Zainabu Abu Daga Kauye_ 6 to 8
ZAINABU ABU DAGA KAUYE KASHI 6 ZUWA 8
PAGE 6
Saukowa yakeyi a hankali idanuwanshi sukaci karo da kyakyawar fuskar zainabu, suna haɗa ido yasakar mata murmushinsa mekyau saura matatta kala ɗaya ya sauko yaja yatsaya ya zuba hannayenshi a rigar sanyin dake jinkinshi zainabu mutuwar tsaye tayi saboda wannan kyakyawan saurayi.
Yayanta saukowa yayi yaje da gudu ya rungumi yayanshi sannan fatima itama taje da gudu ta rungumeshi zainabu ko tsayawa tayi tana kallon su da alama waya takeyi don dady ya siyamata waya babba me kyau duban shi yakai gurinta azuciyarshi yana cewa tsarki ya tabbata ga Allah da yayi wannan kyakyawar halitar to ita wacece da bazata zo tayimin sannu dazuwa ba.
Bayan tagama waya tace "yaya haidar mu wuce ko shidai nasir a iya tunaninshi yasan me wannan muryar ba wata bace illa yar kauyannan amma dai yaji muryar babu kauyanci a cikinta bude baki tayi domin talura da satar kallon da nasir yake mata tace you're well come my brother mutuwar tsaye yayi su dai su Fatima sun zama yan kallo yaya aliyu ne yace momy najiran mu a gida fa karasawa sukayi gun mota inda nasir yayi saurin shigewa baya don yasan inya shiga gaba zata iya shigewa baya yaya aliyu ne da Fatima suke a gaba itakuwa rannan yasha kinba sosai takulu can dai ya nisa yace "am brother ina yar qauyannan ne kokun barta a gidane ko kuma takoma qauyensune, zazzaro ido zainabu tayi jin ya kirata da wannan sunan murmushi aliyu yayi a zuciyarshi yace "wato nasir be san zainab ta zarce tunanin shiba a fili kuwa cewa yayi "ai ta dade da komawa.
Hamdala zainabu tayi sannan ta jiyo karar wayarta acikin hand bag dinta tana ringing murmushi tayi tace hii daga can bangaren akace amincin Allah yatab bata agareki farincikina kinsan tunda nayi tozali da fuskar ki nakasa samun nutsuwa speak out tayi amma na kusa da itane zai jiyo muryar fatima ko guntse dariya tayi nasirne yarasa tunanishi a zuciye yace wai wannan daga ina take kuma meta taka data ke damuna da waya aliyu najinshi yaki kulashi kara kuluwa yayi yaja tsaki fatima da ga darya na damunta amma babu halin yi sake kashe murya tayi tace wallahi kasan kaina ke tunani tundazu saboda wallahi in banji muryar kaba har zazzabi nake aliyu ne yakasa boye mamakin shi waishin yaushe zainabu tazama hakane itako zainabu tayine domin ta baiwa nasir haushi dan basan saurayin takeba shima dai saurayin wannan uban kalami da tazu bamai bakaramin farin ciki yayi ba sallama sukayi tamaida hankalinta ga titi hira suke jefi jefi itada Fatima nasir ko rannan kamar zeyi kuka sun isa gida inda suka sauka nasir da aliyu tare sukashiga falon momy fatimako da zainabu dakinsu suka wuce suna kuwashewa da dariya kan makeken gadonsu suka fada inda zainabu tace anty fati yanzu dai mungama d wannan sashin seme zanyi tunani tayi tace yawwa tunda dai haryanzu bega neki ba jeki shiga wanka kifito akwai wani shirin da zamuyi wallahi sekin riki tashi.
PAGE 7
Washe gari kowa ya gama karin kumallo sun koma kan kujerun da suke zagaye a palorn zuna kallo momyce ta kirawo sunan nasir amsawa yayi yamaida hankali ga momynshi tambayarshi tayi "kana da wacce kake sone, sunkuyar da kai kasa yayi yana Sosa keya yace "momy wallahi haryanzu dai bansamu ba amma dai inanan ina nema fatimace da zainabu suka hada ido sukayi murmushi momy ce a karo na biyu ta kuma kiran sunan nasir tace "munyi maka mata. a gigice ya dago kanshi idanuwanshi sun kada zuwa launin ja yace "momy auren dole? amshewa tayi da "karu femun baki nasir tun yaushe mukayi dakai akan kafido matar aure amma kaki.
