Yadda Kasa Yarushe Akan Ango Da Abokansa Suka Mutu.....
Yadda Kasa Ta Danne Ango Da Abokansa Su Huɗu Har Suka Mutu a Kano Yayin Taya Shi Gina Gidansa.
Wannan shi ne mafi munin bala'in da muka taɓa gani a wannan ƙauyen namu, rasa matasa biyar da ke kan ganiyarsu a lokaci ɗaya. "Ba mu taɓa ganin haka ba, bai taɓa faruwa a wannan yanki namu ba, kuma muna fatan kar ya sake faruwa."
Wannan shi ne abin da ɗaya daga cikin ƴan uwan mutum biyar ɗin da zaftarewar ƙasa ta yi sanadin mutuwarsu a ƙarshen mako a ƙauyen Yanlami da ke Kano a arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan shi ne abin da ɗaya daga cikin ƴan uwan mutum biyar ɗin da zaftarewar ƙasa ta yi sanadin mutuwarsu a ƙarshen mako a ƙauyen Yanlami da ke Kano a arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne wata guda kafin a yi auren ɗaya daga cikin matasan mai suna Jubril Musa, mai shekara 25. Matasan sun taru ne don taya abokin nasu da zai angwance wato Jubril gina gidan da zai zauna shi da amaryarsa, kamar yadda ake yi a bisa al'adar garin.
Musa Mohammed shi ne mahaifin angon, ya na cewa ya san shirin da abokan suka yi na taya ɗansa ginin, kuma ya ma gan su da daddare suna tattauna yadda tsarin aikin zai kasance.
Mu a kauynemu haka ake yi, abokai su taru su taya abokinsu gina gida idan an sa ranar aurensa. Shi ma Jubril a baya ya sha taimakon abokansa wajen gina nasu gidajen idan za su yi aure. Ganina na ƙarshe da shi kafin faruwar wannan iftila'i shi ne ran Juma'a da daddare, ya zo ya gaishe ni kafin ya tafi kwanciya bacci, ammafin sannan na gan shi da abokansa a waje suna tattaunawa kan yadda za su tsara aikin ginin. Malam Musa wanda ke da wasu ƴaƴan har shida ya ce mutuwar ɗan nasa ta girgiza shi, amma ya sanya wa zuciyarsa cewa haka Allah Ya ƙaddaro.
Wannan shi ne abin da Allah Ya tsara faruwarsa, kuma mu a matsayinmu na ƴan adam ba za mu iya dakatar da faruwarsa ba. Ina addu'ar Allah Ya jikansu shi da abokan nasa Ya haɗa mu a aljanna.
Yadda Al'ammarin Ya Faru
Hashim Yunusa abokin Jubril ne kuma shi da wasu ganau ɗin biyu da aka yi a gabansu sun bayyana yadda abin ya faru. Yadda aka tsara shi ne su biyar za su shiga cikin rami su dinga tono ƙasa suna wato ta waje ni kuma ni da Sani sai mu dinga tattara ƙasar a cikin amalanke don kai wa wajen ginin.
Har mun kai sawun farko har muna wasa da zolayar juna, mun tafi mun kai sawu na biyu muna komawa sai muka hango ƙura ta turnuƙe sai muka yi gaggawar ƙarasawa wajen inda muka tarar dukkansu ƙasa ta rufe su sai hannu ɗaya kawai muke iya gani.

A nan ne muka ruga da guda zuwa cikin gari don kiran jama'a, kan kace kwabo wajen ya cika da mutane har ma daga maƙwabtan ƙauyukan don a ceto su amma cikin rashin sa'a a lokacin da aka ciro su duk sun mutu.
Daya daga chikin abokin ango
Hashim ya ce wannan lamari da ya faru a ranar Asabar da safe abu ne da ba zai taɓa iya mantawa ba a tsawon rayuwarsa. Wani kawun Jubril ya ce ko da aka kira ƴan kwana'kwana sai da aka yi awa guda kafin su isa ƙauyen Yanlami, kafin sannan tuni ƴan ƙauyen sun ciro gawarwakin. Sai bayan awa ɗaya suka iso nan, a lokacin tuni mutane sun ciro gawarwakin daga cikin ramin.

Saminu Yusuf, shi ne mai magana da yawun hukumar kwana, kwana ta Kano, ya kuma ce an kira su a waya ne da misalin ƙarfe 11:32 na safiyar Asabar sannan sun isa wajen da ƙarfe 12:05 na safe. Abin da muka yi shi ne miƙa gawarwakin ga rundunar ƴan sandan ƙaramar hukumar Bichi da kuma Dagacin ƙauyen Yanlami. Saminu ya kuma bayana cewa wannan iftila'i abu ne marar daɗi amma wanda da an bi tsari da za a iya guje masa.
Abin da muka sha gaya wa mutane shi ne su dinga kula kan irin wadannan abubuwan, duk sanda suke son tona rami don tara ƙasa su daina raja'a a ɓangare guda saboda hakan zai iya jawo zaftarewar ƙasar, don haka dole a dinga kula.
Lokaci na ƙarshe da irin wannan ya faru a baya-bayan nan shi ne lokacin da wasu mutum shida suka mutu a ƙauyen Bauli sakamakon irin yanayin da su Jubril suka rasu.

Yadda Yataba Faruwa a Baya Baya.
Lokaci na ƙarshe da irin wannan ya faru a baya-bayan nan shi ne lokacin da wasu mutum shida suka mutu a ƙauyen Bauli sakamakon irin yanayin da su Jubril suka rasu.
Lamarin ya faru ne ranar 13 ga watan Fabrairun 2020 a lokacin da wasu mutum shida suke tona rami don tara ƙasar da za su gina gida.
Wanne Mataki Yakamata a Dauka.
Sani Musa wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a jihar Kano ya ce, rashin dokoki ne ke jawo faruwar irin wannan lamarin. Tsawon shekaru a yanzu mutane suna yawan haƙar ramuka don kwasar ƙasa kuma babu wata hukuma da ke duba yadda suke gudanar da lamarin. An yi bakam kamar ba abin da ke faruwa, don haka ne irin wannan abin da ya faru a Yanlami ke ci gaba da faruwa.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home