Friday, February 11, 2022

Tun Ina Karama 11to 12



readerglobe.com.ng
      

              TUN INA KARAMA

Page 11

 Koda ya wuce daki yana shiga ya cire kayan jikin shi ya wuce toleit yayi wanka, wanda ya zame mashi jiki duk idan zai kwanta sai yayi wanka, haka ya gama ya fito daure da towel ajikinsa yana daure da daya yana kuma tsane jikinsa da dayan saida ya gama goge jikinsa sanna ya dauko mai lotion din shi mai dadi da laushi yabi jikin sa ko ina ya shafa sanna ya dauko spray dinsa na jiki ya pesa ko ina haka ya gama shirinsa na bacci ya dauki wasu kaya T-shit fara da shot nick yasanya ya dauko laptop dinshi ya dawo pallow ya zauna da niyyar duba wani aiki da yake son kammalawa amma abun ya gagaresa gaba daya ji yayi baya iya aiwatar da komi, haka ya tashi yakoma cikin bedroom din sa ya kwanta ba don yana jin dadi ba.
















Tunanin kawai yakeyi aransa ina zai samu mafita? yasan dai umma ba sauraren, gaskiya dana bi shawarar Abba dayace in fito ayi mani aure da hawwa da haka bata faru ba gashi tun ba'aje ko ina ba abubuwa na shirin lalacewa, naso in barta ta fara karatu domin ta kara samun wayewa ne amma kash, kishinta bazai barni ba ina sonta itace mace ta farko dana ke jinta araina amma bata sani ba ina ganin tayi kankanta da zan nuna mata wacece ita agareni.don har yanzu kallon dan uwanta takeyi mani na jini ba wai ta fahimci sona take ba, gaskiya nayi kuskure yakamata hawwa ta san tun tana karama nake dakon sonta. 

Kuma ai ina nuna mata banbanci tsakaninta dasu nabila  da nafisa kuma me yasa dana tafi india kullum mukayi waya sai tayi kuka wai in dawo kuma umma tana fadi mani in rike alkawari kada in yarda wata mace ta shiga rayuwata bayan hawwa don ta lura hawwa akwai soyayyata mai tsanani atare da ita gaskiya akwai  sona ranta saidai bata fahimci sona take ba, haka dole ya samu mafitar cewa mami ce kadai zata nuna ma Abba ya amince cikin sauri ayi auren nan namu.dole ne gobe insha Allahu inje kaduna in samu mami da maganar.haka bacci barawo yayi gaba da shi, itama hawwa da nabila haka suka shiga daki tare da tunani kala kala  wanda mamaki ya hana su kwanciya kowa da abunda yake tsakawa akan abunda ya faru, haka nabila ta zaunar da hawwa bakin gado itama ta zauna cikin damuwa"ta dafa kafadarta tace hawwa kiyi hkr insha Allahu komi zaiyi daidai amma ki bari kawai koma waye yayi mana wannan abu Allah zai tona masa asiri"cikin kuka nace ni wallahi nabila yanda naga yayana ya dauki abun ne tsoro ya kamani yanzu idan har Abbanah yaga wannan picture din ai na shiga uku nabila"nabila tace kema kinsan yaya bazaiyi haka ba kawai dai abunda na lura kishi ne kawai ya ruda yaya, cikin hanzari hawwa ta daga kai ta kai dubanta ga nabila "tace kishi kuma? jinjina mata kai nabila tayi alamar gaskiya ne " to ni sbd me zaiyi kishina? saboda yana sonki to ai kuma yana sonku A a hawwa yana mana so na yan uwantaka ne amma ke soyayyace tsakaninki dashi."haba nabila ni bai taba cewa yana sona ba ai ba sai yace ba mu da muke tare daku mun gane ai juya wa nayi na kwanta nace bar maganar nan saida safe.

















