CUTUTTUKAN DA DUKKANIN
KAYAYYAKIN TABA KE JAWOWA
CIWON DAJI NA HUHU.
Masu shan taba na iya kamuwa da ciwon daji na huhu (9) har sau ashirin da biyu fiye da wadanda basu taba shan taba ba. Shan
taba shine babban dalilin kamuwa da ciwon daji na huhu, wanda ya kan haddasa kashi biyu bisa uku na mutuwa sakamakon
ciwon huhu a duniya, wannan kuma yana shafar kimanin mutane miliyan daya da dari biyu a kowace shekara.
Wadanda ba su taba shan taba ba, amma kuma suna shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a gida ko a wurin aiki suna cikin hadarin samun ciwon daji na huhu.
TOSHEWAR MANYAN HANYOYIN JINI MASU KAIWA GA HUHU
A duk mutum biyar da ke shan taba mutum ɗaya na iya samun matsananciyar cutar toshewar manyan hanyoyin jini masu kaiwa ga huhu (COPD) (10) a rayuwar sa, musamman ma mutanen da suka fara shan taba a lokacin yarinta da shekarunsu basu wuce ashirin ba, tun da yake hayakin na taba na jinkirta girma da ci gaban lafiyar
jiki.
Masu shan taba sun fi sauƙin kamuwa da cutar toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya har sau uku zuwa hudu. Shan taba yana haifar da kumburi da fashewar jakar iska a cikin huhu wanda ya kan rage karfin shakar iskar ‘oxygen’ da kuma damar fitar da iskar ‘carbon dioxide’.
Har ila yau, yana haifar da zaunewar majina wadda kuma kan sa tari mai zafi da kuma wahalar numfashi. Mutanen da su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa tun suna yara har suka girma suna dayawan kamuwa da cututtuka a hanyoyin numfashin su,a sakamakon haka kuma suna cikin hadarin samun toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya (COPD).
CUTAR ‘ASTHMA’
An san cewa shan taba na tayar da ciwon asthma ga mutanen da suka manyanta, wanda yakan ƙuntata musu, da kuma karawa rashin lafiya tsanani da kuma kara haɗarin cutar wanda yake buƙatar kulawa ta gaggawa. Yara‘yan makaranta da iyayen su ke shan taba suna da haɗarin shakar hayakin tabawanda ke zama musabbabin faruwar cutar asthma da kuma tsananin ciwon kumburi a hanyoyi da ke isar da iska zuwa ga huhu.
CUTUTTUKAN DA A KE SAMU
DAGA HAYAKIN TABA
Dukkan kayayyakin taba suna da illa, kuma babu wani matakin da zai iya nunawa rashin lahanin taba. Shan hayakin taba shi ne mafi yawadaga cikin hanyoyinamfani da taba a duniya baki daya. Sauran kayayyakin
cin taba sun hada da taba gari, da ganyes, da anguru, da sauransu wadanda a ke sanyawa a lofe da shishaa shata bututun ruwa, da sauran kayayyakin taba na zamani.
CIWON DAJI NA BAKI DA KUMA SAURAN
CUTUTTUKAN BAKI
Yin amfani da taba (ta hanyar shan hayakin ta ko wani nau’i na tabar) yana zama dalilin kamuwa da cututtukan baki da yawa. Dukkanin nau’ikan tabar su kan zama sanadin samun ciwon daji na baki (5). A kasashe da yawa, da wuya a rayu sama da shekaru biyar bayan gano cutar daji a baki. Wadanda ke warkewa daga ciwon daji na baki sukan sami lahani a fuska da kasa yin magana, ko haɗiya ko tauna wani abu. Yin amfani da taba yana kara haɗarin cutar dasashi, waccedasashi ke kumburasannan ya dauke ya kai ga kashin mukamuki har ya haifar da asarar hakori (6).
Shan taba da kuma amfani da kayan taba ba yana jirkita yanayin sinadaran da baki ke dauke da su, wanda ke sa makalewar bakin datti da sa hakora rawaya da kuma haddasa
mummunan numfashi.
CIWON DAJIN MAƘOGARO
Amfani da kayan taba tare da shan hayakin taba bayana kara haɗarin Ciwon daji na ka da wuya, wannan ya hada da lebe da kuma cikin baki. Cire ciwon na buƙatar aiki na musamman (7), yadda za a huda rami awuya yadda za a sami damar yin numfashi.Yin amfani da hasken na’ura wajen kawar da ciwon yana da illa kwarai wajen lalata harshe har ya kasha dandano, da rage yawan gudanar yawun baki da kuma kara samar da majina a makogoro, wanda zai sa ciwo da kuma wahala wajen cin abinci.
