Monday, December 6, 2021

Tsaran Boye (30)




SARAN BOYE


Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da dady ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam. Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.💟

Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi. Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda kike so,. Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama Ubangiji da neman taimakonsa a kowane daƙiƙa.














Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin. "Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata guri".Baki ta tura gaba tana ɓata fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wallahi Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zancen.💚

Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Ita ɗin sa'arki ce. "Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba ALLAH". "Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko".💥

Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya. Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi faɗa. Manshanun ta ɗauka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki ciki. Bata damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata harara.
















Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah,". Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu hannunta ɗauke da Al-qur'ani. "A'a Aymah ce a wajen namu". Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ɗan damuwa tace, "Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz". Kafin ta ƙarasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko. "Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani. Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki rama mata ne?”.👻

“Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ɗakinta kinji ko". Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wallahi, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan.

















Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa, dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata. Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH". "Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn ta faɗa a harzuƙe.💅

"ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam. Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki,. "Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan".💘

Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki,. "Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza". Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa. Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah".💫

Eh wallhi Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wallahi bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk yan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu.


















Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama. "Kubrah". Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a palow. Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci. "Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa".Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa. 'Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.💢

Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa". To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa"."Wallahi Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce". Kai!, Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wallahi sainayi ƙololuwar ɓatama mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ƙasa Nu'aymah ce kuma ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na faɗa miki”. Ta ƙare maganar da matuƙar zafin rai tana sake yima Kubrah gargaɗi da hannu.💓

Sai kuma ta juya ga Nu'aymah dake sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Nu'aymah jeki wanke fuskarki kinji kuma kar naji wannan maganar a wani waje, kiyi haƙuri".Kai Nu'aymah ta jinjinama Addah, babu musu ta shiga toilet ɗin dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga ALLAH hankalinta a tashe yake matuƙa da kalaman Kubrah.

















Koda ta koma sashensu ɗakinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu'aymah yarinyace da bata da tsoro sam. Amma yanda tai matuƙar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi ALLAH wadai da ita, ƙilama baba Malam da Ummi sun tsine mata albarka.Sake rushewa tai da kuka kamar zata shiɗe wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta shiga share hawayen, harta nufi ƙofar fita sai kuma tai saurin dawowa. Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli sannan ta fita.💨

Zaune ta iske baba malam da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, "Lafiya kuwa? Naga idonki kamar wadda tai kuka? Mamana!".Kafin tayi magana Umm dake hararta tace, "Saboda namata faɗa akan rashin kunyar data iya". (dan ita tazata faɗan datai matane ya sakata fushi har yanzun).👥

Baba malam baice komaiba sai maida kansa da yaga tv kawai. Fuska a ɗaure Umm ta nuna mata trayn dake a kan centre table. “Ki ɗauka ki kaima baƙo a pallow baba. Kai kawai ta jinjina mata ta koma ɗakinta ta ɗakko hijjab. Batare datai maganaba ta ɗauka tiren ta fice. Sai da ta fice gaba ɗaya sannan baba malam ya ɗauke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm da itama take kallon nata. Addu'a ya kamata ki cigaba da mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu'aymah yariyace ƙarama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata buƙatar yawan takura. Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ƙuruciyar.















Amma Malam ka tunafa ya mace ce ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ƙaddara daba yanzu tana ɗakin miji ba. Wallahi sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba nikam. Murmushi baba malam yayi yana miƙewa, “To ayi haƙuri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya huci zuciyarki.

Yanda yay maganarne ya saka Umm yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nishaɗi sosai kam, musamman data san yafi kowa ƙin jinin tsiwar ɗiyar tasu. Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene.

A gabansa ta dangwarar da trayn, murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, "Ina yini".

Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani sabon takaicin ya sake lulluɓe ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata faɗa harda duka akan tsiwa, sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene baƙon nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin yayunta. Haɗiye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon. Yoohan da tun shigowarta idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ƙaramar jakkar dake gefensa da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yay saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare.















Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen ƙamshin turarensa na nan manne da shi. Shaƙa ɗaya Nu'aymah tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici. Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa ya rufe mata bakin, yau ma, tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka. "Oh my God! Just relax. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.

Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yay azamar riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa. "Wayyo Abbana ɗan iska ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba. Wa'iyazubillah!! Iskancin naku da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?” Kubrah data shigo falon tamkar an jehota ta faɗa hannu bisa kai tana mai waro idanu waje.  Tashin hankali, tsabar ruɗewa Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa. Saurin sakinta yay yana faɗin “Ouch!!!” dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ɗoura hannun nasa bisa cikin ya riƙe yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.

Nu'aymah dake ja da baya tana hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, “Ɗan iska kawai, ALLAH ya isa ban yafeba. Wallahi daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ƙosai, na tsane ka wallahi. "kefa! Ƴar iska bar wani pretending kinji!,. Kubrah ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin falon sosai.

















Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai fita tace, “Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wallahi tallahi kinji na rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa. "K dalla saurara mani! Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH, inhar kika sake faɗin tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke ciki".Ƙasa Nu'aymah ta durƙushe tana ƙara sakin kuka maiban tausayi. 

Yayin da Yoohan da sam bai fahimci Kubrah ke faɗa ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu. Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Muƙut ta haɗiye maganar tata ƙirjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin suɓutar baki ta firta ‘Tsarki ya tabbata ga ALLAH". Sake ɗaure fuska Yoohan yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin wanda Kubrah ke masa na ƙurulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take faɗaba ne ɗazun, sai dai ya fahimci ba magana mai daɗi takema Nu'aymah ba. Dan haka ya watsa mata wani mugun kallon da manyan idanunsa yana miƙewa.


















Ganin ya nufita ya sata saurin zabura tai baya, sai dai kuma a mamakinta yama ɗauke kai daga gareta gaba ɗaya, raɓata ya nufi Nu'aymah dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin datasan a yau babu makawa sai Kubrah ta tona mata asiri. Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, "Hello!". A razane Nu'aymah da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Ta waro idanu waje sosai da saurin duban inda Kubrah ke tsaye tana kallonsu kamar ta samu television. Kamo hannunta yay, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin."

Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. "Shi!"ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.

Ruf,. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yay mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, "Silly girl".Baya taja jikinta, dai-dai da sakar mata hannu da yayi ya miƙe shima. Batare da ya kalli ko inda Kubrah take ba ya ɗauka jikkar da Nu'aymah tai tuntuɓe ya fice abinsa. Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. Dan duk da baiji mi Kubrah ta faɗaba ya fahimci ba abune mai daɗi ba musamman yanda Aymah take kuka, Yana ficewa Kubrah ta bi bayansa da sauri.

"Aunty Kubrah!" Nu'aymah ta faɗa da hanzari tana miƙewar itama. Amma sam Kubrah batako jiyoba balle ta nuna zata saurareta ta ficewarta.

اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.

Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.

Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.

Nu'aymah dake jin wata hajijiya na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta da sauri. Da ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya?. 


contact-form

Labels: ,

Monday, November 22, 2021

Ummin Kaduna Sako Ga Ma'aurata Kawai? Banda Gauro


Ummin Yar Kaduna...


Ummin Yar Kaduna

Bakin ummi d'auke da sallama tashiga cikin had'ad'en parlour na gidan inda ta iske hajiya hajara na zaune tana faman yiwa muwaddat fada kamar zata bugeta, sallamar ummi ce ta katse fad'an da take mata ,atare suka amsa mata sallamar sannan muwaddat ta mike da cikin sanyin jiki ta rungume ummi tana zuba shagwaba tace "ummi nah oyoyo sannu da zuwa ,nayi kewarki ta fad'i haka muryarta a raunane tmkr zatayi kuka duk da tana cikin murnar ganin ummi amman kana ganinta kasan ranta a 'bace yake,. lokaci daya ummi ta fahimci tana tattare da matsananciyar damuwa, amman hakan bai hanata jin wani irin sanyin dadi aranta ba, duk duniya babu halitar da take so kamar muwaddat "rayuwarta ce muwaddat, domin kuwa ta sameta kafin tasamu duk wani farinciki daya danganci jin dadin rayuwa a bangaren ya'ya, zareta tayi ajikinta ta kamo hannayenta a rud'e suka isa kan kujera ta zaunar daita kana ta zauna tana ajiye jakar hannunta ,sannan ta tsura mata ido tana dubanta fuskarta d'auke da tambayoyi "ki dai mata fad'a ba tsura mata tsumammun idanunki zakiyi ba, koda yake ai duk kece kika lalatata , in ji cewar hajiya hajara. "haba aunty hajara yaya kuke son nayi da yarinyar.













