Bayani Game Da Mekesa Amarya Ke kuka Lokacin Aurenta.....
Bari Muga Ko Mekesa Amaraya Kuka A Lokacinda Zata Je Gidan Mijinta....
A yanayin rayuwan mu a na yau game da yadda al'ada ta wajen yi aure ga ya mace ta wajen yin kuka a lokacin da za a yimata aure ko bayan an daura mata aure sai kaga tana tayin kuka, wasu sunce al'ada ce wanda zakaga mace tana kuka akan "wai zatabar gidansu" wasu kuma sunce "tana kuka wai akan zata shiga wani rayuwa wanda bata taba ganiba.
Amma wasu sunce wannan al'adan a yanzu mata basa yawan kuka a yanzu, yanuna akan cewa an fara juya masa baya game da yadda yanayin rayuwammu a yau yake. A yadda mukayi bincike game da wannan al'adar ta mace a marya idan za a kaita gidan mijinta sai tafar kuka, kokuma sai ta gudu zuwa wani wuri ta buya wanda zai s da ker za a samota. To shin; menene amfanin wannan kukan bisa al'ada.
Tambayan da mukayi wa wani bawan Allah wanda yake da zama a jahar Maiduguri wanda sunansa Bukar Hamisu, yace bisa addini da kuma yadda al'ada yanuna, shi zamantakewa ga al'umma a yanzu sai da zaman aure yadda addini yace, dan zaman aure abune wanda ta kunshi wata rayuwace wanda kowane dan adam baisani ba sai yayi wannan auren kamin yasani, yasan yaya ake rayuwa bayan anyi aure, kuma wace rayuwace zai fara dosawa kokuma zamuce wace rayuwa ce ita zata fara dosawa bisa addini da kuma al'ada.
Inji malam Bukar Hamisu yakara mecewa, abinda yasa mace tana yawan yin kuka bawai wani abu bane sune tunanen yadda zasuyi rayuwa a lokacinda suka bar gidan iyayensu, kuma da wane irin sirika ne zasu hadu, zata rabu da kannenta ko yayunta wanda zai sa har idan ta na so taga iyayenta ko yan'uwanta sai da izini wato wajen mijinta.
Wata baiwar Allah tana mai cewa akan yawan kukan da mata keyi ta wajen aure ya dangana ga yadda auren yasameta, misali kamar zakaga wata anyimata aure alokacinda tana da shekaru kadan to soro zai shiga zuciyarta da kuma fargaba dan tana tana da shekara kankani, wata kuma yakan zama auren da aka yimata ko bata so, wato auren dole shima yakan sa kaga mace tana ta kuka dan anyi mata abinda bataso wato auren dole sai kaga mace tana ta kuka.
Wata kuma baiwar Allah maisuna Hadiza tana mecewa kukan aure yazama dole ne ga ya mace tayi, dan yafaru da ita, tace koda mace ita yarinya karama ko babban mace wanda shekarunta yakai aure ne sai tayi kuka. takara cewa, ita anyimata aure yun tana da shekara (13) aka yimata aure aka kaita can kasar Nasarawa, tunda aka kaita ba abinda take yi sai kuka, bayan mutane sun wase sai nayi kokari na gudu zuwa can maka barta a can nake kwana nake barci kowa yarasa inane na shiga ba dan komai bane dan kawai ina soron ginda miji ba wai bana son sa bane dan zuciyana ya sinke.
Kara mecewa, yawancin kukan da tana yi game da wannan auren ba dan komai bane dan mace zakaga zata rabu da iyayenta da kuma sauransu, kokuma za a kaita wani gari mainesa wanda har zai sa dole ne tayi kuka dan tasan ita da kara ganin jama'rta sai ya dauki lokaci da dama. Wannan shine dalilin da yasa a yanzu ana barin mace tayi kokarin kara karatu dan ta fahimta wasu abu game da rayuwa.
Ita ma wat baiwar Allah tana mai ce wa, anyi mata aure ne tun tana da (14) dan iyayenta sunce ita dole ne sai ta aure yarensu "Bafulatani" bayan an kai ta zuwa gidan mijinta, tayi kusan kwana goma (10) bata ganmijinta ba, surkuwarta ne tana kula da ita har zuwa kwana gooma kamin sai ga mijinta yadawo shine kallon farkon da ta yimasa bayan auren da aka yimusu da shi. Sai dai tace a zamaninmu a yanzu yawancin ba a samun irin wannan kukan ta amare, dalili shine, cingaban da aka samu game da zakaga mace tana waya da wanda zata aura koda baya kusa da ita duk nesan da yake zakaga kamar tana tare da shi.
