Tuesday, February 1, 2022

Auren Wata Daya 15 to18


readerglobe.com.ng

      AUREN WATA DAYA 

Page 15

Tana hawa saman kai tsaye ta mika masa kayan daki sannan ta gyara dakin tsaf ta feshe shi da room freshener da turaruka masu kamshi komai yayi tsaf tana gamawa kai tsaye dakinta ta wuce tafara aikin chart dinta data saba. Tunda ta tafi ta barshi cikin tunani anya yarinyar nan lafiyarta qalau kuwa, mace ace kullum dabi'ar ta sauyawa take washe garinda aka kawota atsorace take dani har zuwa kona 2 magana kawai innayi mata hawaye ke biyo baya tsabar tsoronta, bayan kwana biyu kuma masifar tsiwa naga tana damunta,yanzu kuma abubuwa musu wuyar mantawa take jifana dasu tundaga shigarta mu amalar ta kai komai ma, lumshe idonsa yayi yana fadin ya ilahi gaskiya da sake dole na dauki mataki tun kafin yarinyar nan ta illatani.

Yana zaune har kusan 1hrs amma baiji takuma sakkowa ba tashi yayi yanufi saman kai tsaye dakinsa ya nufa yana bude kofar ya tsaya cak yanabin dakin da kallo wani daddadan kamshi yaji yana ziyartar hancinsa a hankali ya sauke wata ajjiyar zuciya yana kallon ko ina yayi tsaf sai kyalli yake sabanin yanda yafita yabar dakin kaca kaca ko ina da datti, jiyayi kawai ta burgeshi domin yanason mace mai tsabta a iya kwanakin dasukayi ya fahimci khairat nada tsabta sosai bai taba ganin kura a gidan ba ko yaga ta ajje wani Abu a wajanda bai dace ba in bai mantaba tun a gida yana yawan jin mom na yabonta sosai ta wajan tsabta, karsawa yayi ta zauna bakin gado tana tunani barka tai daga baya kuma yasaki wani dogon tsaki yana fadin komai yasa ma nake yabonta oho nidai nasan bana sonta kuma dole na nuna mata cewar nima dan zamanine tunawa yayi da Abdul ya dauko wayar sa yana fadin duk kai kabani matsala wallahi wannan shawarar taka batada wani amfani.




















Kiran layin Abdul yayi yana nagawa yace kai Malam kana ina dariya Abdul yayi yace kadai tsaya mu gaisa ko Bana bukata nidai kawai ka fadamin kana ina Murmushi kawai yayi yace ina gida Yauwa dan Allah kazo gidan yanzu kaji magana zamuyi dakai sannan ka tsaya a hanya kayomin takeaway Owk Babu damuwa kabani 30mins zan karaso, Owk saikazo ya kashe wayar ya tashi ya fito parlour din sama ya zauna yana danna Waya.

Can jimawa yaga kiran Abdul yana shigowa ya amsa yana fadin y dai? na iso ina harabar gidan kaAmmafa kayi sauri ka shigo parlour kofar abude take yanzu zan sauko ya kashe wayar. Ya nufi dakinsa ya sauya kaya  ya sanya Jens da t-shirt ya sauko kasan a parlour ya iskeshi zaune harya kunna TV yana kallo karasowa yayi suka gaisa yace kaga mikomin abincinnan naci wallahi wata muguwar yunwa nakeji.

Dry Abdul yayi yace haba sadeeq wai ina khairat dinne take barinka da yunwa? Ina ruwanka banson tsurku barni nagama cin abincinnan sai muyi magana yajawo abincin ya bude yafaraci shiko Abdul kallonsa kawai yake.Yana gama cin abincin ya ya tattara ragowar ya mikawa baba mai gadi sannan ya dawo ya zauna kusa da Abdul yana kollonsaShima jiyowa tayi yana kallonsa yace toh inajinka fadamin meke faruwa?Wata harara sadeeq ya jefa masa yace ai kafinin sanin meke faruwa tunda kaika bani shawarar na dauko matsala na ajje a gidana sannan kuma ka tambayeni meyake faruwa.

