Ashe Kaine Mijina 19 to 23
ASHE KAINE MIJINA
Page 19
Duk lokacin dayaji ta furta Kalmar ta hakura dashi saiyaji gaban sa ya fadi, baisan dalilin dayasa Kalmar ta tsaya masa a zuciya ba musamman idan ya tuna ada yadda khairat take matukar sonshi duk da dai bata fiya nuna masa ba kuma bata taba fada masa ba, koda yake ba sakar mata fuska nakeba bareta samu damar fadamin, saboda haka yayi niyyar sakin jiki da ita tamkar yadda suke wasa da darya da Aisha dama can shi ba ban ban tasu yakeba kawai dai shi bayaso taga yana sakar mata face ne tayi tunanin yana sonta, dole ya sanyata farin ciki saboda kar lokaci ya cika yayi niyyar gabatar da kudirin sa iyayan su suga kamar ba gaskiya bane abinda zaije musu dashi, da wannan tunani yayi niyyar daga yau zai fara nunawa iyayan sa irin sonda yakewa khairat.
Da daddare yana dawowa daga masallaci ya shiga dakinsa ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda yayi kyau sosai ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motar sa ya fito,tsayawa yayi a parlourn yana tunanin yaya zaiyi ya kira khairat shidai bazai iya koda kwankwasa kofar dakinta ba bare kuma ya shiga ciki, gashi ko number bashi da ita hasali ma shi kwata kwata bai taba sanya number dinta a wayarsa ba, shuru yayi yana tsaye har wajan 5mins yarasa abunyi,ji yayi ana taba kofar alamun za'a bude da sauri ya sauke wata ajjiyar zuciya, tana bude kofar taganshi tsaye nesa kadan da kofar dakin yana kallonta murmushi tayi masa shima ya maida mata tace yayana kayi kyauYake yayi yace Allah kanwa.
Suna tafe a hanya amma babu Wanda yacewa dan uwansa kala, itakuwa khairat a zuciyarta tana mamakin ina zasuje haka kuma. Ita ba abin ta tambayeshi ba tunda bai bata dama ba saboda haka taja bakinta tayi shuru, suna fara shiga unguwar ta gane inda suka dosa amma duk da haka bata yarda ba har sai da taga mortar tayi parking a kofar gidan sannan ta yarda tabbas nan din sadeeq ya kahota, horn yashiga yi saiga mai gadi da suri ya zuge gate din sadeeq yacinno hancin motarsa gidan, mai gadi yana gani khairat yafara washe baki yana fadin haji sannu da zuwa murmushi kawai tayimi suka wuce wajan da ake parking sadeeq yanufa ya ajje motar,tun kafin yayi parking din motar taji kar ta balle murfin tafito amma ta dake har sai da ya tsaya,yana tsayawa ta bude murfin motar da niyyar fita harta foto da kafar ta daya taji ya ruko hannunta da sauri ta juyo kamar zatayi kuka don gani take kamar wasa yake mata ba barinta tashiga zai yiba, dariya ce takusa kufce masa saboda ganin yadda tayi kalar tausayi amma saiya basar yace inkika sake muka shiga kayi wani abu ba dai dai ba nida kene kindai san menake nufi, daga masa kai tayi alamun ta fahimtar sannan ta juya zata fita, da sauri yace ji mana ai ban gamaba.
Sake juyowa tayi tana kallonsa yace magana ta biyu ba dadewa zamuyi ba saboda akwai inda zamuje don haka in nace ki tashi mu tafi karki sake ki musamin. Nan ma kada masa kai takumayi sannan ta juya ta fita tana fita da gudu ta karasa gidan tana isa parlour ta iske Mommy zaune a daya daga cikin kujerun parlour din rahama zaune a cinyarta tana zuba mata shagwaba sai sageer dake zaune a kasa yanacin abinci, sallama tayi batare da tajira an amsaba ta tafi da gudu ta rungume Momy da rahama tana fadin I really miss you my mom and my sweet sister.
