Tuesday, October 12, 2021

Tarihin "Musa Dan Kwairo" Da Iyalensa Da Magadansa

 


A yadda bayanai suka nuna game da yadda aka zantar a wata masarauta game da tarihinsa dakuma yadda yayi rayuwa da jamma'a, da yadda yana kirkiro wakkan da yana yi da kuma tayaya yake sarrafa su da kuma kide kiden da yana yi da sauransu.

    Shi dan kwairo anjima da dama nanta duba gameda su Digiri da yayi daga nafarko har zuwa na biyu a fadin duniya yadda yasamu wasu dabaru game da yin wakarsa. Kuma shi Da kwairo yayi gasa da mutane masu wakar kaman shi, na kidin gargajiya, inda ba wanda ya bugeshi a waka daga ciki har zuwa waje.

    Alokacinda aka yi hidiman taron shekarar rasuwansa ta shekara (30) ga wani bawan allah mai suna yayi bayani game da tarihinsa mai suna ) Sa'idu Mohammad Gusau) wanda yana da cikakken bayani game da tarihin dan kwairo.  Yayi bayani game da wasu takardun da shi dan kwairo ya bari wa magadansa zuwa na cikin gida, da kuma na waje, wanda har a yau suna amfani da shi, kuma sun rike wannan littafin a matsayin tarihi ga meda wakokinda shi marigayi dan kwairo ya wallafa.

    Shi wanna takardun da marigayi dan kwairo ya rubuta, yakunshi gameda yadda al'adun hausawa yake dakuma al'addun gargajiya da kuma al'umma. Shi kuma wannan bawan allah da yayi bayani game da tarihin dan kwairo kamar yadda yayi rayuwarsa da sukayi da dan kwairo a lokacinda suke zama ninsu. Shi wannan bawan allah yayi bayani game da yadda a lokacinda shi marigayi yake rera wakarsa a shekara (1973) musamma a lokacinda ake kamun kifi kokuma taro a fadar kano sai yafara rera wakarsa, yataba al'adun gargajiya, rayuwarsu ta hausawa.

    Shi wannan mai ba da tarihin shi marigayi dan kwairo game da abubuwanda littafinsa ya kunshi game da babban dansa da yagaje sa wanda haddace duk littafin da ma haifinsa ya wallafa tun kamin allah ya dauke ransa. A kwai wani magajinsa wanda ake kiransa (Alhaji Mohammed Maigaya) wanda shima mukayi kokari mukaje muka nemi wasu bayanai game da shi marigayi dan kwairo.

    Munsamu wannan tarihinne a dunkule, wato wasu munsamu daker, wasu kuma sai mun bi daddaki kamin mu fahimta gameda rayuwarsu da marigayi Dan (Kwairo). Kuma ta kunshi wasu abubuwan halifofinsa har zuwa kashi uku (3).

Bayanai Game Da Haifuwarsa:

    Shi wato Marigayi "Musa Dan Kwairo) da magabatansa Sun Fitone daga daga jahar ta (Kadau) dake yankin ta Bakura a jaharmu ta zamfara a yamzu. Mahaifin marigayi dan kwairo mai suna (Usman Dan Kwanaga) wanda a tarihi yanuna shine ya haifi (Musa Dan Kwairo). Shi mahaifin dan Kwairo shine wanda aka fisani da "Da dan kaka Maiganga" shi Usman dan kwanaga an haifesa ne daga can dan kadau dake bakuraa yadda bayanai na tarihi suka nuna.

    Shi Usman Dan Kwanaga" mutu ne wannda aka fisani da shi babban manomine, kuma yana waka game da yin noma da sauransu? kuma jarimine ta wajen wakar yin hausa wanda har yakan shiga jikin mutum kamar ruwan sanyi a jiki. Kuma yagada wannan kidan nashi ne a wajen "Kaka Maiganga" wanda har yaza jarimi saka makon yin kida.

    A wasu kidan dan "Usman Dankwanagga" yayi kirarinsa a wata wakar yadda tarihinsa yanuna akan a shekara ta (1914) ne yanemi yabar garinda yake gabadaya da iyallensa dan nwman wajen da zai yi noma. Daga nanne sai yabar assalin garinsa sai yayi hanyar gabas, sai alah yahada shi da wani sarkin da ake kiransa da sunan "(Alhaji Ibrahim" a shekara ta (1904 har zuwa 1923) wanda aka sansa da 'Sarkin Maradun" anan ne wannan sarkin yabashi mafaka tare da iyallansa gaba daya, kuma yabashi wurinda zai yi noma, daga bisani yazama shine mawakinsa.

