Thursday, November 11, 2021

Kuna Da Sani (Mijina Shine Sirrina) Kashi Na (17)




                    Mijina sirrina? Kashi Na (17)


Sai da ta hade rai sannan tace "Koda na amince munyi aure to ba zaka kusanceni ta karfi ba har sai da yardata da amincewata. Duk da cewar yaji maganar tata wata iri amma sai yaji tazo masa da sauki saboda bai zaci wannan maganar zata fada ba, "Shiru yayi yana nazari amma kuma zuciyarshi tana ta tausarshi ta hanyar cemishi."Tunda kana sonta kawai ka amince da kanta zata nemeka badai mace bace ai mata akwai rauni, ganin yaki yayi mata magana yanata murmushi shi kadai yasata yin magana,
"Kai nake jira fa kayi magana" "Ni ai na amince karki samu damuwa " Galala tayi tana kallonsa domin koda wasa bata dauka zai amince acikin sauki ba duba da cewar shi saurayine ba taba yin auren yayiba, "Shikenan tunda ka amince amma kasani alkawari fa ka dauka" "Nasani." Yabata amsa, "Shikenan yayi kyau" tafada tana kokarin bude kofar motar domin fita, gaby zan samu maganin zazzabi agidanku? Wallahi zazzabi ke damuna yanzu ma ba kiji jikina ba" "Za a iya samu bari naje na duba" Fita tayi yabita da kallo "baby riigima" yafada acikin zuciyarsa.

Paracetamol ta dauko masa sachet daya sannan taje falon abba ta dauko bottle watar guda daya marar sanyi tafito yana nan kamar yadda ta tafi tabarshi haka ta dawo ta sameshi,mika mishi tayi yatashi ya karba ya balli maganin guda biyu yasha yana yamutsa fuska, sake kwanciya yayi ajikin sitiyarin, dukkaninsu sunyi shiru babu wanda yake cewa komai da haka har bacci ya dan fara daukarshi sama sama, juyawa tayi ta kalleshi da niyyar tayi masa sallama ta koma gida amma kamar da wasa sai taga wai yayi bacci, zuba masa ido tayi tana kallonsa, hakika duk inda ake neman cikakken namiji to amadi yakai matsalar kawai ita har yanzu bata sake dashi bane gudun kar akuma sake maimaita abinda yafaru abaya.

Sai da yashaki baccinsa ya more sannan ya bude idonsa bai zaci zai ganta ba amma sai yaganta zaune, baby yi hakuri wallahi ban ma san time din da baccin ya daukeni ba, shiru tayi bata tanka ba dama kuma yasan ba tankawar zatayi ba, "Bari naje na tafi. Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda bude kofar motar ta fita, ko akwalar rigarsa abin da tayi, tashin motarsa yayi yakara mai ya nufi gida. Kwana biyu da faruwar haka hajiya tace masa ta amince ya auri bazawara mutukar hakan zai samar masa da kwanciyar hankali duk da bata so tayi nesa dashi, tara yayunshi hajiya tayi tace musu subar amadi ya auri nadiya kamar yadda yake so kuma itama yanzu taji auren ya kwanta mata arai, babu wanda yayi magana acikinsu saboda dama sun san hakace zata faru tunda dan gaban goshi ne.

Murnar da amadi yayi kamar zaiyi me, nan yaseen yace duk da haka dai zai koma karatu, amadi bai damuba saboda yasan idan har aka aura masa nadiya angama mai wahalar ko bata tare ba. lokacin da yayi mata waya yace manyanshi zasu zo bata yi wani murna ba shi kadaine kawai ke murna, nan ta kashe wayar ta ajiye gefe tana dan karamin tsaki. Anty nadiya nifa ina jiye miki wani abu guda daya, karfa yanzu yaya Ahmad kawai lallabaki yake sai kunyi aure yazo ya rama duk wadannan abubuwan da kike yimasa ko kuma yabari sai kin kamu da sonshi sannan ya rama koma har yayi doubling, " Amira dake gefe tana yin sak'a da kwarashi ta fada. Amira kenan idan har yayi min haka ko fiye da haka zan barshi ne da Allah kawai kamar yadda nabar yaya kabeer da Allah, nasan haushina kukeji kuna ganin kamar bana kyautawa Ahmad saboda abubuwan da nake yi masa, Amira shi so yanada wahalar gaske sannan duk zuciyar da ta samu kanta acikin halin da na samu kaina dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi amma bawai samun farin cikiba.

