Monday, January 31, 2022

Auren Wata Daya - 13 to 14

 


       AUREN WATA DAYA

Page  13

Tana shiga daki ta sauya kayan bacci tayi kwanciyarta tanajin zuciyarta tayi mata wasai bata da wata damuwa sai matsanaicin soyayyar sadeeq datake damunta ako da yaushe domin amadadin taji yana fita a ranta sakamakon tsantsar tsanar da yake nuna mata amma abun ba haka yakasance ba zuciyarta tayi nisa a soyayyar wanda baya ra'ayinta.

Tunawa tayi yau kwananta 5 a gidan hakan yana nufin saura kwana 25 ta rabu da farin cikin zuciyarta hawaye taji sun fara bin kuncinta amma takasa gogewa domin fitarsu kesan taji sassauci acikin zuciyarta, afili ta furta koda soyayyarka zata kasheni yaya sadeeq dolane kafin nabar gidannan na tabbatar da na gasaka gashi mai wahala wanda kobayan nabar gidan ka dolene abubuwan dana aikata suyimaka yawo akwakwalwar ka domin bazai taba yuwuwa kamaidani bazawara a idon duniya ba domin Babu mutumin da zai kalle ni amatsayin budurwa.










 Tana zuwa nan tayi shuru na yan mintuna saikuma ta fadada murmushi a fuskarta ta juya ta dauki wayarta ta kashe ta gyara kwanciyarta  tayi addu'a hadi da runtse idanunta.Tunda ta mike yakebin bayanta da idanu harta bacewa ganinsa ajiyar zuciya  ya sauke yace kai amma wannan yarinya akwai shu'uma ni dutse ne dazatazo gabana tana irin wannan karairayi jiki saikace wata tarwada, ai gaskiya dole na dau mataki a kanki yarinya domin zan iya jure kowane wulakanci amma banda irin wann yaja wani dogon tsaki yana cewaYaran yanzunema duk sun lalace inba hakaba yaza'ayi wannan gansamemiyar yarinyar tazo gabana babu ko kunya tana kararraya, shi kadai yayita surutu daga baya ya mike ya rufe ko ina na gidan ya kashe kayan kallon ya koma dakinsa yayi wanka sannan ya kwanta yana lumshe idanunsa har yanzu jinsa yake tareda wani bakon al'amari tun abunda khairat tayi masa dazu, lumshe idanunsa yayi afili ya furta  ammafa wannan yarinyar Allah yayi mata zubin halitta ahaka har bacci ya kwasheshi.

Washe gari karfe 7:00 khairat ta fito daga dakinta sanye cikin wani material dinkin Riga da siket yayi mata kyau sosai gyara gidan ta soma yi tundaga dakinta zuwa parlour sama dana kasa gidan yayi kal dashi ko ina sai kamshi yakeyi tana kammalawa ta tashi da niyyar fitowa ta gyara harabar gidan domin tunda tazo gidan bata fito wajan ba barekuma batun gyara wajan sau daya ma ta taba ganin wajan lokacin da zata raka su aisha washe garin kawota kenan,  sanin datayi babu ko mai gadi a gidan ne ya sanya ko hijab bata dauka ba ta bude kofa ta fito turus kawai tayi tana bin wajan da kallon mamaki gurin kal yake ko ina a gyare yan flowers dake wajan duk anbasu ruwa da alama kuma ba'a jima dayin aikinba, daga kata tayi daidai inda takejin sautin radio kasa kasa wani dattijo ta gane zaune a inuwar  dake bakin  gate din yanajin radio idanunsa arufe da alama ma baisan da fitowarta ba domin akwai tazara a tsakaninsu saboda gidan babban gida ne, tabe Baki kawai tayi ta juya ta koma ciki tana fadin lalle ma matumin nan har mai gadi ya samo amma koya fadamin kwafa tayi tace uhm ina naga wannan darajar.Kai tsaye tashi kitchen tafara hada break fast tana tunanin toh yan, u wannan dattijon ne yayi duk wannan aikin chab amma gaskiya yayi kokari, tana kammalawa ta dauki plet ta zuba ta zuba awani shima ta fito ta koma daki chan tafito sanye da hijab ta dauki abincin ta fita.