Ke da yaya kun sata gaba da damuwa ,nima shine kuke son na damu rayuwarta, "shiyasa bata kaunar zuwa gidan nan nake matsa mata zuwa hutu. "daman wa yake bukatar ganinta, kema kinga damar zuwan nata ne, data zo da karta zo duk daya ne agurina ,matukar dai yarona auwal zai zo garemu meye idan ita bata zo ba, muwaddat na gama jin abinda mahaifiyarta ta fad'a ta rushe da kuka. Ummi ta dubi hajiya  hajara ranta a matukar 'bace tace "gaskaya aunty hajara bason irin abinda kuke yiwa yarinyar nan, karatu ne dai dole tayi domin inganta rayuwarta, amman duk wani takura bashi bane maslaha ba , karku damu tunda abun yazo da Kora da hali yanzu zamu yi tafiyarmu,mu bar muku gidanku " ko ba shikenan ba, "ku fi jirgin sama tafiya ,Idan ma kun tashi tafiyar kar ku tsaya a kasar nan, ku bar kasar gabadaya nan zan San ranku ya 'baci ,ta juya fuuuuu ta shige cikinn d'akinta.❤

Shiru ya biyo bayan tafiyar hajiya hajara ,kafin daga baya ummi ta kamo hannunta duka cikin nata ta kira sunanta ahankali "muwaddat meke damunki akan rashin son karatu haka? Kukanta ya tsananta har da shesheka ,ta goge hawaye wasu na sake gangarowa ,ummi ta runtse idanunta saboda jin zafin yadda take zubda hawaye akan abinda itace zata ci gajiyarsa a karshe, ganin kukan nata yaki tsayawa domin hawayenta har saman hannunta take jin digarsa, ta bud'e idanunta da kyar tana sake dubanta "kinga ba kuka na tambayeki ba"me yasa baki son zurfafa karatunki simple as that,. Muryata cike da kuka tace "babu komai ,ni dai haka kawai na tsinci kaina da rashin son karatu, ta k'arasa mgnr tana sake rushewa da wani matsanancin kuka. "ki tsani karatu muwaddat ? ummi ta maimaita tana kallonta, muwaddat ta d'aga mata kai ala'mun" eh"tana sake rushewa da kuka tamkar wacce aka aikowa sakon mutuwa.😬

"is okay banason jin kukaki yana taba min zuciya,. "to me zakiyi idan bakiyi karatu ba arayuwarki,. "ko kuma aure kike so? wata irin matsananciyar kunya ce ta kamata , tabbas idan da zasu barta ,ita kan aure take so akan karatu,tafi son tayi aure fiyye da komai ,but ba zata iya furtawa umminta haka ba,bazata iya kallonta idanunta ta fad'a mata abinda ke cin ranta ba ,idan ma ta furta ,wa zata aura a halin yanzu? ita da bata kula kowa.















"kinyi shiru kina tunani idan aure kike so ki bud'e baki ki sanarwa umminki? "bazan hanaki yin aure ba, amman kisani auren wannan zamanin yana bukatar jigo acikinsa ,domin baki san wand zaki aura ba tukunna , kiyi k'ok'ari ki zurfafa karatunki so that idan ma auren zakiyi sai kiyi, kina cikin karatunki"amman zance aure yanzu bai ma taso ba ,Sam Sam idan ma shine aranki gara tun wuri ki cire kiyi abinda zai fisheki da rayuwarki,. Ganin muwaddat tayi shiru taki cewa komai har na wasu yan mintuna ,yasa ummi ta sake jeho mata tambaya "ko akwai wanda kike so ne bamu sani ba,. muwaddat tayi saurin girgiza mata kai alamar "a'a" "to meyasa ba zaki saki ranki kiyi karatunki ba, "duba yan mate dinki , kowace yanzu tana mataki na uku a jami'a amman ke sam kin kasa maida hankalinki, idan fa ba zaki maida hankalinki akan karatunki ba ,wallahi zan zare hannuna acikin lamarinki, "haba yarinya sai fama ake dake akan abu daya meye illar yin karatu baya ga martabarki da zai k'ara a idanun duniya ,karatu shine komai duk da shima auren yana da muhallinsa, but at least ki tsaya kiyi facing din karatunki "kalleni a yanzu babu abinda yasa na taka matsayin da nake sai karatu, fad'a ummi tashiga yi mata sosai ta inda take shiga ba nan take fita ba.💃

Muwaddat ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kuka "ummi kiyi hakuri na tuba ,dan Allah karki cire hannunki acikin lamarina, ni dai karatun ne kawai banaso, amman daga yau nayi miki alkwarin zanyi, zan tursasa zuciyata, zan saka lamarin karatu acikin raina, "idan ki kayi min haka zan ji dadi sosai , domin shine burin halinki ,gabad'ayanmu burinmu bai wuce muga mubaki tallafi na ingantaccen ilimi arayuwarki ba , dan baki da wani gata da yanci daya wuce karatu. "matukar kina son mu shirya dake ki saki ranki ki saka soyayyar karatu aranki, "Insha allahu ummi zanyi karatu har sai kince ya isa tunda shine farincikinki ,"ok tashi kije ki soma had'a kayanki nan da awa zamu bi jirgin karfe biyu , jikinta a matukar sanyaye ta miki tasoma daga zararan kyawawan yatsun kafafunta ta nufi hanyar d'akinta har tashige idanun ummi na kanta tana sake nazarinta, domin gano takamaiman abinda take so ,da yasa ta tsani karatu, bayan ga million's of people out there suna neman wanda zai tallafawa rayuwarsu su yi.


















Mikewa ummi tayi ta shiga d'akin hajiya hajara tana zolayarta "gaskiya aunty banason irin abinda kikewa yarinyata, ina dalili wannan takura.? Sai naji saukar ko duka tukunna zan San baki son abinda ake mata,kuma ni ina ruwana aciki, "daman yayanki nake tayawa yakin shiyasa kikaji bakina "Allah ko, "to kijira wannan karon ba duka zanyi miki ba aure zan yiwa yayana in ga kashe bakin tsiwa. "dariya ce ta subucewa hjy hajara aiko tashiga yi "daman nasan duk matakin bai wuce haka ba ,Amman dai kin sani ba tun yau ba ,ni hajara bani tsoron kishiya, a da can ma ban ji tsoron zuwanta ba ,sai yanzu Dana San kota zo babu abinda zata tarar na gama tsotse komai.👩

Suka sa driya gabadayansu suna tafawa ,kana suka shiga halin nasu da suka saba na shakiyanci a junansu ,sannan daga baya suka shiga wata hirar. Ita kuwa muwaddat tana shiga d'akinta,a madadin ta had'a kayanta kmr yadda ummi ta bata umarni ,sai ta fad'a kan makeken gadon ta kwanta ruf da ciki ta lalimo pillow ta manne ajikirjita tana jin wani iri agabadaya ilahirin jikinta, hannunta daya tasa ta lalu'bo wayarta dake yashe agefe ,ta kunna tana duba screen din wayar miss Call ,tagani rututu akalla zasu kai guda ashirin, kuma duk na M.A ne.💬

Jikinta na rawa tashiga nema layinsa kira daya biyu ya ya d'auka yana sauke naunayen ajiyar zuciya had'e da buso mata iskar bakinsa Wanda hakan yasa gabadaya Gabobin jikinta mutuwa ,sai dai lokaci daya hankalinta yayi mugu mugun tashi saboda shirun da yayi yaki magana,tsawon minti goma suna haka batare da suncewa juna qala ba ,illa numfashinsa dayake aikin buso mata ,suna kashe mata sansar jiki ,take kirjinta yashiga wani irin mahaukacin bugu da karfi gaske ,sakamakon rashin jin sautin muryarsa. Jarumta ta Nemo ta sanyawa jikinta ,kana ta bud'e bakinta da kyar ta kira sunansa "auwal dan Allah kayi min magana shirunka na d'aga min hankali" "a wani dalili hakan zai d'aga miki hankali, tun dani ba kowa bane agurinki , at least mis call nawa nayi miki?" haba muwaddat kinsa yadda zuciyata taji alokacin kuwa? "kayi hakuri ba laifina bane ni kaina bana cikin natsuwata, duk abinda nayi ina yinsa ne kawai amman hankalina na gurinka ... takarasa mgnr cikin rawar muryar kmr zatayi kuka, kana ta kashe kiran.



