifi daga wajen namiji, dan shine allah yabashi ikon tsakanin ma aurata shi yake da izini yasaketa, muji tsoro allah zakaga mace tana tafiya amma jikinta yana wani waje dan rashi zaman lafian da bata da shi tare da mijinta, wata idan tayi maka bayani abina yake faruwa da ita in kaji na watanku sai kaga gwara na wancan dan mu mazan muke fara kawo matsala a tsakaninmu da matanmu sai mu mayar da su kamar bayi dan kai ne allah yabaka izzinin aiwatar da komai ko wani idan yaga tafito daga gidan da iyayenta basu da karfi sai yamayer da ita kamar baiwa a gidansa hakan baya da kew, ka guji hukuncin allah dan lokacinda hukuncinsa ya haukanka zaka yi kuka wanda kana neman hawaye ma ya sauka bazai sauka ba.

Zakaga namiji yamayer da saki kamar wani abin wasa, sai kaga yau ya aure wata bayan wani lokaci kadan sai kaga yasaketa kuma yakar auran wata bayan yasamu abinda yakeso sai kaga kuma yakara saketa duk bawani dalilin da har yakai wanda zai saketa, to irin wannan bashi da kew dan lokacinda allah yakamaka, har kamutu rayuwarka ba zai yimaka kew ba har idan baka tuba ka koma ga allah ba.

Shi a rayuwar mu na yau game da matan aure da mijinta ba wanda zai samu natsuwa ga juna sai da mijinta, shima mijin ba zai samu natsuwaba sai da matarsa, wannan allah ne yashiyar mace bazata iya rayuwaba sai da namiji, kuma namijima bazi iya rayuwa ba sai da mace, tu a zamani annabawa sunyi bayani game da mace abune kamar zinariya, ko wane irin kudin da allah ya baka zakaga mace tana juyashi tana zoliyarsa kamar yaro karami ba komai bane kawai allah ya dauramusu abu ne wanda yana jikinsu har idan akwai soyaiya a tsakaninsu na aure.

Zakaga wani yana neman wani abu a wajen wani sai kaga yagagara samu, amma idan har yabi ta wajen matarsa sai kaga anyidace, to mata abune wanda allah ya basu wani abu ajikinsu wanda zakaga namiji zai mayar da kanasa kamar yaro karami.

To dan allah aji tsoron allah adena yin sakin mace kamar wata dabba, dan a lokacin su kakkanninmu sunci nasara ba dan komai bane da hakurin da sukayi na zaman aure shiyasa suka ci ribar aurensu ba dan komai bane dan sunbi yadda shari'a yace, amma mu yanzu sai kaga kunlum namji yane cewa mace sai na sakeki ai' kunlum zakaga yana furtawa a bakinsa to hakan ba dai dai bane abi shari'a a zauna lafiya a cin ribar aure.

A dinga daraja mata har idan sunyi laifi kayi musu nasiha kuma ka dinga yaba mata shi arayuwa soyaiya bata tsufa sai dai masoya su sufa, kulawa da juna ga maurata yakan kara soyaiya a tsakaninku, amma sai kaga mace idan tayi wani laifi kadan sai kaga namiji yafar mata tsawa kamar ita ba mutum bane, har idan matanka tayilaifi kokuma tanayin wani abu ka hanata ta takiji sai kace mata taje gidansu ta zauna wani lokaci ita da kanta zata yi nazari akan laifinda tayi, wata har idan tana da imani zata baka hakuri akan laifinda tayimaka to dole ne tasan tayi kuskure zakaga baza ta karayiba.

Kuma mata kuna da naku laifi, wata idan taji mijinta zai karamat kishiya sai kaga tafara daga hankalinta kuma allah ya hallatta namiji yakan iya kara mace biyu har zuwa hudu. Dan annanbi (SAW) yace mata zasu shiga wuta dan tawajen bijirewar dan mijinta zai karata kishiya wanna shurmen banzane dan allah yariga ya hallatta in har kinnuna bacin ranki, to kina jajjawa da abinda allah yafada. Muji tsoron allah a dinga yin hakuri, Annabi (SAW) duk macenta ta kafircewa mijinta zata shiga wuta "Bukhari".

