Auren Wata Daya 10 to 12
Auren Wata Daya
Page 10
Tashi tayi cike da farin ciki taje ta saka kayan bacci tabi lafiyar gado ta kwanta. Da asuba ta tashi tayi sallah sannan ta fara gyara dakin tana kammalawa ta sauko ta gyara parlour din ta Sanya turaran wuta hadi da room freshener, tana kammalawa ta koma daki tashiga toilet tayi wanka ta kinmtsa kanta acikin wata bakar doguwar riga tayi fakin gashinta ta dauki red dan kwali ta yanashi a kanta kamar bandana ta feshe jikinta da turare ta ta sauko parlour.
Kai tsaye ta shige kitchen ta fara hada breakfast. Tana kammalawa ta zuba abinta ta fito parlour ta ajje ta koma dakinta ta dauko wayarta tafara ci tana latsa wayarta.Tunda yafito daga dakin yaji wani kamshi ya daki hancinsa lumshe sexy eyes dinsa yayi ya budesu yafara sakkowa daga steps din.
Tsayawa yayi cak yafara kallonta hankalinta kwance tanacin abinci tana latsa Waya tana murmushi alamun tanajin dadin abunda takeyi a wayar A hankali ya furta masha Allah gaskiya Allah yayi halitta a wajannan A jikinta taji kamar ana kallonta da kamar ta dago sai tayi tunanin daga ita sai sadeeq ne a gidan don haka tasan shine yake kallonta hakanne yasanya tasake mazewa ko dagowa takiyi ta nuna alamun batasan da zuwansa ba.
Sai da yakai kusan 3mns a haka sannan ya karaso parlour din ya zaunaSai a lokacin ta dago tana murmushi tace yaya ina kwana. Be amsaba sai wani hade rai dayayi yace ubanwa yabaki izinin zama babu dankwali a gidannan? Waigawa tayi gefenta alamun tanaso taga dawa yake magana sannan ta juyo tace Oh wai dani kake Bude baki kawai yayi yace Eye wannan kuma wani salon iskancine dama akwai wani dan iskanne bayan nida ke acikin gidannasa.
Saida ta kurbi tea dinda ke hannunta sannan taceA'a gani nayi nidai na sanya dan kwali Wannan dan iskan kyallen dakika zizara a goshi shine dankwalin? Bude baki tayi tana kallonsa harya dasa aya sannan tace Nifa yaya banason takura yanda na saba a gidamu kenan don haka Babu yadda za'ayi ka hanani abunda nakeso Oh rashin kunyar taki kenan yau akaina zatayi aiki kenan?
Tukunna ma nan kinga yayi miki kama da gidanku? Babu daya sai dai inkaji haushin ka daukeni ka maidani gidan ubana kamar yadda suka kawo maka ni, ta miki ta tattara kayanta datayi amfani dasu ta wuce kitchen. Mamakine ya hanashi kwakkwaran motsi dama haka wannan yarinyar haka take ban sani ba? Tabbas dole na koya mata hankali yafada yana cije lips dinsa na kasa yana karkada Kansa.Tana fitowa daga kitchen kai tsaye ta wuce dakinta ta kwanta domin bacci tskeji ta saba indai ta tashi da asuba saita koma. Zama yayi yarasa mema zaiyi ga wata masifaffiyar yunwa dayakeji domin rabinsa da abinci tun jiya da yamma.
Ganin bashida wata mafutane ya sanyashi dauko wayarsa ya kira Abdul Yana dagawa yace ango ango kana sha'aninka Tsaki kawai sadeeq yayi yace kaga Malam banason shirme inkasan batsmin rai zakayi na kashe wayata Owk sorry abokina inajinka meke faruwa naji kiranka da sassafe haka ko akwai matsala ne? kai harka tambayeni matsala bayan kasan ita kanta matsalar ni da kaina na ajiye cikin gidana Haba sadeeq khairat dince matsala karka manta yar uwarka ce ko wani kaji ya fada ai ka dauki mataki barekuma kai da kanka, yarinyar ce sai a hankali ni banma san batada kunyaba sai yau Dariya Abdul yayi yace ban gane batada kunyaba metayi maka. Kwashe labarin abinda ya faru yayi ya fada masa Dariya sadeeq yakuma shekewa da ita yace toh kaima ina ruwanka da shigarta wallahi nasha fada maka kanason khairat amma kaki yarda kawai dabi'arka ta gadoce ta sanya kake karyata zan ciyarka kah.
Kaga Malam dakata tunda ka fara wannan shirmen naka yanzu zaka batamin rai Sonake ka fito ka rakani na samo abincin don wallahi yunwa nakeji tun abincin da mukaci jiya har yanzu.
Haba sadeeq yunwa kuma ina khairat din?Ina ruwanka inbazaka fito bane na sani na tafi ni kadai. Yi hakuri kafito saimu hadu mu tafi Owk kawai yace ya kashe wayar ya dauki key dinsa ya fice daga gidan....?