Zainab ita ma tace mana tana mamaki game da wai zakaga mace tana kuka wai dan za a yimata aure ko idan za a kaita gidan miji, ta ce shi aure abune wanda dole ne zaka yi tunanensa amma ko da yaushe mace ta san zata rabu da iyayenta da sauran yan uwanta koda yake tace ita tayi ayre ne sai da tagama karatunta na jami'a kamin aka yimata aure. Takara cewa, a yanzu ansamu chingaba ta wajen hanyar ta sadarwa kamar su wayan hannu wato salula ko kuka zaki iya yin waya wanda kuna kanlon junanku kamar kuna tare. Tace ko da kinyi kuka ko bakiyi kuka ba, dole ne za a kaiki gidan mijinki har idan auren soyaiyane kikayi, tace ita auren soyaiya ne tayi shiyasa ma tana marmary ta je gidan mijinta ba wai sai tayi kukan wai zata ta rabu da iyayenta ba.
Halima tace, itama tayi auren ne ta soyaiya kuma tana sonsai sosai kamar shima yadda yake sonta, harma tace tana marmarin zuwa gidansa,amma da lokacin auren yadawo sai tafara wani tunane wanda zai banbanta da gidansu wanda zata koma karkashin wani wanda kuma shineyake da iko da ita har sai daga bisani hawaye yafara fitamata ma bata sani ba amma batayi kuka kamar yadda wasu suke yiba zakaga suna kuka kamar yarinya karama.
Yawanci irin wannan aren kamar zakaga anyiwa yarinya aure da danginta wanda iyayenta suna so su hada zumunci sosai wani lokacinkuma sai kaga yariya tana kuka akan wannan mijin da aka aura mata bata sonsa shiyasa zakaga tafara kuka har a kaita zuwa gidan sa. A wani lokacikuma yakan faruwa ne ga macenda ta dauki shekaru ba ta samu mijin aure ba, sai iyayenta su zaba mata miji, kokuma iyayenta suna dubawa ne zata yi auren farko bata san wane irin miji ne za ta aura ba shiyasa iyayen sai susa bakinsu game da nijin da zata aura, sai kaga ana ta guje guje da yarsu akan wannan auren da za a yimata.
Wata sunanta tace Hauwa tace bata taba sanin lokacinta na aure yazoba, tana makaranta ba kwana sai kawunta yada wo yakawo mata wasu abubunda zata yi amfani da shi a makaranta, sai ya ciro katin na aure ya mika mini yace "Hauwa wannan katin da na mika miki, muriga munyi shawara da iyayenki mun daura miki aure da wanni bawan allah wanda mun tabbatar da yana da hankali, sai tace masa to kawu. Amma har idan wani lokaci iyaye masu cinma nasaraba ga auren farko ga ya mace, to za su barta ta zaba nata wanda take so.
Wasu suka kara cewa a zamanin mu a yanzu sunce yawan karatun da ya mace da takeyi shiyakan fahimtar dasu ta zamantakewa wanda a yanzu ba auren ta dole ne akeyiba auren ta soyaiya ne shiyasa komai ya canzu ba kamar na da ba.
SOYAIYA MAI ZAFI
Wani abu mai daci Alh Madu Indabo ya hadiye Jin abinda yayan nashi yace, "to ..Allah ya sanya alkhairi." kawai yace ya ajiye wayar. Gaba daya hankalin mutanen gurin yatashi so kawai suke suji abinda yake faruwa, kasa jurewa mami tayi tazauna gefen shi tareda dafa shoulder dinsa tace "dear meyake faruwa wai.
Naga gaba daya kashiga damuwa." Still shiru yayi baice komai ba don baima san ta inda zai fara musu bayani ba. Baby dake gefen shi zaune tarushe da kuka harda birgima tace "abba kafadamin abinda ke faruwa, ko wani abu yasamu yayana " Kuka tarinka yi harda tsalle kamar wata karamar yarinya . kamota abban yayi yazaunar da i'ta kan cinyarsa yace "stop crying baby na, ba abinda yasamu yayankiyana cikin koshin lpy. "To abba kafad'a min abinda yafaru." Tafada tana kokarin fashewa dawani kukan , saurin rungumo ta yayi yace "karkiyi kuka zan fada maki .." Kollon mami yayi da hankalinta yaba daya ya tattara yakoma kansa haka small mom da samha dasuke tsaye. "Abbey yakirani yacemin ya daurawa Aliyu aure! Yanzu haka yana tafowa tareda matarshi.
