Tun Ina Karama - 17 to 18
TUN INA KARAMA
Page 17
Cikin azama ya karasa wurinta tare da fisge wayarsa a hannu jamila wani mugun kallo yayi mata wanda sai da zuciyarta ta buga saboda tsoro amma cikin dakewa ta ce masa"daga na taimaka na amsa maka ma shine zaka wani karya mani hannu, "uban wa yace ki daga mani waya.
Yusuf ya tambayata cikin tsawa da hasala ke dai wallahi baki da hankali baki san ciwon kanki ba am last waning kika kara shiga hurumin da ba naki ba sai na ci ubanki nonsens fita yayi batare da ya kara saurarar ta ba, cikin jin zafin abun ta juya itama ta bar wurin.
Zubewa kasa tayi batare da tace komi ba hawaye ne kawai ke zuba a idonta matsawa nabila tayi tana girgizata hawwa gaya mani don Allah me ya faru kallon nabila hawwa takeyi cikin kuka " hawwa tace nabila yaya ya cuceni ashe yana da yan mata awaje wadanda ya ajiye yanzu cikinsu ne wata ta daga wayarsa bata boye mata komi ba ta fada mata cikin rashin fahimta nabila ta bude baki zatayi magana wayar nabilace tayi kara gaba dayansu dubansu yakai ga screen din wayar sunan yayane ya baiyyana a wayar nabila.
Cikin sauri ta daga tare da sallama bai tsaya amsa gaisuwarta ba ya tmby ina little? "yaya ban san ya akayi wata ta dauki wayarka ba ta fada mata magana gashi can kuka takeyi kuma ta jefar da wayarta ta fashe, abunda yake zargi ya tabbata "cikin damuwa ya ce wallahi nabila caji nasanya na shiga inyi alwalla jamila ta daga mani waya kuma ke kin san jamila bata da hankali.
Nabila cikin mamaki tace aunty jamila?tabbas zata iya amma menene ribarta in tayi haka? katse mata tunani yayi da cewa ki hadani da hawwa, to yaya ta amsa tare da mika ma hawwa wayar wadda tunda suka fara magana take saurarensu amsa tayi tare da sake fashewa da kuka bata yi magana ba shikam jin kukanta yakeyi tamkar saukar wuta a zuciyarsa cikin damuwa yace little nima kukan kiso inyi ne.
Ya tambayata cikin rauni girgiza masa kai tayi kamar yana kallonta ya cigaba da cewa don Allah littel kiyi hakuri wallahi ban san komi ba shirin jamila ne kuma wallahi zanyi maganinta please my sweety nah kada kowa yaji wannan maganar ku barta daga ke sai nabila please ya kara she magana cikin sanyi murya "cikin damuwa tace ni yaya ban san me nayi ma aunty jamila ba ta tsane ni haka? amma ya dace ta fada mani wannan mgnr me nayi mata.
Bin wayar yayi da kallo yana smile, ita ko dariya takeyi nabila ma dariya takeyi suka rungume juna nabila na jin dadin yanda hawwa take daukar shawararta akan lokaci kuma tana tir da halin yayarta na son zuciya.
Haka suka warware babu wanda yasan abunda ya faru tsakanin su. suka gyara jikin su suka fito wurin kawayensu cikin jin dadi.haka shima yusuf yaji dadin yanda littel ta fahimce shi kuma ta yafe masa i love her ya furta tare da fita daga cikin motar tunda dama ya yanke shawarar zuwa gidan ne idan har hawwa bata fahimce shi ba to ya gode ma Allah da shedancin wannan makirar baiyi tasiri akan su ba Allah ka shiga tsakaninmu da ita nima Amin nace yusuf haka abubuwa suka kasance har dare karfe 7:30 motocin kai amarya sun cika unguwa hawwa ta sha kwaliya da wani less sky blue komi na jikinta sky blue ne abunka ga farar fata abun sai wanda ya gani.
