Monday, March 21, 2022

Rahotanni Game Da, Yadda Jirage suka Kashe Shugaban ta ISWAP Dake Jahar Borno





Lugudar Wutar Da Sojojin Sama Ta Nigeria Sukayi, Har Yayi Sana Diyar Mutuwar Jagoransu





Bayanai sun ce mai yiwuwa an kashe jagoran kungiyar ta Wanda aka fisani da ISWAP na yankin yammacin Afirka, mai suna Sani Shuwaram.

Rahoton sun ce  shi Shuwaram da wasu mayakan sa ta kungiyar sun rasa rayukansu ne sanadiyar wani hari ta sama da sojojin Nigeria da ke yankin Marte na jihar Borno ta arewa maso gabashin  ta Najeriya. 

Ta shoshin yada labarai ta Nigeria ta bayyana cewa jiragen saman Najeriya ciki har da super Tucano sun yi lugudan bama bamai a yankin da Shuwuram ya kafa sansanin sa.

Bayanai sun ce Shuwaram ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da ya samu a lokacin da jiragen yakin suna lugudar wuta suka kai farmaki sansanin ISWAP da ke yankin Sabon Tumbuns na tafkin Chadi. Kafar ta PRNigeria ta ce wata majiyar tsaro ce ta tabbatar mata da kisan Shuwaram.

Shuwaram yana daga cikin 'yan ta'adda da rundunar sojojin sama ta kai wa hari a Sabon Tumbuns kusa da Kirta Wulgo a watan Fabrairun 2022.














 Hare-haren da aka kai ta sama daga bisani sun yi sanadin mutuwarsa tare da wasu mayakan ISWAP da ake yi wa jinya ciki har da Abu Ibrahim al-Hashimi al- Kurayshi, in ji majiyar .

Sai dai kafar ta PRNigeria ta ce bayanan da ta samu sun ce an zabi Mallam Bako Gorgore a matsayin sabon shugaban kungiyar ta ISWAP wanda zai maye gurbin Shuwaram.

Air Commodore Edward Gabkwet, Ya kuma shaida wa manema labarai cewa sojojin sun kashe 'yan ta'adda amma ba a tantance ko su wane ne ba. Ya ce abu ne da ke bukatar a yi bincike kafin a sanar.

A watan Nuwamban shekarar 2021 ne mambobin Majalisar Shura na ISWAP suka nada Shuwaram, mai shekaru 45, a matsayin sabon shugaba kungiyar.

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home