Kallonsa kawai Abdul yayi yace naji nina baka shawar karka bijirewa iyayanka akan auran khairat amma ai bani nabaka shawarar kayi AURAN WATA DAYA da itaba wannan ra'ayinka ne saida nace maka bazai yuwauba amma kakawon wata banzar hujjarka wacce batada amfani sannan yanzu kace nina baka matsala. Kallonsa kawai sadeeq yayi ya karka da kai yace naji abinda ya wuce ya riga ya wuce yanzu kawai sonake kasama mun mafita. Mafita kuma?ca  nake yau kwananku shida ko bakwai da aure kaga kenan lokacin dazakaje wa su dad da maganar sakin khairat baizoba ko rabi ba'aciba.





















Nasan da haka nidai ayanzu banajin zan iya cigaba da zama da khairat a gida daya yarinyar sotake ta haukatani kawai Da mamaki Abdul ya kalleshi yace ban fahimta ba fahimtar dani yadda zan gane khairat naso ta haukataka. Gyara zama yayi ya bashi labarin kwana 2 yadda dabi'un khairat suka sauya da irin abubuwan datakeyi masa harda rashin kunya.

Juyowa Abdul tayi ya dafa kafadatsa yace sadeeq inaso ka nutsu kayi tunani sosai khairat ba haukataka takeson yiba kuma ba ita take sanyaka damuwa a zuciyaba kaine kake sanyawa kanka wadannan abubuwa, soboda ka hana zuciyarka abunda takeso tun da dadewa,  bazan fasa gaya maka cewar zuciyarka tanason khairat kuma kaima kanason khairat kawai kana hana kanka farin cikine saboda wata banzar dabi'arka da batada amfani. Karkada kai kai sadeeq yashi gayi yana fadin karya kake ni bamasonta kuma kafi kowa sanin bana sonta.

Kalaman da suka daki kunnan ta kenan lokacin datake sakkowa daga step din tsayawa tayi tanajin wani zafi a zuciyarta kunnan ta yana amsa kuwwar kalmar dataji sadeeq yana fada hawaye taji yanabin kuncinta tayi saurin gogewa. Babu Wanda yasan da zuwanta hakan ya sanya sadeeq bai tsaya da maganar saba na kuma fada banason ta kuma kaima kasani nasan cewar banida wata wadda nakeso amma kuma bana ra'ayin rayuwa da khairat shiyasa tundaga lokacin Dana fahimci khairat nasona tadaina ganin koda dariyata ne don haka zanyi hakurin zama da ita zuwa lokacin dana diba mata ya ciki.

Yes tunda haka kace Allah ya taimaka amma bazan kara baka wata shawara akanta ba dole nasan wata rana da idanunka zaka zubarda hawaye akan khairat ka ajje wannan magana a brain dinka dole wata rana lokaci ya nuna mana. Ya bude baki da niyyar yin magana yaji motsinta tana shigowa don haka ya fasa yanemi waje ya zauna. Karasowa parlour din tayi tana sakin wani murmushi tana fadin yau a gidan namu ai nazata saimunzo biko. Dry Abdul yayi yana fadain a'a mun sarara mukune kugama cin amarcin.
























Wata uwar harara sadeeq ya watsa mata ganin kayan dazune ajikinta haka kurum yaji zuciyrsa namasa zafi dalilin fitowar khairat a haka har Abdul ya ganta jiyayi gabada ransa yabaci kamar ya cemata ta koma tasako hijab amma ya danne.Ta fahimci abinda me damunsa dan haka ta karso gaban Abdul tace barinakawo maka abinshakoA'a na gode yanzu mukagama cin abincin ma ai Toh kawai ta fada ta karasa gaban sadeeq ta sunkuya har sunajin numfashin juna ta sanya hannu ta shafi gefen face dinsa tayi kasa da voice dinta yanda shikadai zaiji tace haba dear bakayi wankaba bafa naga ka sauya kayan ka barinaje na hada maka ruwan wannaka.

Kallonta kawai yake hatta Abdul da baijin metakecewa ba kallon mamaki yake mata murmushi tasakarwa sadeeq ta huramai iska a fuska tace bani 5min yanzu zan hada maka tayi gaba batare da tasake juyowaba...?

 Page 16

Bin bayanta kawai sadeeq yayi a zuciyarsa yana fadin bariya tafi zakiga abinda zan miki dama iskancine ya sanyaki fitowa ah aka kuma kinyi kinji dadi zamu gauraya ne letter.