Gamin kya suna pallor Abba aunty zainab ce rike da hawwa ummah na zaune kusa da Abba sai mami dake gefe sai hajiya kaka da itama tana kusa da Abba yusuf ne jikinta sai aunty rabi atu da itama tana wurin hakika yau naji abunda ya girgizani na bani tarihin rayuwata ashe mamice mahaifiyata ummah mahaifyar yusuf gaskiya na shiga rudani asheni marainiyace wanda ban taba sanin maraici ba gaskiya ina jinjina ma Abbah da ummah da yan uwan mami da ita kanta mami shima kuma yusuf ya cancanci a yaba masa kuka nakeyi wanda babu mai iya tsaida mani shi ashe picture din danke gani adakin ummah shine mahaifina Alhaji mansir kanin ummah da akace ya rasu.
Bayan ankai ni gidansa dake barhin wanda ya tsaru yayi kyau sosai haka daga nan muka shirya zuwa wuri dinner wadda umar ne ya shirya komi su kansu kayan zuwa wurin dinner ya sha banban da namu na nan don komi daga india aka kawu mana kayan da zamu sanya wurin jamila bata san da wannan shirin ba hankalinta ya tashi sosai ganin wannan shirin namu duk sai ta raina kanta mune karshen tafiya umar ne zai kaimu daga ni sai yaya sai umar da ke jan motar zaune muke abaya hannuna cikin nashi yake rada mani akunnena wai idan munje don Allah bai son inshiga da kunyata in ajiyeta baki kofar mota kafin in fita murmushi kawai nakeyi duk abunda mukeyi umar na kallon mu ta madubi dariya kawai yakeyi har suka isa hall din dai bakin kafar yayi parking da sauri ya bude ya fito ya zagayo ya bude masu kofa kama hannunta yayi suka fito tare ai aka shinfida kafet tunda ga wurin motar har zuwa ciki ga masu binsu da flower suna watsa masu ga kida na tashi abun gwanin ban sha awa haka suka isa har wurin da nasu ne na musamman wapre table suna zama kowa ya zauna sai tafi rab ke tashi nan da nan ya fara jawabi babu wanda amarya da ango basu birge ba haka aka kira babbar kawar amarya tabada tarihin amarya wanda kowa sai da yayi dariya haka nabila ta koma ta zauna aka kira umar shima yayi bayanin ango wanda duk maganar da sukeyi da turanci sukeyinta sbd abokansu da basa jin hausa haka mc ya kira amarya da ango suka shigo fili haba dan da na wuri ya kaure da ihu ana tafi umar kuwa tunda ya balle dolars zuba masu kawai yakeyi haka sauran abokanin su suma dolars ce kawai ke yawo wurin cikin hikima jamila ta shiga filin ta fara zuba nata kudin akan amarya da ango da dabara ta kama rigar hawwa tasa reza ta jata ai ko nan da nan bayanta ya baiyyana umar ne kadai yaga abunda tayi cikin azama ya iso ya rike hannun jamila jikake pes, pes ya dauke jamila da mari jin karar marin sai hankalin mutane ya dawo gare su.
Masha Allah godiya nake kawata sibara madugu present tace masoyan Tun ina karama ina godiya Allah yabar zumunci.....?
Page 18
Agaskiya ke muguwa ce bayan sharrin da kika hada dazun yanzu kuma kin zo da wani cikin takaici nabila ta girgiza kai tace kaicho da kika zama yar uwata ta jini amma walhi baki iya raba hawwa da yaya yusuf duk makircin ki "umar ne ya jawo nabila yace mata kyaleta sister cikin baki ciki ta sake ta tana kukan takaici " umar ce ma yusuf ya bar wurin da hawwa shi takaici ma ya hana shi cewa komi ita ko hawwa hankalinta yayi mummunan tashi hannun ta ya kama batare da yace komi ba suka bar wurin mutane da ba kowa ya fahimci komi ba kowa sai ya koma hidimarsa yasu yasu ne kawai suka san abunda ya faru cikin family din.
yusuf na fita daga hall din wurin motar da suka zo da ita ya nufa ya bude ya zaunar da hawwa wadda ta zama kamar wata status saboda mamakin jamila yana shiga ya tada motar batare da ya tsaya sauraren komi ba ita ko hawwa tana shiga motar taji wani kuka yazo mata wanda tun dazun take son yinshi amma yaki zuwa bai ce mata komi ba sbd iyakar bacin ran dake zuciyarsa yayi yawa shima da zai samu yayi kukan wata kila daya samu sauki aransa.