Mata dan allah ku rika yin tsafta dan idan mijinki yashigo gida ganin farkon da zai fara yimiki daga sama har zuwa kasa, har idan tayi kwalliya zai yi sha'awa ko su rungume juna, amma har idan kina nan kwasap ba dankwali, kai a tsefe, kinannan kamar wani namiji to hakan bai da kew, yakan sa namiji yafar neman mace a waje. Har idan aka bi wannan abinda muka fada to za'a samu sauki game da mutuwar aure da yake faruwa.

Ina yin fatan alheri ga muji soron allah a duk macenda aurenta yamutu har yayi sanadiyar tazama bazawara, sai ta kama kanta, tarike mutuncinta allah zai bata mafita har idan ta kama kanta. Allah yabamu dama kuma yaganar da mu a duk wata hanyar da ta sabawa shari'a. Assallamu Allaiku.

Hakika ina jin takaicin a yadda yau aka wayi gari mace-macen aure ya yi yawa musamman a kasarmu ta Hausawa ko in ce matanmu na Hausawa, musamman idan ina kallon sauran yarurruka a fili ko a fim.

Babban abin da yake kara daga min hankali shi ne yadda za ka ga kafin aure, mace lokacin da mace take gidansu ana shan soyayya rigidi- rigidi, a wuni ana chatting a waya, dare na yi a taho zance, duk watakulawa ana yiw a juna yadda yakamata amma da zarar an yi aure an dan gama cin amarci, an gama rububin juna, sai ka ga an fara samun sabani. Kamar da wasa sai ka ga ba a shekara ba sai ka tarar sun ishi juna daga nan sai taruwar matsaloli daga nankuma sai ji ji saki ya auku. Wa iyazu billah.

To abin tambaya a nan ita ce me yake jawo haka? Me ya sa mata zawarawa suka yi yawaa kasarmu ta
hausawa? Wani abin tausayi shi ne yau har an wayi gari duk da kunya da kawaici irin na ’ya mace sai ka jimace bazawara ta fito gidan radiyo tana tallar kanta wai idan da mai so ya kawo kansa su sasanta.
To a bisa nazari da binciken da na yi abubuwan da na fahimta suke janyo yawan mace- macen aure a yausuna da yawa kuma ba bangare daya ne kawai yake da laifi ba, kowanne bangare yana da nasa laifin.


  •  Abu na farko da na nazarta shi ne kwata-kwata auren ba a gina shi domin Allah ba. Wasu sun gina shi akan karya, wasu kwadayi wasu kuma domin wasu abubuwa da yake hange a tattare da macen wanda suke burge shi wanda da zarar an yi auren ya ga ba yadda ya zata ba, to sai ta fi ta daga ransa sai ya fara yi mata wulakanci daganan ya saketa. Wannan maganar da na fada ba ina nufin kowa ba, ina magana akan mafi yawancin mutane.
  •  Sannan abu na biyu wanda shi ma yake taka rawar gani wajen mutuwar aure shi ne kwadayayyun iyaye. Sai ka ga mai kudi yana neman auran yarinya ko ba ta so iyayenta za su tursasa mata sai ta aure shi saboda kwadayin abin hannunsa, ba za a tsaya a yi kyakyawan bincike ba saboda yanad a kudi, sai a dauki yarinya a aura masa, wanda a karshe sai irin wannan aure ya zama na nadama. Da ta shiga gidansa sai ya fara gwada masa irin halayensa na cin mutunci daga nan kuma sai saki ya biyo baya.
  •  Abu uku kuma shi ne karya. Namiji zeai je ya yi ta yi wa mace karya, ya rudeta ta don ta aure shi wanda da zarar an yi auran sai ta tarar da sabanin abin da yake mata karyarsa daga nan sai ka ga an fara samun matsala, daga nan sai saki.
  •  Abu na hudu shi ne rashin hakuri tsakanin ma’aurata, shi ma yana taka muhimmiyar ruwa.
  • Abu na biyar shi ne rashin iya rike juna da amana da tattala juna da nuna wa juna soyayya daga dukkan bangarorin biyu. Sannan kazanta tana taka rawar gani wajen mutuwar aure, musamman daga bangaren mace. Akwai abubuwa da yawa wanda yakamata mu lura da su domin magance wadannan matsaloli na mutuwar aure.