Ta rike wayar a hannunta tana jujjuyawa tana tunanin wasu abubuwa dake faruwa atsakaninta da M. A,. hawaye ne yashiga gangarowa daga cikin kwarnin idanunta "tana mugun son M. A amman tasan soyayyar tasu babu abinda zai haifar ,M. A kaninta,sannan ba lallai iyayensu su yarda da hakan ba, Dan haka tayiwa kanta alkwarin zata tsaya tayi karatunta tunda shine burin iyayenta ,ko bama haka ba ita kanta zata fi son farincikinsu Akan nata. 💟

Tun daga wannan lokacin muwaddat ta maida hanakalinta akan karatunta hatta M. A ta tattarashi ta ajiye a gefe daya, ko ta hau online bata shiga contact dinsa sai dai tayi abinda zatayi ta sauka,idan ma ya turo mata sako bata wani bashi full time dinta ,sama sama zata bashi amsa , shima a bangarensa yana tsane da sabon salon datazo masa dashi Amman ya shareta saboda shima yana jina zafinta a game da katse masa wayar da tayi ,amman ganin idan suka ta tafi a haka shi zai fi cutuwa ,yasa yau yayi shawarar kawo karshen abun ,ya turo mata da sakon voice note ta WhatsApp. " ni wallahi muwaddat ina da matsala guda daya da ke, ni bansan abinda ya faru ba kika juya min baya ," ni me nayi miki ne? "da bakya son kiyi magana dani ni ban San laifin da nayi miki ba, idan wani abu, ni keda alhakin yin fushi dake ,"ni dalibinki ne muwaddat ni yayanki ne ,ni Dan gatanki ne Dan Allah muwaddat, Dan Allah ki daina min haka kinji ki bari mu cigaba da abubuwanmu kamar yadda mu keyi tun farko ,rabon da muyi hira dake mai dadi tun randa da zaki bar ilori ,yanzu sam na lura baki da lokacina., haba muwaddat kema ki duba kigani mana ,ina wata kasa ina bukatar kulawrlarki, ya k'arasa yana Jan manager da sakin numfashi sannan ya tura mata.👰

Cikin minti biyu ta turo masa da sako "kace dai muryarta kake son ji? "Alamar dariy ya turo mata sannan ya rubuto mata "eh. "okay ina zuwa,. Cikin sauri ya rubuta mata "no ki tsaya please ni so nake muyi hira "Okay Dan kanina gani kusa anything for, wace irin hira kake son muyi ?yana jin ta fad'i hakan ya ki rata ta d'auka had'e da yin sallama, batare daya amsa ba yace "Idan fa kina cewa Dan kaninan naki za'a d'auka fa wani yaro ne qarami ,gwada dai ki dinga cewa yayanki kawai kiyi shiru kinga mutane bazasu d'auka Dan kani bane ,Dan ni ba Dan kankani bane wallahi,. "gaskiya kwanakin kin wahalar da zuciyata, ki dan mun magana naji muryarki ko zata dawo min da natsuwata, "ko ka yarda ko karka yarda ni auntynka ce shekara uku zuwa hud'u ba wasa ba, murmushi yayi yace "matukar na kiraki da wannan kalmar na gama rusa cikar burina dana girma dashi muwaddat, sannan karki manta an samu cikina tun kafin asan za'a dasa naki kwan, Allah kad'ai yasan abinda yake nufi, daya kwantar da cikina ya tada rayuwarki, "dana rigaki zuwa duniya kinsa shekaru nawa zan baki.















Ta yatsina fuska tana ta'be baki kamar tana gabansa tace "kana son girma dayawa auwal, ina jin da'ace ka girmeni da bansan yadda zakayi ba "no no wannan ba zance son girma bane, koda kin girmeni, zan iya girmanki ta wani bangaren ,saboda ni namiji ne dan haka ki daina tunanin ni kaninki har abada ni yayanki ne saboda na girmeki aciki, "ni kuma ba girmeka a haihuwa ba tana gama fadar haka ta katse kiran daman shirin kwanciya take, ta kwanta lamo tana jin jikinta wani irin mika tashigayi wani irin mahaukacin feelings na taso mata ahankali dai har bacci barawo yayi nasarar daukata.💅

Sannu a hankali M.A yake janta ajiki batare da ta fahimci komai attare dashi ba, wata irin sabuwar shakuwa ce mai karfi ta sake shiga tsakananin muwaddat da bunayya, komai ya gadamar fada mata fad'a yake batare da jin kunya ko shakkanta ba, sai ma itace take nannakewa a wasu lokunta, saboda matsayin dayake dashi agurin uwa uba ita magana ba damunta tayi ba. kamar kowani daren duniya daya saba kiranta a waya hakan ce takasance yanzu, batare da 'bata lokaci ba ,ta d'auka a natse muryarta ta doki dodon kunneshi " assalamu alaikum kanina. "ya gida da karatu 'd'an kanina? "D'an mara kunyar kanina ta k'arasa maganar tana hamma "na soma gyangyad'i bacci nakeji fa"ta k'arasa maganar tana kashe masa murya take joystick dinsa ta Mike kyam, yayi saurin d'aura hannunsa d'aya akan joystick dinsa ya dafeta,yana murmushi kmr tana gabansa ,muryarsa a tsarke ta fito yace "maganarki ta saukar min da kasala gabadaya , sai naji kamar ina ma najini acikin jikinki ina romancing dinki please muwaddat karki hanani jikinki duk ranar Dana dawo ,idan ma da hali ki barni nayi yadda nake so dake, "Kamar ya kenan na barka kayi yadda kake so dani karka manta ni yayarkace "and so what idan ke yayata ce, wallahi matukar zaki barni zan tabbatar miki da zan ci,. ya katse maganar yana furzar da numfashi.😛

Jin yayi shiru yasa ta janyota numfashi ta fesar kana tayi kasa sosai da muryarta tace "bunayya ka daina tunanin zaka iya cina ,ai ka fahimta, kwa'kwaluwarka ta daina hasko maka zaka iya cina ,ko kuma zan bari ka cini ,saboda bazan ta'ba cuwuwa ba agurinka, tana magana dariya ta su'buce mata " bazaka ta'ba kusantata ba, namiji da zai iya kusantata daban yake bawai rainaka nayi ba , ta cigaba magana "gaskiya Wanda zai iya sarrafani bakaramin gwarzo bane, murmushi ya dinga yi yana jin ina ma suna tare daya nuna mata shi din ya zarta gwarzo "muwaddat, "na'am, "ina son nono kinji baby nah ya k'arasa manager muryarsa tamakar mai shirin yin kuka, tayi shiru ta kasa ce masa komai, ya sake kiran sunanta " Ayshatul muwaddat.💭

Wani irin taji ajikinta saboda yadda ya kira sunanta gobadiya tsigar jikinta ya Mike, da kyar tace "na'am bunayya, "ina son nono please, "Na had'aki da girman Allah karkice a'a ni dai kawai ki turo min su ina son gansu ,nayi matukar kewarsu, wallahi idan bangansu ba komai zai iya faruwa dani, muwaddat ina son brest dinki ,suna mugun rud'ar dani a duk lokacin Dana kallesu, yanzu haka bakiji yadda nakeji ba ,komai nawa ya sauya joystick dina ta mike taki kwanciya nasan ganin brest dinki kawai zai sa ta kwanta kinji muwaddat dina duk wannan maganar da M.A ke yi hannunsa na dafe da joystick dinsa da ta sake mikewa kamar ana hurata, muwaddat tayi shiru taki ce masa komai domin lamarinsa nason fin karfinta duk yadda take da tsanani bukata M. Aya zarta fiyye da tunaninta.



Labels: ,

Monday, November 15, 2021

Karshe "Kashi Na (61 to 80)


Karshe Kashi (61 har zuwa 80)


💋KARSHE💋

Kashi (61 to 80)


"Nurayya tace yayana kasan Abinda kake fada Kuwa, Muhammad yajoyo yace nasani mana nurayya Kobazaki soni ba?? Nurayya tace yayana kafi karfina kyau daidaini marar iyaye nifa tsintaciyyace bansan kowaye iyayena, Kyau kaje Gidan marayu kasamo man daidai Dani Amma nibazan iya soyaya dakai ba. Tajuya tagudu tashige ciki tana kuka,

💋ABUJA💋

wata yarinyace bazata wuce 12 years ba tashigo daki dagudu mamy kinga Afnan ya Amshema chocolate wadda dady yayoman tsaraba, Amma wadda Ake Kira mamy batasan tana iyiba, Takurama wani photo na Hannu ta ido tana kuka, Yarinya takara matsawa kusada ita tace mamy sannan tadago fuskarta tafara tsiyayar Hawaye tace yesmeen yaushe kika shigo ne. Tace mamy inatayimiki magana bakiji kin kurama wannan pic din ido wacece ita tacikim photo "Mamy tagoge fuska tace yayarkuce Meenat wadda tabata shekaru 16 dasuka wuce tana yar shekara 2 tabata haryanzu babu labarinta, Kiyi Addua intana Raye Allah bayyanata kinjiko, Domin jikina yanabani meenat tana raye kuma takusa bayyana garemu, Toro kofar Akayi Da Amsa da Ameen Hibba,

can baya nakirata da "Saudat" mistake dafatan zaayi man Afuwa, Mamy tajoyo taga mijinta tane uban yayanta ya Amsa Mata da Ameen, Tace Alhaji inaji A jikina Meenat ta kusa bayyana gareni, domin Ina mafarkinta kwananan tanakuka Alhaji yace Allah yatabbatar mana da Alkairi to tace Ameen.