Abdul ne ya tabashi yace  Malam ta dade da tafiya fa naga kabi hanyar databi tun dazu kana kallo, idan ancen kana sonta kacewa mutane karya ne bayan, Kaga malam dakata haka abar maganar haka ka manta da maganar dakayi ne? Ban manta ba kuma shawarace nace bazan sake baka ita akan khairat ba kuma abinda na fada maka dole ya faru wallahi kaji rantsu guda 3 danayi maka bb babu kagfara acikinta nan da wasu kwanaki zaka gane gaskiyar danake fada maka kuma saikayi dakasani.

Toh Malam naji Allah ya kara basira irin wannan fasahar zance da hangen nesa gaskiya kayi kokari. To sadeeq kasan, Cikin zafin rai sadeeq ya daga masa  hannu ya isa haka nace nagode da shawarar ka arufe maganar haka. Kallonsa kawai Abdul yake azuciyarsa yace yaro bakasan wutaba sannan yace Toh shikenan dama tafiya zanyi ni. Toh Allah y kiyaye hanya ka gaida min hajjiya najima banshiga gidan ba. Shikenan zataji ya wuce yayi tafitarsa ko bakin mota sadeeq bai rakashiba.

Tunda ta hau saman kai tsaye dakinta ta shige ta fada gado tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya tana danasanin sauka kasan datayi harta jiyowa kanta bakar Kalmar da harta koma ga mahaliccinta bazata taba manta taba, bana sonta kuma kafi kowa sanin bana sonta kalaman sadeeq keta mai maita kansu a cikin kunnanta da sauri ta toshe kunnenta tana karanto Addi'oi domin jitake kamar zuciyarta zata fashe'a fili ta furta yaya sadeeq bansan cewar tsanar dakakemin harta kai hakaba insha Allah daga yau ko ganinama kadainayi ko fita parlour indai kana gidannan bazan sake kuskuran yin hakaba har zuwa lokacin daka diba min yacika domin nasan wata rana ido da ido zaka kalleni ka furta baka sona.






















Wayarta taji tana kara kamar bazata daukaba saboda kar wani ya fahimci kuka tayi, harta katse aka sake kira shima harya kusa katsewa sai tayi tunanin ya kamata taga wayake kiranta, mika hannu tayi saman gadon data ajje wayar tana dubawa taga mom din sadeeq ce sauri tayi ta sai saita kanta ta amsa wayar hadida sallama mom ta amsa suka gaisa sannan mom tace Khairat yanaji muyarki haka meke faruwa? Sauri tayi tayi murmushi tana fadin mom mura nakeyi yau kwana biyu kenan tama dan ragu saboda inashan magani.

Ayya toh Allah yabaki lafiya har yanzu khairat bazaki daina shan kayan ssnyi ba kenan? A'a mom aina rage Toh Allah yasa da gaskiya kike. Ameen mom ina aisha ne? Wallahi tunda ta tafi school bata dawoba ina tunanin sai magriba saboda da rana ta tafi. Owk ina dady fah? Yanzu kikasan da dady din kenan uhm khairat nima tunda akasa ranar ku da sadeeq kika daina zuwa gadan iyayan naki koda aka kaiki baki kirani ba sai yanzu dana kiraki.

Rufe fuskarta tayi da hannu tace wallahi mom ni kunyarku nakeji keda dady.Salati mom tayi tace kaniyarki  khairat mu kikejin kunya ai mu iyayanki ne ba surukaiba don haka ki daina kinji Toh mom Nan dai taware sukasha fira rabi nasihace mom tayi mata saboda tasan halin dan nata sannan tace dazar kinga yayi mimi wani abun bacin rai ki fadamin saboda nasan halin sadeeq Toh kawai tace sukayi sallama ta kashe wayar.

Tagumi takumayi hawaye nabin fuskarka addu'a taci gaba dayi jin yanda zuciyarta har yanzu take mata wani mugun zafi ya ilahi kabani hakuri da juriyar da zan cinye wannan jarabawar taka ya Allah kaga zuciyata bani na tursasa iyayan mu suka hada wannan aureba ra'ayinsu ne a haka ya Allah ka yayemin soyayyar wannan bawa naka acikin zuciyarta ya Allah.

Wani Sabon kukan ne yaci karfinta ita yanzu tausayin kanta takeyi tana cikin damuwa amma babu Wanda zai jata jikinsa ya rarrasheta ya ilahi wannan wace irin rayuwa ce,  haka ta zauna tanata Abu daya har magriba tayi tashi tayi taje tayi alwala tazo tayi sallah ta dade tanata addu'oi har akayi issha'i bata tashi daga wajan ba tanayin sallah ta tashi yau ko wanka batayi ba bare kuma ta sauya kayan bacci kawai ta kwanta.