Tana karasawa wajan mai gadi suka gaisa tace baba abunci na kawo maka amma kayi hakuri bansan da zuwanka ba shiyasa ban dora da wuri Mur mushi yayi yace Babu komai hajiya ai tun jiya nazoma kuma alhaji yabani kudin abinci ai  A'a baza ayi hakaba ka karba abincin duk sanda na dafa zan kawo maka basai kasiya ba Godiya yayi mata sannan ta koma ciki tayi break fast din tana kammalawa ta koma daki takira wayar aisha tana ringing amma ba'a dagaba harta katse sannan ta sake kira said a takusa katsewa sannan aka daga.

Shuru Aisha tayi mata kawai ta sanya wayar a kunne batare da tace komai ba Khairat najin haka tasan fushi aisha tayi dan haka cikin raha tace sister ya kike kwana 2? dama zakice HK tun ranar da muka zo ko nemana baki kuma yiba ko mom ma naga yanzu andaina kiranta.

Ayya sister wallahi ba haka bane maganar mom na fada miki kunyar ta nakeji ke kuma nasan nayi laifi amma kiyi hakuri kinji  toh inbanyi hakuri dakeba khairat yakikeso nayi?Yawwa yar Uwa haka nakeso nandai sukasha hira tace ta gaida mata mom kafin tazo sukayi sallam ta ajje wayar ta kwanta.Tunawa tayi kwata kwata bataji duriyar sadeeq ba dan haka ta tashi da niyyar fita tadan duba......?

Page 14

Tana fitowa ta sakko kasa taga tana tunanin me sadeeq yakeyi da har yanzu bai fitoba?    komawa tayi saman ta fara sanda zuwa kofar dakinsa ta saka konnenta jikin kofar shuru taji Bb wani motsi anya kuwa lafiya sadeeq yake? ta furta azuciyarta wani dan karimin tsaki kuma taja ta nufi dakinta tana fadin ko ina ruwana ma oho tana shiga ta kwanta ta soma bacci.

Sai wajan 2:00pm ta farka tana salati ta duba wayarta taga time ya salam wane irin bacci nayi hk da har akayi sallah ban farka ba?Cikin sauri ta mike ta shiga bayi tayi alwala tafito tayi sallah tana kammalawa taji cikinta yana kugi ta shafa cikin nata tana fadin wannan wace irin yunwa ce saikace banyi break fast ba. Mikewa tayi ta fito da niyyar shiga kitchen ta dora abinci turus ta tsaya tana kallon parlour din dataga da alama tunda ta koma sama Babu wanda yashigo parlour din hasalima kofar data rufe tananan arufe alamun kwata kwata ba'a budetaba kenan hakan yana nufin har yanzu sadeeq bai fitoba gashi ko matsinsa bataji a samaba.










Tafi 10mins a tsaye tana tunani badai wani abune yasamu sadeeq ba tunawa tayi jiya a halinda ta tafi tabar sadeeq da daddare a firgice ta furta ya salam meyake faruwane? kardai ace ni da kaina na cutar da mijina ashefa ba mijina bane ta fada tana komawa sama(kaji wata yarinta ta khairat tunda aka biya sadaki kuma muka shaida ai sadeeq yazama naki Kai tsaye dakinsa ta nufa ta dora hannuta a hankali ta tura kofar gabanta yana faduwa, wayam taga dakin gashi duk a hargitse kan gadon harda kayan dayasa jiya toh ina ya shiga ko yana toilet ne cikin sanda takarasa shiga cikin dakin ta tsaya bakin toilet din kusan 2mins amma bataji motsi a acikiba kai tsaye ta bude taga babu kowa aciki fitowa tayi daga dakin tana tunanin ina sadeeq yake?  ko bai kwana a gidan bane? dabara  ce ta fada mata ta koma dakinta ta sanya hijab ta fito harabar gidan kai staye tanufi wajan dakin mai gadi dataga baya bakin gate din tasan yana ciki  tsayawa tayi nesa da dakin tana sallam da sauri ya fito yana fadin  hajiya lafiya Tace lafiya kalau baba dama tambayar ka zanyi Babu Wanda yazo gidannan domin zanyi baki ne tun dazu sai bacci ya kwasheni kuma wayata a kashe take sai yanzu na tashi.