Abangaren nurayya kuma tana shiga ta iske babu kowa falon dagudu tashige Cikin dakinta, Tafada bisa Gado ta fashe da kuka tace wayyo zuciyata nasan kina son Yaya Muhammad Amma yafi karfinki, kinfara sonshi tunranar dawowarshi daga England, Amma yaya Muhammad ba Ajina bane, yana da iyenyenshi, Tafashe dakuka tace ya Allah kafiddaman yaya Muhammad Cikin raina, Kadda ciwon son yaya Muhammad yakamani kamar yadda Yakama saffeya Akan Dr Ahmed, Wasa wasa duk yadda Muhammad yaso su hadu da. Nurayya Abun yafaskara wayar dayabatama ta kasheta ta Aje, Abun yafara damun Muhammad yarasa yadda zayayi su hadu da nurayya, Yauma zaune yake yayi tagumi Kawai sai wata shawara tafado masa da sauri yatashi yashiga Cikin ya iske momy tare da ikram da lubna Suna Kallo yace ke ikram kiraman nurayya tagyaraman dakinna Momy batace komai jin wahala zaasa nurayya, Ikram tatashi tashiga dakin nurayya tafadamata sakon Muhammad Nurayya tatashi tafito Muhammad yanaganin tafiyarta yabi tabaya ya isketa.

Nurayya tana tura kyauren dakin wani kamshi yaziyarceta taga daki tsaf babu inda yayi kura Tajuya tacema ikram kodai ba gyaran daki yasaba, Kawai tayi kicibus da Muhammad dasauri takoma ciki Cikin tsoro, Muhammad yace kisameni A garden inbahaka Zan biyoki har dakin ki yajuya yatafi, Nurayya tabi bayanshi suka isa garden Muhammad yace " nurayya meyasa kike guduna, "Nurayya batace komai yace kisani fa babu Wadda yafi wajen Allah sai wadda yafi tsoronshi, Nurayya son tsakanida Allah nake miki har Cikin zuciyata, Amincewarki kawai nake bukata da dady yadaw nasanardashi nasamu Mata, Nan Muhammad yakashe nurayya da zafafan kalamai har ta Aminche tana sonshi.

💥BAYAN WATA BIYU💥


Soyaya tayi nisa tsakanin Muhammad da nurayya babu Kama Hannu yaro Amma haryanzu momy batasan Sunayiba. Yauma zaune suke garden inda suke haduwa suyi firar love dinsu, Muhammad yawaigo yakalli nurayya yace Amaryata, Ta sunna Kai Cikin kunya, Muhammad yace kidaina jin kunyata domin nakusa mallakarki yau dady zai dawo Zan fadamasa, Dadadre dady ne zaune da iyalensa Anata fira saiga, Dady yace wai Ina nurayya tunda tayiman sannu dazuwa bangataba, Lubna kiraman ita, Lubna Cikin kumbere kumbere tatashi takira nurayya, Dady yace nurayya lafiya tunda kikayiman sannu dazuwa banjikiba tace lafiya lau daddy yace Ina fatan babu matsala ko tace Eh, Muhammad ya shigo Cikin sallama, Nurayya tatashi zata tafi dady yace dawowar ki nurayya Ayi firar dake, Nurayya tadawo Cikin kunya tazauna, Muhammad yace dady nasamu matar Aure fa, Dady yace mai babban suna Inakasameta, "Muhammad yace nan Cikin gidan Wato nurayya Zumbur hajiya saratu ta mike wa kace..... "Itazatama uwar yayanka tsitatar magen wadda baasan Asalinta itace kake fatan tazama matarka? Dady yace ya isa saratu zauna, Momy Cikin fushi takoma tazauna tana huchi, Dady yajuyo wajen Muhammad yace Mai babban suna nurayya kakeso yace Eh dady, Kanemi yarda tane, "Eh dady ta Aminche Dady yace tashi kaje zamuyi magana, Muhammad yatashi yafita, Dady yajuyo wajen nurayya jeki kema daki Yakalli su lubna yace kuma kutashi kutafi, Dady yace. 

Saratu meyasa kike wannanan maganar gaban yarinyar nan Don basan kowaye maihaifinta shine kike Aibata Haba saratu kowaya taimaki wani Allah zai taimakeshifa Momy tayi shiru domin bataji wannan sai kada kafa take, Tace Alhaji bazan yarda ba ya Aure ta fa yarinyar dabaasan Asalinta ba wayasani ko shegiyace batada uba yake neman hada kanshi da ita, Dady Cikin fushi yatashi yabata wuri domin yaga batajin maganar dayakemata, Nurayya kuma tanashiga daki takara fashewa da kuka tace Allah kabayyana man iyayena insuna Raye, Adainayimani gori, Rashin. Asali, Tanawannan tunenen har bacci yadauketa tayi mafarkin wata mata tatafo gareta tana buda Hannu taho yata nadade ina kewarki A tare Dani, Nurayya taruga dagudu kingi kiris ta ida kaiwa ga matar nan kawai tafarka firgice tatashi, Tace Allah kabayyana man mahaifiyata idan tana Raye, Tayi Addu' takoma ta kwanta.

Washe Gari Anyi break lafiya lau dady yatafi office shida Muhammad, Momy tashigo dakin nurayya tace fito munafuka makira, Algunguma, nurayya tadiro daga kan Gado jin muryar momy ta iso Momy tashigo har inda nurayya tajawo ta keyy!! Har waje Tace uban mikakayi ma dana ya likemakine, "Tahau jibgarta kamar jaka nurayya tafara Ihu, Saiga lubna tafito itada Ikram, Lubna tana ganin Nurayya ce Ake bugu kawai koma daki tayi Ikram kuma gaban momy tazo tace momy don Allah kiyi hakuri ki kyaleta, Momy tasaketa tana numfashi tace, Muzuba nidake inhar kindage sai Muhammad wallahi kin gamu da wahala Kala Kala, Har sai Kince kin hakura, Kuma kitashi ga wanki can kiyiman, danawa Dana su Ikram, Banza tsintaciyar mage, Marar Asali Nurayya Cikin kuka tatashi ibe kayan wanki tanufi, waje Dady yadawo dadddre yatarasu baki daya yace Muhammad nabaka nurayya nanda wata daya insha Allah zaayi bikinku, Nurayya Cikin kuka tace nidai dady banasonshi, Yanemi wata,ya Aura, Dady yace ke nurayya banason maganar banza nariga nasa saidai kinuman iyakata, Nurayya tatashi tashige daki tana kuka, Momy tamike tace wallahi bazata sabu ba bindiga Aruwa muzuba mugani fuu tashige daki, Muhammad yanafita yakira wayar nurayya saidayayi Kira ukku bata dauka yana na Hudu tadauka.

Tayi shiru, Muhammad yace nurayya, Tayi shiru yace nurayya pls kiman magana, Cikin sheshekar kuka tace mezance yayana don Allah muhakura da juna tunda momy, bata so Yace kull nakarajin wannnan zance, Nurayya ruwa ko iska bazai rabani dakeba, Nan yakashe ta zafafan kalamai itama taji babu Abinda zai rabata da Muhammad itama, Nurayya tanashan wuya yanda Baku zato masu karatu wajen momy da lubna da dady da Muhammad sunfita Zasu Fara sata bauta, Su duketa Abinsu San ransu kuma momy tace tasake tasanar da dady tana shan wani duka wadda yafi wani, Wasa wasa yau bikin ki nurayya da Muhammad kingi sati daya duk wani Abun da uba zai ma diya dady yama nurayya.

💧ABUJA💧


Alhaji sadiq ne zaune da iyalensa falo yajuyo wajen Hibba matarshi yace mata Kishirya jibi zamu bikinki dan Alhaji Lawal mai Kula da company na Kaduna, Hibba tace Allah yakaimu lafiya wallahi Alhaji kanafadin kaduna gabana yafadi yace kiyi Addu'a to Dady ne zaune falo yana rarrraba invitation na biki Hajiya saratu sai kumbure take tabi duk yadda zata Hana wannan Auren yaki yiwuwa dady yace takara magana Bakin Auren ta, Shiyasa tayi shiru Amma badon ranta yasoba Dady yadago yakaleeta yace Gobe Yallabai zaizo bikin Muhammad, Kuma nan zasu sauka, Momy tace Allah shi kaimu, Washe Gari Nurayya ce cikin kitchen sai girki domin momy tace baki zasuyi kuma manya taki Abinchi marar dadi taji duka wallahi, Nurayya ta idar da girki tana jerawa bisa dinning, Taji karar mota Momy tafita dasauri tatarbo su Hajiya Hibba ce ta Iso Domin Alhaji yace tafara yo gaba Anjima zai tafo, Wani Aiki ya tsaidashi office Momy tataro Hajiya Hibba, Cikin murna, Itakuma nurayya tashiga ta hado juice, Daidai fitowar wata Hajiya Hibba suka shigo, Tas!! plate Hannu nurayya yafadi domin Gabanta yayi wata muguwar faduwa.