Hakuri ya shiga bata murmushi tayi tace "bani ce nazartar da hukunci ba hajiyace dA dadynku da sauran yan uwa shi yayanka be yimana gardama ba sekai zaka kawomana matsala to wallahi karma ka kuskura dady yajika dan ranka ze baci. momyce tace "Dama d zainab zamu hada ku nan da wata biyar saboda mungama shawar warinmu kuma harda bikin abba za a hada. takira sunan Fatima amsawa Fatima tayi momyce tace to dady yace kituromai saurayin da kikeso koda yake anjima m zai kiraki seki shirya nasirko salati ya shigayi yana maimaita sunan zainabu a bakinshi yace "Momy yarinyarnan yar kauyece gashi shekararta sha biyar fa wallahi ni tayimin karama ko kwalliya bata iyaba yanzu idan abokanaina sukaji dariya zasuyimin please momy nasan halinki zaki iya temaka min.
Zainabuce ta dago da idanuwanta da sukayi ja tsabar bakin ciki d cin mutunci dama yayan masu kudi sun iya cin mutunci? Azuciyarta taketa saka da warwara momyce takai duban ta gurin zainabu talura da yana yinta setayi kamar bata gantaba cewa tayi "zainab kinason yayan naki kuwa da gowa nasir yayi a razane yana tambayar kanshi wai dama itace wannan kodai ba wacce yasani bace wanan.
Kallonta ya karayi yakuma cewa amma ai to kamar waccan tafiya tsiwa. momyce tayi maga ta dawo dashi daga duniyar tunanin da yaje cewa tayi "zainab baki bani amsa ba dago jajayen idanuwanta tayi takai dubanta gun momy seta ga bekamata tace batason nasir ba kodan rikon da momy tayi mata bata bam bantata da fatimaba momyce a karo na uku takuma maimaita tambayar ta tace ",Zainab bazamuyi miki auren dole ba kifadamin abinda ke cikin zuciyarki in baki sonshi wallahi karki damu sunkuyar da kai tayi tace "momy na yarda. nasirne ya dago kai ya dubeta kanta a kasa tana wasa da kayanta. momy farinciki taji domin tana tunanin kaf yayanta sunyi sa ar surukai zainabu ce tamike da gudu domin takasa rike kukan da ya zomata nasirne yayi tsaki dagowar da zeyi sukayi ido biyu da momy Harara ta dallamai yamike yanufi dakinshi se jin kanshi yakeyi a farin ciki ne koko bakin ciki yakasa bawa zuciyarshi amsa zainabu ko kuka takeyi sosai gunin ban tausayi
Da daddare dadyne yakuma tarasu a dakinshi domin tattauna maganar biki. Yaya aliyune ya gaida dady inda dukkansu suma suka gaidashi sunan nasir ya fara kira ,amsawa yayi yace "na,am dady" magana dady yafara kamar haka "nasani mune mukayi muku zabin matan aure dalili kuwa shine shekarun baya mun baku zabi amma seku kayi watsi da maganarmu to shine muka ga ya dace da muhadaku da yan uwanku dama tun zuwan hajia mun gama maganar.
Abba saura kai to alhamdulilahi munyanke shawar hada ka aure da zainab tunda ya sunkuyar da kai bedago ba shidai yanjin maganar da dadyn keyine kawai. Bayan dady yaga jawabansa suka mike sukayi waje kowa yanufi sashin shi.
Washe gari yaya aliyune na hango yashirya cikin shadda meruwan kasa tasha aiki sanye da hula da takalminshi me kyau ya fito da mukulin motarshi yayi dakin momy besameta a dakin ba domin tana dakin dady kiranta yayi a waya bata dau lokaci ba segashi ta iso bude baki tayi tace Abba " inazuwa da safiyarnan murmushi yayi yace "my momy wallahi yau inason zuwa Zaria ne adu,a tayimai sannan tashige bedroom dinta tadan jima kadan tamikomai wani Abu aleda tace yakaiwa umman hafsat mikewa yayi yazo fita suka hadu da nasir nasir ne yagaisheshi yake tambayrshi ina zuwa aliyu ne ya dake yace "gurin matata mana can zani, nasir ne ya rike baki yace brother Allah dai yakayauta wallahi wannan ai raini zejanyowa mutane gaba aliyu yayi ya je inda motarshi take yatayar yanufi Zaria.
Tuki yakeyi amma hankalinshi yana ga hafsat dinshi domin a ysnzu yana jin sonta nashiga jikinshi gudu yakeyi a tskiyar titin kirane yashigo cikin wayarshi dauka yayi hade da sallama momyce daga can bangaren tace "abbana kakusa kuwa? amsawa yayi da wallahi momy yanzu nawuce kaduna amma insha Allah bazan kai la'asarba adu a tayimai tareda fatan Allah ya saukeshi lafiya katse wayar yayi number na hafsat yakira bta daga ba akaro na biyu ma shiru ana ukun ne tafito daga dakin ummanta kenan taji karar wayarta shigowa tayi da sauri takara a kunnenta tace "Assalamu alaikum. wani sanyi yaji tukun yace wallahi aiki salam my hafsat murmushi tayi tace my brother munyi missing dinka kaki zuwa ko.
Amshewa yayi da ba haka bane my baby wallahi aikine yayimin yawa bude baki tayi azuciyarta tana cewa kodai yamance dani yake waye suranane shirun da yajine yace "baby kinajina kuwa, tace domin kunyace tacikata magna yafara kinsan menene tace a A yace albishirinki tace goro fari koja tace fari kal kal yace insha Allah nakusa zuwa Zaria wani tsalle tadoka tayi dakin umma da gudu tace umma wallahi yanzu mukayi waya da brother na yace yanan zuwa anjima kashe war yayi domin yanata magana bata jishiba suna mgna da umma kicin suka shiga suka fara hidimar tarbar angon hafsat number hajiya yafara kira dauka tayi domin tagane me muryar tace megida yakika suka dan taba hira kadan yafada mata yanan zuwa itama mikewa tayi ta kwalawa me aikinta kira.
Bangaren su zainabu kuwa fatimace taketa aikin rarrashi a cewarta bazata yarda da cin mutuncinda nasir yake mataba domin wannan cin fuskane kirane yashigo wayar Fatima murmushi tayi tace yau she zasuzo yace mata gobe insha Allah murnatake farincikin fuskarta yaki boyuwa tarungume zainabu suna murna zainabu tace wai yaron abokin dady ne iyayenshi zasuzo gobe, fatimace tace eh mana kinsan wallahi inasonshi sosai.
Aliyu yasauka lafiya gidansu masoyiyarshi yafara zuwa wato gidan umman shi horn yayi megadi ya budemai yanayimai sannu, kudi aliyu yaciro ya mikamai yanata zubamai godiya saboda akuwais.
PAGE 8
Dakinsu ta wuce tanata dariya hira suka dan taba da umma tamike domin gabatar da sallah shima duba lokaci yayi yamike yanufi masallacin dake cikin gidan bayan yayi sallah ya tsaya a gurin flowers din gidan yana kare musu kallo yana murmushi domin ma abocin son furanni ne wayarshi yaciro ya danna number hafsat tanata ringing bata daukaba har ya fidda rai zata dauka can seyaga tayi receive tace "ka dawone, kasa da murya yayi yace "kizo kisameni a gurin flowers dinnan zatayi magana yace kiyi abinda nace tashi tayi daga kan sallah yar ta dauko hijab dinta tafito a hankali take tafiya ,ashe tunda tafito yake kare mata kallo niko nace sekace ba daga gidan kafitoba .
Karasowa tayi tace brother memakon kashigo cikin gidan shine kazauna anan, tunda tafara magana yake kallonta harta kare beku lataba, kujera taja nesa dashi tazauna. Aliyune yace baby magana nakeso muyi, kallonshi tayi taga babu alamun wasa a tattare dashi yace kina jina, hankalinta ta mayar gurinshi .
Hafsat. Ssai da gabanta yafadi domin yaushe rabon da yakirawo sunanta amma yau shine harda kiran sunnan to wanne lefi ta yimaine, take tambayar zuciyarta shirune yabiyo baya domin takasa magana.
Mikewa yayi yaje yayiwa umma sallama kana yafice daga gidan umma nata samai albarka gurin parking din motocin gidan yanufa yadauki tashi yana shirin ficewa sega mutuniyar tashinan na dagamai hannu alamar yatsaya kintsayawa yayi seda yanufi gurin get din megadi nashirin budewa takaraso da sauri dariya yake tayi itakuwa rantane ya baci domin tsakaninsu da get din akwai tafiya seda tayi gudu bude motar tayi kana, tashige ko kulashi batayiba.
BREAK
Shikuwa dariya yaci gaba dayi kukane ya kubuce mata domin takasa tare bacin randa yazo mata har yafara tafiya yaja yatsaya domin gimbiyar ta rikicemai, parking yayi a kusada kofar gidan domin basuyi nisa ba.
Hanunshi ya dora akan nata ,saurin janye nata tayi, kana tajuya fuskarta tana kallon wace domin tunda take ,wani bata mu amula da namiji da har zesami damar taba mata hannu ba shiyasa take kiyayewa a matsayinta na mace me rauni.
Hakuri yashiga bata domin yakuma gano yabata matarai sai da yasata dariya tukun tabude mota zata fice yace gidan hajiya zaki rakani fa rau, rau tayi da idanu alamar zata kumayin kukan tace please am sorry my brother yarufe mata baki kana yace mena fada miki dazu tace sorry na mantane amma yanzu kaina ke ciwo ficewa zatayi ya ce kitsaya kikarbi tsara barki tsayawa tayi yamiko mata Abu a bakar leda kana yace kikulamin da kanki semunyi waya.
Gidan hajiya yawuce yasamu ta tafi yawon nata nafama domin bata gajiya da ziyara shiyasa takeda mutane sosai.
Hanyar abuja yadauka karatu yakunna kirar alqur'ani maigirma dan danan se gashi har yashigo abuja yanufi gidan su yana shirin fitowa daga moto sega kiran hafsat nan yashigo gyara tsayuwarshi yayi kana yace baby seyanzu kika kirako muryar dayayine yabawa hafsat dariya domin akwaishi da ban dariya sallama sukayi yafada mata ya iso amma beshiga gidan ba, Da shigarshi ya hango yammatan gidan suna shirin fita domin yagansu kowace da gylle a hannunta zainabu ce takaraso da sauri saboda takalmin da tasa babu halin tayi gudu, nikuwa nace su zainabu anwaye .
Washegari dady ne yakuma kiran iyalan nashi bayan sungama breakfast ya kirawosu zuwa dakinshi dukansu sun zazzauna a kasa momy na kujerar kusa da shi sunajiran jawaban da dady zaiyi dady ne yace, kunsan dacewar bikinnan saura 1 month ko nada anyi other kayan dakin zainab dana Fatima kukuma kuje kudu ba gidajen inbeyi muku ba sekuyi magana yaya aliyune yace dady wallahi gidan yayi Allah yakara nisan kwana, dady ne yanisa kana yace amen abbana Allah yayi muku albarka ina alfahari daku .
Dady ne yakai dubanshi ga nasir da tunda suka shigo kanshi yake sunkuye bedago ba,
Dady ne yace nasir naji kayi shiru koda problem ne saurin dago kanshi yayi yace no dady Allah yakara budi momy ce takarada baza muyi muku abinda ze cutar dakuba, Kowannensu suka tashi sukayi dakunnansu nasir ne ya lula duniyar tunani yace wallahi ko na auri wannan yar qauyen nan sena auri wacce nakeso domin ba zabina bace zabin iyayena ce.
Momy ce tafito domin raka dady zeyi tafiya zashi gurin hajiya sallam sukayi yawuce yadauki hanya zuwa zariya. Remain 3 weeks biki momy sekara gyara yayan nata takeyi domin kudi taware na mussaman domin su gyara ake yi musu Wanda babu algus acikinshi kuzo kuga amare gunin ban sha,awa domin zainabu tafi Fatima haske amma dukkaninsu sunyi kyau . Ayaune kayan dakunan su Fatima ya iso daga London acan dadi yaba yar , ayimusu.
Fadawa kan kujerun da suka kwata dakin sukayi domin dakin nasir na jikin na aliyu kuma kayan ciki duk kala dayane dakunan ma dukan su ciki dayane se gado se bed site a gefen gadon dakunan sun tsaru kamar na wata amaryar abokanan nasune suka shiga yiwa aliyu tsiya akan cewar yaje ya bugo invention card batare da sanin nasir ba.
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home