Haka muka tashi da asuba mukayi sallah da addu'oin mu tare da tilawar alkur'ni mai girma, wanda dama mun saba saida gari ya fara wayewa muka tashi, na kalli nabila nace mata sister zan dan koma in kwanta don kaina ke dan ciwa ok ba damuwa tace ki kwanta ki huta ni zanje in taya Asabe break, to shikenan nace na koma na kwanta.nabila tana shiga sashen umma ta shiga dakin tare da sallama, umma tana hada wasu kaya da zatayi amfani dasu ta juyo ta amsa ma nabila sallam cikin fara' da kulawa nabila har kasa ta tsugunna ta gaishe da umma bayan sun gama gaisawa na ta tambaya hawwa ko lafiya nabila ta amsa da bacci ne ta koma ta kwanta"umma tace to ba damuwa kema ki koma ki kwanta mana a a ummah zan taya Asabe ne break to shikenan ki sameta kichen din, yaya yusuf koda ya tashi da asuba yaje masallaci ya dawo ya gama abunda yakeyi ya shirya tsab tunda ya gama yanke hukuncin tafiya wurin mami kaduna, bayan ya gama ne ya fito ya wuce part din ummah ya shiga dakinta tare da sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa bayan sun gaisa ne yake sheda mata tafiyar da zaiyi kaduna, hmmm kawai tace tare da fadin Allah ya tsare hanya yasa a adawo lafiya.

Amin ya amsa mata tare da jin darin addu'arta gareshi, saboda duk fushin da ummah tayi bata fasa yima yaranta addu'a haka ya tashi duk da baida wata walwala amma yaji ranshi ya fara sanyi, bayan ya futa ta girgiza kai aranta tace zan nuna maka darajarta kafin in tabbatar maka da aurenta bazan bari ka rasata don ita ta dace da rayuwarka insha Allahu.bayan ya fita yaje wurin motarsa tare da budewa ya saka jakar laptop dinsa ya shiga motarsa tare da Addu'a yayi rivos ya nufi get baba ya bude masa tare da ftn alhairi ya amsa da amin Yana fita bai zame ko ina ba sai wurin umar, to freind dama shiyasa nace maka indai har zaka saurari jamila to zata samu galaba akanka yanzu kai ka yarda da wannan picture din? da har zaka tada hankalinka? umar yace ni dai ban yarda ba walhi amma kuma auren naku shi zafi tun wuri kafin wannan shidaniyar ta lalata komi ya kamata ka baiyana ma hawwa tun tana karama kake kaunarta simple.




















Yusuf ya sauke ajiyar zuciya tare da kallon agogon hannunsa yace yakamata mu wuce ko?"umar ya daga kai alamar eh haka suka fito daga part din umar  inada suka samu Ammi a falon gidan su umar suka gaisheta cikin girmamawa Ammi tace yusuf yasu hajaya ya amsa da lafiya klau Ammi "to masha Allah Allah ya taimaka suka amsa da Amin suka mike tsaye zasu tafi umar yace Ammi zamuje kaduna sai yanda ta yiwu  to ba komi Allah yasa adawo lafiya  amin suka amsa suka fita tabi su da kallo tana jin dadin alakarsu sosai haka suka shiga motarsu suka fita umar na tuki sai kaduna garin gwamna sai muce Allah yasa a dace yusuf.

Bayan na tashi wurin karfe 10:30 sbd babu wanda ya tasheni saka makon umma tace abarni in huta, ina tashi da addu'a bakina tare da salati na mike na shiga toleit bayi wanka  na fito na shafa mai  ajikina tare da spray masu dadi ina cikin bude drawer ne in dauko rigar da zan sanya sai wata leda ta fado ina kai hannuna zan dauka gabana ya yanke ya fadi cikin sauri naje wurin window na yaye labulan inda yake parking babu motarsa ya salam!ina ka tafi bayan kace yau zamu bude wannan ledar yaya? why kayi avoiding me?

To fa yanzu aka fara wasan fa menene burin jamila yaya hawwa zata dauki aurenta da yusuf? wace irin kalubale ke tare da rayuwarsu? to koma me kenan mujira dawowar Abba, nagode da kauna masu biyoni a picture suna nuna mani soyayyarsu da littafina mai suna tun ina karama insha Allahu  nima ina akai aku don jin dadinku.