To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma ba iri daya bane. Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya banbanta su. A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya Ahmad da yaya kabeer" "Menene shi" 

Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na mamajo, shi Ahmad din waye yafada miki baya kula yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji domin bashida tabbas" "Da yana kulawa ai da zaki sani" "Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi. Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani dariya. Amma dai ya kamata ai ki sani" "Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani tunani takeyi. Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda zai tafi zuwa London. Batare da matsalar komai ba baki sukayi sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki.

Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro yayi sallama yace wai ana kiranta awaje, hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye yazo ba, gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya kabeer da tayi domin yau bata san da wacce yazo ba. Tunda nadiya tafito kabeer ya zuba mata ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta amincewa bukatarsa. Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki fuskarta babu yabo babu fallasa "Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda wannan ya haifar mata da tsananin mamaki domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba, "Kina mamakine nadiya.

Bai kamata kiyi mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da muhimmancinki acikin rayuwata da kuma rayuwar 'yayanmu" "Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin fuskarta tana dauke da mamaki, "Nadiya nasake shawara, naga kamar bai daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu koma yadda muke ada" "Ban fahimceka ba yaya kabeer".."Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu kulawa" Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta kalleshi, "Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.

"Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa wani abu bane sabo,da yawa daga cikin ma'aurata wadanda suka samu matsala irin tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su koma suci gaba da rayuwarsu. "Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin yanzu ma da ranar auren wani akaina. Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya ya dubeta cikin tsantsar kishi, yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida aurenmu" "Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da har zan aikata babban sab'o ' "Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa, "Sai anjima.

Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita kadai. Cikin satittikan da basu wuce (2) zuwa (3) ba Amadi ya kammala komai nashi na tafiya karatun da zai koma lokacin saura sati biyu (2) daurin aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan akan dokin rigimarta bata sauko ba, duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata lefe ba idan taje gidanshi. Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye shiryen komawa makaranta domin hutunsu yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer yaketa yimata akan dole sai sun hada baki sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma gidansa, ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin komawa makarantarta take, na saura kwana biyar daurin auren amadi yaje gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar biki,  adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu, mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa, "Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba, aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata, nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin Amira.

Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma zan sake auren " "Allah dai yasa ayi cikin nasara" "Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar kayan tashiga daki.

Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar gaban da take ji nan mama tace mata tayita addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi.

Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance bata da niyyar tashi domin dama tace babu abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan abbansu kabeer za adaura auren domin shine waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da kannenshi suka zo gidan sannan umman sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa, shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu kakeji, duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata iyaba daga kan baki har zuwa ja, lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson ma tunda dai abune na lokaci guda sannan gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta take, wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga daurin aure har andauro,sadakinki dubu (50).

Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a, shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda yana son yazo yaganta amma bata dauka ba gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima guest palace domin tayashi murna, duk danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka gidan acike yake da baki, bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana son taje dinner din amma yasan dakyar idan zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida hankali kan wayar, "Baby ina kika shigane.

Meya faru? "babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne shiru bakiyi picking ba" "Bana kusa ne" "To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki saboda da akwai dinner da" Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba, kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama" Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya." "Nifa babu inda zanje. Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace yaturo masa da number din mama, babu bata lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa ba, kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi yakai kararta wurin mama.

K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya, acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar nan murtuk babu fara'a ko kadan, kowa agidan yiwa nadiya dariya yake yi k'asa k'asa saboda yanda ta cunbure fuska ita adole an takura mata amma kuma ba karamin kyau tayiba fa, umman sumaila ce ta shiga dakin bayan tayi alwala, "Haba'yarnan ki saki fuskarki mana irin wannan shan mur haka, dan Allah ki saki fuskarki sai kifi kyau" Sai lokacin ta dan saki fuskarta, wayarta ce ta fara kara nan taduba taga shine, "Baby Ku fita anzo daukarku,yana jiranku awaje. ko amsawa bata yiba tayi yunkurin katse wayar, "Karfa ki kashe min waya, saboda ban gama ba"  "Ina jinka." "Ke haka akeyi ne, sai guduna kikeyi bakya son jin koda muryata meyasa? Yanzu fa mijinki ne ba saurayi ba." "Naji" tafada tana yatsina fuska, "To shikenan sai kunzo.

