Saturday, January 22, 2022

Auren Wata Daya 8 to 9


Auren Wata Daya



                Auren Wata Daya

Page 8


Tana shiga dakinta tarufe kofa ta fada gado ta fashe da matsa naicin kuka tana fadinYa ilahi me nayiwa wannan bawan naka da baya kaunata.

Ya Allah ka sassauta min yanda nakejinsa a zuciyataYa Allah kasan ni mai rauni ce ina rokonka ka bani hakuri da juriyar da zan jure dabi'ar wannan bawan naka ya Allah nasan kai ka sanyamin soyayyar wannan bawa naka Allah ka sassauta min abinda nakeji, Wani sabon kukan takuma fashewa dashi kamar ranta zai fita.





























Yazo giftawa ta kofar dakinta yaji alamun sautin kuka, yanaji tasan abinda yayimata ne yasanya ta kuka tabbas yasan cewar bai kyauta mataba ko babu komai taci darajar soyayyar da takemasa.

Harya taba kofar da niyyar shiga komai yatuna kuma sai kawai yayi tsaki ya wuce dakinsa ya kwanta yanata tunani. Tana zaune har zuwa wani lokaci banda kuka babu abinda takeyi wayarta ce ta fara ruri Dauka tayi ta duba taga momy ce ke kira saida ta tsaya ta sai saita kanta domin bataso kwananta daya a gida mom tafara fahimtar cewar akwai matsala.

Saida wayar ta katse wani kiran ya shigo sannan ta amsa hadi da sallama. Sun gaisa da momy ta tambaye ta babu wata Matsala a gidan Babu komai momy tabata amsa tana murmushi.

Anan momy ta sanar mata su maryam suna hanya sun kirata bata shigaba sai yanzu mom din ta sameta. Shikenan toh mom sai sun iso Yawwa khairat sai anjima amma ki ringa hakuri da duk wani Abu dazaki fuskanta domin shi aure dan hakuri ne kinji.





























Tadamuwa mom zanyi kokarin yin hakan ki gaishemin da dady anjima zan kirashi.

Sunayin sallama ta tashi ta shiga toilet ta wanke face dinta tadan shafa powder ta sauko parlourn kasa ta zauna. Bata jima da zama ba taji ana taba belt din kofar tashi tayi ta bude kofar rahama ce a gaba ta taho da gudu ta rungume ta. Dau karta tayi tana fadin auta nayi missing naku sosai.

Ku shigo naga kuntsaya anan khairat ta fada tana kollon su Aisha dasu tsaya kawai suna kollontaShigowa sukayi suka zazzauna khairat na fadin shine baku bari sageer ya biyoku ba? Aisha ce tace wallahi munce yazo mu tafi momy tace a'a aishi namiji ne kawai ya zauna a gida. Ayya amma banji dadiba khairat ta fada tana mikewa ta nufi kitchen.

Jallof din taliya tafara kokarin dorawa maryam ta shigo tana fadin sister me zakiyi a kitchen kuma, Wallahi girki zan dora mana ta bata amsa tana greeting din kayan miya. 

Ayya bashshi kawai na dora mana tunda naga kamar taliya zakiyi ai? Eh ita zanyi domin itace zatayi sauki.

Toh kawo na karasa hada kayan miyan owk gashi ta mika mata tafara kokarin tsai da sanwa. Suna kammalawa khairat ta zuba ta mikawa maryam tace mika mana parlour barina zubawa rahama nata.

Harta juya zata tafi tadawo tace banga kin zubawa mai gidanba. Hawaye ne kawai suka fara zubo mata maryam ta kalleta race, na fahimta share hawayen naki karki bari Aisha ta fahimci komai zata iya fadawa hajiyar su daga haka dady zai sane share hawayen kawai ki fito muci abincin anjima zamuyi magana.



