Tas!! Plate yafadi daga Hannu nurayya domin gabanta yayi wata muguwar faduwa gani fuskar Hajiya Hibba, Momy tace to marar Asali halin naki zaki nuna gaban mutane, Tsintatar mage, Hajiya kinga wadda Muhammad yalikemawa Zai Aura batada Asali kokadan, Alhaji daga tsintar ta yarakitimana ita, Har Muhammad yagani yalikemawa zai Aura, Hajiya Hibba tajoyo wajen Nurayya Kawai itama gabanta yawani yanke yafadi, Tace Meenat! Nurayya tace sunana nurayya ba Meenat ba, Hajiya Hibba tamatso kusa da nurayya tace yakikaji dakika ganin.

Nurayya tace naji wani sonki da Kaunarki dabantaba yima wata Arayuwata jinake Hajiya Hibba tajawo Hannu nurayya Suka zauna tace bani labarinki nurayya Nurayya tafara bata labarin yadda Baffa yabata, Taceyaceman ya tsinceni A katsina Hanyar zuwa kwado, Dasauri HajiyaHibba tamike tace wallahi Meenat ce yata Allah Nagode maka, yau kanunaman Meenat. 

Dasauri tabude jaka tazaro waya hello Alhaji yau Addu' a ta karbu naga Meenat gata kusadani Alhaji Sadeeq yace ganinan Bisa Hanya, Momy ko mutuwar tsaye tayi tarasa Abinda zatace ne, Itako hajiya Hibba tarike nurayya kam kamar zata gudu, Bayan Alhaji Sadeeq ya iso shida Alhaji Lawal suka shigo, Tare da Muhammad Hajiya Hibba tamike Alhaji kaga Meenat yau Allah yagwadamana Meenat Allah nagode maka yau ga meenat gabana, Alhaji Sadeeq yace Hibba samu wurin muzauna naji komai, Nan suka rankaya suka zauna Yacema nurayya tasake bada labarinta, Nurayya tabashi kamar yadda taba Hajiya Hibba Alhaji Sadeeq yace tabbas ki yar muce, Nurayya domin mu da maifiyarki Yan Asalin Garin katsina ne Unguwar Gafai Nida mahaifiyar ki makotane Muntaso muna son junan mu Har Allah yahada Auren mu.

Shekaramu daya Allah yabamu ke Mukasamu miki Meenat Ranar da Allah yayi zaki bace kuma Munje unguwar kwado nida maihafiyarki Gidan Abokina Munazaune muna fira harkika fita bamu Sani sai can maihafiyarki ta farga bakinan Aka fantsam nemanki Baagankiba Aka Kai cigiya Gidan radion ta television, Amma baadaceba, Maihafiyarki tashiga wani Hali, Na rashinki Ana haka Nasamu Aiki Abuja muka koma, Nan Allah yabudaman nagida company Kasar wajen danan Cikin Garin Kaduna Alhaji Lawal shine manager, Ashe da rabon zamu sake ganinki Alhaji Lawal Nagode Babu Abinda zance face, Nagode Nagode sosai Alhaji Lawal yace babu damuwa Dana kowane Ai Momy Kuwa da lubna Jiki yayi sanyi, Yau DARE DAYA Allah yahada nurayya da iyeyenta Kuma karkashin iyeyenta suke cin Abinchi, Nan Hajiya saratu tanemi yafiyar Nurayya Akan tayafemata,duk Abinda tayimata,Nurayya murmushi kawai tayi tace tayafemusu duk Abinda sukayi Mata itada lubna, Adaura Auren Muhammad da nurayya Anyi hidima Alhmdlh saiga hajiya saratu tana lalllaba nurayya, Ankai nurayya Gidan Muhammad, Masha Allah Gida yayi kyau Sunatasha love, Ga Nurayya yau gaban mahaifiyar ta da maihaifin ta suna nunamata soyayya kamar ita kadaice yarsu, Sundawo Kaduna kusada ita.

Bayan shekara daya Nurayya ce nahango takara kyau sosai, takarazama babbbar mace, tana shayar da diyarta kairat, Wadda ta Haifa, Can Muhammad yashigo. Shima yakara kyau da girma, Khairat tanaganin maihaifinta tadinga bangala dariya, Dadyn nurayya sunje kauyen tsanyawa, inda Nurayya tatashi, yagina musu masallachi babba tare da rijiya, Nurayya suka shiga Gidan Gwaggo, Gwaggo takoma Abin tausayi kafa ta rufemata sai tsotsi take, gashi babu mai taimakonta, Nan tanemi yafiyar Nurayya.

Nurayya tadauki gwaggo takawota Asibiti Ayanke kafar, Ilu kuma yahaukace saboda shaye shaye, Anyi Auren ikram da lubna domin yanzu lubna tana ganin girman Nurayya sosai Hakama hajiya saratu Abu kadan tace Nurayya,domin yanzuma Dadyn nurayya ya mallakama Muhammad daya daga cinki company sa na kano, Bayan shekara biyu Sallama ce Akayi dagudu khairat taruga tataro dadyn ta ya sabeta, Suka shigo ciki Yazauna kusada Nurayya maman khairat fushin ne Ake Dani to don Allah Adaina taso kiji wata magana, Ya rugumenta Ajinkisa yace Taso mushiga ciki Asamarma khairat Kane, Ni kuma naga bazan iya bin su fa sai kawai ta tattara komatsai na na barsu don su soye abin su.

"Al Hamdullillah"

contact-form

Labels: ,

Wani Babban Labarine Ga Wasu Guda Biyu (Khalifa & Khalifa)



😍Khalifa & Khalifa😍


Masoyane Abin Abin Gwanin Ban sha'awa Da fari sun kasance Suna Matukar so da kaunar junan su tsawon Shekaru kusan (3) Suna Tare kwatsam watarana Sai Allah ya Jarabci khalifa saurayin Hafsat da Rashin lafiya Takai ta kawo Har Jarinsa Ya Kare na kasuwanci akan neman magani domin ko tashi baya iya yi sai an kwantar sai An tayar 'yan Uwansa wasu Har Sun Gaji Da Dawainiya Dashi Yarinyar nan Hafsat Amma Kullum Tana cigaba Da Rike Soyayyarsu ta kasa Rabuwa dashi tana iya bakin Kokarinta domin Bicike akan maganin rashin lafiyarshi kullum bata da Zance sai nashi ta Nace Dole Sai Shi 'yan Uwanta Suka fara tsangwamarta akan cewa ta fito da miji ta rabu dashi Tunda tana da manema ga 'yan uwanta Na jini Samari.💝

Amma Taki Kula kowa rannan kwatsam tana bibiyar Kafofin Sada Zumunta Sai taci karo da wani Bawan Allah Yana Mika Sakon godiya Ga wadanda Sukayi dawainiya dashi Har ya samu lafiya wanda shima Irin wannan Rashin Lafiyar ta taba faruwa dashi wanda ya bayyana Cewa A Indiya ya samu Maganin Cutar da Take damunshi Hafsat Batayi Kasa A guiwa Ba ta tutubi bawan Allannan ya bayyana mata yanda Za'ayi Saurayinta Insha Allahu Zai samu lafiya Kai tsaye batayi kasa a guiwa ba Taje ta samu Mahaifinta Ta Rokeshi Akan Tunda Suna Da Hali ya taimakawa Saurayinnan Nata A kaishi Indiya Shima Ko Zai samu sauki Haka Kuwa Akayi Mahaifinta Alhaji Naseer da yake yana Matukar son Abinda Take so.💕

Sai ya Amince Aka biyawa khalifa Saurayin nata Kudi Zuwa Wani Asibiti A Indiya bayan an kaishi Indiya Cikin Ikon Allah a cikin Watanni Shida zuwa bakwai Sai Allah ya Bashi Lafiya Ashe Lokacin Da yake Jinya kafin ya Karasa Samun Lafiya A Sallameshi Soyayya Ta shiga tsakaninshi da Wata daga cikin Masu Kula dashi wata Baiwar Allah Likata Nurse ce Safeenat Wacce Asalin Iyayenta 'yan Nigeria ne Amma Mazauna Indiya Ita Haifaffiyar Indiya ce Soyayya Tayi nisa A Tsakanin Khalifa da Safeenat.💗

Sai ya bayyana Mata gaskiyar cewa Shifa bashi Da komai a yanzu Amma yana Sonta taya Za'ayi Aure ya tabbata A Tsakaninsu? Safeenat Likitannan Tace Ba komai indai wannan ne zata bashi Kudi Masu Yawa Wadanda Zai ja Jari amma A kasar indiya take so su zauna Idan har ya Amince To? Sai Ya tabbatar mata cewa ya yarda ya Amince cewa Idan An sallameshi Zai dawo yayi sallama Da iyeyenshi tare da Sanar musu, Haka kuwa Akayi bayan an sallameshi Ta bashi Kudi masu yawa dazaiyi kasuwanci.💞