Page 11
Tunda ta kwanta ba ita ta tashiba sai misalin karfe 1:00 tana tashi ta dau wayarta ta duba taga lokaci a fili taceYa salam Ashe na dade ina bacci gashi tun safe bankira Momy ba Sai a lokacin ta tuna tun jiya dasu aisha suka tafi bata kira taba kuma itama Aisha bata kirata ba hakan yana nufin tayi fushi kenan.
Ajje wayar tayi tana fadin bari nayi sallah na kimtsa duk zan kiraku.Tashi tayi tayi wanka tayi alwala tafito ta shimfuda sallaya tayi sallah tana idarwa ta mike tashirya kanta cikin wata hadadditar atamfa da akayi mata dinkin riga da siket suka kama mata jiki, abinka da mace mai diri sai kayan sukayi kamar ajikinta aka dinkasu, ta feshe jikinta da turare sannan tayi simple makeup ta daura dan kwali.Ita kanta sai da ta tsaya ta karewa kanta kallo tabbas tasan cewar tayi matukar kyau dimin ita kyakkyawace uwa uba kuma ga zubin halitta da Allah ya bata godiya tayi riga Allah daya bata wannan baiwa ta kyau dakuma kyawun halitta. Jikinta ne yayi sanyi lokacin data tuna da sadeeq tambaya tashiga yiwa kanta wadda tasan bazata samu amsarta ba sai abakin sadeeq din.
Shin wai meyasa yaya baya sona, shin banida kyawun da'biane, ko bani daga cikin irin matanda kowane cikakken namiji yakeda burin ya mallaka ne. Hawaye taji ya fara taruwa a idonta tayi saurin kauda tunanin da takeyi ta dauki wayarta ta sakko parlour kasa ta kunna TV ta nemi kujera ta zauna.
Wayarta ta dauko ta fara kiran Momy suka gaisa har dasu sageer da rahama, sannan momy ta kuma yimata nasiha da tayi hakuri da duk abunda zata tadda a gidanta domin shi aure Dan hakuri ne mussammam ma dai irin nata, suna gama wayar ta kira dady da tunda aka kawota basuyi wayaba.
Yana dagawa suka gaisa a shagwabe tace dady tunda aka kawoni baka kirani kaji lafiya tah ba sai Momy ce kawai ta kirani Banda abunki mamana ai kinsan kina raina kuma ina tambayar mom dinki kuma gashi ke kin kira ai Dady kenan ai yazama dole na kiraku mu gaisa tunda nasan saina jima kafin na ganku ta fada kamar zatayi kuka. A'a banda kuka mamana kinji Toh Dady.
Shima saida yakuma yimata nasiha sannan sukayi sallama Yunwa tafara ji tace kai yaseen bazan iya girki ba yanzu barinaje na dauko hollandia kawai nasha nayi girki da daddare. Kitchen ta nufa ta dauko hollandia mai sanyi hadi da cup sannan tadawo parlour ta zauna ta tsiyaya ta fara sha.Tunawa tayi zata kira aisha ta dauko wayar da niyyar kiran ta turo kofar da akayi ne hadi da sallama ya katseta daga abinda zatayi. Sadeeq ne ya shigo a ciki ta amsa mai sallama ya karaso ta zauna akan kujerar dake kallon tata.
Ko kallonsa bata kuma yiba ta maida hankalinta ga TV din data kunna. A hankali ya juyo ya saci kallonta a zuciyarsa yaceWai meyasa wannan yarinyar kowace irin shiga tayi kyau take yarinya kamar aljana. Murmushi yayi a fili a zuciyar sa kuma yace barina latsata kawai.
Juyowa yayi yace mata Ke wai a sakarci irin naki da yarinta haka kikaga ana tarbar miji inya dawo? Kallon sa tayi shekeke da mamaki tace toh ina mijin yake. Murmushi yayi yace kin manta lokacin da dubban jama'a suka taru suka shaida aurena dake a bainan nasi. wannan ai sunane agurinsu ne yake aure amma tsakanina da kai Babu wannan maganar kafi kowa sani.
Dariya ya sheke da ita yace yarinya kinaso kina kawai kasuwa ki daina wani basarwa kawai kiyi biyayya tunda Babu Wanda lya sani na lallaba na zauna dake kafin na auro wacce ta dace dani.
Wani mugun tsaki taja tace ai bazaka burgeniba sainaga yau dinnan ka shigo da dai dai da kai nikuma ka sallame ni.Ni kikewa tsaki ya fada yana hade rai aina ba baba na bane kai kuma ba miji ba bare kaci wannan darajar ni zanyi kokari naga nayi hakuri zama da kai zuwa lokacin da dibar mana amma fa wlh a iya lokacinnan bazan iya jurar rainin hankaliba, matukar ka rakani to nima saina rama.