Takawai tace taci gaba da abinda takeyi. Suna kammalawa Aisha tashiga ta wanke kayan da aka bata suka zauna suka fara fira. Lokacin sallah nayi suka tashi suka yi sallah Aisha ce tace sister wai yaya baya nan ne, Yanan bacci ya koma tabata amsa Owk shiyasa najishi shuru, bata gama rufe bakinta ba tajiyoshi tana saukowa daga steps din.

Murmushi yake yana fadin Aisha yaushe kukazo gidan, Wallahi tun dazu mukazo kanata bacciMurmushi yayi ya matsa kusada khairat yanawa rahama wasa Sai a lokacin maryam ta gaisheshi itama Aisha haka itako khairat kasa kallonsa ma tayiCikin sakin fuska ya amsa musu ya dubi inda khairat take yace Toh madam ni zan fita amma ba jimawa zanyi baDa mamaki take kallonsa wato shidai bayaso kowa yasan abinda ke tsakaninsu kenan.

Murmushi tayi tace toh yaya adawo lafiya Ameen yace ya juya ya kalli su maryam yace toh ni dai nayi nan inkun koma ku gaidamin mutanan gidan gobe insha Allah zan shigo Aisha ce ta iya cewa toh yaya Allah ya kaimu Ameen ya fada sannan ya fice abinsaSai wajan karfe 5:00 su maryam suka fara shirin komawa gidaYanzu maimakon kutsaya inya dawo saiku tafi tunda kunga ni kadai zaku bari a gidan khairat ta fada tana yiwa rahama rolling mayafin kanta.

Ki hakuri wata rana zamu dawo tunda kinga yanzu inna koma gida zan shirya na tafi nabar hajiya ita kadai a gida maryam ta fadaToh shikenan Allah ya kaimuHar sun shiga mota dayake a mortar Aisha sukazo maryam ta fito tana fadin nayi mantuwa.

Karasowa tayi inda khairat ke tasaye a gurguje tace anjima zamuyi waya dake banaso Aisha tasan abinda ake cikine shiyasa kikaga banyi miki maganaba amma jima ina komawa zamuyi wayaToh shikenan ki gaida min hajiya kinji Toh zataji ta fada ta koma mortar sukaja khairat tana daga musu hannu har suka fice daga gidanSaida takai kusan 5mins a tsaye sannan ta koma cikin gidan.

Page 9


Bayan sallah magarib tana aune parlour tana kallon wani series a Bollywood tana shan madarar holandia sabida batajin cin abinci kwata kwata.

Sallamar sace tasanyata dagowa ta amsa murya kasa kasa, Karasowa yayi ya nemi kujerar dake kallon tata ya zauna tana kallon ta tayi wani karamin tsaki kawai yayi ya maida hankalin sa kan TV din.

Daukar robar hollandian dinta tayi ta tashi da niyyar komawa dakin Binta kawai yayi da idanu saida tafara hawa steps din sannanya kira sunanta Tsayawa tayi kawai tana kallonsa amma bata dawo inda yakeba Ganin bata da niyyar komawa yasashi yin magana Wane irin iskanci ne kinaji ina kiranka kinwani tsaya kikam ko sokikeyi ni na tako nazo inda kike.

Girgiza kanta kawai tayi alamun a'a sannan tadawo ta zauna. Saida takai kusan 5mins da zama sannan ya kalleta yace Duk ranar da nakuma shigowa gidan nan ki kayimin irin wannan iskanci wato ga dodo ko daga shigowata kin wani kwashi kafa zaki koma daki.

Wai gidanma nakine, A hankali tace a'aToh karna sake ganin irin wannan sakarcin domin ni banason shashanci. 