Da sauri Momy ta rungume ta tana fadin me too my dear, khairat tasa hannu ta dauki rahama daga cinyar Mommy sannan ta zauna ta dorata a cinyarta ta juya ta kalli sageer tace yes! sageer ko magana Babu bata rai yayi yace ai dakika shigo baki kulaniba Mommy kawai da rahama kikayiwa magana. Ayya dan uwa yi hakuri ai kaga kai babba ne shiyasa na fara, sallamar sadeeq ce ta tsai da ita Mommy ce ta amsa tace barka da zuwa dana Ashe tare kuke.
Murmushi yayi sannan ya gaidata cikeda fara'a ta amsa tana fadin badai wannan shagwa babbiyar ce ta sanyaku fitowa yanzu ba. Kallon ta yayi yaga tayi kasa da kanta ya juya wajan Mommy yace toh kinga ai saboda batada gaskiya ta kasa koda kallon mu, dagowa tayi tana fadin ka dai fadi gaskiya ni babu ruwana Mommy bani na takurasa masa ba ta fada tana cinno baki.
Da sauri ta sakko tana murna ta tafi da gudu tana fadin barinaje na fadawa Yaya sageer, dariya sukayi gaba dayansu sannan suka taba fira ta yan mintuna daga baya sadeeq yace Mommy dady bai dawo bane. Ya dawo ya fita yana da baki dasuka zo daga abuja shiyasa ya tafi sai anjima zai dawo, mikewa sadeeq yayi yana fadin toh Mommy nidai na wuce inya dawo a gaishe mana dashi,ya juya ya kalli khairat yace kekuma ina jiranki a mota, ya wuce gaba Mommy tana fadin toh saiki tashi ki bishi, bataraitayi tace Mommy nidai anan zan kwana, harara Mommy ta watsa mata tace banson shirme khairat bakiji dadin danaji ba ganin Ku danayi haka da alama babu wata matsala tsakaninki da sadeeq din koh.
Hadiye wani Abu dataji ya tokare mata a makoshi tayi ta kakalo murmushi tace lafiya kalau muke Mommy addu'arki ta karbu komai ya sauya ba kamar yadda mu kayi tunani ba ta karasa maganar tana goge hawayen da yazubo mata, rungume ta Mommy tayi tana cewa masha Allah amma naji dadi ke kuma ki rike biyayya a auranku duk da nasan halinki bazaki bamu kunya ba, gyada mata kai kawai tayi sannan Mommy ta dada yimata nasahi sannan ta tafi tana kuka ta fito ta bude kofar mortar ta shiga yana kallon yadda take kuka amma ya shareta ya tada motar mai gadi ya bude musu suka fita.
Da sauri khairat tace yi hakuri dan Allah muje wajan Mom din na daina kukan, bai cemata komai ba sai wani kyalle daya dauko ya mika mata ta amsa sannan yaja motar suka fara tafi. Suna isa kofar gidan yayi horn mai gadi ya leko yaga waye, kasan cewar Dady yadawo,yana ganin motar sadeeq yayi saurin bude musu suka shiga, tare suka fito suka nufi cikin gidan suna zuwa bakin kofar parlour din sadeeq ya dakatar da khairat ta hanyar rike hannunta kallon sa tayi yayi mata murmushi sannan ya kara hade hannunsa ya sanya daya hannun ya bude kofar suka shiga hannun su sagale da juna, mom dake zaune a kujera ce ta dago idanunta ta kallesu tare da fadada murmushin ta tun kafin su karaso ta mike ta karaso inda suke ta riko hannun khairat tana fadin barka da zuwa my daughter, murmushi kawai khairat tayi ta gaishe da mom, da fara'a mom ta amsa shima sadeeq ya gaishe da ita ta amsa a lokacin ne Dady ya sakko daga part dinsa yana fara'a yana fadin kace yau ya'yan nawane suka kawomin ziyara,nan dai suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ftn dai suna lafiya suka bashi amsa da lafiya kalau suke, Aisha dake fitowa daga daki ce ta karaso da sauri ta rungume khairat nan dai sukaita fira har saida sadeeq ya tashi Aisha takawo musu abinci