Tun Ina Karama 7 to 10
Page 7
ASALIN LABARIN
Shi kuma Alhaji bello gaskiya yafi karfi a govment saboda yanzu haka shine commissioner na manoma watau agric.ita kuma hajiya mariya sakamakon mijinta mai haline yana da tarin dukiya sosai shiyasa ita bata aiki sai kawai ta fada harkar kasuwanci, tana fita dubai tana kawo kaya sosai.sai Rabi'atu wadda itama tayi aure amma tana aiki da ma'ikatar lafiya ta kano, gaba dayansu kowa yana da rufin asiri daidai gwargwado saboda Alhaji moda koda yake da kudi bai yarda ya bar yaranshi ba babu ilimin addini dana zamani ba, bayan rasuwar maifinsu ne Alhaji mado Alhaji bashir ya koma katsina da zama a inada ya auri diyar aminin babansu Alhaji garba mai dala, wadda dama suna soyayya dashi wadda hakan yasa iyayensu sukayi masu alkawarin auren junan su kuma Allah ya kaddara
Shikuma Alhaji bashir dalilin dayasa ya koma katsina da zama saboda duk harkokin mahaifin shi suna can to koda ya rasu sai ya tattara gaba daya ya koma da zama, yaso ya tafi da mahaifiyasu amma ta nuna mashi tafi son zamanta anan kankiya cikin danginta haka nan ya hakura badon ranshi yaso ba, amma duk satin dunya yana zuwa ya kwana biyu wurin mahaifiyarsa saidai idan baya kasar, kuma yana zuwa da matarsa hajiya khadija wadda mace ce mai karamci da nuna kulawa ga yan uwan mijinta shiyasa ta shiga ran kowa na family dinsu Alhaji bashir, ita kanta hajiya hauwa'u tana kaunar sirikar tata sosai bata son taji ance ga laifinta, shikuma Alhaji bashir ganin yanda take kula da mahaifiyarsa da yan uwansa yasa yake kara ganin darajarta da kimarta.
Kuma yake kyautata mata, itama haka zamansu yake cikin mutunci da girmama juna, to amma duk da haka basa shiri da hajiya mariya saboda ita gaskiya halinta ya sha banban yan uwanta, ita mace ce wadda tasa duniya gaba bata tunanin komi sai son zuciya, saboda tana fita kasashe tana haduwa da kawaye sun zugata tana ganin kowa ma bai isa ba, saboda haka ne basa shiri da Alhaji bashir yayanta shikam duk harkar wani shashanci baya cikinta, kuma shi mijin nata saboda son dayake yi mata baya iya magana duk yanda take so to haka za ayi Allah ya kyauta,itama mijinta dan katsina ne nan suke zaune a le out, shima Alhaji bello yana katsina tare da iyalinsa, sai hajiya rabi'atu dake aure a kano ita mijinta dan kano ne a nan kundila suke da zama anan take aikinta a ma'katar lafiya dake jaha.
Allah ya Albarkaci Alhaji bashir da haihuwar yara uku aunty zainab ce babba sai yusuf sai kuma Nafisa wadda itace auta, rayuwar farin ciki da kaunar junan su haka rayuwa take tafiya, hajiya khadija su uku ne wurin mahaifinsu Alhaji suleman shine babba sai ita umma sai kuma babana wanda shine kaninta Alhaji mansir shine mahaifina Allah yayi masa rasuwa ne a sakamakon hadarin mota, daga kaduna zuwa katsina, Allah ya gafarta ma iyayenmu yasa Aljannace makoma Ameen ya hayyu ya qayyum.
Diyarshi wadda matarshi tabari itace babba wurin mami sai wadanda ta haifa guda uku yaran shi hudu amma baka cewa mami ta haifi ummi ba sai Abdul da khalid da halimatu sune yaran mami Hajiya mariya yaranta biyu jamilace babba sai kanwarta nabila sakamakon tsada haihuwa datayi wai ita bata son ta tara yara kuma su tsaida mata harkokinta nabila ba halinsu daya ba da jamila shiyasa gaba daya basa shiri shiyasa koda yaushe tana gidan umma muna tare ita kuma hajiya mariya ta tsani hakan shiyasa ko hidima akaje ta rinka yima umma habaici kenan ita kuma bata kulata.
Page 8
Yaya yusuf da umar cousins ne saboda umar shine babba wurin Alhaji bello kanin Alhaji bashir baban yusuf, tare suka taso tun suna yara babu abunda ke raba su sai in yazama dole, ko karatunsu tare sukayi shi india couse dinsu ne ba daya ba shi yusuf permacy ya karanta shi kuma umar Account ne, duk da haka dasuka dawo gida nigeria suna tare a company daya wanda dama na su ne company babu abunda akeyi cikin shi sai hidimar magunguna sakamakon dama abunda yusuf ya karanta kenan, kuma suna samun kwangila daga gwamnati saboda babu kasar da basu kawo magani kuma masu inganci basu yarda su hada hulda da kasashen da suke yaudarar kasarsu saboda kishin kasa.