    Bayan Usamn Kwanaga aka bashi waje, amma sai yazaba wata wuri ne da akekira "Kaya" wannan wurin shine yake da albarkascin yinnoma, duk wanda har yayi noma a wannan kauyen sai kaga yasamu alheri sosai a wannan jahar ta "KAYA" daga nan ne su iyallensa suma suka samu ma zauna a wannan kasar ta 'Kaya' wanda kasar ta na da arzikin noma.

Bayan samun mafakan a garin ta Kaya, bayan shekaru da daman har yakai ga lokacinda yasufa, daganan ne Usman Kwananga sai yayi murabus ya bargari, amma tarihin bai nuna garinda yajeba, daga nan ne sai aka baiwa dansa mukamin ma haifinsa wanda sunansa da aka fisani da (Abdul Kurna) wato ana yimasa kirarin "Sarkin dan sarkin kidan "Maradun".

Wacece Mahaifiyarsa:

    Ita ma haifiyar "Kwairo" wanda aka fisanita da (Yarnunu) a tarihi yanuna itace ta haife (Alhaji Musa Dan Kwauro) kuma ita ne wanda aka fisaninta da cikakkiyar jahar "Goran Namaye" ita kuma yar asalin ta (Bazamfara ce). 

Abdu Kurna:

   A yadda tarihin Abdu Kurna yanuna, shi anhaifesa ne a jahar ta kadau dake jahar ta Bakura karamar hukumar at Zamfara a lokacin (1899) tare da Abdul Kurna da Usman Dan Kwanaga ne suka bar (Dankadau) suka zo suka samu wajen zama a "Tunga birnin Maradun. Abdu Kurnu shine yagaji ubansa Usman Dankwanaga ta wajen kidi dan sarki sarkin maradun.

   A wannan lokacinne aka Nada shi " Abdu Kurna" s matsayin sarkin makada a yayin lokacinda mahaifinsa yasufa bai da karfin da har zaiyi kida, sai yanemi a nada dansa Abdu Kurna ya gajeshi  kuma yagajeshi ta wajen yin kidda shine kawai burinsa.

"Tayaya Aka Haifi "Musa Dan Kwairo"

   Tun lokacinda ake mulkin mallaka aka yi kirarin anfaife Musa Dankwairo, amma bayanai sai yanuna cewa bayan shekaran ta (1903) Jim kadan bayan mulkin mallaka yawuce, sai aka haifeshi jahar Kadau na Bakura dake jahar ta zamfara kami mahaifinsa sukoma zuwa jahar tunga kauyen Kaya dake Maradun.

   A lokacinda shi marigayi Musa Dan Kwairo da yacika  shekaransa bakwai (7) a duniya, ananne sai yafara koya abin yin kida shima yafara koikoyon mahaifinsa  Usman Dankwanaga. A cikin makadan Musa Kwanaga, wani bawan allah da allah yabashi murya mai zaki sosai, har idan yafara waka sai kaji kamar "Dan Kwairo".

Suwayene Iyallen " Dan Kwairo".

    A yadda rayuwanmu a ana yau duk mutum bil'adama yana so yaga ya kafa zuri'a nagari ta wajen auren hallal. Shi " Dankwairo" yayi aure ne tun allokacinda yafara yin waka inda ya aure matar sa ta farko, daga bisani kuma ya yi aure da dama inda suka hafemasa yara guda gomasha bakwai (17).

Suwanene Matayen Da "Musa Dankwairo" Ya aura,  Dakuma Yaranda Ya Haifa da su:

  1. Hauwa Taladan.
  2. Hajiya Hadiza (Tashika).
  3. Amina.
  4. Tumba.
  5. Rabi.
  6. Maryam.
  7. Hauwa.
  8. Maimuna.

Suwayene Musa "Dankwairo Ya Haifa (Maza Da Mata)

  • Hauwa (Taladan)
  • Hajiya (Tashika)
  1. Mohammed Dan makada ( shine na daya)
  2. Alhaji Marafa ( shine na biyu)
  3. Audu Wakilin kida.
  4. Habiba dakuma
  5. Zulaihat.