saboda dazu Mommy tace akwo musu sukace sun koshi yanzu kuma cikin su yadan ragu, nan Aisha takawo musu abinci sukaci suka koshi aka zauna akaita faman hira daga baya mom da dady sukayi musu nasiha sosai saboda sunji dadin ganin yaran nasu Babu wata matsala, musamman ma mom sbd a tuna ninta sadeeq yaji nasihar ta, sai wajan karfe goma da rabi suka tafi gida, suna isa khairat ta kwanata a kujera domin jinta take duk ta gaji, sadeeq ne ya kalleta yace yauwa dai wallhi nagaji tabashi amsa tana cire mayafin datayi rolling, binta yayi da idanu a zuciyarsa yana fadin kai wannan yarinyar komai nata mai kyau ne gaskiya duk wanda ya samu khairat matsayin mata ya dace yarinyar ga kyau Uwa uba ga ilimi da son addini, uhm amma duk wadan nan abubu wa dake tare dake bazan iya rayuwa dake ba saboda wani dalili bayan hakama bana jin sonta araina yanzu nema kawai nake danjin tausayin ki, sadeeq kenan ya manta cewar tausayin yana daya daga cikin rukunnan soyayya, haka zalika duk soyayyar data fara da tausayi tafi dorewa musamman shida baisan cewar damacan yanason abarsaba.
Cikin kinkina ce, dama, rigar nan ce, zip din yake bani wahalar, cirewa dazuma da kyar na sanya.wani kallo yabita dashi zaiyi magana tayi saurin kara tsayi ta sanya dan yatsanta daya ta rufe masa baki, sannan tace karka manta har yanzu matsayin matarka nake ba'ayi sakin ba don haka ba haramun bane koka manta ni kanwarka ce. Bai bata amsaba haka itama batayi tunanin zata samu ba don haka tacire hannunta daga bakinsa ta juya masa baya, sai da ya jima sannan ya sanya hannu ya fara zuge zip din,tun a farko daya sanya hannunsa yafara zugwa dan yatsansa ya taba fatar bayansa da sauri ya zaune hannunsa saboda wani shock dayaji, dry khairat taso tayi amma ta basar,maida hannunsa yayi ya karasa zuge mata mutuwar tsaye sadeeq yayi saboda gaba daya yana ganin shape din bayanta wani Abu yaji ya tsarga masa tundaga kansa har tsintsiyar kasa mutsi yayi,shurun da khairat tajine yasan tayi dariyar mugunta sannan ta juyo tana juyowa suka hada ido ta kashe mai ido daya sannan tace thanks tawuce gaba tashige daki na dariya.
Saida yajima awajan a tsaye sannan ya juya yanufi dakinsa yana fadin yarinyar nan ta gama dani nasan yau kwata kwata bazan iya bacci ba kamar yayi kuka ya bude kofar dakinsa ya shige ya rufe kofa.....?
Page 20
Kasan cewar yau weekend ne ya sanya da khairat ta tashi tayi sallah asuba ta koma baccinta, sai wajan 8:00am ya tashi ta sauko kasa, kai tsaye kitchen tafa nufa tafara hada break fast, saida ta tabbatar tagama hada komai sanan ta fito tafar gyara gidan kafin ya karasa, tana gama gyara parlourn ta wuce kitchen ta sauke ta zuba a flaks ta zuba zubawa baba mai gadi ta kaima sa nasa , sannan ta dawo taci gaba da aykinta, saida ta tabbatar tagama gyara ko ina har dakinta dakin sadeeq ne kawai ya rage,sannan ta tashi tashiga wanka, tana kammalawa ta shirya cikin wana rantsatsiyar atamfa da dinkinta ya amshi jikinta kai kace ajikinta akayi dinkin,tana kammalawa ta fito sai zuba kamshi take, kitchen ta nufa ta dauko abincin tazo ta jeresu a dining sannan ta nemin kujera ta zauna, ji tayi kawai tana kewar Mommy ta daga idonta ta kalli agogo taga 10:30 wayata ta dako takira Mommy suka gaisa hardasu rahama da sadeeq, rahama ce mai tambayar ta yaushe zasuzo da Yaya sadeeq aje shan ice cream din.