Bayan ya dawo Nigeria da yake Ba State dinsu daya da shi da Hafsat ba ita 'yar Katsina ce shi kumaKhalifa Dan Kano sai ya kasance Bata san Cewa ya dawo Nigeria bama Daga Karshe Hafsat Sai Labarin Bikinshi Taji Wallahi Abokina ne Sosai Da Sosai so tight Ni kuma Bansan Me yake faruwa ba Domin tun lokacin da yake Jinya A Nigeria Ni kuma Na samu Scholarship Na Tafi sudan karin Karatu sai Da Ina Sudan ne ma Na Samu Labarin Cewa An kaishi India kafin ya dawo daga India ni kuma Na dawo Nigeria Hutu har bayan Dawowarshi nima bansan ya dawo ba kwatsam Sai dai naga Kiran Hafsat jiki a sanyaye cikin sanyin murya kalar tausayi tana kuka Cewa Wai Ance Za'ayi Bikin Abokina amma Bazamu iya fada mata me yake faruwa ba Dan Allah da gaskene Abinnan Ko karyane wai taji cewa shi da wata 'yar India zasu yi Aure.💔

Gashi Ko ta kirashi bata samunshi ya Canza Layima Kwata kwata Nace Bansani ba Wallahi tabbas Nima bana samunshi a waya Amma Zan Bincika Mata Inji bayan Da nayi kokari na Sameshi na tambayeshi Sai ya tabbatar min Da hakane Gaskiya Banji dadi ba wallahi Saida Nayi hawaye Domin Daga shi har iyayenshi Basu kyautawa Hafsat da iyayenta ba Ko dayake ba Lallai iyayenshi sunsan Me yake faruwa ba, Da kyar Na Iya Kiran Hafsat Ina ta zullum akan maganar haka dai na dage na kirata na fada mata cewa Maganar nan Da Gaskece fa saura wata Biyu za a yi Bikinsu a yanzu haka, amma wallahi nima bansani ba kafin in gama magana sai naji shiru Wallahi Yarinyar nan Ashe a take Ta Fadi Sumammiya Sai Asibiti.💓

Bayan haka Da na sameshi na sanar dashi Halin Da Hafsat Take Ciki Karshe ma Tashi yayi ya bani guri Yace min Idan Sonta nakeyi Inje Inyi Jinyarta mana Gaskiya maganar nan Batamin dadi ba Tsawon kwana uku ina fama Dashi Sai ya daina Yaddama kwata kwata mu hadu Bayan sati guda Na Shirya Naje Katsina domin In duba Yarinyar nan Allah sarki tana Gadon Asibiti Ko magana Da Kyar take iyayi na tausaya mata A haka naci gaba da Jerangiya zuwa katsina, hanyar Katsina Ta zamo kamar Titin Unguwarmu Har Allah ya baiwa Hafsat Lafiya domin ko ba komai tare ta sanmu kuma idan Abokina yaci Amanarta Tamkar nima naci Amanarta ne iyayenta Da har Sunce Zasu Dauki mataki Amma daga baya Sukace ko dayake da Ai sunyi sunyi da ita akan ta rabu dashi amma Sai ta nuna taurin kai taki yadda wai dama mazan kano Ance ba abin yadda bane dan Haka Yanzu babu ruwansu bazasu yi mishi komai ba.💞

Yaje shi Da Allah Kwatsam ana haka Saboda yawan Tuna Abinda Khalifa Abokina yayiwa Yarinyar nan Da tunawa akan kudin goro da yasa aka yiwa mazan kano ana kallon bamu da Amana Abin baimin dadi ba da kuma Tausaya matan da nakeyi a duk sanda na tuna ko bacci wallahi bana iyayi sai naji Na kamu da son yarinyar nan Banyi kasa a guiwa ba kuwa sai na kirata a waya Na sanar mata cewa Ina Sonta amma dai dan Allah kar tayi tunanin wani abu ta fara yin shawara tukunna Daga baya zan bayyana mata dalilaina akan Sonta ba kuma dama can ina sonta bane wallahi yanzu ne Allah ya jarabceni da sonta amma tayi tunani ai kuwa babu jima A ranar da yamma ta sanar dani in fada mata dalilina amma dai ta amince kafin ma taji dalilu sai na kwashe na fada mata dalilaina akan sonta saidai wani hanzari ba gudu ba amma Gasikya a yanzu bani da Halin Aurenta domin Karatu nakeyi amma Dai idan ta Amince Da Zarar Na Kammala Karatu saura Shekara daya sai Muyi Aure Idan Allah ya nufa Haka kuwa Akayi.💕

Iyayenta ma Suka Amince Ganin Yanda Nayita dawainiya da bata da lafiya Kusan Kullum sai naje. Ana Haka Sai Saura kwana tara (9)   bikin Abokina Da Safeenat 'yar India zata je Bikin Birthday na wasu kawayenta su biyu Dake (Mumbai) tayi Accident Akan hanyarta ta zuwa kafin aje Asibiti rai yayi halinsa ta Rasu Bayan An kammala Jana'iza da kusan Sati biyu sai Ya dawo daga India kai tsaye yazo ya Sameni cewa Shifa wallahi Yanzu yana son Budurwarsa ni kuwa ban nuna masa Cewa soyayya mukeyi ba. Sai nace masa yaje ya sameta ai ba wani Abu bane Sai yake cewa Dani amma yana Tunanin Da wuya Ta Hakura Akan abinda ya faru shifa dama wallahi Yana Sonta kawai dai Kaddarace Ta riga fata bazai Iya Dakatar da zuciyarshi akan soyayyar Marigayiya bane Sai Nace Hakane Ai ina jin ba matsala yaje ya Sameta sai yace to inzo in rakashi nace masa bazan iya ba Da can kullum ai ba dani yake zuwa gurinta ba bayan haka ta faru bawan Allahnnan yaje ya sameta Ita kuma bata ji kunyar fitowa ta bayyana masa komai ba Domin Jin kunyar mara kunya Ai Asarane Ta nuna masa Cewa ita fa Yanzu Ni take so kuma Soyayya muke haka suka rabu babu dadi.💘

Bayan ya dawo Wai Shine Yake cewa dani wai Naci Amanarsa Kuma Munafiki Ne ni Dan Kuka haka ya karemin Zagi bance dashi komai ba karshe dai yanzu Akan Abin Ya sami iyaye na Shine Mahaifina Yake cewa dani Bai kamata wannan ya Raba tsakaninmu ba Kawai in hakura in bar masa Akwai mata da yawa a duniya Ni kuma Duk Duniya Ita nake so wallahi Ba dan wani Abu nake sonta Tausayinta yasa Na sota domin In saka mata Da Alkhairin Abinda Abokina yayi mata kuma A Zahirance Ina Sonta So Bilhakki da Gaskiya domin Allah har Cikin Raina. Wai Shin mutane me yasa Muke manta Wanda yayi mana Alkhairi kafin mu zama wani Abu amma da zarar mun zama wani Abu Mun samu rayuwar da tafi ta baya sai Mu manta da Alkhairi Allah yasa Mu gane.💗

Dan Allah Jama'a wai shin Menene Mafita kuma Wai shin dama Haka Cin Amana Yake.💗

Kayi Comment 👇


contact-form


SO NE KO YAUDARA?


Duk wani abu da ake yi wa ’ya mace na kyautatawa wanda zai kara so da kauna da aminc ida yarda, bakin gwargwadon iya karfina ina yi mata su.

