Friday, January 21, 2022

Adu'ar Da Yata Hanifa Tayi Kamin A kasheta - Mallam Abubakar



Hanifa


Hanifa Wanda Aka Kasheta Bayan Kwana Arba'in Da Bakwai (47) Kamin Aka Samo Gawarata

Yan uwan wanan yarinyar ko zamuce danginta na wanan yarinyar nan Hanifa da ake zargin malaminta ya sace ta, tare da kashe ta, kana yakuma binne gawarta a gidansa a jahar Kano na ci gaba da alhinin rasuwarta. 

A Ranar Alhamis ne rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da gano gawar Hanifa Abubakar a wani kabari da aka binne ta bayan an kashe ta. Cikin kuka da hawaye, mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdussalam, ya shaida cewa ga manema labarai cewa, sun shiga cikin mummunan tashin hankali sakamakon lamarin da ya faru, har ta kai ga an kwantar da mahaifiyar marigayiyar a asibiti ko magana bata iyayi.

Lokacin da mahaifiyar ta samu labari ta kaɗu, mun kai ta asibiti yanzu haka an sa mata ruwa an ba ta magunguna, ba ta iya ko cin abinci kullum sai kuka, ni kaina bana iya cin abinci ba na iya barci in ji shi. Ya ƙara da cewa, Ina ofishin Hukumar ta (DSS) aka kirawo ni aka sanar da ni cewa ga shi an gano gawarta, don haka suka ba ni haƙuri suka ce ƙaddara ce daga Ubangiji in yi haƙuri."

Wasu abubuwanda zan rika tuna Hanifa dashi

Mallam Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa ƴarsa Hanifa yarinya ce mai haba-haba, kullum fuskarta cikin annuri ba ta da wata matsala kuma mutane da dama da suka san ta za su shaida ta hakan.


Hanifa yarinya ce da duk wanda ya san ta a unguwa makwabta da dangi ya san cewa tana da basira da hazaƙa, ba wanda take so kamar babanta, kuma yanzu ga halin da ta rasu a ciki," a cewewarsa shi ma haifinata Mallam Abubakar.


Sai dai ya ce ya yi imanin cewa abun da ya faru jarraba ce daga ubangiji. ''Shi dama ubangiji yana da hanyoyin jarrabarsa da abubuwa da yawa, don haka wannan ba jarabawa ce'' in ji shi. 











Maganan da nayi ta ƙarshe da Hanifa'



Magana ta ƙarshe da na yi da ita ce wadda na yi da ita ranar da za a sace ta, ta zo za ta tafi makaranta mahaifiyarta ta ce Hanifa ba ki yi addu'a ba, ta ce na yi, ta sake yi tana cewa 'Bismillahi Tawakkalt Alallah', tana yi da ƙarfi don ta ji cewa ta yi ɗin, ina ce mata to Hanifa kin yi, na yadda kin yi yanzu, ta tafi ta je tana sallama da mahaifiyarta, tana ce mata tun da za ki tafi kasuwa idan kin je ki taho min da alewar madara ina son zan yi sadaka da hannuna," a cewar Malam Abubakar.


Ya ce lokacin da ya samu labarin an kama mutumin da ya sace ta ɗin ya ji daɗi, bisa tsammanin cewa zai nuna wurin da ya ɓoye ƴarsa, amma daga baya sai ya ji abun da ya saɓa da hakan.


Ya kuma shawarci iyaye su ƙara zage dantse wajen kula da ƴaƴansu, sannan a ci gaba da addu'ar Allah ya ba da zaman lafiya mai ɗorewa.

SAURAN BAYANEN



A ranar Asabar 4 ga watan ta Disamban shekarar da ta ƙare ta 2021 ne aka sace Hanifa mai shekara biyar a unguwar Kawaji da ke birnin Jahar Kano.


Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku. Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu Hanifa, saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu, a cewar Suraj Zubairu, kawun Hanifa.

Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a daidaita Sahu kuma suka ce za su kai su gida.


Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita."


contact-form

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home