Wednesday, September 15, 2021

Labari Mai Abin Tausayi? Duk Wanda Yanema Taimako Kataimakesa..

 



Duk Wanda Yanemi Taimako Ka Taimakamasa.......

A cikin KADO anguwar hausawa dake babbar birnin taraiyya Abuja dake anguwace mai lunguna ga tarihin bishiyoyin mangorori hakan ne yesa anguwar take da inuwowi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe shida (60 tayi to sai an haska fitila sabar duhu in dai ba farin wata ba.

Anguwace mai tarihin jama'a ko ta ina kaduba mutane ne kowa na uzirinsa. Akwai masu saida kayan makulace na yara da kuma sauran kayan marmari. Sai ga wata yarinyace tazo sanye da wata dogowar rigar fara amma ta koma baki dan datti, idan ka kaganta yarinyace kekkyawa amma dan kazanta sai tazama wani iri kamar ba ita ba zunzurutun datti.

Kuma ta na da gashi sosai dan kafin taga gabanta sai ta daga gashinta kamin tagani, kuma duk wanda yaganta sai ya tausayamata dan ita abin tausayine in ka ganta. Sai tana tafiya ta iso bakin wani shago tana kanlon shagon ta chikin gashinta, sai mai shagon ya daga kansa ya kalleta sai yaga wata gashinta yarufe fuskanta sai gabansa yafadi dan idan ka kalleta abin sorone.

Sai yace mata ke yarinya me kuma zan kara yi miki, jiya kinzo na baki nakoreki, gashi kuma yau kin kara zuwa uban me zan yimiki yau kuma in ji mai shagon kenan mai suna "Muktar" yake gayamata wa ita yarinyar a kofan shagonsa kennan. Sai ta dauka hannunta ta nuna mishi cikinta amma shi bai ganeba akan tana jin yunwa ba, daga baya sai wani yace masa ai tana jin yunwa ne, sai maishagon yace mata ki bar kofan shagona, ni na aifekine kunlum zaki zo mini shago kice kina jin yunwa. Sai yace mata bari kijirani ki gani sai yashiga shago ya dauki wata dori yace mata bari insameki kigani abin da zai faru dake.

Amma duk dahaka bata ji soron bulalan da ya dauka ba, tana kara cemasa tana nuna masa cikinta tana jin yunwa bata ji tsoronsaba duk da ya dauka bulala akan zai daketa. Sai yabude kofar shagonsa daya, sai yafito yafara yimata bulala"yace mata kin dauka bazan zanikiba ko, kunlum kina zuwa min shago kamar nine na haifeki" tun tana kuka a hankali har tafara yi da karfi, sai mutane na makwobta suka ji wata tana kuka sai hankalisu ya dawo gurin sai wasu daga ciki suka kwace bulala daga hannusa, sai wani dan saurayi daga ciki ya kwaceta yana lallashinta bai ji kiyamar jikinta ba yana cemata kiyi hakuri ko sannu baza mukara barinsa yadukekiba inji shi matashin da yajata daga hannunsa.

Sai daya daga cikin mutanen da suka karbeta yace a she kai mugun mutumne har ma yara kanana baka bari ba, sai yace ehh mana ban bariba wannan ma kadan kuka gani yace musu. Sai wani daya daga cikin mutanen su nansa Kamal, yace masa banza mugu kawai yarinya karama ba abin da tayimaka sai ga dinga dukanta dan ta cemaka tana jin yunwa kawai, sai yace ai gobe ma idan tazo sai nayimata fiye dahaka inji shi mai shagon kenan.

Sai shi mai suna Kamal yarike hannunta yatafi da ita gidansa sai yayi sallama matarsa tana shara sai ta amsa sallamar sai ta ganshi yashigo da wata yarinya, sai matarsa tace "Baby sannu" sai takara cemasa Baby Kamal wannan kuma daga ina take, sai yagaymata duk abin da yafaru sai matarsa Khadija tausayi yashiga ranta, sai ta ja ta jikinta ta ce mata kiyi shiru kinjiko ta goge mata hawayenta tana cemata karkiyi kuka kinji ba wanda zai kara dukanki kinji.

