Friday, February 18, 2022

Tun Ina Karama - 15 to 16

 

readerglobe.com.ng


       TUN INA KARAMA


Page 15

K wanannn Abbah biyu da dawowa ya kira hawwa da yusuf domin basu hakkin su na tabbatar mashi da son junansu gaba dayan su sun tabbatar da cewa suna kaunar junansu "masha Allah Abbah ya furta bayan jin ta bikinsu tare dayi masu fatan Alhairi, bayan fitar su ne Abbah ya kalli umma wadda take zaune gefensa kana kallonta kasan tana cikin farin ciki yace hajiyatah insha Allahu zan tabbatar maki da cika alkawarinki da kika dauka batare da wata matsala ba." Cikin jin kunya ta ce nagode Alhaji Allah ya kara kauna jawo ta yayi jikinsa tare da cewa Ameen khadinaga alamar dai Abba da umma soyewa za'ayi shiyasa na rufe masu kofa na dawo ma yaran nasu masu juran gadosuna zaune a falo daga gani suma cikin farin ciki suke hawwa ce tace yaya zan shiga in kwanta nasan nabila na can tana jirana , cikin tsokana irin tashi yace "ai dai tsan tare kike da mijinki ko? cikin jin kunya tace haba tun yanzu ai nabila bata cancanci haka ba, nasani ya bata amsa amma ai nasan gulma zaku kuyi ko kafin kuyu bacci haba yaya mu kuma gulmarwa zamuyi? ta tambaya shi tana dariya tawa mana ya bata amsa" to me kayi ta tambayan shi.















Kice mata ina sonki kamar in kashe kaina to fah ta zaro ido tare da dafa gabanta cikin shagwaba tace ai ba sai na fada ba kowa ma ya sani tashi yayi yace to tashi ki shiga nima zanje in kwanta cikin jina danayi nayi missing dinshi muryata a sanyaye nace saida safe yayana , daga mani hannu kawai yayi tare da shigewa part dinsa haka muka rabu tare da kewar junanmu.

Labari ya isa ko ina aurena da yaya yusuf wanda har kankiya wurin hajiya kaka ta bada goyon baya dari bisa dari haka mahaifin ummah tare da sauran yan uwa kowa na murnar auren sai dai ta bangaren hajiya mariya da jamila abun yazo masu a bazata wanda hajiya mariya saida taje har kankiya wurin hajiya kaka tayu korafi akan umma ta gaje masu komi na dan uwansu kuma sannan dole ta hada auren yusuf da hawwa, hajiya kaka taka mata birki tayi nacewa kada ta kara zuwar mata da irin wannan maganar banzar idan bazatayi masu fatan Alkairi ba to tayi shiru da bakinta.

Haka ta koma jiki ba kwari jamila kuwa hankakinta yayi mummuna tashi wanda ya kaiga har ciwo tayi saboda damuwa ana cikin wannan halin ne kawar hajiya mariya ta bata shawara akan su nemi mafita tun wuri kada ta jazama diyarta  wahala haka kuwa akayi don ta nemo masu mafita wurin zuwa wani kauye dake kafur wurin wani boka da yake can, da wannan shawarar suka yanke zuwa wurin bokan, haka suka kama hanya suka tafi batare dajin tsoron komi ba bare shakkar ubangiji Allah ka tsare mana imanin mu Ameen ya Allah.





















