Thursday, September 23, 2021

Halayen Namiji Wanda Ke Burge Mata? Da Kuma Yaudara Sakanin Mace Da Namiji




Halayen Maza Wanda Yake Sa Mata Farinciki Da.....

Game Da Yaudara Sakanin Mata Da Maza.....


Mene halayen wanda ake maganansa yake burge mata? to zamu ga kowane irine kamae yadda aka ce.

    Wato abubuwa ne guda biyar wanda mata suke so a duk lokacinda ne suke bukatar zamantakewa ga ko wane namiji dan su cinma burinsu ga da namiji a ko da yaushe. Kuma akwai wasu halayen da zakanayi dan yakara maka kwarjini ta wajen soyaiyar ka a ko da yaushe. amma a kwai wasu halayen da mata basaso game da kowane da namiji, sai kayi kokari ka kauda kanaka game da wannan yanayi.

    Kuma a kwai wasu lyalle kyallen da zaka yi wa mace dan ko da yaushe zakaga tana so taga tana so yati magana da kai a ko da yaushe dan a kunlum zata ga ta amsamaka duk wani maganan da kayi dan tayi farinciki.

Mene Abubuwan...


















  • Nafarko mace tana so taga saurayinta yazama mau hukunci, wato ma'an shine a duk kowane namijin da baya daukan duk wani mataki game da abin da yasameshi to yakan karya gwiwar mace dan zata ta yi tunane game da har idan wani abu yasa meta to baza ka iya kareta ba dan rashin ba ka iya daukan mataki na jagorantar na mazantaka.
  • Nabiyu kuma bayan jaruntakan ka, kar kazama bakada tausayi, yazama kana da tausayi a ko da yaushe a duk wani abinda yafaru da kai, ko kuma idan wani yayi maka abu sai kayi hakuri in har abin bai zama hasari ne a gareka ba, to mace tana so taga kazama hakan dan har idan tayi maka wani abu zuwa gaba, zaka iya yin hakuri amma idan baka da hakuri zata dinga tunani akan idan har tai wani laifi bazaka yimata afuwaba. To a koda yaushe kazama mai tausayi a gareka ko da yaushe dan tausayi yakan kara imani ga kowa a duniya.
  • Na uku kuma, kowane namiji yazama yana da fatan alheri kokuma kekkyawan zato ko da abin yanada wahallan samu kana yawan yawaita alheri ga kodayaushe dan mata suna son suga ko da yaushe kana cewa musu allah ya barku tare kuma yadada kara kwarin gwiwa a sakanin ku da ita, to zata jidadi a ranta dan kana yin fatan alheri a sakaninku da ita. Mata suna son suga kowane namijin da yana da wannan halayen a ko da yaushe.
  • Na hudu kuma shine, kowane mace tanaso taga namiji yana girmamata wato kamar idan zatayi wani abu sai kace mata baby bari inyimiki, kuma tasan dole ne ita ne yakamat tayi, ko da tasan kai bazaka iya yimata ba, kafada dan ta ji dadi ko da bazata barka kayiba. To kagani mata suna son irin wannan zoliya kana yimusu a kodayaushe dan suga kafaranta musu rai na yau da kunlum.
  • Nabiya yazama kana girmamasu a koda yaushe, dan kasan mata kowane sakan suna so suga kana yabasu, kwalliyan da sukayi, takalmin dasuka sa, kayanda suka sa, jambakin da suka shafa da sauransu. to kasani mata suna son yabo a kunlum yana sasu suzama suna farinciki a ko da yaushe, shiyasa suna so yabawa a kunlum.


    Wannan shine abin da kowace mace tana so taga namiji yana yimata a kunlum na yabawa dan zai sa suyi tunane akan bawan da kakeso ko kuma akan ba wanda ya kai su kew a duniya har idan kana yabasu a kunlum suna so suga sun hada fuska da kai dan ka yabamusu da kwanliyar da suka yi.

Mata abinda yasa suna son yabawa ba wai dan komai bane kawai, a rayuwa mata suna son yabo dan suna so suga sun zama yarinya karama a ko da yaushe. Ko da yarinya karamace har idan tayi kwaliya sai kayaba wannan kwalliyar da tayi sai kaga tana murmushi ko kuma kace mata, "matana yau tayi kew" to zakaga tana murmushin farin ciki.

               MACE KONAMIJI WANE YAFI YAUDARA A SAKANINSU.









   




 A yanayin rayuwanmu na yau shine, anna ta magana game da yaudara sakanin mata da kuma maza, wasu suna cewa akan wai maza ne sun fi yaudara, wasu kuma sunce matane suka fi yaudara, to bari mugani wanne ne dagaciki yanuna allama sun fi yau dara, mace ko na miji.