Page 12

Ban san lakacin da hawaye suka zubo mani ba nayi sauri na nasaki labulen na koma wurin drawer na maida ledar da ban san menene ciki ba nace nima bazan bude ba har sai idan ya daina fushi dani haka na shirya cikin doguwar rigata ja mai stone agaban ta na dauki vell dinta na saka powder kawai nasa batare danayi make up ba haka na sanya takalmina simple na fito nasame su su duka gidan suna falo ummah da Asabe da nabila Asabe mai aikinmu ce amma mun dauketa kamar kaka saboda shakuwa dakuma kirkin matar shiyasa ta zama tamkar yar uwa ta jini da yanda ta dauki umma shiyasa umma ta jata ajikinta sosai gani na kowa da murmushi a fuskarsa  umma ko cikin ranta cewa tayi masha Allah yayi hallita wurin please yusuf ya tashi hankalinsa don hawwa mace ce kyaunta yanzu yake kara fitowa sosai isowa nayi na zauna kusa da ummah na dora kaina bisa kafadarta shi ya dawo da ita tunaninta nace ummatah ina kwana lafiya klau ta amsa tare da cewa ya ciwon kan naki ya bar ciwo ko?na amsa da eh ummatah ya bar ciwon kafin mu kara magana nabila tace ai sai ki tashi kije kiyi break kike ta wani shishigema ummah na dan harareta to yar sa ido.
















Dariya su ummah sukayi mana na kalli Asabe nace kakas ina kwana daftn dai kinyi mani kunun gyada kwarai kuwa autar hajiya nayi maki , "ummah ta kalleni cikin kulawa tace tashi kije daning kiyi break dinki ke dai dama ya rage na amsa to tare da mikewa tsaye na nufi daning ina zama na zuba abunda zanci na gama na dawo cikinsu hira sukeyi ina jefa nasu baki jefi jefi amma bawai don ina fahimtarsu ba hankalina gaba daya yana wurin yaya yusuf tunda ya saba mani idan har zai fita bai ganni ba to zaiyi mani text " kamar haka sleeping girl in kin tashi ki nemi yayanki yana son jin muryar littel din gidan su.

Na kanyi dariya in kirashi ya gama tsokanata mu rabu cikin annashuwa saboda yusuf mutum ne mai son tsokana, to amma yau shiru kuma banji ummah tace komi ba.hmm nasan fushi yakeyi dani, amma fa duk mai son hadani da yayana bazan yafe masa ba. Duk abunda nakeyi nabila na lura dani kuma tana tausaya mani tunda naki yarda da cewa soyayyace tsakanina da yaya yusuf, lokaci nata ja naji shirun tayi yawa wajan 11:30 kawai na yanke shawarar yi mashi text haka kuwa akayi"sweet brother don Allah kadaina fushi littel sister dinka please haka kawai nace masa na tura masa ina gamawa na dora wayata akan kijina na lumshe idanuwa na kamar mai bacci Dai dai zasu shiga jaji wayar shi yaji alamar shigiwar text ya dauka ya duba sai umar yaga yana murmushi cikin zolaya umar yace little dance ko.

















Ya jinjina kai alamar yes, umar yayi dariya bai dai ce komi ba, reply ya bata kamar haka. (sorry littel sister ummanki tana sonki da yawa bazata bari in rinka fahimtar dake gaskiya ba don haka nina tafi kaduna wurin mamita sai Abba ya dawo zan dawo gidanku an good luck all ur best littel i miss you too) idona lumshe kamar mai bacci naji shigowar sako cikin hanzari na bude amma abunda nagani ne yasani mikewa tsaye tare da fadin what! da karfi na fashe da kuka cin ta shin hankali kowa ya ya taso gareni walhi umma kadunanan bazan zauna ba nima yaya yace ba zai dawoba nima can zan koma ya za'ayi a rabani dashi umma ya zaki barshi yabar gidanmu baki hana shi tafiya ba, tunda na fara magana cikin kuka kowa kallona yakeyi  suna ma kasa cewa komi, nabila ce ta matso ta dafani tace wai hawwa me ya farune haka? ki sakeni nabila nima binshi zanyi umma bata sona tunda har ta barshi ya tafi wayyo Allah zan mutu, ran umma yayi mugun baci da jin kalamin dake fitowa daga bakina hankalinta ya tashi wai bata sona yau ita hawwa take fadi ma haka lallai dole ta koya mata hankali don gaba.bata san lkcn da ta daga hannu ba ta dauketa da mari ba ta sake dauke ta da mari akaro na biyu, kowa na wurin saida suka tsorata  ni ko wata juwa nagani tana dibana wanna shine tarihin arayuwata wanda umma ta dora hannunta akaina.