Haka suka kurda cikin dajin wurin wannan mushiriki koda suka isa kafin suyi masa bayanin komi yace basai sun fada ba yasan da zuwansu haka ya zaiyyana masu komi kamar yadda suka sani cikin wata irin dariya to yace masu kar ku damu akwai nasara amma ba yanzu ba saboda wannan auren sai anyi shi kuma duk wanda yace zai raba to zai mutu ne amma bayan auren muna iya juyar da hankalin shi yaron akan diyarki yaji duk duniya bashi da kamarta kuma ko uwarsa da take tsaye akanyi mashi Addu'a bazai saurareta ba har sai ya auri diyarki abisa sharadin bazata taba yarda ta haihu dashi ba saboda shi mutum ne mai son haihuwa kuma har matar daya aura itama bazata haihu ba mudin ta yarda ta barta ta haihu to komi ya lalace  kuma da zarar haka ta faru to ni ba ruwana don zai tsani diyarki fiye da tsanar da yakeyi mata yanzu  kin amince za'ayi aure nan ba da dadewa ba amma ba haihuwa cikin tsoro mariya ta kalli kawarta ita kuma ta daga mata kai alamar ta yarda cikin sauri hajiya mariya ta amsa data amince boka yace to ku tashi ku tafi sai bayan an gama hidimar bikin shi da wannan yarinyar zaku dawo akwai abunda zan baku da zarar sun hadu shikenan angama to boka mun gode ba ayi mana godiya ku tashi ku tafi haka suka tashi jiki na rawa ta bude jakarta ta debo kudi batama san ko nawa bane ta ajiye mashi tunda ya juya bai sake yi masu maganan ba har suka bar wajen.












Suna cikin tafiya ne hajiya mariya ta kalli hajiya lami kawarta"tace anya lami jamila zata amince da sharadin bokan nan kuwa?dariya tayi tace to ai ba fada mata zakiyi ba cikin hikima zaki nuna mata kada ta yarda ta saki jiki ta haihu yanzu saboda haihuwa na sanya tsufa ta bari tukunna sai nan gaba kuma sannan duk yanda za'ayi kada ta bari wannan yarinyar ta haihu saboda za'ayi zarginta ace itace bata son haihuwa tunda tafita wayo da gogewa."kai lami shiyasa nake son harka dake gaskiya kin kawo shawara nagode sosai "kai haba kawata ai wannan yima kaine to ba komi komi zaiyi daidai zan nuna mata ta saki ranta lokaci ne kadan tafawa sukayi tare da shewa a haka suka koma katsina cikin farin cikin samun mafita Allah ya tsare mana imaninmu Amin ya rabbi.

Shiri akeyi ta ko ina acikin family don yanzu haka na aunty zainb taje dubai ta hado lefe tunda bikin wata dayane aka sanya haka cikin hikima mami tace ummah ta barta tazo kaduna ta kwana biyu saboda akwai wata kawarta yar maiduguri ce tana yin gyaran amare haka kuwa akayi saura sati biyu ummah ta sanya yusuf ya kai hawwa kaduna ita da nabila don nabila tace bata iya zama ita kadai tunda aunty zainab da nafisa ta tafi dubai haka yusuf yaji ba dadi duk da dai ya kasa fahimtar komi kuma mami tace mashi basai yazo kaduna ba tare zasu dawo katsina da hawwa in lokaci yayi.

Tabbas wani kaya sai amale hakika mami ta kashe kudi wurin gyaran diyarta don gaskiya ina tausayama yusuf ko kuma ince yusuf zai shiga gidan alfarma nayi shiru aunty zainab ta dawo ta hado kaya kam nagani na fada kowa ya gani sai ya kara kallo koda jamila tasamu labrin irin lefen hawwa ai saida ganin kwaf dinta yasa mata ranar ta kasa bacci saboda tsakani da Allah sun zubda kudi kamar basu san ciwon su ba hankali tashe ta bar gidan umma saboda tsabar hassada.

 Gidan yusuf dake barhin aka tsansarama hawwa kayanta wanda aikin Abbah ne wanda ya hana kowa yin komi yace shi ya dace yayi a gaskiya gidan hawwa ya hadu kamar a turai komi nata lemon green an white sunyi kyau sosai hidima tazo yau saura kwana biyar haka yusuf ya matsama mami don Allah su taho haka nan saboda akwai abokaninsa a zasuzo da sukayi krtu daga indian zasu fara programm haka mami ta tattaro iyalanta helux biyu sukayo zuwa katsina ta dikko dakin kara kunya gareku ba dai tsoro ba koda suka iso gida ya fara cika ita kanta umma mamakin canzawar diyarta tayi masha Allah kawai take fadi tare da godiyar Allah da ya ba danta wannan mata kowa yaba kyauwun da hawwa tayi yakeyi lokacin da suka iso yusuf  nacan dashi da umar suna busy bai samu shigowa gida ba sai da yamma likis kuma gida ga mutane dole ta baya ya shiga ya nufi part din shi yana shiga ya nufi bedroom dinsa sai yaji kamar motsi cikin sauri ya karasa tare da bude kofar daga ita sai towel daure jikinta ganin mutun yasa ta saki wata irin karaaa! wadda saida shikanshi yayi saurin juyawa a sukwane ya rufe kofar gam...