Haka nayi krtuna primary da secondary anan katsina lokacin dana gama secondary ne ina da shekara 17 kuma ashekarar akayi mani aure da yaya yusuf wanda dama wai jirana kawai yakeyi saboda duk matan dake bibiyarsa baya ma kula su ciki ko harda jamila, bai so maganar aurena yanzu ba amma hakan bata samu ba.
Saboda yaso ace na fara jami'a kwatsam sai gashi ya canza shawara saboda wani dalili nashi, hakan yasa aka gaggauta yin auren mu. Bana manta wannan ranar da akayi bikin wata cousing dinmu Aisha wanda aranar ne ne komi ya canza a sakamakon wani hoto da da jamila ta hada tare da wani saurayi ta turo ma yusuf shi kuma lokacin yana gida.abunda ya faru, mun shirya nida nabila kanwar jamila zamuje wurin dinner to dama gaskiya itace kawata sai na nafisa autarsu yusuf tunda duk kanmu daya kuma mun shaku da juna sosai, to nafisa tana wurin aunty zainab a Abuja, mun gama shiryawa muka fito daga dakina muka samu ummah tana zaune tana kallon tashar sunnah tv tana ganinmu ta fadada murmushinta cikin kulawa tace masha Allah kunyi kyau yan matana cikin jin kunya muka rufe fuska tare da isowa kusa da ita muka zauna gefen ta muka sata tsakiya, cikin shagwaba wadda tariga ta zame mani jiki nace ummatah ina yayana? tare da kallon kofar da zata sadaka da sashin shi cikin kulawa tace yaje masallaci amma naga alamar kamar ba zai fita ba, yanzu dai bari in sanar ma Adamu driver ya kaiku tana magana tana kallon wayarta dake caji kafin tayi ta kara mgn na mike na dauko wayar na mika mata, bugu daya ya dauka ta sheda masa abunda zaiyi ya amsa da to hajiya mikewa mukayi tare da yi mata sallama tace kada mu wuce karfe tara komi mukeyi insha Allahu muka ce tare da fita waje muna fita muka ga Adamu yana kokarin fiddo wata katuwar jeep prado blue sai shaning takeyi har inda muka tsaya ya iso ya bude mana muka shiga baya muka zauna tare da gashe shi ya amsa mana cikin walwala baba mai gadi ya bude mana muka fita sai liyafa place inda akeyin dinner .
Innalillahi wa'innailaihin raju'un, haka kawai yake maimaitawa.sakamakon wasu hotona da jamila ta tura mashi na hawwa tare da wani saurayi kamar suna mgn ita kuma hawwa tana dariya wanda ita bama tasan saurayin yana kusa da ita haka ba.
Jikin shi har rawa yakeyi yasa hannu ya dauki key din motar shi a sukwane ya fiti pallow babu umma hakan ya bashi damar fita kawai inda yayi parking ya nufa ya shiga motar a rude sbd tsabar kishi, baba mai gadi ya bude mashi get tare da daga masa hannu adawo lafiya yace, haba ina ko ji bayayi haka ya fita cikin tashin hankaki da rikicewa hoton hawwa kawai yake gani tana yima saurayin nan dariya, hawwa kina son feedback me nayi maki?
Page 9
Yanda taga alamunshi, tasan akwai matsala haka ta karasa jiki ba kwari cikin tsoro tace yaya kaine?" Shiga mota kawai yace mata"yaya nabila kafin ta karasa ya daka mata tsawa! wanda har Adamu saida ya firgita"shiga mota ya sake cewa cikin rudewa ta bude motar ta shiga, ya juyo yace m Adamu kajira nabila ka taho da ita. cikin girmamawa ya amsa da to yallabai, a fusace ya isa wurin motarsa ya bude ya shiga ya fita a180_200 ran maza ya baci to hawwa ina tausaya maki hannun yusuf Adamu mamaki kawai ya hanashi motsi har na tsawon minti biyu atsaye sannan ya juya ya koma wurin motarsa cike da tunanin mai ya bata ma oga rai haka? to koma menene Allah ya kyauta.
Duk abun nan dake faruwa tsakanin yusuf da hawwa, su jamila na kallonsu tana cikin motarta inda tayi parking suna zaune itada kawarta dama suna jiran ganin shigowar yusuf saboda ba kowa zai lura da ita ba a inda tayi parking suna zaune ita da kawarta samira wanda dama samira ce ta shiga ta dauko wannan hoto wanda shi kanshi wanda ta hada tayi masu hoton baima san tanayi ba har tagama kulla sharrinta ta fito, motad yusuf na fita daga get din suka tafa ita da samira suka kyalkyale da dariyar mugunta"jamila tace yau na fara dasa masu tashin hankali atsakaninsu ke nan kinga yanda dai ya fusata gashi dama akwai zuciya kuma na lura irin mazan nan ne masu kishi kinga tunani da yawa zaiyi akanta yarinka ganin dama tana kula maza awaje "yes samira tace wannan haka yake cikin dariya samira tace to yanzu me kike ganin zaiyi mata? "jamila tayi murmushin mugunta tace ubanta zaici kawai.