Shiko sadeeq tunda ya fito yake kallonta har ga Allah tayi matukar yimasa kyau domin shi yanzu ya daina mamakin irin wannan kyau na khairat kullum gani yake kamar sauya ta ake,a zahirnace ba kyawun datayi bane yasanya ya dade yana kallonta hakaba kawai yana kallo tane yana fasalta irin hukuncin da zai mata saboda jiya tana sane tayi abinda tasan zata tada masa hankali dadin dadawa ma harda sanya shi yayi abinda tasan tababas in yayi saiyaga surar jikinta, tunawa yayi da yadda jiya kwata kwata baiyi bacci ba ga wani azababan ciwon mara dayayi a daran, tambaya kansa yayi toh wai kodai khairat ta fahimci yadda nakeda saurin sha'awa ne tabbas tunyana gida haka yake abu kadan ketada masa hankali, amma baisan yadda akayi wannan muguwar ta fahimtar ba,koda yake Babu wani hukkunci da zan mata zulamata ce tajawomin sannan nida nake so na lallabata ai fushi ba nawa bane.
Karasawa yayi inda take ya zugun na gabda ita ya sanya hannu ya dago habarta a hankali suka hada ido jiyayi gaban sa yayi wani irin faduwa, da sauri yayi kasa da kansa da kyar ya dake yaseke kallonta yace kanwa yau ko gaisuwa babu.
Batarai tayi cikeda shagwaba tace toh ba kaibane tun dazu na kammala break fast amma baka fitoba. Yanda tayi maganar ba karamin burgeshi tayi ba a rayuwar shi yana matukar son Mace mai shagwaba yarinyar ta hada duk abin da yakeso, murmushi yayi ya rike hannunta yace ayyah sorry yar kanwata tashi muje muci abincin, tashi tayi tabishi ya zauna a kujera itakuma ta zuba musu abincin suka soma cin abincin. Bayan sun kammala ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta dawo parlour din, zaune ta ganshi yana kallo ta samu guri kusa dashi ta zauna, har tsawon yan mintuna suna zaune babu wanda yayiwa wani magana,bacci khairat taji yana dan fuzgarta saboda batayi dan gadon data sababa,jingina jikinta tayi a jikin kujerar dasuke zaune,tun tana gyan gyadi har tasoma bacci domin haka kurum taji batason kwanciyar domin wani lokacin har gajiya take da kwanci amma kuma bacci baya isarta wayarta ace bataci abinci ba.
A hankali ya tsurawa dan karamin lips din ta idanu mika hannu yayi yana zagaye lips din nata da hannunsa, itakuwa khairat baccinta take cikeda kwanciyar hankali batasan abinda ke wakanaba. Jiyayi yanayin jikinsa yafara sauyawa, hankalinsa yayi mugun tashi tabbas inyaci gaba da zama a haka za'a samu matsala,dan karamin tsaki yaja a hankali ya zame khairat daga jikinsa ya kwantar da ita kan kujera ya dauki key din motarsa ya fice daga gidan.
Kuyi hkr da jina dakukayi shuru jiya banida lafiya ne, yanzuma da kyar na iya yin wannan sbd haka zaku iya jina shuru amma insha Allah innaji da dauki zan yi kokarin yimuku typing, ina godiya da irin kaunarku gareni...?
Page 21
Tunda sadeeq ya fita gidan kaitsaye ya wuce wajan Abdul, tunda yaje Abdul ya dameshi akan maganar maryam har abun ya isheshi domin shi yace babu ruwansa da maganar gashi ga maryam dinnan amma shi ya barshi yaji da damuwarsa, ganin bashida niyyar kyaleshi ne ya sanya ya kwanta ya rintse idanunsa har baccin dole ya kwasheshi. Sai da Abdul yaji ana kiran sallar azahar sannan ya tasheshi sukayi sallah, suna idarwa sadeeq yayi masa sallama ya wuce gida.