Tunda Abdul ya tafi sadeeq keta jiran sauko warta shi adole saiya koya mata hankali akan fitowar datayi da wannan kayan harda zuwa gaban Abdul din yadda zaifi kare mata kallo, jinta dayayi shiru ne yasa ya tuna tace zata hada masa ruwan wanka tashi yayi yanufi dakinsa kai tsaye toilet yanufa ya bude yaganshi Babu ruwanda ta hada amma kuma bayin sai kamshi yake gyaran datayi dazu, lumshe idonsa yayi shi dai yana matukar son kamshi arayuwarsa,shiga yayi ya hada ruwan wankan yayi wankansa yana fitowa yaji ana kiraye kirayen sallah komawa yayi yayi alwala sannan yafito yayi sallah, shiryawa yayi ya dauki key din motarsa ya fice daga gidan.

Sai wajan karfe 9:00 ya dawo gidan ya rufe ko ina duba parlour yayi yaga alamar tun tafiyarsa khairat bata sakko ba kenan hakan yana nufin ko abinci bataci ciba, a fili ya furta wannan yarinyar yar matsalace wallahi salon wani abin yasameta tajamin salalan tsaya dama dazu mom takirani tanata fada ko maita gaya mata oho Kai tsaye ya wuce dakinsa ya sanya kayan bacci ya kwanta lumshe idonsa yayi saboda wani sihirtaccen kamshi dayaji yana tashi a gadon sai a lokacin ya kula har zanin gadon da rigar filo ta sauya kuma su suketa zuba wannan kamshin, jinsa yayi kawai zuciyarsa tai wasai rufe idanunsa yayi hangota yayi adazu data sanya wani lallausan kyalle mai kamshi tana share masa fuska tana wani fari hadi  da hura masa iska a face dinsa, jin wani shock yayi ajikinsa kamar a lokacin hakan ta faru jiyayi gaba daya yanayinsa ya sauya, juyi yayi hadi da tsaki ya rufe idanunsa yana fadin aikin kawai da ace macen danakeso na aura da yanzu haka bata faru daniba(ni dai kallonsa kawai nayi domin khairat CE macen dayakeso amma yakasa ganewa)Washe gari yana tashi yayi shirin tafiya office yana fitowa ya duba yaga khairat bata fitoba zama yayi a  parlourn sama har wajan karfe 8:00 amma baiji motsintaba gajiya yayi ya tashi yayi tafiyarsa.




















Yau gaba daya tashi tayi batajin dadi gashi da daddre bata samu bacciba sai tashi kawai tayi ta jero nafilfili har zuwa asuba sannan tasamu bacci. Da kyar tashiga bayi tayi wanka ta kintsa kanta cikin wata doguwar riga mara nauyi irin roba dinnan, da kwanciya zata koma tayi saboda kwata kwata batajin cin abincin tunawa tayi da baba mai gadi ta mike tashiga kitchen ta hada mai tea da soyayyar indomie da kawai ta zuba mai ta mika mai sannan ta dawo ta koma dakinta ta kwanta.

Wajan karfe 3:00 yabar office kai tsaye gidan su ya wuce, mom naganinsa ta watsa masa harara murmushi yayi yana Sosa kyeya ya gaisheta. Ko kallonsa batayiba ta amsa aisha dake gefe ta gaisheshi ya amsa sannan ta tashi tabar musu parlourn dan taga alamar yau lefi yaayan nata yayiwa mom.

Zuwa yayi kusada mom ya zauna yace mom wai menayi naga kinata fushi dani? tun jiya da dakika kirani naji kinata fada nasan nayi laifi. Jiyowa tayi tadan saki fuska tace sadeeq jiya nakira khairat muryar ta kawai naji nasan da akwai matsala na tambayeta tace batada lafiya, amma banyyarda ba nabiye matane kawai, sadeeq inaso kasan cewar khairat amana ce awajamka kuma kobabu komai kasan yar uwar kace batada ban banci da Aisha awajanka karka manta hakan kuma inka cuceta sai Allah ya saka mata karkaga Babu Wanda yake kallonku kasan Allah naganin duk wani Abu daxaka aikata afili ko a boye inaso ka rike wannan aranka.Jiyayi jikinsa yayi sanyi yace shikenan hajiya karki damu insha Allah zanyi kokari naga na sauke duk wani hakki nata da yake kaina.