Ai hajiya tun safe da alhaji ya tafi aiki babu wanda nakuma budewa gate a gidannan sai mai bawa shukokincan ruwa dayazo ya gyara gidan ya tafi kuma shima tun kafin fitowarki ta safe ne. Sai alokacin ta lura babu mota guda daya a gidan in bata mantaba ranar da su rahama sikazo mota ukuta gani yanzu kuma biyuce. Juyawa tayi tace toh baba inajin sun fasa zuwane barinaje na dora abinci an barka da yunwa.

Ai Babu komai hajiya Murmushi kawai tayi ta koma ciki tana fadin wato yau aiki sadeeq ya tafi amma konaji labari bansan lokacin da zai fara daukata koda amatsayin yar uwarsa danakeba,ma aikata har 2 ya dauka amma ko yasanar dani hawayen datayi sabo dasune taji sun fara zuwar mata tayi saurin gogewa tana fading aiko kaima yau saina baka mamaki.

kai tsaye ta shige kitcin ta dora abinci mai rai da lafiya tana kammalawa ta,uba ta mikawa baba mai gadi nasa sannan ta zuba ragowar tacinye kayanta domin su 2 kawai tayiwa ta wanke kayan data bata ta dada gyara kitchen din sannan ta dada gyara parlour din ta sanya turaruka da room freshener sannan ta koma dakinta tayi wanta tana wanka taji ana kiran sallar la'asar dan haka tayo alwala  ta fito ta tayi sallah sannan ta zauna ta tsara kwalliya ta dauko wani wando da riga wondon irin pencil dinnan ne sai kuma ta dauki bes ta sanya ta dauki irin falmaran dinnan da ake daurewa ta gaba ta sanya wacce tsayinta yake iya kugu ta gyaragashinta tayi farking dinsa ta sanya irin hular nan da bayanta yake a bude ta fito da gashinta tana fadin ,andai kira aisha ko maryam wata tazo tayimin kitso.

Tana gamawa ta feshe jikinta da tura ruka sannan ta juya ta kalli mudubi tana murmushi(nima lekawa nayi ina fadin yau za'asheke yaya sadeeq kennan)Wani dan karamin kyalle ta dauka ta feshe shi da turare ta dauki wayarta ta ta dauki cingum guda daya ta jefa a baki ta sauko kasa sannan ta shiga kitchen ta dauko hollandia mai sanyi tareda karamin cup ta ajje a parlour tana murmushi ta zauna ta kunna TV tana kallo.

Bata wuce 1mins da zama ba ya turo kofar hadi da sallamar da tsaya a kasan makoshinsa, tsayawa kawai yayi yana kallonta dayake kujerar dake kallon kofa ta zauna, mikewa tayi ta amsa sallamar tana dakin wani lallausan murmushi ta nufo inda yake.Tunda ta mike ya karsa daskarewa awajan domin gani yake kamar ba khairat ba yarinya Uwa aljana irin wannan madarrar kyau haka.










Sannu da zuwa take mai amma taga bemasan tanayiba kawai yayi mutuwar tsaye ne, matsawa tayi gab dashi ta dan kara tsayi ta huramai iskar bakinta tana fadin you are wellcom yayana ta sanya kyallen tana goge masa fuska tana wani kashe ido daya wani dadda dan kamshi yaji yana shaka ya lumshe idanunsa a fili yafurata ya salam Murmushi tasake yi tace yadai naganka hakan? Da kyar ya tattara nutsuwrsa yace Babu komai Owk kawai tace ta amsa briefcase din dake hannushi tana nuna kujera da hannun tana fadin muje ka zauna nasan ka gaji da yawa tayi gaba Babu musu kawai yabita ta nuna mai kujera ya zauna, sannan ta dauki cup ta tsiyaya hollandia din ta mikomai tana fadinGa shi nasan kana bukatar abu mai sanyi Nan ma bai musa mataba ya amsa a zuciyarsa yana yana fadin anya yarinyar nan tana da hankali kuwa, be kai ayaba yayi saurin kallon kasa jin tana cire mai safar dake kafarsa da sauri ya kalleta ta kuma kashemai ido tana dada fadada murmushinta tana gamawa ta mike tana hada kayan ta nufi sama binta yayi kawai da idanu domin ko magana ya kasa da abin mamaki yake bashi yanzu kuma tsoro abin yakoma bashi anya kuwa Babu aljanu a gidannan? Ya fada azuciyarsa.

Khairat kuwa tana hawa saman ta tsaya tana dariyar mugunta tana fadin zaka gane kuranka ne ko a haka na barka nasan na figitaka.

contact-form

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home