Yana isa gidan ya iske khairat harta tashi gidan sai kamshi yake da alama har tayi girki, waigawa yayi ya kalli dining yaga kulolin abincin a kimtse falon sai kamshi yake zubawa ta gyara shi tsaf murmushi yayi a fili ya furta yarinyar nan badai tsabta, motsinta dayaji ne ya sanyashi kasa karashe maganar sa ya juya yana kallonta tana sakkowa daga steps din. Sanye take da farin wondo jins sai orange din t-shirt ta sanya farin dan kwali a kanta kitsonta ya sakko gadon bayanta, da murmushinta ta karaso kusa dashi tana bata rai kamar tayi kuka tace uhm sannu da zuwa yaya.
Amma fa kanwa kinyi matukar kyau kamar bakebaKalam da suka tsaidata daga lissafe lissafen da takeyi a zuciyarta kenan waige waige tashiga yi ko zataga wanda yayi maganar duk da tana kallonsa lokacin da yayi maganar, ganin yanayi mata murmushi ne ya sanya ta kauda kanta gefe batare da tace mai kala ba. Hannu ya sanya ya juyo da fuskarta yace uhm wannan fushin kuma na mene tunda na shigo ko murmushi bakiyiba meya faru ne.
Tsuke dan karamin bakinta tayi kamar bazatayi magana ba sannan tace ba kai bane ba Murmushi ya sake yi yace toh a fadamin me nayi saina bada hakuri tun dazufa ina bacci ka lallaba ka fita ka barni ni kadai bayan kasan yau weekend ne Babu inda ake zuwa. wannan ne laifina. Kai kawai ta daga masa, Toh kanwa yi hakuri wani uzuri ne ya fitar dani kuma naga kina kina bacci ne kinsan Babu kyau tashin mutum yana bacci musamman ma keda kike kanwata banason naga na katse miki jin dadinki.
Yes kamar gaske nidai nasan wani abun kake bukata kake wani lallabani saikace kwai A zuciyarta tayi wannan furici A fili kuwa murmushi tayi tace toh shikenan ya wuce muje muci abinci, tashi sukayi gaba daya suka nufi dining din inka gansu gwanin sha'awa(nima saida na kyasa amma narasa dalilin dayasa sadeeq bayason khairat amma muje zuwa) zaune suke a falon Dady yana cin abincin shida rahama sageer kuwa yana dakinai ,dady ne ya kalli Mommy yace amina (sunan mahaifiyar khairat kenan) dazu mun hadu da Yaya(mahaifin sadeeq kenan) yake sanarmin su sadeeq sunzo jiya.
Ayya mantawa nayi alhaji saboda jiya saida nayi bacci ka dawo, ai har nan gidan sukazo amma basu samekaba. Ayya amma banji dadin hakaba,amma dai babu wata matsala a tsakaninsu dai ko. Washe baki Mommy tayi tace yadda dai nagansu jiya Babu wata matsala tsakaninsu baka gansuba gwanin sha'awa sai dai kawai mucigaba dayimusu addu'a. Masha Allah ai haka akeso Allah yabasu zaman lafiya ya dauwwamar musu fa farin ciki azaman auransu. Ameen ameen Mommy ta fada yayin datake daukar rahama data fara gyangyadi ta wuce daki da ita.
Page 22
Jiyowa yayi yace akwai abinda nakeso zan dubane amsa mukullinnan ka rufe motar, amsar mukullin Abdul yayi shi kuma ya shige gidan. Da sallah ya shiga gidan tana zaune a daya daga cikin kujerun fake parlour din ta amsa masa tana kallonsa ganin yadda ya kura mata idanu. Ajjiyar zuciya ya sauke ganin ta dayayi sanye da atamfa riga da zani a jikinta, tunda tazo gidan bai taba ganin ta da zaniba sai sicket ko riga da wando ko doguwar Riga, murmushin jin dadi yayi saboda tunda suka taho da Abdul yake jin faduwar gaba, haka kurum yaji bayaso suzo su shigo shida Abdul su tadda khairat da irin shigar da take ta kanan kaya shiyasa yake ta sauri domin yariga Abdul shigowa ya sanyata ta suturta jikinta sai kuma yayi sa'ar samunta da shigarda baiyi tsammaniba.