Toh Allah ya taimaka mom tace sannan tada yimasa nasiha sannan ya tafi, a hanya ya tsaya yayi takeaway sannan ya nufi gida...?

 Page 17

Yana isa gida kai tsaye dakinsa ya wuce yayi wanka sannan ya fito yaci abinci yayi zamansa a parlour, harya gama zamansa baiga khairat ba abin yabashi mamaki amma kuma saiya basar, har akayi magarib akayi ishsha amma baiji motsinta ba haka ya karaci zamansa ya koma daki ya kwanta.

Saida sukayi 2 days a haka kwata kwata sadeeq ya daina ganin khairat haka kawai sai yake jin Babu dadi a zuciyarsa musamman inya tuna nasihar da mom tayi masa akan amanar khairat sau tari yakanyi kokari ya nufi dakinta da niyyar ya shiga amma kuma saiya kasa duk abun duniya ya isheshi ya rasa yadda zaiyi kobabu komai yanzu hakkin khairat ya ratayene a wuyansa shiyasa abin yake damunsa.


























Ta bangaran khairat kuwa duk abin duniya ya isheta ko abinci bata iyaci, kwanan ta 2 babi lafiya amma ko sau daya batasha maganiba,wayar tama gaba daya ta kashe ta takan kunnata ne idan zata kira Mom da dady ko kumaa mom dinsu sadeeq domin yanzu tana kiranta har su gaisa da alhaji su sadeeq, ko maryam bata kira a waya ita kawai tana jiran kwanakinta su cika ne sadeeq ya kawo mata takardar ta wuce ta koma gida, ko parlour bata fitowa sitaji yunwa ta isheta ne take zuwa ta dauko hollandia ta dansha baba mai gadi kuwa ta sanar mai yaringa siyan abinci batajin dadi ne kwana 2.

Yau kwanan khairat uku rabonta da ganin Sadeeq shima haka domin ta haram tawa kanta ganinsa. Kwance take a daki ta idar da sallah ko tashi batayi ba daga wajan datayi sallar, sallama taji anayi a parlourn kasa shuru tayi jin kamar muryar  maryam takeji, kin amsawa tayi domin tafi bukatar maryam ta taho har saman.

Maryam dataji ba'a amsa sallamar tataba ne yasanya ta fara hawa steps din tana isa kofar dakin maryam ta tura kofar hadi da sallama tsayawa tayi cak tana kallon khairat wacce ta juyo tana yimata murmushi. Bakida lafiya ne khairat? Maryam ta fada tana karasawa kusa da khairat, khairat bata bata amsa ba sai mikewa datayi ta cire hijjab dinta ta ninke shi ta ajje sannan ta juyo wajan maryam.























akawai maryam keyi ganin yadda duk ta rame amma kuma tayi fari fat kamar Babu jini a jikinta duk ta dashe. Khairat ce ta dubeta tace lafiya kike maryam naga duk kin wani zuba min idanu kamar yau kika fara ganina.

Mikewa maryam tayi ta kama hannun khairat suka zauna bakin gado sannan ta dubi khairat tace baki bani amsa taba na tambayeki rashin lafiya kikayi ne? Naganki kin wani rame sai wani fari da kikayi?Murmushi khairat tayi tace to kwana na 3 banida lafiya yaune na tashi jikin da dan sauki. Kar kiyimin karya khairat kinsani babu wani abu da zaki iya boyemin nasan akwai abunda yake faruwa, karki manta tun kafin kiyi aure ban sanki da kina kashe waya ba amma kuma abin mamaki sai gashi yanzu dakikayi aure wai ana kiran wayarki ba'a samu, haba khairat kwana na 3 ina kiran wayarki amma kuma koda yaushe a kashe dazuma saida na kira amma ban samu ba gashi kema kin daina kirana shiyasa na shirya na taho domin nasan a kawai matsala. Hawaye khairat ta fara yi maryam ta daga mata hannu tace no khairat karmuyi haka dake. 