Katse wayar tayi ta tashi ta fita tana kiransu Amira wadanda ke can dakin mama sunata faman shiri itada aisha kanwar kabeer domin itama tace zataje, dukkaninsu suka fito har amir da husna walida dasu fadeela ne kawai ba aje dasu ba, wata hadaddiyar jeep ce aka zo daukarsu da ita wadda ta yaya yaseen ce drivernsa ne ma yazo daukarsu, Basu san irin gudun da drivern yayi ba saboda kafin 8 sukaji su acikin kano tsilin, Adaidai wani round about drivern yayi packing saboda dama akwai wata lafiyayyiyar croutoure black agefe tayi packing tana jiransu, "Yawwa amarya ga motar da zakije can Ahmad din yana ciki nikuma zan karasa da wadannan din can wurin dinner din." "To, Amira zo ki rakani.." Tafada kamar wadda take jin tsoro, tare da Amira suka fita zuwa wurin motar suna karasawa amadi ya fito daga bayan motar, "Amma kunyi sauri baby, Amira ashe kema zakizo.

"Yaya Ahmad ba dole ba" "To baby ku shiga mutafi" "Yaya Ahmad ni kaga motarmu can A'isha na cikima tana jirana" Bata jira komaiba ta juya ta koma motar da aka kawosu tabar amadi da nadiya tsaye awurin, Dan kallonta yayi, ba karamin kyau tayiba sai dai babu annuri akan fuskarta sannan babu wanda zai kalleta yayi tunanin ta taba yin aure sai dai wanda yasani, "Baby muje ko?"

Bude mata kofar motar yayi ta shiga ta zauna ya rufe ya zagaya daya side din shima ya shiga, sai lokacin ta dan kalleshi har taga shigar da yayi, milk colour din wani hadadden yadine ajikinsa mai manyan zane marar kauri mai tsananin haske sannan yasa hula itama milk colour, sai zuba kamshi yake kana ganinsa babu tambaya kasan angone, "Baby bamu gaisa ba" Shiru tayi masa ta dauke kanta hakan da tayi yasashi matsawa kusa da ita, "Haba baby yanzu kuma ai ya kamata ace ana bani matsayina na miji, idan ina yimiki magana ya kamata ki rinka amsa min kidaina yimin wannan fushin..." Yakare maganar yana kai mata wani sanyayyen kiss awuyanta domin ba karamin kyau tayi masaba sannan yadade yana kwadayin yin hakan agareta, Jin bakinsa akan wuyanta yasata sake daure fuska amma bata yi magana ba, "Wannan yaron wai meyake nufi ne?" Tafada acikin zuciyarta saboda jin har lokacin bata kiss yake asassan wuyanta, "Baby." Yakira sunata cikin tsokana, "Uhmmm" "Kinyi kyau wallahi sosai kamar kada nabarki ki koma gida, ko zaki zauna." "A ina? Ai ba haka mukayi dakai ba" Murmushi yayi ya kamo hannunta, "to ai basai munyi haka dakeba, ra'ayinane."

Bata sake yimasa magana ba tayi shiru abinta saboda taga fitina yakeji da ita wayaga sabon shiga dama kuma tasan dole haka tafaru tunda shi ba taba yin auren yayiba, Har sukaje wurin dinner din yana rike da hannunta, dakanshi ya fita ya bude mata kofa ta fito suka shiga ciki wanda tun daga waje masu camera suka fara haskasu. Sai yau nadiya ta tabbatar da cewar amadi cikakken dan gatane agidansu, suma yayun nashi dukkaninsu sai da sukayi mamakin ganin nadiya domin basu zaci zasu ganta hakaba tunda sunji yace ta haihu har yara biyu duk azatonsu zasu ganta ta tsofe amma sai sukaga sabanin haka anan dukkkaninsu suka yaba da zabin nasa, "Lallai anty amadi dole arude ace aure akeso.." Inji anty hamida, "Kedai kibar yaron nan kina ganinshi silent.." Anty Dija ta fada tana dariya, "Gaskiya yayi zabe, matarshi kyakkyawa da ita wallahi amma kuma zanga yanda zasu kwashe da zee kanwar dad din su jawahir.." Anty siyama ta karbi zancen, "Bata san yayi aure bane?" Anty hamida ta tambaya, "Wallahi bata saniba, ai kin fada mata nayi saboda ba karamin aikinta bane kiganta ta hado kayanta ta taho domin tana sonshi wlhi kuma koni naso ace ya aureta."