Ke bakiga yanda ya fusata ba"hakane amma baki ganin mamanshi zata taka mashi burki akan hakan tunda dama kince bata son abunda zai taba yarinyar samira ta tambaya jamila."kada ki damu kawata shine dalilina na bata alkarsu saboda uwarshi ta dauki burin duniya ta dora ma wannan shegiyar yarinya wallahi na tsaneta mtsss nasan zata fusata da zaran mata wani abu kuma kinga daga nan sai abubuwa su fara canzawa nikuma a lokacin zan fara game dina wanda duk families dinmu zasu san muna tare da juna wallahi samira zan iya aiwatar da komi akan yusuf dalilin i love her with all my heart: ok kawata komi zaiyi dai dai don ma mommy bata kasar amma komi zai zama normal"samira ta jinjina kai alamar gamsuwa da maganar kawartata."jamila tace mu wuce ko?"samira ta amsa mata da yes, haka suka tashi mota suka fita dama abunda ya kawo su kenan kuma sun ai watar zuciyarsu wasai saura suji feedback.
Hankali atashe yake tafiya da mota saboda gudu kawai yakeyi kamar zai bar gari .nidai jikina rawa kawai yakeyi zuciyata na bugawa tunda nashiga motar kafin mu shiga unguwar mu naga ya gangare gefen titi yayi parking, cikin razana na dago kaina da nufin yin magana "waye shi? naji yace, cikin rashin fahimta bansan abunda kake nufi ba" ki fada mani tsawon wane lokaci kuke tare shi? yakara tambaya, "wallahi yaya bansan abunda kake nufi ba. juyowa yayi cikin tsawa! yace shut up! my friend ki sanar dani alakarki da shi tun kafin ranki ya baci! bansan lokacin da kuka ya kufce nani ba nace ni bansan komi ba amma kaki yarda." ok kawai yace tare da jefo mani wayar shi akan cinyata duba kigani tunda nasa ba yi maki karya, cikin sauri na dauki wayar tare da ganin wani pic nawa da wani saurayi kamar muna magana ina dariya.
Page 10
Cikin sauri na dauki wayar nice zahiri ba karya amma ban san wanene wanda yake kusa dani ba har ina dariya nasan dai fatima kawata nake magana da ita a lokacin amma ya akayi wannan mutumin kusa dani haka, na shiga uku! an bata ambata wallahi yaya ban san shiba asalima nasan na tsaya wurin nan amma bada shi nake maganaba amma ban sanshi ba yaya cikin kuka na karashe maganata tare da jin wani zafi a zuciyata "tunda nafara magana yake kallona yaso ya gasgata maganata amma kishi ya hana yaga hakan tare dani." Ok bani wayata na mika mashi zan kara magana ya daga mani hannu sbd gaba daya kukan da nakeyi har cikin ranshi yake jin shi. kamar bashi yayi maganar ba naji yace hawwa aure kike so?cikin sauri na girgiza kai alamar a'a to ko ba kiso yazama dole saboda bazan iya wadannan abubuwan"walhi yaya banida saurayi bare ince ina son aure to wazan aura.
Ba " nabila tace ma umma Adamu yace rai bace yaya yazo cikin mamaki tace to koma menene ai sai ya dawo mani da ita gida ko, bata rufe baki ba na fado falon da kuga gaba daya juyo sukayi cikin mamaki suna tambayar ta me yafaru? cikin kuka nace umma kada kibari yaya ya fadi Abbanah ina son aure na hade hannuwa na alamar rokonta.cikin rashin fahimtar maganata ta zaunar dani kan kujera nabila kuma ta zauna gefena tare da rike hannuna "umma tace wai meke faruwa? waye baki so kuma?" Yusuf ne ya shigo tare da sallama amma fuskar nan tashi babu annuri sai ji sukayi yace dama kin daina kuka ki fara shirin aurenki."cikin daga murya umma tace wace by irin mgn kakeyi yusuf? me ya faru ne?"umma ki tambaya ta abunda tayi dama ni nace abarta ta fara jami'a to yanzu ra'ayina ya canza zan jira dawowar Abbah tunda ya fara magana umma ke kallonsa tana nazarin irin soyayyar hawwa tsantsa a idon shi da kishin ta cikin kauda kai umma tace baka isa ba yusuf babu wanda zai takurata da mgnr aure"amma umma ya kamata ki saurareni mana"cikin tsawa tace banda lokaci saurarenka zai kara mgn ta daga masa hannu tare da cewa ya isa haka bai kara magana ba ya nufi sashensa yana jin wani zafi a zuciyarsa ta juyo tace na nabila tashi ku shiga daki ku kwanta.
contac-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home