SAURAN CUTUTTUKAN DAJI
Yin amfani da taba ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’iuka goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba da a ke kaiwa ga jiki. Daga yawancin sinadaranna taba, akalla nau’ika saba’in an gano sunahaddasa cutar daji. Masu shan taba suna cikin haɗari mafi girma na samun cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci (8a); da hanji (8b), da koda (8c), da hanta, da matsarmama (8d), da ciki (8e) ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayayen haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna alakar shan taba da kumakaruwar hadarin samun ciwon daji na nono (8f),musamman ma mata masu shan taba da suka fara shan taba kafin su fara daukar ciki.
Haka kuma shan taba na kara hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan (8g) da ke fama da cutar da kananan kwayoyin cututtuka ke haifarwa. Haɗarin waɗannan cututtuka na yawan ƙaruwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da a ka yi a na sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai masu guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wanda ke haifar da ciwon daji na cikin baki da makogoro da kuma matsarmama. Ci gaba da yin amfani da taba bayan an ganociwon daji yana kara tsananta cutar, saboda da hayakintaba na iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarda ga maganin ciwon daji; da kuma ƙara yawan matsalolin maganin.
MUTUWAR DAN TAYIN CIKI
Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin taba a lokacin daukar ciki na ƙara haɗarin mutuwar dan tayin ciki. Mata da suke shan taba ko kuma ke shakar hayaƙin taba lokacin da suke renon ciki suna cikin haɗarin zubewar cikin. Zubewar ciki (haihuwar tayin da ya mutu a cikin mahaifa) na faruwa a lokuta da yawa a sakamakon rashin isasshiyar ‘oxygen’ da rashin dai-daiton mahaifa wanda iskar ‘carbon monoxide’ke haifarwa daga hayakin taba da sinadarin ‘nicotine’dake cikin taba. Masu shan taba suna cikin haɗarinsamun ciki a wajen mahaifa, mai mummunan haɗari ga mahaifiya, a nan yayin da ta ke reon cikin ya kan makale a wajen mahaifa.
Saboda da haka, daina shan taba da kuma samun kariya daga shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa yana da mahimmanci ga mata masu haifuwa, ko kuma masu shirin daukai ciki da kuma yayin renon cikin.
HANA GIRMAN DAN TAYIN DA KE CIKI.
DA HAIHUWAR DA MARA CIKAKKEN NAUYI DA HAIHUWAR DAN DA BAI CIKA WATA TARA BA
Duk wani nau’i na amfani da taba ko kuma shiga cikin hayakin taba yayinrenon ciki zai iya zama abu mai illa ga lafiya da kuma girman dan tayin yaron da ke ciki. Yaran da aka haifa ga matan da suke shan taba, ko yin amfani da taba gari, ko kuma su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a lokacin da suke renon ciki suna da haɗarin haihuwar bakwaini da kuma haihuwar yaron da nauyin sa bai cika ba. Yaran da aka haife su a bakwaini da kuma wadanda nauyin su bai cika ba na iya samun matsalolin rashi lafiyana tsawon rayuwar su, ciki har da samun cututtuka masu tsanani bayan sun girma.
CUTUTTUKAN DA A KE SAMU
DAGA HAYAKIN TABA
CIWON DAJI NA HUHU
Masu shan taba na iya kamuwa da ciwon daji na huhu (9) har sau ashirin da biyu fiye da wadanda basu taba shan taba ba. Shan taba shine babban dalilin kamuwa da ciwon daji na huhu, wanda ya kan haddasa kashi biyu bisa uku na mutuwa sakamakon ciwon huhu a duniya, wannan kuma yana shafar kimanin mutane miliyan daya da dari biyu a kowace shekara. Wadanda ba su taba shan taba ba, amma kuma suna shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a gida ko a wurin aiki suna cikin hadarin samun ciwon daji na huhu.