Kallon satar zuciya da bayanai masu sanyaya rai da zuciya yadda za su kwanta kamar tsumma a randa, ina yi mata su, har wayar salula nake kokarin in saya mata, amma ina dar-dar, don gudun kada in saya mata lasisin da zai dada bayar da damar yin shakwalatin bangaro da batuna, sannan kuma na dada bude mata hanyar Magana da wasu samari, dama ga shi har yanzu na kasa gane a babin da nake ciki.😁

Wai a yadda nake jin labari, idan ba na nan tana maganata, wasu kawayenta har suna kiranta da sunana amma idan mun hadu da ita babu alamun haka daga gare ta, to yaya za a yi in tabbatar da wancan labari gaskiya ne? Shi dai kare da aka ce ana yin biki a gidansu cewa ya yi mu gani a kasa.😇

Wani abu kuma da na lura da shi shi ne, abubuwan da masana soyayya suka alakanta su da so, ban ga tana nuna min su ba, domin sau da yawa abin da masoyinka yake so kakan so shi, amma ita ba haka take ba, ba ta iya daurewa, ko da ina son abu ita ba ta damuwa da shi, kawai abin da take so shi ne daidai kuma shi zan bi, ba ta daure zuciyarta ko alkunya ta yi, ta nuna abin da na damu da shi ita ma ta damu da shi.😃

Lokacin duk da muka hadu nakan nuna mata so na a fili amma ita ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, kuma ba ta san ana yi ba harara a duhu. Idan muna hira da ita ba na kosawa, amma ita sai kaga tana hamma, wato tana nuna min alamar barci take ji. Da ta fara hamma sai in fara hada karena, domin wannan hammar ita ce agogonta na jin barci ko kuma kammala hirarmu. Da na tambayeta abin da ya sa take yi min haka, sai ta ce “Ba ka san kunyar ka nake ji ba.😂

Wannan lamari yana ba ni mamaki da kuma sa ni cikin tunani, kuma ina tambayar kaina da kaina, mene ne wannan, So ne Ko Kuma Yaudara.😆

Kayi Comment 👇

contact-form



Labels: ,

Thursday, November 11, 2021

Kuna Da Sani (Mijina Shine Sirrina) Kashi Na (17)




                    Mijina sirrina? Kashi Na (17)


Sai da ta hade rai sannan tace "Koda na amince munyi aure to ba zaka kusanceni ta karfi ba har sai da yardata da amincewata. Duk da cewar yaji maganar tata wata iri amma sai yaji tazo masa da sauki saboda bai zaci wannan maganar zata fada ba, "Shiru yayi yana nazari amma kuma zuciyarshi tana ta tausarshi ta hanyar cemishi."Tunda kana sonta kawai ka amince da kanta zata nemeka badai mace bace ai mata akwai rauni, ganin yaki yayi mata magana yanata murmushi shi kadai yasata yin magana,
"Kai nake jira fa kayi magana" "Ni ai na amince karki samu damuwa " Galala tayi tana kallonsa domin koda wasa bata dauka zai amince acikin sauki ba duba da cewar shi saurayine ba taba yin auren yayiba, "Shikenan tunda ka amince amma kasani alkawari fa ka dauka" "Nasani." Yabata amsa, "Shikenan yayi kyau" tafada tana kokarin bude kofar motar domin fita, gaby zan samu maganin zazzabi agidanku? Wallahi zazzabi ke damuna yanzu ma ba kiji jikina ba" "Za a iya samu bari naje na duba" Fita tayi yabita da kallo "baby riigima" yafada acikin zuciyarsa.

Paracetamol ta dauko masa sachet daya sannan taje falon abba ta dauko bottle watar guda daya marar sanyi tafito yana nan kamar yadda ta tafi tabarshi haka ta dawo ta sameshi,mika mishi tayi yatashi ya karba ya balli maganin guda biyu yasha yana yamutsa fuska, sake kwanciya yayi ajikin sitiyarin, dukkaninsu sunyi shiru babu wanda yake cewa komai da haka har bacci ya dan fara daukarshi sama sama, juyawa tayi ta kalleshi da niyyar tayi masa sallama ta koma gida amma kamar da wasa sai taga wai yayi bacci, zuba masa ido tayi tana kallonsa, hakika duk inda ake neman cikakken namiji to amadi yakai matsalar kawai ita har yanzu bata sake dashi bane gudun kar akuma sake maimaita abinda yafaru abaya.

Sai da yashaki baccinsa ya more sannan ya bude idonsa bai zaci zai ganta ba amma sai yaganta zaune, baby yi hakuri wallahi ban ma san time din da baccin ya daukeni ba, shiru tayi bata tanka ba dama kuma yasan ba tankawar zatayi ba, "Bari naje na tafi. Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda bude kofar motar ta fita, ko akwalar rigarsa abin da tayi, tashin motarsa yayi yakara mai ya nufi gida. Kwana biyu da faruwar haka hajiya tace masa ta amince ya auri bazawara mutukar hakan zai samar masa da kwanciyar hankali duk da bata so tayi nesa dashi, tara yayunshi hajiya tayi tace musu subar amadi ya auri nadiya kamar yadda yake so kuma itama yanzu taji auren ya kwanta mata arai, babu wanda yayi magana acikinsu saboda dama sun san hakace zata faru tunda dan gaban goshi ne.

Murnar da amadi yayi kamar zaiyi me, nan yaseen yace duk da haka dai zai koma karatu, amadi bai damuba saboda yasan idan har aka aura masa nadiya angama mai wahalar ko bata tare ba. lokacin da yayi mata waya yace manyanshi zasu zo bata yi wani murna ba shi kadaine kawai ke murna, nan ta kashe wayar ta ajiye gefe tana dan karamin tsaki. Anty nadiya nifa ina jiye miki wani abu guda daya, karfa yanzu yaya Ahmad kawai lallabaki yake sai kunyi aure yazo ya rama duk wadannan abubuwan da kike yimasa ko kuma yabari sai kin kamu da sonshi sannan ya rama koma har yayi doubling, " Amira dake gefe tana yin sak'a da kwarashi ta fada. Amira kenan idan har yayi min haka ko fiye da haka zan barshi ne da Allah kawai kamar yadda nabar yaya kabeer da Allah, nasan haushina kukeji kuna ganin kamar bana kyautawa Ahmad saboda abubuwan da nake yi masa, Amira shi so yanada wahalar gaske sannan duk zuciyar da ta samu kanta acikin halin da na samu kaina dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi amma bawai samun farin cikiba.

To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma ba iri daya bane. Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya banbanta su. A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya Ahmad da yaya kabeer" "Menene shi" 

Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na mamajo, shi Ahmad din waye yafada miki baya kula yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji domin bashida tabbas" "Da yana kulawa ai da zaki sani" "Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi. Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani dariya. Amma dai ya kamata ai ki sani" "Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani tunani takeyi. Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda zai tafi zuwa London. Batare da matsalar komai ba baki sukayi sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki.

Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro yayi sallama yace wai ana kiranta awaje, hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye yazo ba, gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya kabeer da tayi domin yau bata san da wacce yazo ba. Tunda nadiya tafito kabeer ya zuba mata ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta amincewa bukatarsa. Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki fuskarta babu yabo babu fallasa "Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda wannan ya haifar mata da tsananin mamaki domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba, "Kina mamakine nadiya.

Bai kamata kiyi mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da muhimmancinki acikin rayuwata da kuma rayuwar 'yayanmu" "Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin fuskarta tana dauke da mamaki, "Nadiya nasake shawara, naga kamar bai daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu koma yadda muke ada" "Ban fahimceka ba yaya kabeer".."Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu kulawa" Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta kalleshi, "Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.

"Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa wani abu bane sabo,da yawa daga cikin ma'aurata wadanda suka samu matsala irin tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su koma suci gaba da rayuwarsu. "Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin yanzu ma da ranar auren wani akaina. Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya ya dubeta cikin tsantsar kishi, yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida aurenmu" "Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da har zan aikata babban sab'o ' "Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa, "Sai anjima.

Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita kadai. Cikin satittikan da basu wuce (2) zuwa (3) ba Amadi ya kammala komai nashi na tafiya karatun da zai koma lokacin saura sati biyu (2) daurin aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan akan dokin rigimarta bata sauko ba, duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata lefe ba idan taje gidanshi. Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye shiryen komawa makaranta domin hutunsu yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer yaketa yimata akan dole sai sun hada baki sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma gidansa, ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin komawa makarantarta take, na saura kwana biyar daurin auren amadi yaje gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar biki,  adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu, mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa, "Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba, aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata, nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin Amira.

Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma zan sake auren " "Allah dai yasa ayi cikin nasara" "Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar kayan tashiga daki.

Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar gaban da take ji nan mama tace mata tayita addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi.

Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance bata da niyyar tashi domin dama tace babu abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan abbansu kabeer za adaura auren domin shine waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da kannenshi suka zo gidan sannan umman sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa, shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu kakeji, duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata iyaba daga kan baki har zuwa ja, lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson ma tunda dai abune na lokaci guda sannan gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta take, wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga daurin aure har andauro,sadakinki dubu (50).

Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a, shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda yana son yazo yaganta amma bata dauka ba gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima guest palace domin tayashi murna, duk danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka gidan acike yake da baki, bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana son taje dinner din amma yasan dakyar idan zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida hankali kan wayar, "Baby ina kika shigane.

Meya faru? "babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne shiru bakiyi picking ba" "Bana kusa ne" "To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki saboda da akwai dinner da" Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba, kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama" Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya." "Nifa babu inda zanje. Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace yaturo masa da number din mama, babu bata lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa ba, kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi yakai kararta wurin mama.