    Wasu mazan da na hadu da su suna hira shine, wani daga ciki yana cewa "budurwarsa sunyi soyaiya shekaransa uku suna soyaiya da ita har sai da ta gama makaranta sai allama yanuna tana so ta juyamishi baya, har idan yana so yazo gidansu sai tace masa, "yayi hakuri zatayi aiki" ko kuma tace masa " kanta yana ciwo" kuma ta daina kiransa a waya sai dai shi ya kirata, da ya soma bincike sai ashe wani ne wanda yafisa yana hawan mota ta samu ashe shiyasa tana nema ta juyamasa baya, daga bisani sai yaji anje gidansu anyi gaisuwa bayan shima yayi gaisuwa a gidansu.

    To Shi a rayuwa mata yawanci suna yaudara ta wajen neman mai kudi, zakaga mace tana tare da kai sama da shekara ba wani abinda yataba shiga sakaninku da ita, amma idan tasamu wani sai ka ga tafar maka wani abin da bai taba faruwa, a kwai wani kalmar da mata suna cewa "kowa gidan sauki yakeso" amma su mata ba a dacewa da wannan abinda suke ce wa, garin neman gidan sauki sai kaga tazama abin kunya daga neman dadi yazama wahala, sai kaga nata da nasani. Kuma ya wanci iyayensu ne suke jawo musu wannan balla'i game da neman duniya sai kaga yanuna musu kudi, bayan ya aureta sai kaga bayan shekara daya sai yasake ta dan yasan ta aureshine dan abin hannunsa.

    Naje gaisuwane zuwa wani gidan dan uwan abokina sai naji yara mata guda biyu suna cewa ga uwarsu"mama nikam inaso naga mijina da zai aureni yasayami TV na jikin bango" sai uwartasu tace ku bakusan duniyaba tun yanzu kun fara son abin duniya tun bakuje ko ina ba, tace musu kuyi addu'a allah yabaku namiji nagari da kuma zaman lafiya shine komai arayuwa kuma shine arzikin zaman aure, to gaga wannnan shine uwa ta gari bawai ta yaba musu ba dashike tasan rayuwa a yanzu sai a hankali tace musu kar subi abin duniya sunemi namiji mai addini kua wanda yana da sana'arsa da zai rufe musu asuri bawai duba abin duniyaba.

    To kagani wannan shine uwa tagari, amma duk uwarda zatayi yabon yarta game da abin duniya to kasani ko da yaushe idan wani yazomata har idan yafika to kasani zata zame ta barka, to kagani wannna shine akece yaudara kennnan ta samu wanda yafika.

    A kwai wani labarin da na karanta geme da wata raguwar kudi da kuma kayan da a kayiwa amarya? mamar yarinyar wato amarya tana mecewa ai angon da zai auri yarta bai sa kaya masu sada ba a ciki, dakuma bai biya wani raguwar kudi nara (300) wanda ake binsa, shikuma yace wallahi bai da wani kudi a wajensa, akan wannan raguwar kudin akafasa wannan auren dan naira (300) kawai ta sa, sai da tahana yin auren. 

    Wa iyaye su suke sa yaransu su yaudari namiji dan neman abin duniya, daga baya kuma sai ayi danasani garin neman kwadayi sai a shiga masifan da baza a taba fita ba.

    A wani lokaci kuma Su maza suna yaudaran mace ta hanya da dama babu kamar zakaga mace tana soyaiyarta da wani saurayinta sai kaga wani yazo yace yana sonta bayan tarabu da duk wani saurayinda take dashi sai yayi awun ga yabarta, wani lokacikum a kwai wasu al'ada idan kanaso kayi hira da yarin ya sai ka biya kudin kanlo ko na hira kamin kafara zuwa wanjenta, to wannan ma maza suna amfani da wannan daman bayan sun samu abinda suke so sai suyi awungaba dan sunnuna akan zahiri su suna so na aure ne sai su yaudareta suyi tafuyansu.

    Haka zalika tawajen kudu ma suna yin haka, a kwai wani kudi na musamman har idan kabiya wannan kudin, bawi kabiya sadaki bane amma suna kwatan tawa da sadaki dan duk abin da kace wa yarinya tayimaka zata yima, dan ita tana tunane zaka aure ta bayan yasamu abin da yakeso sai yagudu yabarta, to duk wannan yana nuna allamoin yaudara ne ga namiji kace zaka aureta sai ka shawo hankalinta gaba daya sai yayi awun gabansa.


Zaka Iya Bada Shawaranka Akan Mekake Gani Game Da Wannan Al'amari Bisa Kasa...




contact-form


Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home