Wednesday, January 19, 2022

Auren Wata Daya 4 to 7



Auren Wata Daya

Page 4

CIGABA DA KARANTAWA


Khairat da maryam suna isa gida suka iske momy a parlour harta tashi daga bacci tana waya da dady akan kayan furniture daya tura akawowa khairat daga Dubai. Sallama sukayi khairat taje ta zauna a kasa kusa momcy ta dora kanta kan cinyarta tana fadin momy wallahi duk nagaji.
 
Katse wayar momy tayi tana shafa kanta tana fadin '' kedai khairat raguwace me kikayi da har zaisa ki gaji. Momy da kaina nayi driving fah ta fada kamar mai shirin kuka. Maryam ce ta katsesu tana gaishe da momy amsawa tayi cikin sakin fuska tana fadin ai dama tunda naji khairat shuru nasan gidanku ta biya domin nasan inda na aiketa ya isa ace ta dawo.

Momy kema kinsan in bataje ta kwasoni ba baxataji dadi ba ta fada tana dariya. Sallamar su sageer da rahama ne suka katsesu sun dawo daga school, rahama ta taho da gudu zata fada jikin momy khairat tayi saurin kaucewa karta fado kanta tana fadin ''Kekuma haka akeyi kawai ki wani kwaso aguje kina shirin buge mutane ta fada ta galla mata harara Maryam ce tace Haba khairat ai kema kinsan wajen tane tunda itace auta ba kema.

Fada matadai momy tace tana kollon autar tata data fara digar da kwalla tace. Sorry autata waya tabamin ke ne. Khairat bata jira amsarsuba ta miki taja hannun khairat suka wuce dakinta. 
Suna shiga toilet suka nufa sukayi alwala sukayi sallah, suna idar wa khairat tajawo wayart tana fadin barina kira Aisha yau kwana biyu kenan batazoba kuma bata kirani ba.

























wata kila kin mata laifine maryam ta fada tana kokarin cire hijab dinda tayi sallah. Ringing 2 Aisha ta amsa wayar khairat cike da shagawaba take fadin haba sis dama zaki iya 2 days batareda kinji lafiya ta ko kin ganniba, kwafa Aisha tayi tace ''Eh mana tunda gashi kema tunda akasa bikinku da yaya kika daina zuwa wajena ko wajan hajiya ma bakya zuwa.

Haba sis kema kinsan haka kurum bazanki xuwaba wallahi kunyar hajiya nakeji. Daga maryam har Aisha dariya sukayi Aisha tace ''Chab khairat yau kece kike kunyar hajiya, Eh mana wallahi banaso mu hada ido da ita dan Allah kiyi hakuri gobe kizo kinji, toh Allah ya kaimu wai ina maryam ne mun kwana 2 bamuyi waya da ita ba, wallahi gatanan tana jinki khairat ta fada tana mikawa maryam wayar. Suna gama wayar suka zauna suka fara tsara yadda komai nasu zai wakana batareda ansamu matsala ba, sai wajan karfe 5:00 khairat ta raka maryam gida.

Page 5


Shirye shirye biki ake ta kowana bangare inda ta kama yau ne za'ayi kamu, tun ranar da sadeeq yazo ya sanarwa khairat cewa auran wata daya ne zai kasance a tsakanin su bata sake sashi a idonta ba duk abunda suke bukata maryam ce mai kiransa a waya ta sanar mai, amma ko sau daya bai taba tako kafarsa yazoba sai dai ya turo musu abokinsa Abdul yakawo musu sakon, bai ragesu da komai ba duk abunda sukace suna bukata toh saiya aiko musu fiye da yadda suka bukata.

Khairat kuwa kullum cikin zullumi take gashi wani mugu mugun son sadeeq ne ke kara ninkuwa a cikin zuciyarta kullum cikin sallah da addu'oi take babu kakkautawa gawata muguwar rama datayi kowa yaganta saiyayi maganar ramar tata. Ta bangaran momy kuwa itama ta dage tana mika kukanta ga Allah akan lamarin diyar tata duk batasan halin da ake ciki ba amma tasan sadeeq baya son khairat kawai biyayya zaiyi.

Ta bangaran sadeeq kuwa bashi da wata damuwa shirye shiryan sa kawai yakeyi yana nunawa su dady cewar tana mutuwar son khairat domin bayaso asamu matsala idan ya tashi gabatar da shirin sa. 
Anyi kamu sosai lrin namasu hannu da shuni inda amarya tayi matukar kyau aka cashe sosai Sannan amarya tasha nasiha mai ratsa jiki awajan kamun nata daya samu halartar manya malamai mata.
























Lokacin da kowa ya watse daki khairat tashiga kawai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita domin tasan kwana 2 ya rage tashiga wata sabuwar rayuwa mai wuyar fassarawa domin batasan mai zataje ta tadda a gidan masoyin nata ba wanda ita takasance abar kyama a gareshi. Rahama ce ta shigo dakin da tadda aunty nata nata kuka, karasawa kusa da ita tayi tace Aunty waya dakeki kikeyin kuka.

Sai a lokacin tasan da shigowar rahama dakin tayi saurin goge hawayenta tana fadin babu komai auta kinji gashin idon danasa ne ya shige min ido yake zafi amma karki fadawa momy tunda kinga bataso amma naje na sanya. Toh aunty bazan fada mata ba amma kema kicireshi toh tunda yana saki kuka.

Shikenan tashi kije autar mom yanzu zan cire kinji. Tashi tayi ta fita itakuma khairat tashiga toilet ta gyara face dinta domin bataso Aisha da maryam su fahimci tayi kuka saboda yanzu sun dawo gidan da zama zuwa lokacin gama bikin.

Washe garin ne yakama ranar party tun la'asar aka farawa amarya kwalliya saida suka dau sama da 2hrs ana kwalliya saida khairat tayi kamar ba itaba duk wanda yaganta saiya yaba domin khairat badai kyau ba ita kanta data kalli kanta a mudubi godiya kawai take mikawa ga ubangiji domin it's kanta tasan ita kyakkyawa ce.

Iya kodawa maryam da Aisha sun kodata domin suma ba'a barsu a bayaba kaya iri daya suka sanya da maryam da Aisha sai rahama da sukayi iri daya da ita Sannan suka Hana kowa tafiya da ita tana makale dasu. Saida kowa ya tafi Sannan sadeeq ya turo da mota a dauko su khairat, momy na ganinsu tace masha Allah gaskiya diyata kinyi kyau murmushi kawai tayi sai rahama datace Mom nifa bakice nayi kyauba Ah ai dukanku kunyi kyau auta kuje ana jiranku na tsai daku.

Suna isa wajan su maryam suka fito da khairat suka kaita wajan zamanta aka fara gabatar da abinda ya kaisu. Saida akadau wajan 30mins Sannan sadeeq da abokinsa Abdul suka iso tunda yazo wajan yake kallon khairat aransa yana cewa Dama haka yarinyar nan takeda kyau gaskiya Allah yayi halitta awajannan.

Tana kula da yadda yake satar kallon ta murmushi kawai tayi aranta tace ko babu komai yau nayi abunda ya burgeka. Sai wajan 11:00 suka dawo gida duk sun gaji sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta domin gobe su tashi da wuri domin shirin daurin aure.

Page 6


Washe gare kowane bangare suka tashi da shirye shirye daurin aure inda yan uwan momy dake gombe suma sun samu damar isowa. Hajiyar su maryam ma tun safe ta shigo ake hidimar da ita. Amarya kuwa da manyan aminan nata ansha kwalliya kamar basuba can sasan dady momy ta kaisu saboda nan jama'a sunyi yawa domin sugama shirye shiryensu.

Karfe 11:00am dai dai Dubin al'umma suka shaida auran ABUBAKAR MUKTHAR (sadeeq) DA KHADEEJAH KABEER (khairat)

Daurin auren daya samu halartar manyan mutane daga wurare da dama. Khairat najiyo gudar mutane awaje sun nufo sashen dady taji gabanta yafar faduwa hawaye ne kawai suka fara bin kuncinta Aisha ce ta kula da hakan tayi hanzarin sanya hannu tana goge mata tana fadin sister karki bani kunya kinga mutane sun fara tahowa nan ki daure ki hadiye duk abinda kikeji.

Toh kawai tace ta sanya hannu tafara goge hawayen nata, kanwar momy ce dasukazo daga gombe mai suna hajara ta shigo tana fadin ina amaryar take musa mata Albarka. 
Boye fuskata tafara yi hajara tace Ashe dai diyar tawa akwai kunya ina fatan dai kunci abinci? Aisha ce ta bata amsa da basuci ba, tace bari tasa akawo musu.

Karfe 5:00 dai aka mika Aisha wajan dadi yayi mata nasiha sosai mai ratsa zuciya tunda yafara khairat ke kuka babu kakkautawa shi kanshi dady daurewa yayi ji yake kamar shima yayi kukan saboda yana matukar son khairat.

Ana fito da ita daga gidan dady aka wuce da ita bangaran momy itama nasiha tayi mata sosai harda hawaye da kyar hajara ta lallashesu sukayi shiru Sannan hajara tace ya kamata a fara kaita wajan su hajiya zainab (mahaifiyar sadeeq) dakuma dady saboda suma iyaye ne. Haka kuwa akayi saida aka fara kaita nan suka yimata nasiha Sannan aka wuce da ita gidan ta dake nasarawa.

A hankali kowa ya watse daga maryam sai Aisha suna zaune babu wanda ke iya furta komai a tsakaninsu kusan 30mins kenan duna zaune haka sukaji alamun tsayiwar motar su sadeeq bayan kamar minti 5 sukaji motsinsu a parlourn dake kasa. Maryam ce tafara tashi tadau Jakarta da mayafinta sai Aisha itama ta tashi bude idanu khairat tayi tace Me kuke nufi.

Aisha ce tayi kokarin bata amsa tafiya zamuyi mana Haba sister karkuyimin haka dan Allah kuzauna karku tafi kunji Hawaye kawai maryam taji yafara zubo mata tayi saurin juyawa tana fadin sister mun wuce mudai sai da safe zamu leko miki takarasa ficewa tana zubarda hawaye domin sun shaku da khairat sosai.



























Kuka tafarayi tana fadin sister ki tsaidata dan Allah karku tafi khairat tafiya tazama dole kiyi hakuri kinji da safe zamu dawo da kyar ta lallabata tasamu ta sakko. A parlour ta riske Aisha da sadeeq da abokinsa Abdul suna sallama tare suka fita da Abdul zai saukesu a gida. Suna fita sadeeq ya rufe ko ina na gidan ya nufi steps din.

Page 7


Yana hawa saman koh kofar dakin khairat bai kallaba ya wuce dakinsa yasaka key ya rufe yanufi toilet. Tanajin wucewarsa da rufe kofar takuma fashewa da wani sabon kukan tana nadamar auran sadeeq tana ayyana abubuwa da dama a ranta.

Yanzu da ace wanda yakesonta ta aura da yanzu yanan yanata rawar kafa akanta amma gashi wai itace aka kawota gidan miji a daransu na farko ko waiwayata baiyiba kuka taci gaba dayi babu kakkautawa saida taji kanta kamar zai fashe Sannan ta tashi tajawo wayarta ta duba agogo karfe 12:30 abin yabata mamaki shabi yanzu harda rabi gaskiya ta dade a zaune awajan, babu shiri ta sauko daga kan gadon taje ta cire kayanta ta nufi toilet wanka tayi sannan tai alwala.

Tana fitowa taje ta daukarfe guwar riga ta sanya ta sanya hijab ko mai bata shafaba ta shin fida dadduma tafara sallah. Ita kanta batasan adadin raka'a nawa tayiba ta zauna tana hawaye tana mika kukan ra ga Allah ahaka har bacci ya kwasheta a kan daddumar.