Goge hawayan khairat tayi tabawa maryam labarin abun daya faru, shuru maryam tayi tana jin tausayin kawar tata kallonta  tayi ta saki wani murmushi sannan tace ai ina ganin wannan ba matsala bace,Wani kallo khairat tabita dashi amma takasa magana dariya maryam tayi tace khairat ki nutsu muyi magana dake ida banyi batan lissafi ba yau kwana 10 da auranku da sadeeq kenan. Gyada mata kai kawai khairat tayi murmushi maryam takumayi sannan tace karki damu da kalam da sadeeq yayi saboda ai bake yake fadwa ba kuma sannan baima san kina wajan ba,kuma karki manta bai taba furta miki baya sonkiba a lokacin dayake gaki gashi ba don haka karki damu amma zamu sake shiri yan zunnan a wannan karon saimun danawa sadeeq tarko cikin kwana ki kalilin.

Kwafa khairat tayi tace nifa na hakura da sadeeq kawai ki kyaleshi Dariya maryam tayi tace naji ai nima bance auranku za'a gyara ba kawai inasone shima sadeeq ya wahala akan soyyarki kamar yadda kema kikasha wahalarsa dubi yadda kika koma fa ta fada tana nuna ta. Kallon kanta tayi sannan tace shi yace miki yana sona toh da har zai samu Matsala a kaina.

Kallonta maryam tayi tace ko daya amma jiya munyi waya da waya da Abdul kinsan tun da akayi bikinku wasu lokutan yakan kirana. Kodai ya kyasa ne khairat ta fada tana zolayar maryam Murmushi maryam tayi tace nima alamun danake gani kenan amma kuma bai furta ba, kin ganshi mu ajje wannan maganar zuwa wani lokacin yanzu ta sadeeq muke ina fada miki jiya da mukayi Waya da Abdul yake bani labarin sadeeq ayanda na fahimta sadeeq yana sonki amma nakasa gane meyasa yake karyata hakan,  na tambayi Abdul yace min shima bai saniba, amma yanzu mu zamusashi ya yarda da hakan.
























Kwafa khairat tayi tace uhm kawai dai zan biye mikine amma badan na yarda da wannan magana ba. Naji karki yarda yanzu ya kamata mufara shirye shiryen mu Kallonta khairat tayi tace kamar ya.

Itama binta tayi da idanu batare da ta bata amsaba, idanunta ta saike kan khairat tace bani kayan kitso nayi miki kitso yanxun nan. Mikewa khairat tayi ta kwaso kayan kitson takawowa maryam nan suka fara amma ba kanana ba, kitso yi mata irin Wanda akeyin na baya sannan ayi wani a tsakiya kamar shiku, Suna kammalawa maryam tace mu huce kitchen kinsan yau har gogan naki za'ayiwa girki.

Bude baki khairat tayi tace kin manta kashe din dayayimin ne? tunawa da hakanne yasanya zamuyi dashi Kai tsaye suka wuce kitchen suka fara shirya lafiyayyen abinci har kala 2 saida suka kusa kammalawa ne khairat ta fito tabar maryam ta karasa ita kuma ta fara gyara gidan tundaga dakin sadeeq uwa parlourn sama dana kasa duka saida ta gyara ko ina kamshi ne kawai yake tashi a gidan.

Maryam na kammalawa tajuye kamai a flask ta rufe ta fito tsayawa tayi tana kallon khairat tace gaskiya mutuniyar kin iya gyara Dry khairat tayi tace muje muyi sallah karfe 5:00 ya salam maryam ta furta, suka wuce dakin khairat.Suna idar da sallah maryam tace tashi ki shiga wanka ki barina zuba abinci naci sannan na tafi saboda banaso sadeeq yazo ya sameni nafiso yayi tunanin ke kadai kikayi komai ba hada baki mukayiba.

Owk kawai tace ta mike ta nufi toilet,  tana kammalawa ta fito ta iske maryam harta gama cin abincin tana shirrin kai kayan kitchen zama tayi tayi light makeup maryam ce ta dauko mata wata red din doguwar Riga ta sanya ta daura farin dan kwali ta juyo ta kallo maryam tayi mata far da idanu. Maryam tace gaskiya kinyi kyau murmushi tayi tace na gd ta juya ta sanya turare ,maryam ce tace kinga muje kirakani karya dawo,har wajan motarta ta rakata sannan ta dawo ta zauna tana jiran dawowar sadeeq...?

 Page 18

Ta dade a zaune amma shuru sadeeq bai dawoba har akayi sallah magarib akayi tashi tayi ta koma dakinta tayi sallah,Tana idarwa ta tashi ta koma gaban madubi ta fara gyara kwalliyar ta, tsayuwar motar sadeeq tajiyo ta saki wani lallausan murmushi ta karasa gyara fuskar tata sanan ta mike ta fito.