Hakika aure wata hanya ce wadda ake samun aljanna a cikin sauki a cikinta sai dai ya danganta yadda ma’aurata biyu suka tafiyar da auren cikin tsoron Allah. Haka nan saki shi ma halal ne amma ba a son yinsa a addinance domin Allah (SWT) ba ya son a yi saki domin duk lokacin da aka yi saki sai Al’arshin Ubangiji ta girgiza.

To da wannan dalilai ya sa saki ya zama abin ki wanda ba a son sa sai ya zama dole domin akwai matakan da shari’a ta ajiye yadda za ka bi da mace wanda har in ta bijire to sai a saketa. Amma ba yadda ake yin saki birjik a halin yanzu ba, babu wata hujja mai karfi.

A nan nake kira ga maza su ji tsoran Allah domin su ne suke yin saki domin mace bat a sakin kanta sai dai namiji ya saketa. ’Yan uwana Musulmi maza ku sani cewa mata ba abun wulakantawa ba ne kamar yadda kuka mayar da su a yau. Kowace mace idan ka yi hira da ita za ka ji irin izayar da take ciki a wurin mijinta, idan ka ji na wannan, sai ka ji ai na waccan ya fi muni.

An wayi gari mata a wulakance wasu mazan sun maid a mata tamkar riga idan ya sa waccan, ya sa waccan. Wallahi wannan musiba ce kuke jawo wa kanku don wannan ba burgewa ba ce. Kamar yadda Manzon Allah (SAW), yake fada a hadubarsa ta ban-kwana ina imuku wasicci da alkairi gamata. To ku ji ’yan uwa yanzu tun da Annabinmu ya fadi wannan, mata yakamata su zamo abun wulakantawa? .

Annabinmu mu ne fa ya fadi wannan! Kuma kar ku manta duk rintsi mata ne suka haifeku. Ina nasiha akan masu wannan dabi’a ta wulakanta mata akan su daina. Mace tana da daraja, kalmar mace tamkar zinariya take wajen yin walkiya a kowane lokaci. Mata suna da sinadarai wadanda suke da tasiri, a cikin al’umma wanda har ta kai sun samu matsayi babba. Mata suna da wani launi mai juya mazaje tamkar linzamin doki, komai matsayin mai mulki ko kudi ko sarauta.

Allah Yasa Mudace.


contact-form





















Labels:

Monday, October 25, 2021

Sai Na Aureta Ko Baka Saketaba





ABDULLAHI DA KAWUNSA

Abdullahi ne da wani wanda ake cemasa "Kawu" sunyi wani karamar hira ne amma sai wannan hirar tazama da gaske sakamakon kawu yacewa Abdullahi "Kasaketa in aura" a cikin hira, bayan sungama hira da abdullahi sai yacemsa bari zai tafi wajen buga kwallo sai yayi sallama da shi Abdullahi.

Bayan ya iso gida sai yayi sallama baiji an amsa masa wannan sallamar sa yayiba, sai yashi cikin daki sai yaga "Safina" bata cikin daki, yakara damka ihu Sakina!!! Sai yaci shuru, sai zuciyar ya sinki sai yafito waje yana tambayan makobcinsa ko ta shiga zuwa ciking gidansa, sai yace a'a matarka bata shigo ba, sai makobcinsa yace lafiya sai Abdullahi yace masa lafiya.

