Ko Meyasa Auran Yarinya a Maiduguri Jahar Borno Yana Da Wahala Ta Wajen Biyan SADAKI - Daga GONI GABCHIA
Assallamu allaikum warahmatulla ta'ala wabarkatuhu.
Muna sone muyibayani game da sa'insa da akeyi game da auren yar MAIDUGURI dake hajar BORNO. Mutane da dama da samarai suna magana game da al'adar Maiduguri ta wajen yin aure yana da SADA sosai ta wajen biyan SADAKIN mace.
Samarai na wasu jahohin ketare suna son auren yarinya MAIDUGURI amma dalilin yawan SADAKINSU yakan karyamusu gwiwa dan kudin yayi yawa.
Sadakin mace a Maiduguri a kalla yakan kai naira sama da Dubu Daribiyu (200,000) sadaki kawai banda wasu abubuwanda zai kara biya kamar su kudin TURAREN WUTA da sauransu.
Mun tuntubi wani bawan Allah mai suna GONI GABCHIA mazaunin cikin Maiduguri game da yawan kudin sadaki da ake biya a Maiduguri sai yayi mana Karin bayani yace.
Sadaki na aure a Maiduguri yana da sada sosai bisa yadda aka mayer dashi al'ada har yazama jiki ga duk dan mazaunin garin. Yakara da cewa yau shekara uku 3 da yin auren sa yabiya SADAKI naira dubu daribiyu da tamanin (280,000) banda kudin su turaren wuta da kudin toshi.
GONI GABCHIA yakara cewa duk wani da zai zo ya auri yarinya a Maiduguri koda yana da kudi sai abin ya bashi mamaki sosai bisa abubuwanda za a lisafamasa. Amma kowa yasani har idan akayi wannan auren aka kawo masa matarsa zuwa gida to daga nan ne zai sani kudin da yakashe an dawomasa dashi gidansa.
Munkara tambayan shi GONI GABCHIA ko zai karamana bayani game da yace andawomasa da kudinsa gida.
Nafarko shine ace yabiya kudin sadakinsa naira dubu dari uku( 300,000) banda kudin toshi da kudin turaren wuta. Kudin turaren wuta ace misali yabiya naira dubu Hamsin(50,000) kudin toshi naira dubu talatin (30,000) to wannan kudin sadakinsa za a cire kadan a ciki a kara akan kudin turaren wuta sai a hada mata kayan kanshi kalla kalla zuwa gidanta.
Mun kara tuntubi wata baiwar Allah mai suna YANA BAKURA ita ma mazaunin cikin Maiduguri ce Dan tayimana Karin bayani game da wane ado ne da yanayin kayan kanshin da ake yiwa yarinya in za a aurar da ita.
YANA BAKURA ta ce, mu a Maiduguri aurenmu yana da SADA sosai amma mu mutanen cikin garin na mu BORNO munsaba da wannan al'adar, dalilinda yasa nagaya maka hakan shine tambayan da kayi ta wajen kayan kanshi.
YANA takaracewa muna hada wa amarya turare kalla kalla kamar su....?
- Turaren wanka
- Turaren gasa jiki
- Turaren gasa gabar mace
- Turaren wanke bayan daki (bayangida)
- Turaren wanke baki
- Turaren Ango
- Turaren sawa kayanki da na angon ki
- Da Turaren sawa dakinki.
YANA takaracewa wannan turaren da na lisafamaka har idan za ayi maka number (1) wato original nashi akkalla zai ci kudi kusan naira dubu dari da hamsin (150,000) ko zuwa sama da haka, shiyasa wasu suna cewa sadakin aure a Maiduguri yana da sada sosai, kuma a kawai DILKI da za a yimata shima kalla kalla ne bisa ga yanayin karfin iyayenta wani kuma angon ne zai biyamata kudin DILKI har idan anyimata mai sadan zata dauki tsawon wattanni jikinta sai haske yakeyi kamar tashafa mai.
Labels: Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home