  • Amina
  1. Umaru Dama (Maikidin Noma)
  2. Amina Kasu, Tana maradun dan zam aure.
  • Tumba
  1. Sani (Maizakin Murya)
  • Maryam (Amarya)
  1. Sa'adatu
  2. Mohammed Balarabe da kuma,
  3. Umar.
  • Rabi (Yarzuma)
  1. Aisha Wanda Aka Fisani da (Indo)
  2. Mallam Tunau.
  • Hauwa
  1. Abubakar Kida.
  2. Amina.
  3. Ibrahim Dan'autan amina.
  • Maimuna
  1. Allah bai bata haifuwa ba.
        Alhaj "Musa Dan Kwairo" yayi babban gangami ta wajen yin waka, kuma sai da yayi kokarin yaga yakafa komai yashiga hanya ko da bayan ransa. Kuma Shi "Dankwaro" yana bawa ma kadansa daman sujefa nasu a wajen rera waka dan yakara yin zaki wanda har zai shiga jikin mutane suji yana zaki sosai.

    Hakkan ne shi "Musa Dankwairo" yake rera wakokinsa akoina har idan mutum yana wucewa sai yasaya ya saurare wannan wakar da Dan Kwairo yake yi dan yadda wakar sa yana da zaki kuma ga shigan jiki kamar ruwan sanyi.

Kungiyar "Musa Dan Kwaro" ta Maradun kida, sun hada da:-

  1. Alhajimusa Dan Kwairo (Jagora)
  2. Muhammadu ( Kida na Farko)
  3. Garba Marafa
  4. Daudu :Allah yayi masa rasuwa
  5. Audu (kida da almashi)
  6. Ali (Dan sa'yidu shayi)
  7. Abubakar (ciroma)
  8. Ibrahim (sarki dane)
  9. Muhammadu (Jika halifa)
  10. Sani (Kida da Al,ashi)
  11. Mohammadu (Bara)
  12. Malam (Bara)
  13. Kanka hu (Tsaro Kaya)
  14. Sada (Sankira)
  15. Rabo (kida da almashi)
  16. Nabuba (Kida Da almashi)
  17.  bucaca (Kida da almashi)
  18.  Ahmadu Sankara
  19. Sallah Kwana (Hadimin Gidan)
  20. Daudu (Dan galadima) 
    Shi "Musa Dan Kwiro" a yadda tarihinsa yanun cewa, shi mutunne wanda yanada tausayi ga kowane al'ummansa, kuma mutane da dama suna amfana a jikinsa tawajen ciyarwa da sauransu, kuma yawancin mutanen da suke tare da shi kamar masu tayashi kidi, gaba dayansu suna amsa komai daga hannunsa abinci da komai dai dai gorgodon rayuwa. Kuma yana yiwa iyallansa tarbiya a yadda addinin musuluci yake da kuma wasu al'adun gargajiya ta "Hausa".

    Kuma shi "Da Kairo" a kunlum yana yiwa jama'arsa bayani game da yadda rayuwa yake da kuma zamantakewa ga juna yadda zasuyi zaman lafiya ga junansu ba kiyama ko gaba ga dan uwansu dan suzama sunsiya madauri daya. Shi Dan Kwairo ya tashine a gidansu yaga ana yin noma sosai, a duk lokacinda Damuna tayi sai kaga baza ka gane hankalin kowaba dukkansu kowa yakama hanyar gona dan ba karamin arziki ake samu a wannna kauyen ba.

   A duk lokacinda damina tayi sai kaga Musa Dan Kwairo baya bukar komai har wanda zai kawo masa cikas game da harkarsa ta noma, dan idan har lokaci tayi to yawancin yana zama a gonarsa ne dan yakan kulawa da duk harkokin da yana tafiya.

Rasuwar "Dan Kwairo Maradun"

    Musa Da Kwairo yayi wata gajeriyar rashin lafiya ne na wasu kwanaki kadan sai Allah ya dauki ransa a ranar jumma'a sha uku (13) ga watan desamba a shekara (1991), kuma allah ya dauki ransa ne a gidansa kano dake maradin ta jahar Zamfara.

    Mawakan shi "Musa Dan Kwairo" halifansa ne kuma suna biyaiya bisa yaddad shima yake basu girmansu, kuma a ko dayaushe suna so suga sun bi dukwani ka'idar da shi Dankwairo yabi dan susamu sugajeshi tawajen kida da al'adun gargajiya ta Hausa. Dalilinda yasa basa so ace sun bi wata hanyar da baiyi kama da al'adun Hausa ba.