Wani uban tsalle baby tayi tasaki ihu tana rawa tana cewa " it's finally over alhmdllh yau yayana yayi aure yeeee. Tafice da gudu waje tana rawa . samha dake tsaye gagara daukanta kafafunta sukayi tanemi guri ta zauna kanta yana bala'in juya mata " taya haka zata faru!?, wnn wani irin munafurci ne Aliyu zaiyi aure bayan yasan i'rin son datake masa.
To wama ya aura!?, wace shegiyarce ta!?,,, tabbata asiri akai mishi ya aureta ...to koma waye lalle ta d'ibama kanta saitayi dana sanin shigowa rayuwarsu!." Mami dabata ma fahimci abinda abba yafada ba kawai sai kallon shi datakeyi.
Hajiya maryam nace maki Aliyu danki an mishi aure!." Yafada yana dan hura mata iska a ido don irin kallon datake mishi. Ajiyan zuciya ta sauke tace "kace Aliyu yayi aure ko. Gyada kai yayi yana tabbatar mata da maganar "to Allah yasanya alkhairi." ..tashi tayi ta wuce bedroom dinta donyin bacci ko Allah zaisa kanta yasaki don tafahimci inda maganar abba ta dosa. Don kamar almara haka take ganin abun. Shima abba tashi yayi yafita yabar small mom da samha i'tama data tashi fuuu kamar zata tashi sama tashige falonsu tareda banging kafo. Bayanta small mom tabi aranta tana cewa " ko wace wanan miskilin ya aura sai Allah. " tadaga kafada tashige. Samha bedroom dinta tashiga tarufe da key ta hautsina gashin kanta tana kaiwa da kawowa zufa nata keto mata gaba daya tagama daukar zafi.
Ni Aliyu zaiwa haka?, watoma don tsabar bura'uba da muna firci ba anan akai auren ba don karmuji ko? saidai akawo mana amarya murmushin dayafi kuka ciwo tayi tace "lallai Aliyu zaka had'u da bala'i dakuma tijara irin tawa..muzuba mugani. Daga haka tabude fridge tasha ruwan sanyi amma dukda haka bataji sanyi a ranta ba. Baby tana nan waje ta dasa kujerarta setin get yanda zata hango duk mai shigowa, bayanda abba baiyi da 'itaba amma fir taki shiga ciki tace saitaga dawowan yayanta. Securities da soldiers din gidan sunyi matukar mamaki jin abinda baby tace "wai sir Aliyu got married" kowa da irin tunanin dayake a ransa na mamaki.
Har abba yaje masallaci sallan magrib ya dawo baby na nan zaune, girgiza kai kawai yayi yay shigewarsa apartment dinsa. Karfe 8 dai2 motoci suka fara horn megadi yafara kiciniyar bude get. A guje baby ta tafi lokacin data i'sa harsun gama shigowa ko parking basu gama yiba tafara leka motocin tanaga tayadda zata hango amarya . turus tayi ganin wata mace mai katon hijab kanta sunkuye ba'a kallon fuskanta, mamakine yakamata aranta tace "badai wnn ce matar yayana ba.
Nayi tunanin zanga big gal wayayya wanda tacika mace ...amma ai wnn bata fini bama..." Saurin katse tunaninta tayi ganin Aliyu yafito yana neman wucewa, dasauri tai gurinshi ta rungume shi tace "yayana barka da dawowa, Congratulation Kafin yace wani abu gaba daya ma'aikatan gidan sunyo gurinshi suna mishi CONGRAT Ko wanne fuskanshi dauke da faraa, gagara cewa wani abu yayi sai murmushin yak'e da yakeyi yana daga musu hanu. "Yayana warcanne amaryar tamu.." Tafada tana nuna sahra dake can nesa dasu kanta sunkuye kasa. Kallon gurin datake yayi yaga dogon hijab din jikinta amma baiga fuskanta ba, wani kululun bakin cikine yaji ya kamashi "wai wnn abun aka aura min.
Tsaki yayi cikin ransa azahiri kuwa yayi murmushin yak'e yace 'eh' Ganin yanda baby takafeshi da i'do, daga haka yay wucewarsa batareda yabari kowa ya bishi ba. Takawa inda take baby tayi ta rungume ta tace "barka da zuwa amaryar yayana, i'na fatan zakiji dadin zama damu. Gagara cewa komai sahra tayi sai jikinta dake rawa don kowama rsarinsh take agurin "wannnan wani irin al amari ne". Tafada cikin ranta. Ganin haka baby tace "kikwanta da hankalinki, kisaki jiki damu kinga ba'abinda zamuyi muki. " tai maganar tana kama hanun ta suka shiga ciki.
Labels: Soyaiya
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home