Sai tace mata me sunannaki bata ce ko mai ba sai kanlonsu da ido takeyi,sai matarsa Khadija anya Baby inaga wannan yarinyar fa kurma ce sai Kamal yace nima fa nayi tunanin haka, amma bari inje in sayamat kaya, gashi ko takalmi bata da shi zan saya gabaday sai kiyi kokari kiyi mata wanka ki bata abinci taci kamin indawo in ji mijinta Kamal kennen.

Sai inji matarsa tace to sai kadawo Baby? sai ta dauketa ta kaita bayan daki tayimata wanka, ta wanke mata kai ta goge mata jikinta sosai, sai tayi haske kamar ba ita ba. Amma sai da tayi amfani da ruwa bokiti uku kamin jikinta yayi haske zunzurutun datti. Bayan tagamata wanka sai ta dauki zaninta ta rufemata jikinta, ta zubamata abinci sai tafara cin abincin kamar tayi shekara goma bata ci abinciba.

Sai ga Kamal ya iso da sabon takalmi da riga makkew sai yace wa Khadija Gashi kisamata amma kar ki barta tafita waje bari inkoma shago inji Kamal wa Khadija kennan. Sai Kamal yana ta kallon yarinyar yace ashe wannan yarinyar tana da kew, ashe datti ne yaboyeta to!!! allah kabamu sa'a inji Kamal kennan ga matarsa Khadija tace sai kadawo Baby.

Sai Khadija ta shafamata mai na vasiline takuma ka mamata gashinta ta sa mata ribon sai tasayar da ita, ta kalleta sama da kasa. Sai Khadija tace kukalla yarinya kekkyawa kamar aljana sai tace bari insamiki janbaki, tamanta akan bata magan amma sai taji kamar tace ehh? sai tace dama kina jin maganane sai takara girgiza kai tana ta murmushin jindadin nafarinciki Kahdija tana ta mamaki.

Sai Khadija tafara tambayanta tace ina ne gidanku sai tayi shuru batace komai ba, takra ce mata ina iyayenki sai tafara kuka sai Khadija tace mata daga yau nazama mamanki sai ta girgiza kai sai Khadija ta rungumeta. Wato ita khadija allah bai taba bata aihuwaba sau biyu tana bari shiyasa son yara yashiga zuciyarta sosai na sonyara.

Sai Kamal yadawo gida sai yagansu suna wasa da Khadija sai yayi mamaki, sai Khadija ta bashi labarin duk abinda yafaru sai Kamal yace me sunnanki sai tayi shuru sai Khadija tace masa kamanta bata iya maganane, sai yace inji Khamal ko za mu fara kiranta da suna "Waleeda" sai inji Khadija tace sunnan yadace da ita sai tace mata kinyarda mu kiraki Waleeda nan take sai ta daga kai tace ehh?

Sai dare tayi sai Khadija ta Saka musu abinci suka ci tare da yarinyar bayan sungama sai suka shiga daki suna kallo tare da ita Waleeda sai barci ya kwashesu dare yayi anguwa yayi shuru ba kowa kuma baka jin kukan wani abu in ba na sunsayeba amma shi Muktar mai shagon da ya doki yarinya bai rufe shagonsa ba da shene yake tashi a baya kowa yarufe shagonsa amma bandashi.

Sai Muktar yana zaune a kofar shagonsa yana kokarin kirga kudin da yayi ciniki sai yaga wani abu yawuce da karfi ta kofar shagonsa sai ya daga kai dawuri bai ga komaiba sai yayi tunani akan kawai saurata ne yayi bakomai, sai yajiyo baya sai yakoma shago sai yaji kamar motsi a bayansa sai yajuya sai yaga wata tana zuwa a nisa da kaya fari a jikinta, yana kokarin sa ido yaga ko meye ne sai ta bace masa a idonsa juwowan da yayi sai yaga mace tana zaune a kan kujeransa da yatashi sai yaga wata karama yarinya tana kuka duk jikinta jini yana zuba kuma hakoranta yana zubar da jini sai yayi tunani wanna ba yarinyar da na yi mata dukaba sai ya ruga da gudu yanaso yasere sai yaganta a gabansa sai ya durkusa yana bata hakuri sai ta ketta ta tafi batayimasa komaiba amma yazama masa tari a rayuwarasa.


Wannan shine abinda yafaru da Muktar mai shago.


contact-form

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home