Toh wai meyasa na damu da yaganta a hakane, tabbas nasan cewar hakan yana nufin kishi kenan. Amma mexaisa nayi kishi akan khairat, zuciyarsa ce tabashi amsa da saboda khairat ta kasance kanwar ka dan haka dole kayi kishi akanta kamar yadda kakeyi akan Aisha. A zuciyarsa ya furta tabbas hakane, karasawa yayi kusa da ita yana kallonta. Dauke kai tayi kamar bata ganshi ba, mika hannu yayi ya amsa wayar datake hannunta bata hana shiba ta mika masa amma still bata kalleshi ba, kanwa ya akayi ne.
Toh shikenan ya furta yana sauya channel a TV Abdul ne yayi saurin cewa haba sadeeq yaza kayi min haka kuma. Me nayi kuma bagaka gatanan ba ko sokake na zauna nayi mata bayani a'a Kallon khairat yayi yana Sosa keya yace dama wajan ki nazo nayi wannan bawan magana amma naga rainamin hankali kawai zeyi.
Guri ta nema ta zauna tana cewa Allah yasa ba laifi nayi ba. A'a babu abinda kikayi, dama akan maryam ne ,anyi miki magana, tun kafin bikin Ku naji maryam ta burge ni harga Allah ina sonta nayi niyyar fada mata shiyasa na amsa number dinta lokacin bikin Ku amma kuma inna kirata saina kasa fada mata, bawai ina tsoron fada mata bane. Kawai ina tunanin amsar da zata bani bansani ba ko tanada Wanda takeso shiyasa na kasa fada mata, na damu da yawa shiyasa nace barina yimiki magana saboda nasan ke kadai ce zaki bani kwarin guiwa akan maganar nan.
Ajjiyar zuciya tayi sannan ta juya ta kalli sadeeq taga kwata kwata bama tasu yakeba wayar shi kawai yake dannawa,juyawa tayi ta kalli Abdul sannan tafara magana. Banda abunka Yaya Abdul ai bakada matsala kawai ka sameta kayi mata magana batun kotana da Wanda takesoma bai tasoba saboda kaima kasan ba'ayi mata miji ba dan haka kaima zuwa zakayi ka jarraba sa'arka kuma nasan tabbas zaka dace saboda kanada tsari da zubin hallittar da babu wata mace da zata kika kaima kasan hakan.
Sai a lokacin sadeeq ya dago ya watsa mata wani mugun kallo akayi sa'a kuwa itama ta kalleshi kawai ta dauke kanta. Kai amma fa naji dadin maganar ki insha Allah zanyi mata magana. Har suka gama sadeeq baisa baki a, maganar ba suna kammalawa ta mike ta koma daki. Saida sukayi sallah la'asar sannan sadeeq ya tafi maida Abdul gida saboda a motar sadeeq din sukazo,sunatafe a hanya Abdul natayi masa magana amma yaki kulashi kadan kadan yake bashi amsa, haka kawai yakejin wani mugun bacin rai wai agaban sai khairat zata zauna tana wani yabon Abdul harda cewa wai kowace mace kenan harda ita. Suna isa ya sauke Abdul batare da yashiga gidan ba yajuya motarsa yanufi gidan yana tunanin abin da zaiwa khairat....?