Ni kike gayawa magana, Eh nayi din ta fada tana murguda baki. Hannu yasa zai matse bakin ta kauce tace wlh ka sake ka taba lafiya ta yanzunna zan kira alhajin Ku na fada masa harma da abinda bakaso ya sani.
Zubewa kawai yayi akan kujera yana huci yana kallon ta. Hollandia dinta ta dauka ta juyo tayi masa gwalo Mikewa yayi ya nufota ta kwasa dagudu ta nufi step din....?
Page 12
Ganin ta haye saman da gudu ne ya sanyashi dawowa ya zauna yana huci yana cewa Ashe ke karamar mara kunya ce uhm da ki tsaya kiga yadda zanyi dake acikin gidannan.Tana shigewa daki ta sanya key ta rufe tana dariya tana fadin kai ammafa nasha da kya, zama tayi ta dauki hollandia dinta taci gaba da sha,Tunda ta tafi sama ya zauna yanata tunani a zuciyarsa wai dama haka khairat take ban saniba yarinya Sam bata da kunya, dama kenan lamo kawai tayimin ranar dasu aisha suka zo.
Jira yake ta fito amma shuru harya fita yayi sallar la'asar amma bata sauko ba haka ya zauna kawai yana kallo har lokacin da akayi magrib fita yayi yai sallah ya dawo amma still bata parlour din a hankali ya furta Amma wannan yarinyar bata da hankali ko abinci fah bata ci ba shiga kitchen din yayi ya duba yaga da alama ma tun girkin safe da tayi ta wanke kwanukan bata kuma yin wani ba kenan tana nufin wannan madar kawai itace abincin da zataci.
Gaskiya bata da hankali so take wani ciwon ya kamata tazo tajamin salalan tsiya, dawowa parlourn yayi ya zauna yana fadin to waima ina ruwana ai kanta tayiwa bai gama rufe baki ba kamshin turaran ta ya sanar masa da isowarta parlour din dogo da kansa yayi yaganta sanye da wata doguwar riga irin mai budewa ta kasa dinnan amma mara nauyi da alama bacci kawai tasha abinta batada wata damuwa. Ajiyar zuciya kawai yayi lokacin ta iso ta kalleshi hadi da murmushi tace Yaya ina wuni.
kamar bazai amsaba sai kuma yace uhm lafiya kalau Masha Allah kawai tace ta nufi kitchen. Jalof din shinkafa tayi wacce taji hanta da kayan hadi sai zuba kamshi take sannan ta nika kayan fruit dinta tayi juice dai dai Shanta, tunda ta fara girkin bata fitoba shiko gogan yana parlour duk kamshi ya isheshi lumshe idanu kawai yakeyi ga wata arniyar yunwa dayakeji, jin ana kiran sallah ne ya sanyashi tashi ya tafi masallaci.
Tana kammalawa ta fito ta tafi daki sallah tayi sannan ta sakko ta koma kitchen ta karasa abinda zatayi ta zuba abincin ta fito, yana rufe kofa ta ganshi karasowa yayi ya zauna ita kuma ta ajje abinci ta kuma komawa kitchen din, kallon abincin da ta ajje yayi yana lashe baki azuciyarsa yace kai da gani wannan girkin zaiyi dadi.
Fitowa tayi hannunta dauke da jug din data zuba lemon ta nemi waje ta zauna tafara cin abinta hankali kwance, ganin ko kallonsa bata yibane a zuciyarsa yace amma wannan yarinyar batada mutunci kotayi kara tayimin bismillah. Kamar ta shiga uciyarsa a sama yaji muryarta tana fadin Yaya bismillah tana kallonsa.
Yaja wani dogon tsaki yace Allah ya kiyaye naci wannan kazantar taki ni ai ba wawa bane. Murmushi tayi tace kayiwa kanka dama bada kai na dafaba kawai na fita hakkinka ne taci gaba da cin kayanta. Maida hankalinsa yayi ga TV din a zuciyarsa yana fadin banda karna jawa kaina raini ai da sainaci. Tana kammalawa ta mike tana wata irin mika hadi da salati kawai kallon ta ya tsaya yanayi tana wata irin bankarewa kasa dauke idonsa yayi daga kanta ya kura mata idanu kawai yana ayyana abubuwa da dama a zuciyarsa. Kula da irin kallon da yake matane ya sanyata yi da gayya ganin ya kasa dauke adanunsa daga kantane ya sanyata yin murmushin mugunta a zuciyarta tace ai muddin ina cikin gidannan saina hanaka sakat kafin kwanakin mu su cika.
Jiyayi kawai numfashin sa ya sauya kuma ya kasa daina kallonta har saida ta mike ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta dawo ta nemi kujera ta kwanta ta dauki wayarta tana chart da maryam tana bata labari tana murmushi mugunta.
A hankali yake satar kallonta a tunaninsa bata saniba besan tana ankare dashiba har zuwa lokacin data gaji da zaman ta tashi ta kima dakinta....?
contact-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home