Sai Abdullahi yafara yintunani akan "Kawu" yana yawan cemasa ko da yaushe sai ya dauke Safina, sai yafara zaton akan ba wanda zai aikata wannan abin sai Kawu.

 Sai yaje gidansu Abdullahi yayi sallama akan ko Abdullahi yana nan, sai aka cemasa yafita tunda safe bai dawo ba. Sai yafara tunane akan ina zai sameshi gabadaya Abdullahi hankalinsa yatashi akan wannan yarinyar Safina.

Sai yayi kokarin bari yaje yayi bayani wa jami'an tsaro, bayan ya iso zuwa ofis na jami'an tsaro sai ka wata takaicin bakin ciki da yafaru, sai ga kawu yaturo wani da babbar jaka acike da kudi yashigo zuwa wannan ofishin jami'an tsaro, kamin Abdullahi yayi bayaninsa, sai wannan wanda yana dauke da wannan kudin sai yace DPO ina songaninka anbani sako in baka, sai DPO yatashi yazo gurin wannan bawan allah, Abdullahi yana zaune yana kallon ikon allah mai zai faru, sai yaga wannan wanda yana dauke da kudin yana was DPO magana akunne amma shi Abdullahi bai San me yake gaya masa ba, amma jikinsa yabashi akan kar DPO ya saurareshe.

Sai Abdullahi dayaga DPO yakarba wannan jakar wanda ke dauke da kudi, sai hankalinsa yatashi yarasa abinda zai ce tunda gashi anrufe baking DPO da kudi.

Sai Abdullahi yace wannan Kawu wane irin mutum ne haka, kuma wane irin azzalimine wanda bai da imani a zuciyarsa, Abdullahi yana wannan magana yana zubar da hawaye a idannunsa. Sai Abdullahi Yakima gida dan yayi tunani wace shawara ne zai yi ko wane mataki ne zai dauka game da wannan bawan allah Kawu.

Bayan Abdullahi da yaje gida yace "Wallahi Kawu yajawowa kansa kurar da bazata lafaba, kuma shi da kwanciyar hankali a rayuwarsa yakare har idan bai mayar masa da matarsa Safina ba inji Abdullahi.

Shi Abdullahi yayi shuru da wannan maganar, amma daga bisani sai yayi shawara zai kai magana zuwa kotu dan ta karbo masata matarsa daga hannun wannan azalimin wato Kawu, shi a matsayi kanin ma haifinsane.

Abdullahi yatashi yamiki zarap kamar ansokeshi da allura yagoge idanuwansa ya wanke fuskarsa yarufe ko ina a gidan sai yanufi gidan Kawu, yana kokarin zai shiga sai maigadi yahanashi shiga, yace wannan maigadi nine fa Abdullahi, sai maigadai yace masa angayamasa akan har idan ka karazuwa wannan gidan kar in barka kashiga, sai maigadi yana kofar yarufe kuma yasa kwado yakunle kofar.

Sai abin yabawa Abdullahi mamaki akan wai har yaune zanshiga gidan Kawu za a cemasa ba zai shigababa har mai gadi yana yimasa wulakanci wai har idan shine yazo kar a budemasa kofa, Abdullahi yayi tagumi yatsaya yana ta kallon kofar yarasa abinda yake yimasa dadi ga bakincikin an dauke masa matarsa Safina.

Sai abin ya bawa shi Abdullahi mamaki akan tayaya za a hanashi shigan wannan gidan na Kawunsa, sai yaje tabaya a kawai karamar kofa maigadi yamanta bai kunlle ba, sai Abdullahi ya tura kofar sai ga Kawu yana zaune akan kujera da yakkalla Abdullahi yashigo ta baya, sai yagara murmushi da fuskanrsa da yaga Abdullahi.

Sai Kawu yace wa Abdullahi "Ina fatan kazo da Takardar Tsakin Safina inji Kawu".

