Tun Ina Karama 1 to 6
TUN INA KARAMA
Page 1
Ahankali natashi daga kwanciyar danayi na kalli zoben dake hannuna, sansanyar ajiyar zuciya na sauke tare da sakin murmushi abayyane. cikin natsuwa na saukar da kafata daga kan gadon danake kwance na jawo pillow dake kusa dani na rungume ina jin wani shauki da sanyi a raina, na shiga duniyar tunanin dana saba, kamshin turarensa ne ya tabbatar mani da ya shigo dakin, da sauri na dago kaina na kalli kofar dakina sai naji muryar danake tunani. sallamarsa ce ta dawo da hankalina nayi saurin aje pillown dana rungume na amsa masa batare dana kalli kofar ba, na bude bakina cikin sanyin murya na ce shigo mana yayana.
Cikin natsuwa naji ya bude kofar ya shigo na kalleshi cikin kwarjini irin nasa, ya kalleni yayi murmushinsa mai ban sha'awa ya kira sunana hawwa kintashi lafiya? na kara sunkuyar dakaina kasa ina wasa da zoben hannuna na amsa masa lafiya klau yaya yusuf. Ya kara kallona sosai yace yau baki zuwa skul ne? Naga har yanzu baki shirya ba? cikin hanzari na tashi nace yanzu zan shirya, kafin ya kara magana nayi saurin cewa ka gama ne? ya juyu ya kalleni ya ya jinjina kansa almar yes. dama na tambayi umma ne kina ina? shine tace in dubaki ko kin gama, na girgiza kaina nace a'a, amma yanzu zan shirya, nima banyi tunanin zaka fito yanzu ba.
Page 2
Nasa takalmina simple da jakata sai wayata dana dauka na fito na tunkari pallow mu ina shiga na iske shi da umma suna magana, "ya kalleni sai kuma ya daure fuska cikin daga murya yace umma wai yaushe wannan yarinyar zata yarda ita matar aure ce.
Page 3
Muryar umma ce cikin tsawa tare da daga masa hannu? Yusuf ya isa haka, Wai yaushe zaka daina yaudarar kanka ne? Bayan kasan hawwa bazata taba komawa gareka ba, cikin takaici ta girgiza kai tace to ya isa haka nagaji da wannan rashin imanin naka yakamata kabani takardar ta haka nan ko kuma in dauki mummunar mataki akanka.naso mu rabu lafiya da kai amma kullum sai ka bata mani rai akan wannan auren naka wanda bashi da ma ana why? Wallahi bazan taba yarda da zalincinka ba cikin sauri ta tashi ta shige daki cike da tashin hankali.
Shi kam yusuf tunda umma ta fara magana kanshi yana kasa ba abunda yakeyi zubda hawaye, ni kuma tsaye nake inda nake kamar an da sani saboda aduk lokacinda da irin haka zata faru tsakaninmu ni kaina ina jin tsanar shi araina fiye da tunanin mai karatu, rufewar kofar umma ce tasanya gaba dayan mu dawowa daga duniyar da muka fada ido cikin ido muka kalli juna ya yunkura zai karaso inda nake, cikin hanzari na juya dakina da gudu sbd wani irin kuka daya taso mani.
Ina shiga na rufe kofata da key, na watsa kayana bisa gado na fada kan gadon na cigaba da tariyo abunda ya faru tsakanina da mijina yaya yusuf da kuma matar shi wadda ayanzu itace acikin gidan shi."hawwa hawwa hawwa yusuf ya keta kira bayan ya murda kofata yajita rufe. Ki fito mu tafi zaki makara, please hawwa cikin muryar lallashi, ina jin shi haka na share shi, na cigaba da kukana? Yafi minti goma yana bakin kofata yana rokona in fito, can cikin tsawa naji umma tana ce mashi, yusuf zo kabar mani gidana kafita tun kafin inyi maka hukunci i said get out. Ni kaina saida birona ya fadi saboda tsoro gaskiya bari in dan maida numfashi wai Allah umma daga gani akwai fada.