TOSHEWAR MANYAN HANYOYIN JINI MASU KAIWA GA HUHU
A duk mutum biyar da ke shan taba mutum ɗaya na iya samun matsananciyar cutar toshewar manyan hanyoyin jini masu kaiwa ga huhu (COPD) (10) a rayuwar sa, musamman ma mutanen da suka fara shan taba a lokacin yarinta da shekarunsu basu wuce ashirin ba, tun da yake hayakin na taba na jinkirta girma da ci gaban lafiyar jiki. Masu shan taba sun fi sauƙin kamuwa da cutar toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya har sau uku zuwa hudu. Shan taba yana haifar da kumburi da fashewar jakar iska a cikin huhu wanda ya kan rage karfin
shakar iskar ‘oxygen’ da kuma damar fitar da iskar ‘carbon dioxide’. Har ila yau, yana haifar da zaunewar majina wadda kuma kan sa tari mai zafi da kuma wahalar numfashi. Mutanen da su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa tun suna yara har suka girma suna da yawan kamuwa da cututtuka a hanyoyin numfashin su,a sakamakon haka kuma suna cikin hadarin samun toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya (COPD).
CUTAR ‘ASTHMA’
An san cewa shan taba na tayar da ciwon asthma ga mutanen da suka manyanta, wanda yakan ƙuntata musu, da kuma karawa rashin lafiya tsanani da kuma kara haɗarin cutar wanda yake buƙatar kulawa ta gaggawa. Yara‘yan makaranta da iyayen su ke shan taba suna da haɗarin shakar hayakin tabawanda ke zama musabbabin faruwar cutar asthma da kuma tsananin ciwon kumburi a hanyoyi da ke isar da iska zuwa ga huhu.
CUTUTTUKAN DA A KE SAMU
DAGA HAYAKIN TABA
Dukkan kayayyakin taba suna da illa, kuma babu wani matakin da zai iya nunawa rashin lahanin taba. Shan hayakin taba shi ne mafi yawadaga cikin hanyoyinamfani da taba a duniya baki daya. Sauran kayayyakin
cin taba sun hada da taba gari, da ganyes, da anguru, da sauransu wadanda a ke sanyawa a lofe da shishaa shata bututun ruwa, da sauran kayayyakin taba na zamani.
CIWON DAJI NA BAKI DA KUMA SAURAN
CUTUTTUKAN BAKI
Yin amfani da taba (ta hanyar shan hayakin ta ko wani nau’i na tabar) yana zama dalilin kamuwa da cututtukan baki da yawa. Dukkanin nau’ikan tabar su kan zama sanadin samun ciwon daji na baki (5). A kasashe da yawa, da wuya a rayu sama da shekaru biyar bayan gano cutar daji a baki. Wadanda ke warkewa daga ciwon daji na
baki sukan sami lahani a fuska da kasa yin magana, ko haɗiya ko tauna wani abu.
Yin amfani da taba yana kara haɗarin cutar dasashi, waccedasashi ke kumburasannan ya dauke ya kai ga kashin mukamuki har ya haifar da asarar hakori (6). SShan taba da kuma amfani da kayan taba ba yana jirkita yanayin sinadaran da baki ke dauke da su, wanda ke sa makalewar bakin datti da sa hakora rawaya da kuma haddasa mummunan numfashi.
CIWON DAJIN MAƘOGARO
Amfani da kayan taba tare da shan hayakin taba bayana kara haɗarin Ciwon daji na ka da wuya, wannan ya hada da lebe da kuma cikin baki. Cire ciwon na buƙatar aiki na musamman (7), yadda za a huda rami awuya yadda za a sami damar yin numfashi.Yin amfani da hasken na’ura wajen kawar da ciwon yana da illa kwarai wajen lalata harshe har ya kasha dandano, da rage yawan gudanar yawun baki da kuma kara samar da majina a makogoro, wanda zai sa ciwo da kuma wahala wajen cin abinci.
SAURAN CUTUTTUKAN DAJI
Yin amfani da taba ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’iuka goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba da a ke kaiwa ga jiki. Daga yawancin sinadaranna taba, akalla nau’ika saba’in an gano sunahaddasa cutar daji. Masu shan taba suna cikin haɗari mafi girma na samun cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci (8a); da hanji (8b), da koda (8c), da hanta, da matsarmama (8d), da ciki (8e) ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayayen haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna alakar shan taba da kuma karuwar hadarin samun ciwon daji na nono (8f), musamman ma mata masu shan taba da suka fara shan taba kafin su fara daukar ciki.
Haka kuma shan taba na kara hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan (8g) da ke fama da cutar da kananan kwayoyin cututtuka ke haifarwa. Haɗarin waɗannan cututtuka na yawan ƙaruwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da aka yi a na sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai masu guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wanda ke haifar da ciwon daji na cikin baki da makogoro da kuma matsarmama. Ci gaba da yin amfani da taba bayan an ganociwon daji yana kara tsananta cutar, saboda da hayakintaba na iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarda ga maganin ciwon daji; da kuma ƙara yawan matsalolin maganin.
