Zainabu Abu Daga Kauye 4 to 5
ZAINABU ABU KASHI 4 ZUWA 5
PAGE 4
Zainabu na hango a store tana dube dube wai wake take nema, tayi sa'a tasa mu buhun waken domin yunwa takeji itakuma yau se koko d kosai take so, mudu ɗaya ta auno sannan ta ji ƙashi ɗakin momy tanufa tace "momy turmin gidannan fa tambayarta momy tayi me zata yi cewa tayi ta gaji da cin abincin ƴan binni koko da ƙosai zatayi momy tace ai "bamu da turmi sbda ko dakan yaji bayar wa mukeyi na kuɗi.
Zainabu dajin haka tafito tana tura baki ga wake ajiƙe kugunta taɗaure tayi hanyar fita baba megadine yace "mutuniyar inazuwa ne cemai tayi "zani anguwane adawo lafiya yayi mata.
contact-form
Zainabu na hango a store tana dube dube wai wake take nema, tayi sa'a tasa mu buhun waken domin yunwa takeji itakuma yau se koko d kosai take so, mudu ɗaya ta auno sannan ta ji ƙashi ɗakin momy tanufa tace "momy turmin gidannan fa tambayarta momy tayi me zata yi cewa tayi ta gaji da cin abincin ƴan binni koko da ƙosai zatayi momy tace ai "bamu da turmi sbda ko dakan yaji bayar wa mukeyi na kuɗi.
Zainabu dajin haka tafito tana tura baki ga wake ajiƙe kugunta taɗaure tayi hanyar fita baba megadine yace "mutuniyar inazuwa ne cemai tayi "zani anguwane adawo lafiya yayi mata.
Wani gida nakusa dasu tashiga inda ta tarar da wata datijuwar mata tana dakan kuli kuli hamdala zainabu tayi sannan suka gaisa tsohuwar ta tambayeta daga inatake tace daga gidan allahji Ibrahim ne babansu Fatima ni bakuwace kuma shine nazo aron turmi zan surfa wake tsohuwar tagama dakan tamika mata dan turmin ficewa tayi tana murna bayan tagama surfe memakon ta tambayi gurin zubar da ruwa ina kawai seta sheka shi a tsakar gida Ashe yaya nasir natafe itako batasan ma ya shigo ba saukar wani gigitaccen mari taji ɗago kai tayi domin ganin me marinta kuka tasa hadida cewa Allah ya,isa mugu azzalumi kuma bazakaci kosan ba ya biyota daniyar ƙara mata wani ai zainabu ta jefo tabarya nasir yasule jikake, dagudu tayi cikin gida inda tatarar da anty Fatima taci kwalliya da alama fita zata yi da gudu taƙaraso gurinta tana haki tambayarta tashi gayi.
A HUTA KAMIN ACIGABA DA KARARANTAWA
Labarin abunda yaya nasir yamata ta bata, kana ita kuma ta ɗaura da bata haƙuri ,don tasan baya shakkar kowa se iyayenshi. komawa tayi gurin surfen nan takai niƙa tace "wai za,a kawo kudin bayan takoma gida tasamu momy ta umarci yar aikinta da tayi mata alale da kosai aiko murna ba,a magana a gurin zainabu domin abun nema yasamu zama tayi a hanyar shiga kitchen se kwalalo ido take tana dada sas sauta ɗaurin zaninta.
Yaya aliyu ne yazo wucewa yace a a sister yakika amsawa tayida lafiya sanan taci gaba da abinda yazaunar da ita tamika roba kenan adado mata kosai Sega nasir nan yataho ranshi a ɓace mai aikin yasamu tana kokarin zubawa zainabu ƙosai azuciye yace mata inkin gaji d aikinne ki gayamin banyi miki kashedi akan base anzo Neman abinci ba.
Sunkuyar dakai tayi tace yallabai kayi hakuri wallahi zainabu ce tace yau koko takeso da ƙosai shine hajiya tace inmata badan haka ba da tuni nagama tsaki yayi ya zo wucewa itako zainabu faɗan da yakeyi ko ajikinta burinta shine takai ragowar kokonta ɗaki sboda anjima shi zata sha, nasir ne yayi mata wani mugun kallo yace munafuka yar kauye kawai yakaimata rankuwashi kafin ta kaiga gyara daurin zaninta yakarɓe kofin kokon ya watsa mata a fuska ihu tasa tana tsinemishi.