"Ai autan hajiyanne kalar asararru da sakalai gareshi badan hakaba ai da zai iya yin mata biyu.." Inji anty Dija, "Wallahi fa, ai bazai iyaba.." Inji anty siyama, hirar tasuce ta katse sakamakon kiran dangin ango da akayi zuwa cikin filin, nan suka fiffita kowaccensu tana sanye da swiss lace maroon wanda sukayi iri daya sunsha head baki, hannun nadiya amadi ya kama ya rike yana murzawa ahankali, "Wadancan duk yayuna ne baby uwar mu daya ubanmu daya, kinga waccen wadda ke rike da babyn itace babba sunanta anty Jidda ta kusa da ita kuma anty siyama ita ke binta dayar kuma ita nake bi sunanta anty hamida."

"Allah sarki.." Tafada ahankali saboda gaba daya jikinta yagama yin sanyi haka kawai, "Ko bakya jin dadi?" Ya tambayeta yana shafa hannunta, "Ikon Allah, wai meye haka?" Tafada tana kallonsa, "Allah yabaki hakuri, nadaina" tashi yayi yafita zuwa wurinsu anty Dija yahau yimusu ruwan nairori, Koda aka kira ango da amarya dakyar yasha kanta ta yarda suka fita tsakiyar filin, daga ita harshi babu Wanda ya taka tsayawa kawai sukayi, kallonta yake tayi k'asa k'asa yana jin sonta na karuwa acikin zuciyarshi.

K'arfe 10 aka tashi daga dinner din, hannunta yakama suka fita bayan tagaisa da yan uwanshi, mota ya bude mata shima yazaga ya shiga ya zauna tareda matsawa kusa da ita, "Wai menene haka?" Tafada tana ciccin magani, "A ina? Kodan na matso kusa dake?" Ya tambayeta yana murmushi,shiru tayi masa ta dauke kanta ta rabu dashi, kamar dazu yanzu ma haka ya dameta da kiss, gaba daya ya takurawa wuyanta da hannunta, "Wayaga ba sabanba" tafada acikin zuciyarta, har sukaje round about din da aka sauketa dazu yana manne da ita, "Baby ai ba yau zaki tafiba ke" "Saboda me? Wallahi tafiya zanyi tunda bancewa mama zan kwana ba" "To shikenan zaki tafi, kin yarda gobe inzo, "Um um" ta bashi amsa,kiss yakaiwa bakinta nan yagogi jan bakin dake kan lips dinta bai saniba, "daga yanzu indai muna tare nayi miki magana kika ki amsawa haka zan rinka yimiki idan kuma awaya ne to zan barki da Allah.

Nifa gida nake son tafiya.." Tun kafin ta rufe bakinta jeep din dazu tayi packing agaba dasu, "To ai gashi nan yazo, zaki tafi yanzu kiyi hakuri ba cinyeki zanyi ba, kinji ganin yana shirin kaiwa bakinta kiss yasata fadin "naji" amma duk da haka bai fasaba sai da yayi kissing dinta abaki son ranshi, Har motar dasu Amira ke ciki ya rakata sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma motar da yake, gaba daya yanayin yau na musamman ne awurinsa lallai aure babbar ni'ima ce ba kadan ba, Yana shiga gida su anty siyama ma na shigowa kasancewar akwai haske sosai yasa suka ga jan bakin dake bakinshi wanda ya goga a lips din nadiya, "Anty amadi meye abakinka?" Anty siyama ta tambayeshi tana yimasa dariya, "Ni kuma?" Yafada yana kallonta. Dariya yaga sun saka gaba dayansu sunyi gaba hakan yasa ya tsargu, dakinsa ya shiga yaje gaban mirror ya kalli fuskarshi nan yaga bakinshi dama dama da jan bakin nadiya, Murmushi yayi ya zaro wayarshi daga cikin aljihunsa yafara kiranta>>>>?


contact-form




Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home