Hawayen datake makalewa ne tafara bin kuncinta ta sanya hannu tana gogewa. Bude baki kawai yayi yana mata kallon mamaki sannan tace Wai ke wace irin sakarya ce daga magana sai kuka saikace wata karamar yarinya dalla malama tashi kibani guri wazakiyiwa shagwaba anan wajan yaja tsaki ya juya kansa yaci gaba da kallonsa Mikewa tayi tana goge hawayen dake bin face dinta Tana shiga dakin tasanya key ta fada gado tafara aikin kuka Saida taji kanta kamar zai fashe sannan ta tashi ta shiga toilet tayi alwala tazo rayi sallar issha tayi addu'o inta ta koma gadon ta dauki wayarta ta soma kiran maryam Ringing 2 maryam ta amsa wayar tana fadin Yanzu nake shirin kiranki sai gashi kin kira Bata iya bata amsaba sai wani kuka kawai data fashe dashiYa salam khairat meye haka kuma.


























Bakida wani aiki sai kuka dan Allah ni ki nutsu muyi magana wacce zata amfane ki bawai ki tsaya kinamin kuka ba please Dan Allah ki tsaya haka. Da kyar ta samu ta tsayar da kukan tace inajinki maryam, kinajina ko inajinki ai baki fadamin abinda yake faruwa ba bare nasan ta inda zamu fara Hannu tasa ta share hawayen dake tahowa tace Maryam tunjiya dakuka kawoni gidan nan ban tsinci ko Abu guda daga wajan yaya sadeeq wanda zai sanyani farin cikiba sai tsantsar bakin ciki kawai Dazu da safe ya kafamin wasu sharuda wai karna sake nayi kuskure indan zanyi jagwal gwalon girkina na hada dashi Sannan kuma duk wani damuwa da zai kunsamin kar nasake nabari wani yasani inayi kuskuren sanarwa wani saiyayi maganina a gidan nan bakigadai wulakanci kala kalaba komai nayi sai yayimin tsawa Haba khairat saikace ba mace ba ai wannan bawata matsala bace Ban gane me kike nufi ba wannan ne ba matsala ba.

Tabbas ba matsala bace Abu daya nakeso dake ki jajur ce ki cire wannan saurin kukan naki domin duk wani Abu dazamuyi indai baki daina wannan kukanba toh bamuda mafuta. Shikenan maryam zanyi kokarin ganin na daina insha Allah Yawwa ko kefa  sannan ki cire batun soyayya ki ajje gefe zuwa wani lokaci kadan ki nunawa yaya sadeeq kema ba wani sonsa kikeyiba sannan ki daina jin tsoronsa kwata kwata.

Sai da ta cire wayar a kunnanta tace tabdi jan sannan ta maida tace Haba Maryam sokike nayimasa tsiwa ya zaneni acikin gidan nan dagani saishi. Dariya maryam ta sheke da ita sannan tace haba sis Sanin danayi miki tun muna school bakida tsoro amma meyasa kike tsoron yaya sadeeq, wallahi nima bansani ba maryam na fahimta yanzu dai dole ki daina jin tsoronsa kuma komai da gayya zaki ringa yinsa a gidan nuna masa zakiyi ai ba zaman aure kukeba tunda shima haka yake nuna miki kawai zaman wucin gadine tsakaninku.

Nan dai maryam ta gama tsara mata yanda zata kunta tawa sadeeq domin bazai yuwa yaringa gasataba kuma tabbas dolene ta nuna masa cewar itama macace tunda basuda isheshshen lokaci tunda zaman wata daya ya bukata dole su koya masa hankali kafin lokacin.

Suna raha suka gama wayar khairat ta ajje wayarta tanajin duk damuwarta ta fice a ranta afili taceTabbas yaya sadeeq bazakaci bulus ba sai yanzu na fahimta kanaso kayiwa iyanka biyayya ne saboda karsuyi fushi da kai shiyasa ka aureni nanda wata daya ka kulla wani tuggun da bazasu ganeba ka sake ni Shuru tayi saboda wani tunanin datayi afili tace Toh wane irin shiri yaya sadeeq yayi wanda su dad da mom bazasu ganeba.
























Batada amsa don haka tayi murmushi kawai tace muxuba nida kai, Nima dai gyara zama nayi nace barina zuba ido naga anya khairat zata iya kuwa...?

contact-form

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home