A parlourn sama suka hadu tsayawa yayi yana kallonta tayi matukar kyau amma kuma tayi mugun ramewa sai uban fari data kara, Kawai saiyaji tabashi tausayi a zuciyarsa yace kilama rashin lafiya tayi shiyasa tayi wannan muguwar ramar amma ko sau daya banyi tunanin rashin lafiya ne ya hanata ko fitowa parlour ba.

Karasowa inda yake tayi tana murmushi tace yaya sannu da zuwa amma yau ka dade a office din ko aikine yayi maka yawa, yes kawai yace mata ta mika hannu ta karbi briefcase din dake hannunsa tace muje na hada maka ruwa ka watsa saikayi sallah. Da zai dakatar da ita ne amma kuma saiya fasa yace yau kuma barinaga wane sabon salon aka samo.

Tana shiga dakin ta wuce toilet ta hada masa ruwan wanka ta fito taga bai shigoba dan haka ta fito ta sameshi ya zauna akan kujerar dake parlourn yayi tagumi da alama tunani yake, karasawa tayi kusa dashi tayi ta mika hannunta ta cire hannun dayayi tagumin tace nafa gama kaje kayi wankan. Bai bata amsaba kawai ya mike yashiga dakin, bin bayansa tayi tana galla masa wata uwar harara sannan tayi kwafa tana fadin mu za'a gayawa miskilanci,  karar wayarta tajiyo a dakinta ta Mike ta shiga dakin tana dubawa taga sunan maryam a screen din tayi murmushi sannan ta amsa wayar tana fadin sister kinje gida lafiya kalau ftn dai mutumin ya dawo, yes yanzu ya shigo na hada masa ruwane ya shiga wankaYawwa haka nakeso na fada miki kisaki jiki dashi sosai a kwanakin nan kinji sister Kema dai saikace kin mantani ai nasan yadda zanyi dashi Yawwa barina kashe karya fito munata faman surutu, Owk ki gaidamin hajiya kinjiS hikenan zan fada mata ta kashe wayar.






















wa khairat tayi ta sakko parlourn kasa ta shiga kitchen ta fara kwaso abincin tana jeresu a dining din sama saida ta kammala da komai sannan ta janyo kujera daya ta zauna. Bata jima da zama ba ya fito sanye cikin kananan kaya yanata ,uba kamshi, kallon sa tayi azuciyar ta tace gaskiya kayi kyau, gani tayi yana niyyar sakkowa kasa zai bar parlour din tayi sauri mikewa tasha gabansa tayi narai narai da idanu. Kallonta yayi yace ya dai. Kamar zatayi kuka tace haba yaya sadeeq tun dazufa nake zaune ina jiranka amma kuma ka fito ko kulani bakayi ba zaka tafi abunka ta karasa fada tana dada cinno dan karamin bakinta kamar zatayi kuka.

Baisan sanda yayi mata murmushi bas aboda tayi matukar burgeshi ji yayi kamar ya rungume ta ya tsotse lips din nata dayasha light pink din lipstick wanda tunda tafara magana shi yake kallo,ganin tana shirin kwafsawa Kansa ne ya sanya yayi saurin basar wa yace ai ba fita zanyi yiba zan koma parlourn kasa ne. Owk amma daka zo mun fara cin abincin tukunna saika koma canWani irin kallo yabita dashi yana fadin abinci kuma. Kashe mai ido daya tayi tace eh manaSaida ya kauda kansa tukunna yace banaci, Tsaki tayi azuciyar  ta tace karkaci din Amma a fili sai tayi kalar tausayi tace haba Yaya kar kayimin haka saboda kaifa na bata lokaci na shiga kitchen nayi maka girki amma kace bakaci.

Daure fuskar sa yayi cikin fada fada yace amma idan ban manta ba tun washe garin ranar da aka kawoki gidannan nayi miki kashedin karki sake idan zakiyi girkin ki karki sake kiyi daniba. Hakane yaya amma ya kamata ace mun daina irin wannan rayuwar me zai hana mu zauna a gidannan a matsayin da muke tun ainihi har a yanzu kanwa nake gareka iyayan mu ne kawai da jama'ar Anguwa suke tunanin mu ma'aurata ne, amma nida kai munsan ba haka bane tunda nanda 20 days ne zaka sallameni nikuma na koma gidanmu a lokacin nasan ka fahimtar dasu bazasu gane cewar ka bijirewa umarninsu bane.

