Monday, January 10, 2022

Zianabu Abu Daga Kauye 14 zuwa 18







        ZAINABU ABU DAGA KAUYE

PAGE 14


fitowa daga bathroom ɗin tayi kana tace "Yaya meya faru? Ƙin kulata yayi amma bashida zabi dole yakulata ,harararta yayi kana yace "ki kiramin momyna, riƙe baki tayi kana tace "momy kuma? daurewa yayi yace "ko bazaki kirata bane. Murguɗa mai baki tayi kana tace "mezata yimaka ¿ a fusace yace "ke dan ubanki mekike yimin zaki kiramin momy kokuwa, Zainabu ce ta, tuntsire da dariya kana tace "zan maka komai kaga abar kiransu momy natuba na dena abinda nake yimaka kaji yayana. tsawa yadaka mata kana yace "ni abokin wasan kine da har zan dinga faɗa kina faɗa.

Matsowa kusa dashi tayi kana ta rukomai hannu nuni taymai da hanyar waje ,cemai tayi yaya dan Allah kafitarmin a daki tun,dazu nakeson gyara dakin amma abin ya gagara taso inraka ka dakinka.

Bakinciki da takaici alokaci daya suka dirarmai da yana da lafiya da babu abinda sai yaci uban yarinyar nan amma babu inda ya iya gashi ko tashi baze iyayiba sau sauta murya yayi kana yace "Zai zoki daukomin wayata a dakina inkira su momy Zainabu ce takarbe da kaga karka tayar musu da hankali kabar zuwa gobe sai afada musu yarasa inda zai sa kanshi da wanan fitinanniyar yarinyar, gashi babu halin dukanta juya fuska tayi tanata dariya afusace yace ke munafuka zoki kamani ki kaini dakina da gudu takaraso saboda burinta yafita a dakin tanaso takira Fatima ta tayata dariyar faduwar Nasir.
















Dakyar suka isa dakin nashi megyara yakirawo ba a ɗau lokaciba segashi ya iso duduba kafar yayi kana yace targade kayi amma gurin ya bugu sosai nan da zuwa sati daya insha Allah zaka warke Nasir dai bashida bakin magana tunda aka gyara kafar yakejin zazzabi sosai Zainabu ce ta dauko kudi a dakin ta tami ƙawa megyara godiya yayi mata kana yabasu maganin shafawa a gurin.

Baccine yadau,keshi fitowa tayi daga dakin tanufi dakinta tana tsalle nikuwa nace anya Zainabu tanada imani kuwa "waya sukeyi da Fatima sunata dariya bayan sungama ne sukayi sallama.

Daga tashin Nasir a bacci yaji wata masifafiyar yunwa gashi baze iya tashiba kuma bashida number Zainabu tagumi yayi kana yadubi fridge din dake gefenshi budewa yayi yadauko fresh milk yashanye baccine yakuma daukarshi misalin karfe 2pm yatashi alokacinne Zainabu tafito daga dakinta sanye da yar karamar, riga mekaramin hannu sai wando shikuma dede guwai,warta babu dankwali a kanta kitchen tanufa ta hadomai abincin da tagama shinkafa da miya da kayan lambu dakin Nasir tanufa durkusawa tayi kana tace yaya ya jikin naka dasauki yace mata kana yace waya baki izinin yin wannan shigar sai kace wata yar bebi jibeki ko kyu bakiyiba kin kulashi tayi kana tace ga abincinka kamashi tayi yazauna kana yace kaini bathroom wanka nakeson yi zaro ido.

Zainabu tayi kana tace wanka kuma kaida bakada lafiya gashi jikinka babu karfin sayawa tsawa yadaka mata kana yace ubanwa yafada miki zaki kamani intashi kokuwa turo baki tayi kana tace Indan nakamaka katashi to sai inkoma nima inci abincin ko, hararta yayi kana yace inkingama surutun zoki daukomin towel a bandakin kuma zaro ido tayi a karo na biyu tana daukowa ta mika mai dagudu tayi waje dakinta takoma tana ta maida ,nunfashi rike baki tayi kana tace oh yaya yaushe yazama dan iska.