Sai Abdullahi yace wannan Kawu lalle kai kacika babban azzalumi, kuma kai babban munafuki ne wanda yake kauda da raba masoya, mai kauda sunnan manzon allah inji shi Abdullahi was Kawu......Kawu yacewa Abdullahi " wai meyasa baka da hankaline zaka dawo har zuwa gidana kana gayamin magana, sai Abdullahi yace, meyasa zaka zo kasace min matata ko dan kasan mahaifina baya duniya ne shiyasa zakayimini haka, kuma dan Kaine ma haifina za saka kazama alwalina za ka aikata mini haka.

Abdullahi yace wa Kawunsa kafitomin da matata ko inkaika zuwa koto akan ka dauke mini matata ka boyeta kuma dole ne zaka fitomin da ita inji Abdullahi.

Sai Kawu yazubawa Abdullahi idanu yana ta kallonsa har yagama fada abinda yakeso a zuciyarsa, sai Kawu yace Abdullahi karkayi taurinkai dan taurin kai shiyakan sa jaki ya shaduka, shawaran da zan baka, ka amsa kudin da zanbaka kokuma kayi asara guda biyu, karasa matarka da kuma kudin da zanbaka, dan tunda nagan wannan matarka Safina, sonta yashiga mini zuciya har nafara sonta kar zan iya rasa raina game da har idan na rasa Safina, shiyasa kawai nayi shawara in saceta kawai tun kamin abin yayi mini zafi, kuma ko kaki, ko kaso,sai Safina tazama nawa.

Abdullahi zan baka shawara akan kar ka bata lokacinka akan wai kana so ka samu Safina, bari ingaya maka kaji, Safina tariga ta iso Kasar Amurka, nayi shawara ne dan a kai mini ita zuwa can zuwa wani lokaci ko kuma ta dauki wani shekaru nasan dole ne zaka hakura da ita kabata takar dan ta.

Zancen wai zaka kai kara zuwa wajen huku, to ka kai ni nasa kai baza ka ci nasara ba, har idan kanagani zaka ci nasara to zaka iya zuwa ko i'na har idan kana gani zaka yi nasara. Ina mai baka shawara dan lar ka abata lokacinka ka amsa kudin da nace zan baka sai kaje kayi aure, nasan zaka samu wanda har tafi Safina amma kai zun zurutun kana da taurin kai zai sa ka rasa duniya, ina mai kara ba aka shawara ka amsa wannan kudin kayi tafiyarka.

Sai Kawu yajuye baya ya shiga gidansa, sai mai gadi yace ma Abdullahi dan allah kayi gaba zamu bude kofa ga masu amfani dan allah ka bada hanya sai mai gadi yayi wa Abdullahi Gwallo yashiga gida kayanshi. Wannan shine karshen bayani, assalamu alaikum.

UWAR MATATA WAI DOLE SAI NAYI AMFANI DA ITA.

Da farko ina daukar wannan Tsangayar taka tamkar wasa. Daga bisa na soma tsintar darusa masu amfani a ciki. Can kuma sai na dawo na natsu ma zama cikenken dalibin wannan Tsangayar. Har ya zamto idan ba kayi postin ba bana jin dadi. Al'amari na da matata ne nake so na bada labari saboda samari wadanda basu yi aure ba su dauke darasi daga ciki.

Mun hadu da matata ne a wajen wani fatin bukin kanwar abokina shekaru 8 da suka wuce. Na kamu da soyayyar ta matuka wanda hakan ya rufe mini Idanuwa har bana ganin laifin ta kuma bana so naji an ambata. Kai ko laifin wani na kusa da ita aka ambata sai raina ya baci. bane kuma saboda binciken da aka yi kamin auren mu, sai irin mugayen halayenta da ni na kasa ankara dasu. Kuma ko da an ankara dani bana kula.