A CIGABA DA KARANTAWA
Abba yatara iyalanshi a pallow saboda bashida lafiya shine yakira sunan nasir nan yake gayamai tafiyar da takamashi gashi bashida lafiya shine yakeson nasir ya je a mada dinshi saboda tafiyar shekara biyu zeyi sedai insunsami Hutu ze iya dawowa nasir beso tafiyar nan ba amma duk rashin mutuncinshi baya yiwa dadynshi musu shi kuma yaya aliyu zeje Zaria dubo hajia Dan bata da lafiya momyce tayimusu adu,a fatan alkairi domin bstada abin cewa sun tashi kowa ya wuce part dinshi yayinda tafiyar nasir takama jibi dady ne ya kwalawa zainabu da Fatima kira amsawa sukayi nan yake yimusu albishir da yasamar wa zainabu makarantar boko haɗe da islamiya me koyard a ita agida murna ba, a magana saboda tunda tazo data ga Fatima nazuwa abinse ya burgeta yau gashi itama za tazama yar boko.
Nasirne kita shiri sbda gobe zewuce zainabu kuwa dataji wannan kyakyawan labarin bakaramin murna tayi ba saboda meta kura mata zetafi.
Yau a yaune umma suka kamo hanysr tafiya abuja harda hajia domin tasami lafiya shirye 2 akeyimusu sosai saboda manyan baki su zainabu kuwa tatafi gidan baba me turmi Dan tun lokacin da tayi aron turmi shikenan take zuwa tayata hira kafin tafita seda sukayi fada da megadi domin nasir ya hana adinga buɗe mata ƙofa.
Karar motarsu hajiyane mutan gidan suka jiyo da gudu Fatima tayi waje domin yiwa hafsat oyoyo da gudu suka rungume junansu suna murna hajiyace tasaki baki tana kallonsu tace auni baza,amin oyoyon ba dariya sukayi inda momy farin cikin da take ciki yaki boyuwa dunguma sukayi suka shige dakin momy sai ba hirar yaushe gamo hafsat da Fatima ko hira sukeyi kamar baza,su rabuba zainabu ko tana gidan hajiyan kusa dasu.
Hajiyace tace ina zainab ne nan momy take gayamata gidan da taje aika baba megadi tayi domin yayi sallama yace tazo bakin sun iso aikuwa sega tanan aguje batasan waye a bakin get ba taturo dagudu zata wuce kawai sukaci karo banza mahaukaciya abinda yafito daga bakin nasir kenan aranshi kuwa yana cewa wallahi kafin intafi sena saki kuka itakuma tace barinje ingaida su hajiya wallahi anjima yaya nasiru sekayi danasanin zagina.
Hajiyace ta tara jikokinta da yayanta a pallow nan akayita gaishe gaishe inda ta sanar musu akwai abinda ya kawota zainabu kuwa tana jikin hajiya tana ta murna tunda hajiya tafara magana hankalin kowa nagurinta banda nasir da shikam cheating yakeyi abunshi dady ne yayi gyaran murya sannan hajiya tafara magana dacewar "dama abun da yataramu anan shine munason mu karfafa zumuncinmu saboda ko gaba zamuyi alfahari dashi bare yanzunma muna alfahari dashi dalili kuwa shine munyanke shawarar hada hafsat aure da alhaji wato yaya aliyu sannan takara da cewar "shikuwa nasiru daman mun riga da munyi mai mata ɗago kai yayi da alamun tambaya abakinshi amma ganin babu wasa a tattare dasu yasa yaja bakinshi yayi shiru shikuwa yaya aliyu bacin raine da farga ba suka durarmai itako hafsat babu bakin magana Fatima ko nagefe tanata yimusu dariya hajiya takara dacewar kekuma Fatima yakamata kifi toda gwanin ki nan kusa dalilin da yasanya kuka ga nazo shine wannan dan munyi magana da mahaifin hafsat da kuma babanku umma kuwa da momy fatan alkairi sukayi musu zainabu ce tasaci kallon nasir taga rannan kamar yakurma ihu ta tuntsire da dariya harda gwalo.
BREAK
PAGE 5
Sun gama tattauna wasu aka kawo musu kayan motsa baki sunci sunsha nanne dady yake gayawa hajiya aiyasa zainab a makaranta murna da farinciki ba,a magana albarka hajiya tadinga samai inda sukafara shirin komawa gida shiko nasir saboda bakin ciki wai ace Lamarin shi za,a nemowa mata himma ya yanshi yakira awaya nanfa yake cewa brother wai kana nufin kayar da da wait nan da ake shirin yimaka.
Aliyu yace to yazanyi ba dole inyi biyayya ba amma dai sunsa yarinyar nan tarainani nasirne yace koda yake garama kai tunda nikam bansan dawa za, a hadani ba ai zuwan hajiya wallahi be amfane ni ba.
Su hajiya dai sun wuce gida tunda sungama abinda yakawosu momyce ta kwalawa zainabu kira amsawa tayi dasauri tazo uniform momy tamikamata rungumewa tayi tana tsalen murna tanayi mata godiya ai kawa tayi domin takira mata nasir da gudu tamike domin tana cikin farin ciki bude kofar dakin datayi ne yasata kurma uban ihu abinda tagani yamu gun daga mata hankali.
Hangoshi tayi ya zuba uban tagumi daga shi sai gajeren wanndo tunda take bata taba ganin namiji haka ba abinda ya sata kurma ihu kenan shiko nasir ko ajikinshi tuda ba itaba ce a gaban shi.
Cafko ta yayi yariƙe mata kunne yace ke marar kunya yar kyauye kawai motsi ta hauyi d bakinta can taji saukar mari yatu rata gefe, mikewa tayi tace mugu azzalumi gara da baba yace katafi kaga mun huta mugu.
Ƙwafa yayi , itako bata koma Dakin momy ba tayi gurin me aikinsu tace mata ta sammata yaji aiko tayi sa,a annuko tadi ba a leda sukaci karo da nasir yayi shirin fita don kowanka beyiba hararshi tayi tsaki yamata itako ta tuntsure d dariya tace nasiru Allah yatsare ko kallonta beyi ba ya wuce, dakinshi tanufa taje cikin bathroom dimshi bansan metayi ba tafito tana murmushi tayi dakin momy momy ce tace zainab ina kiran danace kiyiwa yayanku nanfa tahau kamekame.
Tace "momy na shiga ban ganshi ba amma yanzu dai bari inje in kuma duba wa ko yana nan.
Washegari bayan sun gama break fast suna zazzaune akan kujerun d suka fito da ainihin kyan falon Fatima take tambayar dady ya basu kuɗi zasuje su siyo kayan makeup tambayarsu yayi nawa suke bukata zainabu tai murmushi tace "anty fati dady na magana amsawa tayi dace mai 20k ya isama buɗe baki dady yayi yana cewa gaskiya kurage ga 10k amsawa sukayi da Allah yakara buɗi cewa yayi sutashi sutafi dama yaya aliyu be tashi daga bacci ba ficewarsu keda wuya na leko dady da momy naga alamun sunaso abasu guri domin soyayya tatashi dagudu nafito nai zariya wato gidansu hafsat kullum umma akan shirya hafsat take gashi bikinma dasaura bedroom dinta tashiga domin dauko wayarta takira friend dinta tajiyo wayarta na ringing sunan my brother ne keyawo a kan wayar seda tadan jinkirta tukun ta amsa kiran murya a sanyaye "Assalam amsawa yayi yana fadin "fatan dai kina lafiya ko teema amsawa tayi da cewar "lafiya Lau ya kike ysu momy da Fatima Duk suna lafiya ka lau , kana sukayi sallama.
yakashe wayar yanajin bakinciki aranshi yakirata suyi hirar soyayya amma yakasa faɗa mata yana sonta sbda karya zubar da girmanshi. A ɓangarenta kuwa cewa take anya brother kuwa yana sona uhm tatashi domin fita zatayi gidan hajiya.
Bayan shekara ɗaya nasirne yazo hutu gida inda a kashirya zainab da Fatima da aliyu zuwa ɗaukoshi yau kowa murna yakeyi sabanin zainabu da dole ce tasata zuwa tarboshi riga da sket ne ajikinta na atamfa me kyau domin a halin yanzu ainihin kyawunta yakara fitowa kowa yakalleta seya kara kallo tayi haske ta murje tayi kiba ga gayu ga iya tafiya maganar jan aji ba,a magana domin yanzu boko yadan fara zama kuma duk kawayenta babu kazamai shiyasa tayi koyi da ɗabi,unsu musaman ma son kamshi d iya kwaliya eye glass dinta tadauka baki wannda yarufe ilahirin kyakyawar fuskarta sun fito dukkansu Fatima tana cikin doguwar riga pink me adon stone golden baka ramin kyau tayi ba itama mota suka nufa inda sukaje tarbar yaya nasir daga jirgi isowarsu keda wuya sukayi arbada mutanen jirgin sun fara saukowa tafiya yakeyi kamar bazai sauko ba a matakalar jirgin..?
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home