Bakin gadonta tasamu tazauna tunanin rayuwarta da ,tayi a kauyen su, shine yadawo mata gashi tunda sukayi biki su inna suka tafi basu zo, gidanta ba ta, tuna wancan ta, tuna wannan da haka har bacci yakwasheta.

Hafsat taji sauki sedai bata nunawa Aliyu ba saboda fitinarsa da sallama yashigo gidan tun daga bakin kofa yaketa cewa my baby, my baby tana kwance, bata tashiba I'm yakaraso kusada ita kana yace haba my hafsat meke faruwa rau rau tayi da idanu zatayi kuka, tace yunwa nakeji gashi cikina nayimin ciwo dariyama tabashi amma sai ya dake ,kana yace kodai asamomiki yar aikine dasauri ta duro daga kan gadon taruko hannun Aliyu tace yar aiki kuma gaskiya banaso tashi, tayi kana tace yanzudai mekakeson ci kaga harna sami sauki ya kasa tare dariyar datazo mai seda yayi me isarshi sannan yace ni banajin yunwa amma kinsan matsalata futowa nayi daga gidansu Aliyu domin gaskiya sunkoroni nikwa nace sai anjimanku .

Bayan sati daya


Bari muleka gidan su brother na, Nasir yaji sauki sosai gobe zefara zuwa gurin aiki .dakin Zainabu yanufa bacci takeyi, bakin gadon yasamu yazauna yakai dubsnshi ga fuskarta kana yashafi gefen fuskar yatashi yafice gaskiya brother kafara bamu kunya.

PAGE 15

sallah yaje ya gabatar daganan ya wuce gidan su hira sukeyi cikin nishadi gashi ga momynshi da dadynshi sun tambaye shi Zainabu murmushi yayi kana yace "tana lafiya bacci ma takeyi shiyasa na taho, washe baki su momy sukayi sunata samai albarka sallama yayi musu yakama hanya zuwa gida da isarshi cikin gidan ya hango gimbiyar tashi taci kwaliya tahaɗe shaddace me ruwan ganye, dinkin riga da skirt baƙaramin kyau tayiba se tashin kamshi takeyi kamar anyi barin turare. Da sallama yashigo cin karo yayi da Zainabu tana kallo gakuma remote a hanunta tsayawa yayi yana kare mata kallo, saboda bata,masan yananba zagayowa yayi kusada ita yazauna, juyowa tayi kana tace "yaushe kashigo? "yanzu" yace mata, taɓe baki tayi kana tace "yasu momy"
Lafiya yace ya kauda kanshi gefe.

Murmushi tayi saboda tafara tunanin yanzune yadace tafara aikinta tasowa tayi kana tadora kanta akan cinyarshi tsawa yadaka mata kana yace "ke jarababbiyar inane tashi kibani guri! kin tashi tayi tahau waka tsayawa kallonta yayi sekuma yaga alamun akwai raini aciki tureta yayi tafadi kasa.












Ihu takeyi iya karfinta tana kuka sosai Nasir ne tashi daya hankalinshi ya tashi dasauri yazo gareta kana yace "meya sameki please? ƙin kulashi tayi tanata kukanta daukanta yayi ya kaita dakinshi motsi kadan tayi zece sannu karfa ku sauka Zainabu taji ciwone tamm yana fita zata tuntsire da dariya volume din kukan takara da gudu yakaraso yace meya faru tayi da idanu kana tace "indomie zanci da kifi Nasir ne yabude baki yace zandai iya dafa indomi amma shi farfesun kifin barinkira me aikin su momy tayi miki ihu tasaka tana turje turjen kafa tana cewa ni wallahi indai ba kaizaka dafa, zaro idanu yayi, yace wallahi duk abinnan dakikeyi kinci darar sekuma yayi shiru mikewa yayi yanufi kitchen yafara dora ruwa indomin kayan hadi yasa bayan ruwn yatafasa ya, zuba indomie plet yasamo yajuye aciki yanufi dakin tashi Zainabu tayi tafara zuba loma sai da takoshi tasha ruwa sannan tamike tafice da gudu kana tace "oho dai ko yanzu naci banza, yarasa mezai ce mata zama yayi bakin gadonshi yafara tunanin irin rashin mutuncin da zeyiwa Zainabu.

Hafsat ce zaune a palonta tana kallo a TV shirin yatafi da tunanin ta har Aliyu yayi sallama bata jiba kara fita yayi kana yadawo tun daga bakin kofa yake fadin zo gareni baby na da gudu tamike tayi tsale ta dare bayan aliyu juyi yashiga yida ita sunata zagaye pallow tambayarta yashiga yi "yakike my baby shagwabe fuska tayi, tace lafiya ba, kaine tunda katafi tun safe kaki dawowaba ta karashe maganar kamar zatayi kuka sakota yayi daga bayanshi yadubi fuskarta yace "am sorry bazan karaba aiyukane sukayimin yawa dariya sukasa dukkansu kana tamike tajanyo hanun aliyun suka nufi bathroom ruwan wanka tahada mai da turaruka masu dadin kamshi .

kuyi hakuri nafito daga gidansu Aliyu bazan iya zamaba. Bangaren su Fatima tayi kiba takara kyau sosai gunin sha'awa, sagir ne yayi sallama be sami kowa a palon ba, kai tsaye dakinta yawuce begantaba bathroom yaleka nanma batanan, fitowa yakuma yi ya nufi kitchen dinta hangota yayi tana girki da alamu hankalinta yayi gaba rungumeta yayi taba yana fadin haba teema ina kika shiga naduba ko ina ban gankiba juyowa tayi tashafi fuskar shi kana tace "oyoyo my lovely kadawo lafiya, dafatan dai baka bari ankallemin kya kyawar fuskarka ba? murmushi yayi, yace "babu wacce takalleni my teema.

Nasir ne yayi shirin fita saboda yau ayuka sunyi mai yawa ko takan dakin Zainabu beby ba bare yasan takwana lafiya ko akasin hakan motar, shi ya shiga kana yafice daga gidan da isarshi gurin aikin yasamu abubuwa sun sauya, harda sababbin yan ma, aikata dakuma sababbin customers, kai tsaye office dinshi ya yuce kana ya zauna yafara duba takardun shi masu muhimmanci knocking yaji anayi izini yabada batare da yadago"kai ba shigowa tayi kana tace Aslamu alaikum amsa mata yayi dan besan muryar meyin sallamar ba, bare yadago kai kujera tasamu tazauna a kujerar datake kallon tashi cire gilashin dake fuskarta tayi kana tace "amincin Allah yabbata, agareka, yakai kyakyyawan saurayi dagoda kanshi yayi, yakai dubanshi ga wannan budurwa kyakyawace saboda batada makusa ko kadan fara ce doguwa batada jiki sosai sedai daka ganta kasan wayayyar mace, ce anan gurin Allah yayimata halitta me daukar hankali.

Murmushi Nasir yayi Yakima dubanta juya fararen idanuwanta tayi kana tace eh kaidin mekyau ne sosai bude baki yayi cikeda takama yace "gaskiya nagode kema din ai mekyauce musaman idan kikayi dariya hira sukeyi kamar masoya musayar number waya sukayi kana takuma yimai murmushin da yabaiyana dimple dinta ficewa tayi daga office din tunda tafita Nasir ya tura takar, dun gefe kana yafara tunanin wanan yarinyar fuskarta yake hangowa hadeda murmushinta kasayin aikin yayi kana yayi shirin zuwa gida fitarshi a office kenan sai ga wanan budurwar tayi shirin tafiya gida gurin motarshi yanufa itama wanan budurwar nufar gurin motar ta, tayi kana tashige tafice daga ma aikatar tsayawa yayi yanata tinanin yar'anya nan musaman fitowar datayi yanzu bakaramin kyau tayiba nikuwa nace ga kyakyawar matarka a gida mezakayi da wanan.

karkudamu ba ayi komaiba yanzu wasan yafara....?








Page 16











Da isar shi gida besami Zainabu a pallow ba dakinta yaleƙa tunani yafara, gashi yatafi yabar yarinyar mutane sallama yayi, yashiga ɗakin tashinta ya shigayi amma tanaji taƙi tashi domin taci kuka tagaji shine bacci ya ɗauketa wayar Nasir yana ta ringing dubawa yayi domin yaga wacece sunan dayayi saven ɗin number tata yagani wato me kyau dakinshi yanufa yabarta a gurin mikewa tanufi bandaki 10pm tayi alwala ta tada Sallah tadade tana kwararo adu'ar, na Allah  yajuyo mata da hankalin mijinta.

Waya ya keyi hankalinshi kwance sunanta ya tambaya batayi gardama ba tace sunanta saudat. Saudat yajuyo agurin alhaji Bashir shararen mekudi ne ita kadai Allah yabasu kuma basa taba hanata duk abinda tasa kanta komi kyawunsa ko akasin hakan .

Bayan sun gama waya sukayi sallama tundaga wanan rana akullum sayi waya samada sau biyar saboda tsananin shakuwar da sukayi Nasir yafita sabgar Zainabu baya shiga harkarta haka itama Zaman nasu tunda suka hadu da saudat komai nashi yasauya Zainabu tayi mamakin hakan sedai bata gano musabbabin hakan ba taduƙufa rokon Allah ba dare ba rana aikinta kenan.

Saudat ce ta, tunkari mahaifinta da maganar  da tasami wanda takeso mahaifin  nata bakaramin farin, ciki yayiba saboda sun dade suna jiran wanan rananr yanzu gashi Allah ya amsa adu'arsu  kwalawa mahaifiyar saudat kira alhaji bashir yayi dasauri takaraso tana fadin wanan kira haka alhaji, saudat ce tamike ficewa tayi a guje, kana tanufi bedroom dinta tafada gadonta.

Alhaji bashir ne yake bawa hajiya labarin maganar dasukayi da saudat farinciki, ne yabaina a fuskarta kana tace "to Allah yatabbar mana da alkairi zansa abincika min yaron idan sungama dai dai, tawa se tayimai magana yaturo iyayensa.

Zainabu ce tagaji da wulakancin da Nasir yake yimata dakinshi tanufa karar saukar ruwa taji alamun wanka yakeyi samun bakin gado tayi, tazauna ,,tashiga kogin tunani "karar bude kofar taji bata dago kantaba dan batasan a yanayin dayake cikiba, zaro ido yayi kana yace ubanwa yabaki izinin shigomin daki hakuri tashiga bashi sega hawayen da take kokarin,boyewa sun zubo mata tafar dacewa "menayi maka katsaneni? tana cikin maganane sukaji wayar Nasir na ringing, amsa kiran yayi kana yace baby meya faru naji muryarki wata kala ta ɗan shagwabe fuska tayi kana tace "dadyna yace kazo yanason ganinka fara, a ce tabaiyana a fuskarshi kana yace, karki damu anjima inan zuwa.














Da gudu Zainabu tafice daga dakin tun daga ranar tashiga damuwa bata da walwala gashi ko kiransu momy tadena.

Nasir ne yaketa shirin zuwa gurin saudat shiga yayi na dogayen kaya shadda ce me ruwan goro bakaramin kyau yayi ba ko dayake daman shidin mekyau ne lokaci yake jira yacika masallacin dake cikin gidan yanufa domin gabatar da sallahr isha, I karfe 8:30 zetafi gidan su saudat Zainabu ce dakejin tafasar zuciya tarasa mezatayi tahana Nasir zuwa gidan.

















Kitchen tanufa ragowar kubewar, data zubamai ranar tadauko takara ruwa taje hanyar daze fito ta kwara agurin ba lallai kagane abin dake gurin ba saboda ta tace kubewar da rariya ga santsi dakinta takoma ta dauko qur,ani tafara rera karatu...?


Page 18



Yafito rikeda waya a hannunshi yana dariya, be ankara ba kawai yaji yasule ya, dada famo buguwar dayayi abaya ihu yakeyi yana salati, Zainabu nata karatunta ko kulashi batayi ba daga murya, yayi "yace Zainab kina ina tanajinshi taki fitowa cewa tayi dama kasan inacikin gidan ?ashe inada rana rokonta Allah yakeyi akan tafito ta kamashi yatashi amma taki, ihu yakeyi kamar karamin yaro amma bai sa Zainabu tafito ba sassauta muryarshi yayi, yace Zainab dan Allah kifito kitemakeni dariyace fal acikin ranta amma seta dake.

Fito warta tayi dai,dai" da ana kiran wayar Nasir dasauri takaraso dan taduba waye mekiran ,mekyau taga ansa a number dad`a, duba sunan tayi sunandai datagani dafarko dagawa tayi kana tace hello,dagacan ban garen saudat, tace kee bashi wayar saboda Nasir be fadawa saudat yanada mata, ba Zainabu ce tace ke ubanwa yabaki izinin kiran mijina.

Nasir yana zaune babu damar tashi bare yarufe ta da, duka, nikuwa nace wallahi gara ka,lallaba Zainabu ta, temaka maka takaika daki inkuwa kayimata masifa tabarka kakai kanka. Saudat ce tace dan ubanki Nasir dina ba irin, mazannan bane masu kula,kulen yammata Zainabu ce tace nagode amma kisani inma Nasir kikeso wallahi kin makaro saboda yazama nawa.

Saudat ce takashe waya hawaye nazuba a idanunta Nasir yafara galabaita magana ma dakyar yakeyi gashi ran Zainabu yakuma baci yanayin da taganshi ta, tsorata dagudu ta, taho tana kuka tana. Allah sarki mace me raunanna,niyar zuciya Zainabu harta ji tsoro kuka takeyi sosai gashi Nasir baya iya magana hankalinta bakaramin tashi yayi, ba rasa inda zatayi, tayi wayarta tadauko takira Aliyu jin muryarta wata kala, yagano babu lafiya dasauri yanufo gidan saboda baban gidane amma kowa da bangaren shi mota yadauko suka nufi asibiti ruwa aka fara karamai Zainabu ce takira momy take gaya mata halimda ake ciki, mayafin ta dauko tanufi gurin megadi tana tamvayar'shi ina driver nta yake dagu, du driver n yakara, so momy ce hankalinta a tashe, tace maza, zoka kaini asisibi kwatancen asibitin tayimai kana suka dauki hanya.

Da isarsu asibitin suka samu harya far"fado hamdala sukayi kana Zainabu tanufi gadon dayake sannu tayimai baya iya magana daga mata kai yayi kana momy takarasa tana yimai sannu, su Fatima da hafsat duk sunzo suntafi kwanansu biyu aka sallamesu gidan momy suka nufa dakinshi na gidan su aka wuce dashi saboda yakuma hutawa Zainabu kuwa gurin momy tanufa sunata shan hira, duk inda momy tayi domin tabugi cikin Zainabu akan tagaya mata ko Nasir na bata wahala Zainabu taki fada momyn ce talura da irin ramar da Zainabu tayi amma gashi takasa samun cikakken bayani momy ce takoma dakinta ta daukowa Zainabu turaruka masu kamshi dakuma magani tayi mata bayanin inda zatayi amfani dashi karba Zainabu tayi zatayi godiya momy tarufe mata baki momy ce taja Zainabu zuwa bedroom dinta bansan mesukace ba najidai suna dariya.

Nasir yasamu yaji sauki sosai tunanin wayarshi yafara dakuma saudat yamatsu yakoma gida yadsuko wayarshi gashi momy ba bari zatayi ba. A chan gidan nasu, saudat takira wayar Nasir gata abude amma ba, a dauka ba ranta inyayi dubu yabaci zama tayi batada aiki se kuka gashi kowane lokaci sai ta gwada number shi ta, tayarda hankalin iyayenta, batasan gidan suba hakadai tahakura. Kwanan su Nasir daya a gidan momy suka nufi gida da isarsu Nasir ya wuce part dinshi Zainabu ma, haka wayarshi yafara dubawa miss calls yagani samada 40 ziro ido yayi kana yafara neman number saudat kira daya kamar jira take ta dauka muryarta alamun taci kuka ta gaji, kana tace mekyau ina kashiga muryar shi me kamada na mara lafiya yace mekyau banida lafiya nakusa mutuwa nikuwa nace Nasir anji maza.

Shagwabe fuska tayi kana tace dady na yace katuro iyayenka ,yunkurawa yayi dakyar yace ,mekyau nafada miki daga asibiti muke kimin hakuri anjima zankiraki saudat bahaka taso jiba amma tayi hakuri tunda soyaiyyar Nasir tarufe mata ido....?


contact-form


Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home