Bayan mun haifi dan mu na farko ne a lokacin na soma fahimtar kuskuren dana yi na kin bin shawarar magabata. Sai dai ban iya yiwa kowa magana akan alamun rashin darajar da neke gani a tattare da matata ba. Allah Ya rufa mini asiri ina samu daidai gwargwado. Amma babu wani na kusa dani da ya isa ya moreni muddin tana sane. Babu wani dan uwana da zai zo gidana ta bashi ruwan sha ma bare ace ta bashi abinci. Kai hatta uwata da ake kai mata girki daga gidana sai tayi girkin data san mahaigiyarta bata iya ci. Babu wanda ya iya fadamini wannan matsalar sai har ni na gano da kaina.

Nayi kokarin nusar da ita abun ya faskara. Babu yadda za a jiye kudi a dakina na samesu yadda na ajiye su.Idan nayi magana sai ta manna mini hauka tace ai haka nan na kawo kudin. Da abun ya isheni sai na yanke shawarar karo wata matan. A wannan lokacin mun samu haihuwa karo na biyu. Kuma a wannan lokacin ne kuma na gano irin babban kuskuren da nayi na auro wannan yarinyar. Asiri iri iri babu wanda ba a mini. Ina kwance ina barci zan ji ana wanke mini fuska da rubutu. Hayaƙi agidana babu wanda ba ayi har na cikin ban dakin. Duk wani abu da zan ci ki zan sha to tabbas akwai asiri a ciki.

Duk kokarin ta shine kada na yi wani auren. Haka kuma burin ta na talauce na zauna bani da komai kuma bana yin komai. Ida dai mahaifiyar matata tsohuwar kilaki ce har wannan lokacin danake wannan rubutun bata da aure bugaduniyar ta kawai take yi.

Ba labari ba a gabana idan tazo gidana buga taba sigarin ta take yi kawai a gaban yar ta da jikokin ta. Wadanda suka fini sanin ta sun tabbatar da cewa tana shan wiwi haka giya ma bata dai na sha ba.

Zancen bin bokaye kuwa kusan duk dangin su Sana'ar tsubbu suke yi. Don haka ne ta daura wannan yarta akan bin bokaye. Ta cusa mata mugayen akidu na son a nakasa ni da kuma yunkurin hana ni aure.

Sau uku uwar matata tana nema nayi zira da ita ina zullewa kuma na kasa bawa kowa wannan labarin. Anakun cewa tayi idan har na amince nayi zina da ita ni da talauci har abada. Kuma arziki na zai bunƙasa. Nacemata yanzu ma na gode Allah.

Na shirya tsaf ana shirin yin bukina karshen wannan shekarar. Har na samu wajen da zan ajiye matar.

Wannan yasa zafin kishin ta da bakin halin ta na gado ya sake kamari. Masifan yau da ban na gobe daban. Wannan makon ya kama mako na uku kenan da ina tashi daga barci sai na ga an kwashe kayan dakina kafkamar an share. Duk wani kayan kudi kama daga talabijjn, su laptop da sauran su har kujerun dakin ankwashi. Ma'ajiyar kudin shi ma an dauke shi cak. 

Dana tambaye ta sai kawai tace barayi ne suka shigoamma basu dauki komai nata ba sai nawa. Kwanaki biyu da faruwar al'amarin sai na fahimci itace ta daukikayan. Saboda an dawo mini da wasu kayan nawa amma Ma'ajiyar kudina wanda akwai kusan naira miliyan 5 a cikin da nake shirin kaisu banki ba a dawo da shi ba. A yammacin kwana na ukun ne ta kwashe yaranmu biyu ta kai gidan mu ta ajiye mini su. Ta wuce da karamin Ɗan dake hannunta wanda har wannan lokacin ban san inda take ba kuma ta kashe dukkannin wayoyinta guda biyu. Dana tambayi mahaigiyarta amsa databani shine. "Sai ka nemo ta ni kuma na nuna maka inda take". 

Daga wannan lokacin ban sake neman ta bahar wannan lokacin. Sai dai yanzu ina neman shawaran matakin da ya kamata na dauka akan wannan matata tawa. Don Allah masu karatu ku bani shawara. Kuma ku duba da kyau akwai darasi a cikin wannan labarin nawa.

contact-form

Labels: