Magana Masu Dadi Wanda Zakayiwa Mace Tafara Sonka In Har Ka Iya....
Yada Zaka Sace Zuciyar Wadda Kake So Batare Da Kace Kana Sonta Ba, Zata Ji Ta Kamu Da Sonka.
Daya daga ciki shine karika bata dariya wanda har zai sa tayi hawaye dan dariya, wannan ma yana cikin daya da ga chikin wanda zai farantamata rai sosai, dan kasan mata suna son hiran soyaiya kuma ka nayin yabon wani abu a jikinta, kowani kwaliyan da tayi sai ka yaba mata da shi zata ji dadi kuma kunlum zata na nemanka dan kasata dariya ko ka yabe abinda tayi dan kasan mata suna son burgewa game dasu dan suna son suga anna yabonsu akan sunfi kowace mace a duniya ko dame, shiyasa yabon mace ta hanyar soyaiya yana sa mace ta soka har a jikinta.
Duk lokachinda kuka hada ido sai kayimata tattausan soyaiya da kuma mursa ido ta wajen rufe ido dan zata rika satan kanlonka kuma bazata iya juya kantaba kowane minti daya sai tajuya ta kalleka dan tagani ko zaka yimata abinda kakeyi dan tayi murmushi.
Kuma kana yin girmama iyayenta, kana yabon iyayenta kana tambayanta lafiyarsu dan zata yi tunani idan kun kasance tare ashe baza ka manta da iyayenta ba dan akunlum kana tambayan kaji lafiyarsu.
Kuma nana yabonta koda batayi abin yabo ba, kasan yabon mace a kunlum yana karamata kwarjini yasata kamar sai itane a duniya babu kamar ita.
Kuma karika yin kwalliya dan kasan idan kana kwalliya mekew mata zasu na ji a jikinsu, kasan mata idan suka ga namiji yayi kwalliya har zuchiyarsu zai sinke dan zaka shiga ranta chiki chiki sai tayi tunani inama kai kazama mijinta, shiya karika kwalliya dan kakara shiga ranta.
Karika yin tanadin kalmomi masu kew, kasan mata yin kalma masu kew zai sa kashiga zuchiyarta a lokaci kankani. Karika sa kayan kanshi kamar su turare dan kasan mata suna son kanshi sosai kuma duk inda taje in har taji kanshin turarenka a jikin wani a take zata tuna da kai, zata ji kamar kaine kusa da ita dan kanshin yashiga jikinta sosai, shiya kazama mai kanshi idan zaka je wurin budurwarka shima zai tai maka maka ka shiga ranta.
Kuma ka guji maganar wata a kusa da ita dan idan ta fara sonka zata fara tambayanka akan wane irin mace ne kake so, ko kuma wane irin kwaliya kake so matar ka tayi maka, to wannan allama ce ta fara sonka sai ka guji abu kamr su karya da sauransu a gabanta. Kuma zata tambayeka yaushe zaka yi aure ko kataba soyaiya ne duk wannan allamace ta nuna maka ta fara sonka sai kafara kulawa da ita a hankali har kasamu nasara.
Kuma idan tafara yimaka wanna tambayan to kace mata kana da wadda kakeso, sai kaduba fuskanta in kaga ta bata ranta, to allama ta fara soyaiya da kai sai kace mata ba wanda nakeso sai kai dan kafarantamata rai ta ji dadi.
Kuma ba wai dan tafara sonka ba sai ka yaudareta, duk wanda ya yau dare juma shima zai gani a gabansa.
contact-form
Labels: Hausa
1 Comments:
Yayi
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home