Saboda haka mudaina rayuwa cikin kunci ai ba aibu bane danna girka maka abinci kaci koka manta cewar kai yayana ne. Sai da yatafi tunanin a zuciyarsa yace ammafa yarinyar nan tayi tunani irin wanda ya dace saboda matukar ban faranta mataba nasan cewar nima bazan samu cikar nawa burinba saboda a lokacin dana kaiwa iyayena dalilin dayasa zan saki khairat nasan dolane su kirata suji ta bakinta don hk dolane na lallaba ta saboda itama tabani hadin kai.

Jiyowa yayi yaganta tsaye tana jiran amsar dazai bata don haka ya sakar mata murmushi yace shikenan muje. Kai tsaye suka karasa wajan ta janyo masa kujera sannan tafara zuba masa abincin duka biyun ta zuba masa hadi da juice din dasukayi,tunda ta bude flaks din kamshi ya daki hancinsa nan danan yafara hadiyar yau, tana kammalawa tace masa bismillah sannan itama ta zuba nata tajanyo kujera ta zauna tafara ci. Sai dayaga tafara ci sannan ya diba shima yakai bakinsa tana kallonsa ta gefen ido taga yawani lumshe ido alamun dadin abincin ya ratsashi murmushin mugunta tayi kawai ta karkada kai.

Suna kammalawa ta fara kwashe kwanunkan muryarsa kawai taji a sama yana fadin barina tayaki kwashewa abin yabata mamaki amma saita basar tace a'a na hutassheka. Bai kulataba kawai ya kwashi ragowar ya nufi kitchen dasi binsa tayi abaya tana shirin shiga shi kuma yana fitowa garin matsawa ya wuce kafarta ta goce tayi baya kamar zata fadi yayi saurin rikota har saida takusa fadawa kirjinsa tayi saurin gocewa tanayin kasa da kanta kallonta kawai yayi ya tsuna ya diba kayan data zubar ya juya ya ajje su sannan ya raba ta gefenta ya futa. Karasawa tayi ta ajje sauran kwanukan ta wankesu ta gyara wajan ta fito ta wuce sama tana shirin shiga dakinta ta ganshi yana fitowa daga dakinsa tsayawa tayi tana kallonsa ya karaso  yace zan tafi masallaci ko amsarta baijira ba yayi gaba itama bude kofa tayi tashige daki.

Tana idar da sallah ta tashi ta dauko wasu kayan bacci riga da wando dogu pick color masu dan kauri ta sanya ta dauki hular a hannu ta fito abakin kofa ta tsaya ganisa datayi tsaye bakin TV da Waya a hannunsa alamun waya ya gama yi tsayawa yai cak yana kallonta itama binsa tayi da idanu sai a lokacin ta kula kanta yake kallo tayi saurin saka hular tana tuttura kitson daya furfuto waje sannan ta karaso tana murmushi tace nidai zanje na kwanta sai da safe ta juya da niyyar komawa daki. Ji tayi ya kira sunanta bata amsa ba sai tsayawa datayi, tanaji ya karaso har kusa da ita sannan ta juyo tana kallonsa gabanta sai dukan uku uku yake musamman dataga ya mika hannu ya cire hular dake kanta jitayi kafar ta tafara rawa tayi baya kamar zata fadi yayi sauri ya rikota ta fada kirjin sa da sauri ta janye jikinta ta zauna a kasa shima tsugunnawa yayi yana kallon kitson sake kanta sannan yace waya yimiki kitso sai a lokacin ta fahimci dalilinsa na cire mata hula. Da sauri tace Momy na kira a waya ta turomin mai kitso dazu tayimin ta tafi. Oh ai bazata maryam ko Aisha ce sukazo karkada masa kai tayi yace tashi ki tafi matsoraciya kawai Cinno baki tayi tace ai halak neJiyowa yayi yana fadin mekikace.



















Da sauri tace Babu komai tashige dakinta ta kwanta tana fadin yes ai gwara da ka sakko yadda zanji dadin shige maka, amma da alama ba a banza sadeeq yayi saurin canjawa haka ba kwafa tayi tace koma Yaya  ne ni taimakona kayi.

contact-form




Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home