K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya, acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar nan murtuk babu fara'a ko kadan, kowa agidan yiwa nadiya dariya yake yi k'asa k'asa saboda yanda ta cunbure fuska ita adole an takura mata amma kuma ba karamin kyau tayiba fa, umman sumaila ce ta shiga dakin bayan tayi alwala, "Haba'yarnan ki saki fuskarki mana irin wannan shan mur haka, dan Allah ki saki fuskarki sai kifi kyau" Sai lokacin ta dan saki fuskarta, wayarta ce ta fara kara nan taduba taga shine, "Baby Ku fita anzo daukarku,yana jiranku awaje. ko amsawa bata yiba tayi yunkurin katse wayar, "Karfa ki kashe min waya, saboda ban gama ba"  "Ina jinka." "Ke haka akeyi ne, sai guduna kikeyi bakya son jin koda muryata meyasa? Yanzu fa mijinki ne ba saurayi ba." "Naji" tafada tana yatsina fuska, "To shikenan sai kunzo.

Katse wayar tayi ta tashi ta fita tana kiransu Amira wadanda ke can dakin mama sunata faman shiri itada aisha kanwar kabeer domin itama tace zataje, dukkaninsu suka fito har amir da husna walida dasu fadeela ne kawai ba aje dasu ba, wata hadaddiyar jeep ce aka zo daukarsu da ita wadda ta yaya yaseen ce drivernsa ne ma yazo daukarsu, Basu san irin gudun da drivern yayi ba saboda kafin 8 sukaji su acikin kano tsilin, Adaidai wani round about drivern yayi packing saboda dama akwai wata lafiyayyiyar croutoure black agefe tayi packing tana jiransu, "Yawwa amarya ga motar da zakije can Ahmad din yana ciki nikuma zan karasa da wadannan din can wurin dinner din." "To, Amira zo ki rakani.." Tafada kamar wadda take jin tsoro, tare da Amira suka fita zuwa wurin motar suna karasawa amadi ya fito daga bayan motar, "Amma kunyi sauri baby, Amira ashe kema zakizo.

"Yaya Ahmad ba dole ba" "To baby ku shiga mutafi" "Yaya Ahmad ni kaga motarmu can A'isha na cikima tana jirana" Bata jira komaiba ta juya ta koma motar da aka kawosu tabar amadi da nadiya tsaye awurin, Dan kallonta yayi, ba karamin kyau tayiba sai dai babu annuri akan fuskarta sannan babu wanda zai kalleta yayi tunanin ta taba yin aure sai dai wanda yasani, "Baby muje ko?"

Bude mata kofar motar yayi ta shiga ta zauna ya rufe ya zagaya daya side din shima ya shiga, sai lokacin ta dan kalleshi har taga shigar da yayi, milk colour din wani hadadden yadine ajikinsa mai manyan zane marar kauri mai tsananin haske sannan yasa hula itama milk colour, sai zuba kamshi yake kana ganinsa babu tambaya kasan angone, "Baby bamu gaisa ba" Shiru tayi masa ta dauke kanta hakan da tayi yasashi matsawa kusa da ita, "Haba baby yanzu kuma ai ya kamata ace ana bani matsayina na miji, idan ina yimiki magana ya kamata ki rinka amsa min kidaina yimin wannan fushin..." Yakare maganar yana kai mata wani sanyayyen kiss awuyanta domin ba karamin kyau tayi masaba sannan yadade yana kwadayin yin hakan agareta, Jin bakinsa akan wuyanta yasata sake daure fuska amma bata yi magana ba, "Wannan yaron wai meyake nufi ne?" Tafada acikin zuciyarta saboda jin har lokacin bata kiss yake asassan wuyanta, "Baby." Yakira sunata cikin tsokana, "Uhmmm" "Kinyi kyau wallahi sosai kamar kada nabarki ki koma gida, ko zaki zauna." "A ina? Ai ba haka mukayi dakai ba" Murmushi yayi ya kamo hannunta, "to ai basai munyi haka dakeba, ra'ayinane."

Bata sake yimasa magana ba tayi shiru abinta saboda taga fitina yakeji da ita wayaga sabon shiga dama kuma tasan dole haka tafaru tunda shi ba taba yin auren yayiba, Har sukaje wurin dinner din yana rike da hannunta, dakanshi ya fita ya bude mata kofa ta fito suka shiga ciki wanda tun daga waje masu camera suka fara haskasu. Sai yau nadiya ta tabbatar da cewar amadi cikakken dan gatane agidansu, suma yayun nashi dukkaninsu sai da sukayi mamakin ganin nadiya domin basu zaci zasu ganta hakaba tunda sunji yace ta haihu har yara biyu duk azatonsu zasu ganta ta tsofe amma sai sukaga sabanin haka anan dukkkaninsu suka yaba da zabin nasa, "Lallai anty amadi dole arude ace aure akeso.." Inji anty hamida, "Kedai kibar yaron nan kina ganinshi silent.." Anty Dija ta fada tana dariya, "Gaskiya yayi zabe, matarshi kyakkyawa da ita wallahi amma kuma zanga yanda zasu kwashe da zee kanwar dad din su jawahir.." Anty siyama ta karbi zancen, "Bata san yayi aure bane?" Anty hamida ta tambaya, "Wallahi bata saniba, ai kin fada mata nayi saboda ba karamin aikinta bane kiganta ta hado kayanta ta taho domin tana sonshi wlhi kuma koni naso ace ya aureta."

"Ai autan hajiyanne kalar asararru da sakalai gareshi badan hakaba ai da zai iya yin mata biyu.." Inji anty Dija, "Wallahi fa, ai bazai iyaba.." Inji anty siyama, hirar tasuce ta katse sakamakon kiran dangin ango da akayi zuwa cikin filin, nan suka fiffita kowaccensu tana sanye da swiss lace maroon wanda sukayi iri daya sunsha head baki, hannun nadiya amadi ya kama ya rike yana murzawa ahankali, "Wadancan duk yayuna ne baby uwar mu daya ubanmu daya, kinga waccen wadda ke rike da babyn itace babba sunanta anty Jidda ta kusa da ita kuma anty siyama ita ke binta dayar kuma ita nake bi sunanta anty hamida."

"Allah sarki.." Tafada ahankali saboda gaba daya jikinta yagama yin sanyi haka kawai, "Ko bakya jin dadi?" Ya tambayeta yana shafa hannunta, "Ikon Allah, wai meye haka?" Tafada tana kallonsa, "Allah yabaki hakuri, nadaina" tashi yayi yafita zuwa wurinsu anty Dija yahau yimusu ruwan nairori, Koda aka kira ango da amarya dakyar yasha kanta ta yarda suka fita tsakiyar filin, daga ita harshi babu Wanda ya taka tsayawa kawai sukayi, kallonta yake tayi k'asa k'asa yana jin sonta na karuwa acikin zuciyarshi.

K'arfe 10 aka tashi daga dinner din, hannunta yakama suka fita bayan tagaisa da yan uwanshi, mota ya bude mata shima yazaga ya shiga ya zauna tareda matsawa kusa da ita, "Wai menene haka?" Tafada tana ciccin magani, "A ina? Kodan na matso kusa dake?" Ya tambayeta yana murmushi,shiru tayi masa ta dauke kanta ta rabu dashi, kamar dazu yanzu ma haka ya dameta da kiss, gaba daya ya takurawa wuyanta da hannunta, "Wayaga ba sabanba" tafada acikin zuciyarta, har sukaje round about din da aka sauketa dazu yana manne da ita, "Baby ai ba yau zaki tafiba ke" "Saboda me? Wallahi tafiya zanyi tunda bancewa mama zan kwana ba" "To shikenan zaki tafi, kin yarda gobe inzo, "Um um" ta bashi amsa,kiss yakaiwa bakinta nan yagogi jan bakin dake kan lips dinta bai saniba, "daga yanzu indai muna tare nayi miki magana kika ki amsawa haka zan rinka yimiki idan kuma awaya ne to zan barki da Allah.

Nifa gida nake son tafiya.." Tun kafin ta rufe bakinta jeep din dazu tayi packing agaba dasu, "To ai gashi nan yazo, zaki tafi yanzu kiyi hakuri ba cinyeki zanyi ba, kinji ganin yana shirin kaiwa bakinta kiss yasata fadin "naji" amma duk da haka bai fasaba sai da yayi kissing dinta abaki son ranshi, Har motar dasu Amira ke ciki ya rakata sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma motar da yake, gaba daya yanayin yau na musamman ne awurinsa lallai aure babbar ni'ima ce ba kadan ba, Yana shiga gida su anty siyama ma na shigowa kasancewar akwai haske sosai yasa suka ga jan bakin dake bakinshi wanda ya goga a lips din nadiya, "Anty amadi meye abakinka?" Anty siyama ta tambayeshi tana yimasa dariya, "Ni kuma?" Yafada yana kallonta. Dariya yaga sun saka gaba dayansu sunyi gaba hakan yasa ya tsargu, dakinsa ya shiga yaje gaban mirror ya kalli fuskarshi nan yaga bakinshi dama dama da jan bakin nadiya, Murmushi yayi ya zaro wayarshi daga cikin aljihunsa yafara kiranta>>>>?


contact-form




Labels: