Auren Wata Daya 1 to 3
AUREN WATA DAYA
Page 1
''Kwance take kan makeken gadon dake cikin dakin tayi tana kallon fankar dake manne a saman dakin tana juyawa, hawaye ne kebin kuncinta amma kotakansu batabi ba dasunan gogewa, tashi tsaye tayi tafata zagaye dakin tana nemawa kanta mafuta akan matsalar dake tunkarota, momy ce tashigo dakin sallamarta uku amma kwata kwata diyar tata bataki ko daya daga ciki ba, hakan ne yasa tamatsa kusa da ita ta dafa kafadarta hadi da kiran sunanta a hankali.
Khairat make damunki haka harna shigo dakinki ina sallama baliji ba kina tunani gashi kuma kuka naga kukama kike. Fadawa tayi jikin mahaifiyar tata tana wani marayan kuku hakan ne yasa momcy tariko hannunta suka zauna bakin gadon tafara goge mata hawayen tana rarrashinta Sannan tace toh fadamin meke damunki kiji diyata idan baki fafaminba wazaki fadawa, shuru khairat tayi tana tunanin anya nafadawa hajiya cewar sadeeq auran wata daya yakeso muyi kuwa anya baridai kawai naboye mata wannan domin nasan ruwa na ballowa kaina gashi Allah yajarab ceni dason sadeeq gwara nazauna dashi kona 1 month din.
Muryar momy ce ta katseta '' khairat kenake wa maganafa amma kinyi shuru wai meke faruwa ne? Cikin kuka tasoma magana '' mom wai meyasa yaya sadeeq baya kaunata ko kadan baya Tausaya min duk da na kasance yar uwa agareshi tun ina daukin auransa harna fara yanke shawarar fasawa mom wallahi nafara gajiya takuma fashewa da wani Sabon kukan.
Kwantar da hankalinki kinji khairat komai me wace wane babu yanda muka iya tunda kinasonsa addu'a zakici gaba dayi kina mika kukanki ga ubangiji sannu a hankali zakiga komai na zuwa miki da sauki, ki daina damuwa munan dake sai sadeeq yayimiki soyayyar daxaiji kamar ya hadiyeki insha Allah kidage da addu'a kawai itace makarin mumini.
Kallon mom kawai tayi tace anya kuwa mom yaya sadeeq zai soni? Haba khairat wace tambaya ce wannan yanzu ke ba Allah ne ya sanya mi soyayyar saba ko ra'ayin kankine haka? A'a momy da ra'ayina ne ai datini nadade dacireshi araina. Murmushi mom tayi ta dafa kafadarta tace '' ki kwantar da hamkalinki ki abinda nace kici gaba da shirye shiryenku kinga yanzu saura kwana 10 amma akwanakinnan kidage da addu'a kinji nasanki akwai kokari ta nan bangaran, toh momy nagode.
Nan ta dada kwantar mata da hankali Sannan tatashi ta zata tafi. Har takai bakin kofa ta juyo tace au kinga harkin mantar dani abinda yakawo ni, dama sako zaki karbomin wajan hajiya rabi munyi waya da ita nace yanzu zakizo. Toh momy barina shiga toilet na gyara fuskaya saina tafi inkin dawo ina sama saboda bacci zanyi jiya bansamu bacci sosaiba ta fada lokacin datake rufe mata kofar, tashi khairat tayi tashige toilet din.
Page 2
Tana dawowa daga gidan hajiya rabi kai tsaye tawuce gidan babbar aminiyar tata marya Tun ahanya ta kirata awaya tasanar mata tana hanyar gidansu. Tana isa gidan tayi parking ta fito daga motar dan ko direba dama batazo dashiba. A parlour ta iske hajiya sakina mahaifiyar maryam tana kallo tayi sallama hajiya ta amsa cikin sakin fusaka tana cewa amarya amarya anji mutuniyar shuru aka biyo ta kenan. Dari tayi tana cewa eh wallahi hajiya ina wuni lafiya lau ta amsa mata suka dan gaisa tace maryam din ai tana ciki. Mikewa tayi ta nufi dakin maryam tana isa ta isketa zaune abakin gado tana game a waya. Tanajin shigowar khairat ta dago tana fadin amarsu, harara ta watsa mata tana fadin duba time kigani karfe 2:00 yanzu amma ko kizo gida kinsan kuma ina nemanki yi hakuri sister yau kai nane natashi yanamin ciwo Allah yabaki lafiya ta fada tana zama akusa da ita Ameen sister.
Shuru khairat tayi tana duba yatsun kafarta amma tskasa magana idanu maryam tabita dashi tana karantar yanayinta domin tasan cewar tabbas akwai matsala. Ajiye wayar hannunta tayi tajuyo ta fuskanci khairat ta kama Hanna yenta ta rike cikin nata Sannan tafara magana.
Besty yanayinki ne kawai yasar min akwai matsala banason ganinki cikin damuwa ki taimaka ki fadamin abinda yafaru banason kifara wannan kukan dan nasan matsalar baza wuce ta yaya sadeeq ba. Hawaye ne suka fara bin kuncinta shi maryam ta fada hajiya tana parlour banaso taji mu tunda naganki a haka nasan ko momy baki fadawa ba don haka fadamin kawai musan abinyi amma kitsaida kukan kar hajiya tajimu.
Share hawayen khairat tayi takalli maryam tace '' maryam sadeeq baya sona dagaske fah da na dauki abin na dan lokaci ne amma yanzu na fuskanci kawai yanamin hakuri amatsayina na yar uwar sane amma yanzu dayaga maganar auren mu da gaske ne babu fashi hankalinsa duk yatashi tsantsar kiyaya kawai nake gani yanzu a tattre dashi. Nasan da haka maryam ta fada yanzu ni sonake naji yaya kukayi dashi, hawaye tafara Sannan tace jiya da daddare sadeeq yazo amma abinda yazomin da shine yahanani kwanciyar hankali nayi niyyar fadawa momy amma kuma saina tuna kafin yatafi ya fadamin cewar idan har ikirarin ina sonshi da nakeyi har cikin zuciyata ne toh karna sake iyayenmu suji wannan magana domin bayaso iyayansa suyi fushi dashi, kuma tabbasa indai harna bari suka sani kuma yaga wani sauyi a tartare dasu zai dauki alhakin komai ya dora akaina nice rabashi da farin ciki sa kuma dama ba kaunar sa nakeba.
Kukane yaci jarfinta maganar ta tsaya anan tanajin wani irin zafi a zuciyarta. Rarrashinta maryam tayi Sannan tace wace maganace wannan ya fada miki. Saida ta tsaida kukanta tajuyo ta kalli maryam Sannan tace ''Yaya sadeeq yace auran wata daya zuyi tsakanina dashi. Wata daya kuma maryam tafada tane zare ido.Yanda na fada miki haka ya fadamin khairat ta fada tana kallon maryam da mamaki ya gama kasheta a zaune. Dakyar ta tattaro nutsuwarta ta kalli khairat tace yanzu dai kina nufin za'ayi auranku amma kuma bayan wata daya zai sakeki Eh haka yace saboda wai baya sona kuma idan yaki auena iyayenmu zasuyi fushi dashi akan yaki musu biyayya amma inya aureni yasan abinda zaiyi wanda zai rabu dani cikin wata daya batare da ansamu matsala ba.
Shuru maryam tayi Sannan daga baya ta dago ta kalli khairat tace wannan ba matsala bace kawai mu dora inda aka tsaya muci gaba da shirye shiryenmu kawai. Kamar yaya so kike yi nayi aure nan da wata daya nafito marayam. Dariya maryam ta sheke da ita, kallon mamaki khairat tabi maryam dashi harda bude baki. Saida ta gama dry ta Sannan ta kalli khairat tace karki damu zanyi miki bayani kuma zaki gane me nake nufi amma ba yanzuba kawai sonake ke kwantar da hankalinki ayi abinnan cikin kwanciyar hankali daga ranar saga ranar da aka daura muku aure za'a fara wasan.
Da mamaki khairat ta kalleta zatayi magana, maryam ta katseta ainace zanyin miki bayani karki damu tashi muje gida kawai. Mikewa sukayi suka kintasa suka fito, Babu abinda khairat ke tunani azuciyarta tana wa kanta tambayoyi. Shin me maryam zatayi ne, Kuma tacemin babu matsala kamar yaya. A haka ta manta da maganar domin tasan wacece kawar tata.
Page 3
Wace ce khairat da sadeeq
Asalin mahaifin sadeeq da khairat yan uwane na jini mahaifin sadeeq shine babba wato alhaji mukthar mahaifin khairat shine mai binsa sunansa alh kabeer su uku mahaifansu suka haifa akwai mace wacce ke bin mahaifin khairat amma Allah yayi mata rasuwa sakamakon hatsari dasukayi tareda mahaifan nasu sai su biyu suka rage.
Mahaifin sadeeq shahararran dan kasuwane a garin kano, itama mahaifiyar sa haifafiyar garin kano ce hajiya zainab sadeeq shine dansu na fari sai kanwarsa dake binsa mai suna Aisha shekara shida ke tsakaninsu da sadeeq daga kanta Allah bai kuma basu haihuwa ba har zuwa wannan lokacin.
Mahaifiyar khairat haifafiyar garin gombe ce sun hadu da alhaji kabeer ne a garin gombe sakamakon daurin auren wani abokinsa dasuka je a gombe har Allah ya Nufa tazama matarsa. ''Ya''yansu uku ta farko itace khadeeja wato khairat sunan mahaifiyar su alhaji kabeer sai mai binta sageer saikuma autar su rahama, khairat shekarunsu daya da Aisha kwana goma tabawa Aisha, rabin rayuwar ta agidansu sadeeq takeyinsa tareda Aisha tun sadeeq yana gida khairat ke mutuwar sonsa har zuwa sonda yatafi India karatu a lokacin yana karantar medicine babba matsalar shine ko dariya sadeeq baya yiwa khairat ko fira sukeyi inta shigo gidan tashi yake ya fita har hajiyarsu ta fahimta, tayi kokarin yimasa fada amma ya nuna mata shi rainine bayaso shiyasa kawai baya sakarmata fuska da haka hajiya ta hakuri ta kyaleshi.
Lokacin da sadeeq zai tafi India khairat tayi kuka kamar ranta zai fita amma har zuwa lokacin babu wanda tafadawa damuwarta sai kawarta da suka hadu a school wato maryam tana yawan bata labarin yaya sadeeq da irin abubuwan dayake mata kullum maryam na bata shawarar tayi hakuri komai mai wucewane. Lokacin da sadeeq ya kammala karatunsa yadawo gida har ya fara aiki ne mahaifinsa ke sanar masa sun riga da sun yanke shawarar hada auransa da khairat yayi niyyar musawa amma mahaifinsa ya nuna masa umarni yabashi ba shawarar sa yake nema ba.
Ta bangaran khairat kuwa da mahaifanta suka sanar mata jitayi kamar tazuba ruwa a kasa tasha duk da alokacin bata kammala karatun taba amma hakan bai dameta ba domin tafi bukatar zama da masoyinta akan karatun. Abinda yafi daga mata hankali shine yadda yaya sadeeq ke wulakanta ta agaban kowaye babu ruwansa da komai a gaban mahaifansu ne kawai yake nuna mata kulawa, haka kurum zai kirata a waya yayi mata barazana da cewar intayi kuskuran bari aka aura masa ita saitayi data Sanin abinda tabari akayi, inta fadawa maryam takan bata shawarar ta rabu dashi tunda ai ba ita ta sanya iyayensu hada auranba, kuma intayi kus kuran nuna bataso iyayensu zasuga itace ta bijire musu shikuma yabi umarninsu dan haka kawai ta kyaleshi.
Ana hakane yazo mata da wannan magana ta auran wata daya kawai zasuyi sbd yabi duk wata hanya data dace yabi yaga babu nasara shiyasa kawai ya yanke wannan hukunci domin yariga da ya shirya abinda zaiyi kafin wata dayan.
a takaice kenan.....?
Page 4
cigaban labarin
Khairat da maryam suna isa gida suka iske momy a parlour harta tashi daga bacci tana waya da dady akan kayan furniture daya tura akawowa khairat daga Dubai. Sallama sukayi khairat taje ta zauna a kasa kusa momcy ta dora kanta kan cinyarta tana fadin momcy wallahi duk nagaji.
Katse wayar momy tayi tana shafa kanta tana fadin ''kedai khairat raguwace me kikayi da har zaisa ki gaji, momy da kaina nayi driving fah ta fada kamar mai shirin kuka. Maryam ce ta katsesu tana gaishe da momcy amsawa tayi cikin sakin fuska tana fadin ai dama tunda naji khairat shuru nasan gidanku ta biya domin nasan inda na aiketa ya isa ace ta dawo. Momy kema kinsan in bataje ta kwasoni ba bazataji dadi ba ta fada tana dry.
Sallamar su sageer da rahama ne suka katsesu sun dawo daga school, rahama ta taho da gudu zata fada jikin momy khairat tayi saurin kaucewa karta fado kanta tana fadin ''Kekuma haka akeyi kawai ki wani kwaso aguje kina shirin buge mutane ta fada ta galla mata harara Maryam ce tace haba khairat ai kema kinsan wajantane tunda itace auta ba kema.
Fada matadai momy tace tana kollon autar tata data fara digar da kwalla tace. Sorry autata waya tabamin ke ne, Khairat bata jira amsarsuba ta miki taja hannun khairat suka wuce dakinta. Suna shiga toilet suka nufa sukayi alwala sukayi sallah.
Suna idar wa khairat tajawo wayart tana fadin barina kira Aisha yau kwana biyu kenan batazoba kuma bata kirani ba, wata kila kin mata laifine maryam ta fada tana kokarin cire hijab dinda tayi sallah.
Ringing 2 Aisha ta amsa wayar khairat cike da shagawaba take fadin haba sis dama zaki iya 2 days batareda kinji lafiya ta ko kin ganniba, kwafa Aisha tayi tace ''Eh mana tunda gashi kema tunda akasa bikinku da yaya kika daina zuwa wajena ko wajan hajiya ma bakya zuwa.
Haba sister kema kinsan haka kurum bazanki zuwaba wallahi kunyar hajiya nakeji. Daga maryam har Aisha dry sukayi Aisha tace ''Chab khairat yau kece kike kunyar hajiya, Eh mana wallahi banaso mu hada ido da ita dan Allah kiyi hakuri gobe kizo kinji, toh Allah ya kaimu wai ina maryam ne mun kwana 2 bamuyi waya da ita ba.
Wallahi gatanan tana jinki khairat ta fada tana mikawa maryam wayar. Suna gama wayar suka zauna suka fara tsara yadda komai nasu zai wakana batareda ansamu matsala ba, sai wajan karfe 5:00 khairat ta raka maryam gida.
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home