MUTUWAR DAN TAYIN CIKI
Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin taba a lokacin daukar ciki na ƙara haɗarin mutuwar dan tayin ciki. Mata da suke shan taba ko kuma ke shakar hayaƙin taba lokacin da suke renon ciki suna cikin haɗarin zubewar cikin. Zubewar ciki (haihuwar tayin da ya mutu a cikin mahaifa) na faruwa a lokuta da yawa a sakamakon rashin isasshiyar ‘oxygen’ da rashin dai-daiton mahaifa wanda iskar ‘carbon monoxide’ke haifarwa daga hayakin taba da sinadarin ‘nicotine’dake cikin taba.cikin.
HANA GIRMAN DAN TAYIN DA KE CIKI.
DA HAIHUWAR DA MARA CIKAKKEN NAUYI DA HAIHUWAR DAN DA BAI CIKA WATA TARA BA
Duk wani nau’i na amfani da taba ko kuma shiga cikin hayakin taba yayinrenon ciki zai iya zama abu mai illa ga lafiya da kuma girman dan tayin yaron da ke ciki. Yaran da aka haifa ga matan da suke shan taba, ko yin amfani da taba gari, ko kuma su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a lokacin da suke renon ciki suna da haɗarin haihuwar bakwaini da kuma haihuwar yaron da nauyin sa bai cika ba. Yaran da aka haife su a bakwaini da kuma wadanda nauyin su bai cika ba na iya samun matsalolin rashi lafiyana tsawon rayuwar su, ciki har da samun cututtuka masu tsanani bayan sun girma.
KARANCIN TUNANI/MANTUWA
Shan taba abu ne mai haɗarin lalata kwakwalwa, wanda wani rukuni na cututtuka ne wanda kan haifar da karancin tunanin mutum wanda kuma bashi da magani tabbatacce a halin yanzu. Karancin tunanin abu ne da ya ke habaka, ya kan shafi ƙwaƙwalwar mutum, da halayyar mutum da kuma ƙwarewa da tsayawa ga ayyukan yau da kullum. Baya ga abin da wannan ciwo ke haifarwa wajen hana mutum zarafin aiyuka, cutar zata iya zama mai nauyi kwarai ga iyali ko masu kulawa da mai cutar. Cutar ‘Alzheimer’mafi yawa a cikin irin wannan cututtuka, kuma an kiyasta kimanin kashi goma sha huhu (14) cikin dari (100) na cutar a duniya na da alaka da shan taba.
RAUNIN MAZAKUTA
Shan taba yana hanaisasshen jini zuwa azzakari, wanda zai iya haifar da rashin ƙarfin mazakuta (rashin yiwuwar mikewar azzakari). Raunin mazakutayafi yawa a cikin mashaya taba kuma mai yiwuwa ya ci gaba ko zama dindindin sai dai idan mutumin ya daina shan taba a farkon rayuwarsa.
MUTUWAR JARIRAI FARAT-DAYA
Mutuwar jarirai farat-daya (SIDS) ita ce mai faruwa kwatsam, ba tare da wani dalili da a ke iya gani baga yara‘yan kasa da shekara 1.
An san cewa shan taba yayin goyon ciki naƙara haɗarin mutuwar farat-daya ga yara, kuma haɗarin ya kan ƙara karuwa tare da bin ‘ya’yan da suka Haifa,kuma suka ci gaba da shan taba bayan haihuwar.
JININ HAILA/WATA DA YANKEWAR HAIHUWA
Mata masu shan taba zasu iya jinin haila/wata mai ciwo da zafi da kuma samunalamomin yankewar haihuwa. Yankewar haihuwa kan faru cikin shekara daya (1) zuwa hudu (4) ga mata masu shan taba, kasa da lokacin da a ka sani saboda shan taba yana rage damar samar da kwan haihuwana mace, wanda ya kan haifar da rashin samun damar haihuwa da kuma karancin rowan halittar ‘estrogen’.
HAIHUWAR YARA MASU LAHANIN HALITTA
Shan taba na iya lalata kwayar halittatare da lalata kwayar halitta ta gado (DNA), wanda kan haifar da lahani ga halittar jariri. Awasu binciken ilimi angano cewa mutanen dasuke shan taba suna da haɗarin haihuwar yaron\ wanda ke iya kamuwa da ciwon daji. Shan taba ga mace a farkon lokacin da ta ke renon ciki na ƙara da hadarin haihuwar jariri mai yankakken lebe ko baki. An kuma lura cewa mutanen da iyayensu suka sha taba alokacin renonciki suna da ƙarancin yawan kwayar halitta fiye da maza waɗanda iyayensu ba su taba shan taba ba.