Page 23
Kawai dan nafadi gaskya shine zakazo kana huci wai nayi maka laifi ni ai banga aibu a abinda nayiba. Kallonta kawai yayi yace "oh rashin kunyar taki zaki Nuna min kenan, toh wallahi zan gar gadeki duk ranar da kika sake aikata maka mancin irin wannan wallahi ranar zakisan koni waye.Wai kai akan Abdul kazo kake yimin wannan abun, Kallon mamaki yabita dashi a harzuke yace waye shi Abdul din a wajanki, Wai ko kin manta cewar ni mijinki ne kike nuna damuwar ki akan wani harda yabonsa kuma a gabana ku kunyar idanuna bakiji ba(chab su oh oh sai yau aka tuna da igiyar aure)Wata uwar harara ta hurga masa sannan tace aure kai kasan shi kuma nayi din ko kamanta matayin da muke dakai ne acikin gidan nan. Kuma indai akan abin da na fada ne sai dai kayi abinda kaga zaka iya ko auransa nace zanyi bakada yadda zakayi sbd ai ba haramun bane tundai kai dakake dan uwana baka dauki auran mu da muhimman ciba sai yanzu zakazo kana gayamin wata magana kuma wallahi yanzu na.
Bata karasaba taji saukar wani gigi taccen mari a kuncinta, hannu ta sanya ta dafe wajan tana kuka ta dago jajayen idanunta tana kallonsa.Juyowa yayi da niyyar sake magana amma ya fasa ya karkada kai kawai ya wuce dakinsa ya rufe kofa. Saka kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta dafe kanta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, taresa gane metakiji gameda abinda sadeeq yayi mata ita abin yana bata mamaki sannan yana bata haushi da takaici, me tayi masa da zai daga hannu harya kwada mata mari, kawai daga magana ita da tana zaune dashi ne kawai na wucin gadi kafin wa'adinta ya ciki,gaskiya bazata iya juraba tunda gashi yanzu abin ya sauya harda duka wai ita sadeeq ya mara abinda yafi tsaya mata a rai kenan wani kukan tasake fashewa dashi.
Zagaye dakin kawai yakeyi zuciyarsa nayi masa maganar tace keyi masa yawo a kwakwalwa. "Ko auransa nace zanyi bakada yadda zakayi". A fili ya furta ina Sam hakama bazata faruba,dafe kansa yayi dayaji yana Sara wa ya salam wai mena aikata ne. Miye hurumina a cikin maganar nan tasune. Meyasa na damu da kalaman datayi masa ne, Tunawa yayi da Marin da yayi mata sai a lokacin ya kula da sautin Ku kanta dayakejj har cikin dakin nasa, jiyayi baya son kukan nata gaba daya sautin dagula masa lissafi yake yanajin wani ari a zuciyarsa amma bazai iya zuwa ya lallasheta ba.
Ya Allah wannan duk laifi nene khairat bakida laifi ni nasan da haka amma bansan meya tunzurani na aikata hakan ba.sautin kukan tane kawai yake damunsa toshe kunnansa yayi saboda zuciyarsa bazata juraba da sauri ya dauki key din motar sa ya bude kofar ya fito. Har yanzu tana nan inda ya barta tana kuka, kasa kallonta yayi da sauri ya wuce ta ya fice daga gidan. Sake fashe wa tayi da wani kukan, tana bukatar Wanda zai rarrasheta amma kuma bazata iya kiran Mommy ba to wazata kira.
Mezaisa yayi min haka kuwa banda tsanata dayayi dakuma zallar zalunci kawai, ta bata amsa tana dada tuna lokacin da ya mareta. Murmushi maryam tayi tace nop ba haka bane.Wannan Abu da sadeeq yayi yana nufin kishii. Kishi kuma, yes? mana Maryam karki manta fa sai kana son Abu sannan kake kishin sa, shi kuma sadeeq baya sona. Da kenan, maryam ta bata amsa,ba, yeskin dai fada kawai sister amma bawani sona da yake. Bazaki ganeba khairat amma kici gaba da hakuri muna gab da samun nasara. Shikenan sister zanyi kokarin yin hakanYawwa dear Nan dai maryam ta dada rarrashin ta harta warware sannan sukayi sallama,Tashj tayi tashiga daki saboda bataso yadawo ya sameta tayi niyyar saiya gane kuransa tunda har ya iya sanya hannu ya mareta....?
contact-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home