Karar bude kofar sadeeq zai tafi masallaci ne ya tasheta ta bude idonta taji ana kiraye kirayen sallah mikewa tayi tana salati tanufi toilet tayi alwala sannan tayi sallah tana lazmi taji shigowarsa ya wuce dakinsa hawaye takumji sunbiyo fuskarta ta sanya hannunta ta goge. Tana kammalawa ta tashi ta koma gadon ta kita bata jimaba bacci ya dauketa.

Misalin karfe 10:00 dai dai ta farka tana salati dataga rana ta hasketa mikewa tayi ta nufi toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin atamfar ta wacce akayiwa dikin riga da zani ta daura dan kwali batayi wani kwalliyaba powder kawai ta shafa sai white lipsticks ta dubu madubi taga tayi kyau sosai domin khairat irin kyawawan nan ne ga diri gashi Allah yabata gashi domin tabiyo mahaifiyar tane wato Fulani.

Idonta ta kalla taga sun sauya alamar tasha kuka daran jiya kwalli ta dauka ta sanya ta sauko parlour na kasa. Yana zaune akan kujera ya lumshe idanunsa amma ba bacci yakeba ga TV ya kunna amma kuma ba kallo yakeba alamun tafiya yaji ya bude idanunsa a hankali yana ganinta yayi saurin maida kansa gefe.

Taji gabanta ya fadi datayi tazali dashi a parllour domin batayi tunanin yana gidan bama, karasawa tayi kusa da shi ta tsugunna tace Yaya ina kwana. Sai da yayi kamar bazai amsaba sannan ya bude idanunsa ya zuba mata ido tayi saurin kauda kanta sannan yace lafiya qalau Tashi tayi ta nufi inda take tunanin nanne kitchen.

Ina zaki ya fada yanabin inda ta nufa da idanu, kitchen zan shiga nayimana breakfast Kallonta yayi up and down yace ni bana bukata kawai ki dafa ke kadai, toh kawai tace ta wuce abinta. Tea ta fara tafasawa sannan ta soya kwai ta dauki bride data gani acikin kitchen din ta fito parlourn da nufin komawa dakinta taci acan. Ina zaki taji ya fada amma ko kallonta baiyiba, zanje daki naci abinci ne ta fada kamar zatayi kuka. Tsaki kawai yayi yace dawo nan kici inaso zamuyi magana.

Dawowa tayi ta zauna tana goge hawayen daya fara zubo mata. Tsaki yakuma yi yace aikin banza ko mai mutum zai da raguwar macema oho daga magana sai kuka wai ita yar shagwaba. Ko kallonsa batayiba ta cigaba da kallon kasa kawai. Au bazakici abin cin ba saikin batamin lokaci ina jiranki. babu musu tasanya hannu tafara ci tana kammalawa ta miki taje kitchen ta wanke kayan ta maidasu ma'ajiyarsu sannan tadawo parlour ta zauna.

Sai da takai kusan 15mins sannan yace khairat Na'am race tana kallon kasa Cigaba da magana kawai yayi batareda ya kalleta ba. Inaso ki sani nan gudan ba gidan zama bane awajanki inaso ki fara kirgawa daga yau kwanakinki zasu fara kwana 30 ne tsakanina dake wanda zamu zauna a inuwa daya. Kuma inaso ki sani banason raini kuma muddin kikayi wani Abu wanda vaiminba a kwanakin dazakiyi tabbas saina hukuntaki, sannan kisani ni ban dora miki nauyina ko guda daya a kankiba ke dai dai da girkima kiringa yin kayanki ke daya bana bukata na yafe.

Toh kawai tace masa tana kuma sauraronsa, saura kuma kaikayin bakinki ya kaiki fadawa wani irin zamanda muke a gidan nan tabbas ranar saina gasaki acikin gudannan. Daga haka bai kuma cewa komai ba har zuwa wani lokacin itakuma har lokacin bata tashiba tunda bai bata izini ba.

Kitashi kibani waje kinwani zauna kin kafeni da ido ya fada watsa mata harara, mikewa tayi da sauri tanufi dakinta kai tsaye.......?


contact-form

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home