Umar koda yaga dare ya fara yace ma kannen sa duk su hadu a maida su gida sauran abokai kuma sunata tambayar ango da amarya saidai umar yace wani uzurine ya taso suka tafi haka dai cikin hikima ya sallami kowa nabila kuma da nafisa dasu ummi suka hada ma hawwa gift dinta da abokanin yusuf suka bata direct gidan hawwa suka wuce don nan zasu kwana.
Jamila gida ta wuce tare da cewa sai tayi maganin umar saboda shi bai isa ya wulakanta ta ba kuma itama nabila zatayi maganinta da wannan tunanin ta isa gida zuciyarta na zafi don bakin ciki nikam nace yanzu kika fara bakin ciki jamila.
Koda suka isa gidan hawwa sun isketa kamar wani abu bai faru ba harta canza shiga kowa yaji dadin ganinta cikin walwala lallai hassada ga mai rabo takice, " nabila ce tace amarya ina angon yayanmu cikin tsokana da jan fada "nafisa tace inaga ma fa mu da gida muka wuce harararta hawwa tayi tace" kyaji dashi ma gulmaciya dariya sukayi gaba daya daidai lokacin da yusuf yake fitowa daga part din shi shima ya canza kaya gaba dayansu shiru sukayi ganin fitowarsa har ya karaso inda suke sannan cikin kulawa yace"har kun dawo yanzu zaku dameta kuma dariya ya ba kowa amma saidai babu halin yi, cikin kasa da muryarsa yace"little ba rakiya mikewa tayi batare da kallon su nabila ba tabi bayansa binta sukayi da kallo kawai suna fita ya rungumeta cikin husky voice dinsa yace little yanzu shikenan in tafi in barki eh na daga kaina cikin sanyin murya nace "mashi kaga su aunty duk sun iso suna ciki kaga no need ace kana cikin mu tunda yanzu haka in ba su nabila ba babu wanda yasan kana gidan nan nisawa yayi yace haka na aidai daga gobe shikenan ko.
Duk abunda ke faruwa tsakaninmu umar na mota yana kallonmu in banda mamakin abokin nasa babu abunda ya keyi akasalance ya bude motar ya shiga ya zauna cikin tsokana umar yace ai na dauka da ita zaka tafi freind yana dariya " yusuf wanda yanayinsa ya canza yace sunzo sun cika mani gida tayaya zan samu sakewa da matata ai dai daga gobe a kyalemu mu huta ko? "umar yace ai naga alamar ka koya mata rashin kunya itama.
Washegari haka gidan hawwa ya kara cika saboda walima hawwa yau ma shiga kawai takeyi tana fita duk kayan data sai an kalleta an kara kallo haka akayi komi cikin jin dadi kuma tasha nasihohi sosai kannen mami da yan uwanta haka suka zo suna tayi mata nasiha.
Anyi komi cikin mutunci angama yanzu gida ya rage sai su nafisa da nabila da wasu kawayensu suna jiran zuwan ango su tafi gida su ma.don aunty zainab ma dubara tayi zata dauko wani abu daga nan tasamu ta sulle don riketa tayi wai ba inda zata, daga shi sai umar suka zo gidan karfe 8:30 haka suka shigo da ledoji tare da sallama babu wasa tsakaninsu shiyasa gaisuwa kawai sukayi umar ya ce su tashi ya maida su gida.suna tashi nima na mike na rike nabila kallona suka tsaya yi ganin da gaske ne yusuf yazo ya rabani da jikin nabila nasake fashewa da kuka haka ina ji ina gani suka tafi suka barni da kewa da tunanin sabuwar rayuwar da zan shiga.
Masha Allah kuji dadinku amarya da ango amma fa zan dawo don don malama Amina tace ban isaba sai gano masu ya yusuf zaiyi da yar kanwarsa zai tausaya mata ne ko kuwa to ba ruwana nidai....
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home