RASHIN GANI
Shan taba yana haifar da cututtukan ido da yawa, waɗanda idan ba a yi maganin su ba, za su iya haifar da rashin iya hangen nesa. Masu shan taba suna da alaƙa da lalacewar ‘macular’ fiye da wadanda ba su taba shan taba ba, wanda yanayine da zai haifar da rashin hangen nesa. Lalacewar ‘macular’ ya kan shafi yawancin mutane,ya hana karatu, ko tukin mota, da gane fuskoki da launuka da kuma ganin abubuwa yadda su ke. Har ila yau masu shan taba suna da haɗarin samun cutar yanar ido wanda ke kare haske ko gani. Yanar ido (11) na iya haifar da rashin hangen nesa, kuma yin tiyata ne kawai zaɓi don mayar da gani yadda yake. Sababbin hujjoji sun nuna cewa shan taba yana haifar da hawan jinin ido, yanayin da zai kara yawan matsina lamba a idanu kuma zai iya lalata gani. Shan taba na sa radadi a idanu da kuma kara zafin cututtukan idanuga masu shan taba da masu shakar hayaƙinda masu shan tabe ke fitarwa, musamman ma a tsakanin waɗanda suke ɗauketubaran gani na cikin ido.
RASHIN JI/KURUMCEWA
Iyayen da su ke shan taba kan samu yara ‘yan kasa da shekaru biyu masu fama da ciwon kunne wanda ruwa ke zuba daga cikin kunne, Sakamakon shakar hayakin tabar da iyayen su ke sha a gida. Matsanancin ciwon kunne (tsakiyar kunne) ga yara shine dalilin da ya kan sa a sami bebantaka (12) da kurumta. Manyan mutane masu shan taba sun fi fama da rashin ji saboda tsawon lokacin da su ka yi suna shan taba na hana zagayawar jini cikin kunne. Rashin magance ciwon rashin ji ko kurumtana iya tasiri a zamantakewar jama’a, da tunani da kuma tattalin arziki.
RAUNIN KASHI
Iskar ‘Carbon monoxide’ da ke cikin hayakin taba, babbar guba ce irin wacce a ke samu a hayakin mota, ta kan danfarazuwa ga ‘hemoglobin’na cikin jini cikin sauƙi fiye da iskar ‘oxygen’ da jiki ke bukata, don haka sai ta rage zuwan iskar oxygen zuwa jikin mutum. Masu shan taba sun fi saukin samun raunin kashi, yadda karfin kashin ke raguwa da sauƙin karyewa.Idankuma suka fuskanci matsalolin a kashi,akwai jinjiri ko rashinsamun nasarar warkewa.
LALACEWAR FATAR JIKI
Shan taba na kara yawan hadarin samun cututtukan fata na‘psoriasis’ (13), wanda wani mummunan yanayine da ke sa kumburi da dashewar fatata dashe ya bar wani ja a dukkanin jiki. Shan taba yana sa fata ta tsufa da wuri wajen sa sinadarai wanda su ke ba fata da laushi suragutare da daukewar ‘vitamin A’ da kuma hana zagayawar jini. Don haka masu shan taba suna iya samun bushewar fata (14), bayan nan kuma ta yankwane, musamman a kusa da lebe da idanu.
KAYAYYAKIN HAYAKIN TABA
Sune duk wani nau’i da aka yi ko aka samo shi daga taba ta hanyar konawa. Misalai sun hada da taba cigari, da kulli, da babbar taba,
da lofe, da shisha (wanda a ke sha ta bututun ruwa), da sauransu.
kAYAN TABA BA NA HAYAKI BA
Kowane samfurin taba da ya kunshi yankakke ko dakakken ganye, ko garin taba, da nufin sa shi baki ko hanci. Misalai sun hada da snuff, shan taba fure, gutka, mishri da snus.
SHAKAT HAYAKIN DA MAI SHANTABA KE FITARWA
Haɗuwa da hayakin taba wanda ya fito daga baki ko hancin mai shan taba da kuma hayakin»gefe» wadansa suka shiga cikin yanayin muhalli daga ci masushan taba da sauran kayayyakin taba. Hakanan ana amfani da kalmomin “shan tabar daga bayan fage» ko «shan taba ba niyya» duk a na amfani da wadannan domin yin bayanin shan ‘SHS.
contact-form
Labels: Hausa