"Musa Dan Kwairo Da Haliffofinsa"

    A yadda tarihinsa yanuna game da "Haliffofinsa" sune kamar yaranda ya haifesu da kuma yan'uwansa ta zuriya wanda har a yau sune suka gajeshi a ta koina ta sadar da wakokinsa ta Hausa. Halintafakawa shine wata al'ada ta Hausa wanda ake so gaji wannan al'ada ga wanda suka tashi ko sun girma da kuma wanda suke tasowa dan su gaji wannan al'adar ta Hausa. Har ida mutum da aka ce shi mawaka ne, har bayada wani wanda zai gajeshi, to za ayimasa wani gani ne wanda gidansa ya kasa, kuma gidan yakan iya gurgujewa dan rashi magadansa, Daga "Abdullahi Magajin Karfi".

    Kuma shi "Dankwairo" yayi murna ne game da yace ko da yamutu zai bar wata babbar wanda zasu gaje shi ta wajen yin waka, dan da allama sun dauki wakarsa kamar shine yakeyi duk a lokacinda suka fara rera waka. "Dan Kwairo" yasamu yaran da suka gajeshi ta wajen waka wanda suka kure marsu:-

  • Alhaji Musa (Dankwairo) mai kidi har kayi kuka bisa yadda yakeshi jikin dan adam. Kuma allah ya dauki ransa ne a (2009) shima yabar abubuwa da dama.
  • Alhaji Abubakar ciroma, shine na biyu daga wanda suka gajeshi ta wajen waka. Kuma shima allah ya dauki ransa ne a (2010) shima yabar babban tarihi kamar ubansa Dan kwairo.
       Amma a kwai wasu wanda suma suna yin wakar ta irin wanda Dan Kwairo yakeyi, amma basu da wata allaka da shi ko tawajen jini go dangi, suma suna rerawa ne ta harcen hausa kamar yadda shima yake rerawa. Har a yau irin wanda suke waka kamar yadda shi Musa Dan Kwairo yake yi, basu gada daga wajensa ba, suma suntashi ne ta wajen wata hanyar kokuma muce suma sungada daga wajen iyayensu. Kuma yawancinsu suna amfanine da abin makada irin wanda "Musa DanKwairi" yayi amfani da shi watau 'kotso' ta al'adar Hausa.

Suwayene Daga Cikin Makadan:
  1. Abdul Salisu (Zazzau)
  2. Abdullahi Sani (Dankwairo)
  3. Abubakar Tarauni (Kotso)
  4. Abubakar Dan'auta (Anguwa Biyu ta Kotso)
  5. Adamu Usamn (Kotso)
  6. Ado Gwaram (Kotso)
  7. Ahmadu Aucanawa (Kotso)
  8. Ahaji Kaya (Dan kwairo Yakosa)
  9. Alhaji Kebbe (kuci Kotso)
  10. Alhaji Marafa (Dan Kwairo Kotso)
  11. Alhaji Dan'abai (Kwaranyo Kotso)
  12. Alhaji Danjuma (koko Kotso)
  13. Alhaji Danzaki (Kaya Kotso)
  14. Ahmadu Monkey (Sarkin Katsina Kotso)
  15. Auwalu Ma'aiki (Stidiyo)
  16. Bala Mai Kotso (Bagwai Kotso)
  17. Bello Murya (Minna Kotso)
  18. Dadda'u Katsina (Kotso)
  19. Dan Imamu ((Sokoto Kotso)
  20. Dan Jos (Abija Kotso)
  21. Danladi (Kaduna Kotso)
  22. Haruna Ningi (Ningi Sitidiyo)
  23. Haruna Mkarfi (Kotso)
  24. Sanusi Imam (Katsina Kotso)
  25. Arafa Kabiri (Kudu Kotso)
  26. Jibiya Lawali (Kotso)
  27. Sani Mohammed (Futuwa Kotso)
  28. Mande Mohammed (Katagum Kotso)
  29. Muhammadu Musa Dankwairo (Kazaure Kotso)
  30. Dandare Muhammadu (Jere Kotso)
  31. Kudahi Musa (Fakku Kotso)
  32. Santolo Musa (Zango Daura Kotso)

contact-form



 

 




Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home