Ban san lokacin dana daina ganin komi ba saidai jina akayi jim a kasa warwas cikin tashin gaba daya sukayo kaina suna salati umma cikin rudewa ta kamani tana girgizawa cikin rudewa take kiran sunana hawwa ki tashi walhi bazan yafe ma kaina ba idan wani abu yasameki, nabila ma kuka takeyi Asabe ce dabara ta fado mata ta nufi wurin frige ta dako ruwa mai sanyi ta balle gorar ruwan ta watsa mata cikin hukuncin Allah tayi ajiyar zuciya umma tace ma Asabe su kamani su dora ni bisa kujera nabila ta zauna kusa dani umma ta dauko wayarta ta nemi layin amma a kashe ta nemi na umar shima akashe cikin ranta tace lallai yusuf dani kake magana bazan saurara maka ba.yanda Asabe taga umma cikin damuwa tace"hajiya ki kwantar da hankali tunda tasamu bacci data tashi zata warware.


















Umma tace Allah yasa Amin suka amsa gaba daya shi kam yusuf yana gama tura mata text din ya kashe wayar shi cikin hikima ya amshi wayar umar shima ya kasheta batare da umar ya fahimta ba, koda suka shiga kaduna basu tsaya ko ina ba sai unguwar sarki gidan mami suna zuwa saka makon suma yan gidan ne mai gadi ya bude masu get suka shiga sukayi parking gaba daya suka fito daga mota suka nufi cikin gidan, mami na kichen taji kamar muryar yusuf na sallama cikin sauri ta fito zuwa falo tana shiga ta gansu zaune cikin fara'a tace aaa bakin nan kun iya bazata daga ina haka cikin jin dadi yusuf ya ce mami daga gida umar yace mami dan lelenki ne yace ya sai yaga maminshi.

Nima yana raina nan ta zauna suka gaisa cikin girmamawa tare da tambayar yan gida, bayan sun gama gaisawane yusuf yace mami coffee  za a bani tace to ba matsala bari in hada maku kalaci kafin in gama abincin rana dama nasan wanan tafiyar ai bakuyi break ba umar yace ai mami bai bari ba mun yi break tana dariya ta tashi ta nufi kichen ta hada masu komi ta dawo daning ta shirya masu, bayan su gama ne suka dawo wurin inda take  zaune  umar yace mami da dawata magana muka zo maki mami tace haba koda naji to ina saurarenku ya akayi.






















Umar ya gaya mata komi yusuf kansa na kasa don kunyar mami yaji sosai Mami tace ba damuwa barima in kira Alhaji ku kwantar da hankalinku  komi zaiyi daidai insha Allahu, mami ta daga waya ta kira Abba bugu daya ya dauka mami ta gaishe shi cikin girmamawa sannan yace maryam lafiya dai ko? cikin girmamawa tace yaya lafiya klau dama wata yar alfarma nake nema wurinka game da yarona yusuf takarashe magana cikin dariya cikin kulawa yace kamar me fa ki fadi ba abunda zai gagara ai in sha Allahu, nan mami ta zaiyyana mashi komi cikin fahimta kuma ya fahimce ta tare dayi mata alkawarin next week zai dawo daga malaisia in ya dawo za'ayi komi agama insha Allahu ta gaya ma yusuf yafara shirye shirye shi ma da yan uwanta aba kowa hakkinsa, mami tace nagode yaya Allah ya kara girma ya amsa da Amin sukayi sallama.

Bazan fasa godiya ba gareku masoyan wannan littafi nawa na tun ina karama ina jin dadin yanda kuke nuna mani kauna nima ina yinku irin sosai da sosai din nan.

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home