Page 4
Juyawa yayi yana kallon umma batare daya kara cewa komi ba, ya saki kofar ya nufi kofar fita daga falon, yana fita ta bishi ta rufe kofar. Koda ya fita wajan motar shi ya nufa ya bude ya shiga, yafi minti shabiyar yana zaune acikin mota ya maida kujerar baya ya kwanta, tunani kawai yakeyi yanda abubuwa suka rikice masa a lokaci guda.Bayan shidai yasan ba laifinsa bane amma kowa ganin laifinsa yakeyi, in harda iyayensa babu mai goya masa baya.ita kanta hawwa yana hango tsanar shi a idon ta duk irin soyayyar dake tsakaninsu da kauna da shakuwa amma duk ta kauda kai itama tana gasa mashi aya a hannu.ahankali ya furta why? why hawwa bansan komi ba sai soyyarki babu kowa araina saike kaddara ta kenan auren jamila wanda shine silar lalacewar komi tsakaninmu, tun kina karama, kece araina kuma kece mace ta farko danike ji araina da sauri ya dafe gefen zuciyarsa, insha Allah zaki dawo gareni babu rabuwa tsakaninmu da yardar Allah.
Jin tashin motar shi yasa na tashi da sauri na nufi wurin window na na bude labulen daidai da lokacin da baba mai gadi yake bude masa get ya cilla motarsa kan titin unguwarmu fice daga unguwarmu ta G.R.A.
Hajiya mariya zan barta da yusuf a matsayinta ta kanwar mahaifinsa tare da diyarta da yake aure na son zuciya.hmm amma hawwa bazan barki cikinsu ba sbd zan iya yafe yusuf acikin jerin yaran dana haifa amma ke amanata ce. Jin kalaman umma sunyi tsauri nayi sauri dagowa daga kallon kasa da nakeyi, nace ummatah sai kawai ta daga mani hannu ta mike tsaye.
Page 5
Tace hawwa kiyi tunanin zan saurara masu, kedai kawai ina son ki rike abunda na fada maki aranki, tana fadin haka ta juya har takai bakin kofa ta juyu,tace mani kuma daga yau na hanaki bin shi ya kaiki makaranta, yanzu ki tashi kije ki dauki key din motar ki idan kinada sauran lokacinda ki tafi, idan kuma lokaci ya wuce to kiyi hakurin gobe idan Allah ya kaimu.kuma mota duk wace kike so a gidan nan ki hau ba sai wai taki ba kamar yadda kika sani ne baki da shamakin komi agidan nan, kuma ina so daga yau ki daina zubda hawayenki akan yusuf, ki daure ki cire shi aranki, duk dana san abun mai wahalane agareki amma yakamata kiyi tunani akai, ina fatan kin fahimceni, cikin dauriya amsa mata da insha Allahu ummatah, ina kallonta ta fita ta jamani kofar, ajiyar zuciya na sauke a hankali na furta ki gafarceni ummatah amma bazan iya cire yaya yusuf azuciyata ba, kamar yadda nasan shima bazai iyaba.zandai kiyaye dokokinki amma yaya yusuf jinin jikina ne.
Babu alamar wani datti a office din ko ina fes ga wani irin kamshi mai dadi dake tashi cikin office din, saboda gaskiya yusuf akwai tsafta ga son gayu gashi dama Allah ya bashi kira mai kyau kowace mace ta kalle shi to zata so ta mallake shi a matsayin mijin aurenta, in takaice maku dai yusuf handsome ne na bugawa ajarida idan yayi murmushi wushiryarsa ta bayyana dimpul din shi ya lotsa ai kawai kamar ya dauwama ahaka. Zama naga yayi akujerarsa ya fiddo wayarsa naga ya nemo wata no yana kira yana karawa akunnensa naji yace na iso ina office kasameni, banji mai akce ba saidai kawai naji yace ok sai kazo ya ajiye wayar ya fara duba file din dake ajiye kan table din sa, ba don yana jin dadin aikin ba sbd damuwace fal azuciyarsa.
Jamila ta gama shirinta tsab na zuwa hospital wurin aikinta, saida tagama ta fito ta wuce sashen maigidan amma abun mamaki rufe ta ganshi hanyar fita tayi tafito daga cikin gidan tayi harabar gidan wajan parking amma bata ga motar shi ba,tsaki tayi tace to koma dai baya kwana gidan ne? ta dage kafadarta alamar ko oho" tace nasan yana wurin mayyar nan amma zanyi maganin shi mts yana can kamar wani rakumi yana bibiyarta, kwaf tayi ta nufi wurin motar ta ta sa key ta bude ta shiga tayi rivos ta nufi get mallam isah na ganinta ta wangale mata get tazo daidai fita ta sauke gils, "mal yace barka da fitowa hajiya " cikin isa da jiji dakai tace barka dai yaushe mai gidan nan yafita ta jefo mashi tmbyr? "yace ai hajiya zaikai awa biyu da fita batace komi ba ta rufe gilas din ta ja motarta ta fice rai bace, tunani takeyi yau sati guda kenan abunda yakeyi mata kenan, kuma in ya dawo baya yarda su hadu cikin yanayin damuwa ta furta: yusuf Bashir kankiya ka tabka babban kuskure.