Page 16

C ikin sauri ya juya tabbas hawwa ce amma me takeyi haka a dakinsa dama yana mamakin ganin part dinsa bude amma bai tantance ba saida ya ganta, dawowa yayi falon ya zauna bisa kujera yana jiran yaga ikon Allah, hawwa komawar da yayi ya rufe kofar shine ya bata damar sanya key ta rufe kofar cikin tsananin tsoro tare da zama bisa gadon ta dauki turarukan da zatayi amfani da su ta cigaba da shafawa tare da humrar da zatayi amfani da ita.















Cikin fargaba da tsoro takeyin komi acikin ranta tana cewa dama bata biye ma su nafisa ba da suka bata shawarar zuwa part din shi ta shirya saboda mutane ko ina amma babu wanda yayi tunanin dawowar shi yanzu tunda ansan shi ba mai son hayaniya ba, zaune yake yana tunanin koma ya tashi ya tafi gidansu umar ne, amma bari ya jirata yaji me ya kawota ne? tana gamawa ta dauki rigarta ta sanya ta dauko hijabinta ta sanya ta hada komi nata ajakar data shigo da ita ta zura takalminta ahankali ta tako bakin kofar kamar munafuka haka ta sanya hannu ta murza key din kofar ya bude ganin shi datayi zaune a pallow yasa jikinta kyarma cikin dauriya ta karasa fitowa batare data sake kallon inda yake ba shiko kallo daya yayimata yayi tasbihi ga Allah gaba daya yarinyar ta canza mashi tayi wani irin kyau ga jan lallen nan ya zanu ajikinta.

Rabawa tayi zata wuce shi batare datayi mashi magana ba cikin sauri ya tashi ya rike mata hijabi saurin juyowa tayi tana kallonsa a tsorace murmushi yayi mai kayatarwa yace me kikeyi adakin mijinki? tambayar tazo mata abazata cikin inda inda tace mutanene adaki na shiyasa nazo in yi wanka anan bansan zaka dawo yanzu ba amma kayi hakuri."saboda kinzo dakin mijinki kike bani hakuri to  amma hawwa ko ki kirani kice kin iso bakiyi ba, ta lura son janta yakeyi da magana "yaya ai ni tunda muka iso kaina ke ciwo bacci nayi yanzu ma tashi na kenan nazo nan.












Murmushi yayi" yasan fadi kawai tayi cikin hikima ya sakar mata hijabi saboda yaji yanayinsa ya fara canzawa ok shikenan yanzu kin gama komi kika fito ya tambayeta saurin daga masa kai tayi alamar eh sbd a takure take saboda wani irin kallo daya keyi mata are you show? yasake tambayrta?"yes tabashi amsa ok jeki sai na fito tom ta amsa tare da saurin fita daga dakin kallonta ya tsaya yi yana dariya kasa kasa don yaga yadda take hade step.

Tana fitowa ta yi wata ajiyar zuciya tare da gode ma Allah don gaskiya taji kunyar ganinta dayayi wai har yana cewa tazo dakin mijinta kai yaya yusuf shi baima jin komi haka yake sakin mgn ba ruwansa da wannan tunanin ta shiga part din su, bayan ya shiga kamshin daya rikita shi ajikinta shine a dakinsa kota ina wai yaushe littel ta canza turarene haka masu dadi da kamshi lallai zan sha kamshi ya furta tare da nufar toleit don yin wanka shima ga magarib na shirin gabatowa wow ya furta yanda yaji toilet din ya na tashin kamshi towel din datayi wanka ya dauko ya rike tare da rungume shi a kirjinsa yana wani lumshe ido kamar hawwa ce ya rungume kaji su yusuf sabon shiga nidai fitowa nayi na bashi wuri don naga abun nashi sai a hankali.