Page 6
Har bakin motata na shiga da Addu'a abakina na waigo nace umma bye itama ta daga mani hannu tace bye bye adawo lafiya, haka nayi ma motata key a lokacin har baba mai gadi ya bude mani get na isa bakin get din zan fita na sauke glass dina na gaishe shi, shikuma yana yi mani Allah ya kiyaye haka na fita gidanmu na dauki hanyar skul ina tafiya cikin natsuwa da taka tsan tsan a hanya na kunna kirar Ahamed suleman ina saurare ina jin wata natuwa na zo mani, kuma ina tunanin maganganun ummatah wanda sune fal araina.ina neman mafita awurin Allah, saboda ban san kowa ba sai yusuf babu wanda na saba da shi acikin dangi kamar shi haka awaje ma babu shi kadaine abun alfaharina kuma tamkar jinin jikina.wasu hawaye masu zafi suka zubo mani, ummatah idan kika rabani da shi wazan jawo arayuwatah TUN INA KARAMA, nake son shi tun ban san menene so ba tunanina yan uwanta ka ne ashe kaunace mai tsanani tsakaninmu dawannan tunanin na isa skul daidai get din school din mu na UMARU MUSA YAR'ADU'A UNIVERSITY dake cikin garin katsina haka nasa sighnal din motata na shiga cikin school din na nemi wurin da mukeyin parking na parka motata na fito na kulle na wuce block din class din mu inada nasa zamuyi lecture.
Yusuf bai gama duba file din dake gabansa ba aka buga kofar office din shi batare daya daga kansa ba yace yes come in, umar ne ya bude kofar tare da sallama ya isa inda yusuf yake zaune ya mika mashi hannu suka gaisa.sannan ya nemi wuri ya zauna yace wallahi compaming din kayan nan ne tsaya yi amma komi normal in sha Allahu, yusuf yace ba ok ba damuwa umar yasake kallon yusuf yace frnd naga kamar you not feeling okey? yusuf ya dan ya mutsa fuska cike da damuwa, yace walhi umar umma bazata taba yarda dani ba.
Kullum cikin tada mani hankali take wai dole saina sakar mata diya kumani umar walhi bana iya daukar hannuna in yi saki kokuma in furta da bakina wai in saki hawwa tare da nuna kanshi ya girgizawa kamar zaiyi kuka yace frnd i can't umar zuciyata zafi take duk ranar da ummah tayi ikirarin rabani da hawwa.Tunda ya fara magana yaji abokin nashi ya bashi tausayi, karo na farko kenan tunda matsala ta faru tsakanin shi da hawwa ya tausaya masa, sabida shi kanshi haushin shi yakeji saboda bai kyauta ba duk da yasan ba laifinsa bane to amma sbd me bazai dauki tsatsauran mataki ba yana gani ana cutar dashi amma ya kasa magana.
Umar ya nisa yace a gaskiya friend bazan boye maka ba dolene ummah tayi maka haka saboda kayi kuskuren da sai munyi da gaske zamu gyara shi, kuma wallahi kada kasake ayi nasarar rabaka da hawwa kayi duk abunda zakayi ka tabbatar hawwa ta dawo gareka, shine abunda zamuyi, "yusuf yasake runtse idanuwan shi ya kara tura kujera baya ya kwanta yayi blance yace umar ita kanta hawwa ta canza mani maganar ummah ita take amfani da ita yau karara na hango tsanata a idanuwanta.
Cikin damuwa umar ya taso ya dafa kafadarsa yace kayi hakuri frnd insha Allahu komi zaiyi daidai kuma hawwa zata dawo gareke da yardar Allah karka damu,umar ya koma ya zauna yace frnd kasan wani abu? cikin yanayin damuwa ya girgiza masa kai alamar a'a ya cigaba da cewa to dazun jamila tazo wurina cikin tashin hankali ya dago kanshi ya kalli abokin nasahi ido cikin ido yace what?jamila.
contact-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home