Hidima akeyi ba kama hannun yaro ta ko ina yan uwa da abokanin arzuki suna ta fasowa ta ko ina hawwa sun gayyaci kawayensu inda da yawa sun halarci bikin nan yusuf ya kashe kowane party sai dinner kadai saboda yace walhi shidai yana kishin matarsa itama dinner saboda abokaninsa wadanda suka zi daga kasahe daban daban ne kada suga bai kyaut a masu ba shiyasa umar yace lallai yayi hakuri ayita amma anyi walima tsakanin mata kadai kuma abun yayi kyau sosai gwanin ban sha'awa anyi wa'azi akan zaman takewar aure kuma da nasihohi sosai abun dai masha Allah, rana bata karya saidai uwar diya taji kunya ayau ne aka daura auren yusuf Bello mado da amaryarsa hauwa'u Bashir mado haka speaker babban masallacin dake GRA ta gauraye da fadi an daura auren akan sadaki mafi karanci naira dubu hamsin wanda Alhaji bello ne ya biya kowa yaji dadin hakan duk da suna da kudi amma basu nuna alfahari ba.
















To fa yaufa yusuf baki bai rufuwa yasamu abunda yake so tun tana karama me zaiyi banda godiyar ubangiji bayan angama daurin aure ne suka wuce hotel din da bakin su suke domin yin respection.

Biki kam yayi ashe da dangi muka kuriii. gidan Alhaji Bashir babu masaka tsinke cike yake haka gidan Alhaji Bello mutanen kankiya sun cika shi kai sai inda kake so zaka zauna su nabila da nafisa kuwa basa ma ganuwa haka aunty zainab ga aunty Rabi atu ta kano autarsu Abba kowa yana cikin farin ciki in ka cire hajiya mariya saboda tana cikin hdimar amma ta ciki na ciki hakama jamila saboda hajiya mariya tace ta saki jikinta itama lokaci kadan ne indai yusuf ne a hannunta yake shiyasa ta fita ta warware ta shiga anayin komi da ita amma kasan ranta kamar ta kashe hawwa ta huta takeji, ummah kam cikin ranta fes alkawarin Allah ya cika  Addu'a kadai takeyi dafatan zaman lafiya atsakanin yaran nata mami kuwa har kuka tayi saboda farin ciki, tun ranar da suka hadu a part din yusuf bai kara sanyata ido ba saboda gaba daya barin gidan yayi shima umar barin gida yayi suka koma hotel da abokansu kasan cewar ba kamun kai jamila take dashi ba takan zo hotel din wurin wasu data sani da sukayi karatu tare kuma ko don tazo taga yusuf ko bazai kulata ba shiko kamar ya shaketa yakeji yana tir da hali irin nata.

Haka nan taji tana son jin muryar yayan nata cikin sanyin jiki tace "nabila dauko mani wayata ki kunna mani nasan yaya fushi yakeyi dani tunda na kashe wayar nan murmushi nabila tayi " tace kyaji dashi yarinya idan ma zaki cire kunyar nan ki rike mijinki hannu biyu biyu to tun wuri kisan abunyi don akwai kuraye ta karashe maganar tana dariya tare da dauko mata wayar tana mika mata.

Amsa tayi ta bude wayar batare da tunanin komi ba ta danna kiran yaya yusuf, yasanya wayar caji a falon dakin daya ke ya shiga yayi alwalla ita kuma shigowarta kenan zata shiga wurin freind dinta ta lura da wayar yusuf na neman agaji cikin sauri ta duba screen din wayar my angel taga ni yana yawo tabbas hawwa ce murmushin mugunta tayi ta daga wayar hawwa sallama tayi cikin sanyi murya.

Murmushi jamila tayi"tace to ke banda abunki tunda kinyi nasarar auren shi mu kuma ai sai ki barmu mu huta dashi kafin mu mika maki sauran, cikin tashin hankali tasaki wayar kasa gaba daya ta tarwatse shikuma daidai da fitowarsa yana gyara hannun rigarsa ya jamila rike da wayarsa tana kallon wayar tana murmushi mai hade da mugunta.




Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home