Tun Ina Karama - 13 to 14
TUN INA KARANA
Page 13
Bayan mami ta ajiye waya ta daga kai ta kalli yusuf wanda tunda ta fara waya da Abba yake kallonta zuciyarsa cike da fargaba"mami ce ta katse masu shirun da cewa to yusuf ina fatan dai iyakar matsalar kenan ko.
Cikin jin dadin maganganun mami gaba dayansu sukayi murmushi umar yace mami godiya muke Allah ya kara girma yasa kifi haka mami gaba daya suka amsa da Amin, yusuf tashi yayi yaje har gaban mami inda take zaune ya durkusa ya dora hannuwansa kan gwiwarta tare da kwantar da kansa yana jin wani irin son mami a ransa tare da kaunarta a ransa yadda take nuna masa karamci bashi da bakin gode mata sai yanzu yake jin kulu-kulun dake cikin zuciyarsa yake fashewa hawayen farin ciki ne kawai ke zuba daga idanuwansa yana jin wani rahama na sauka aransa mami kasa cewa komi tayi sai ma daga masa kai tayi tana share masa hawayen dake zuba daga idanuwansa tana jin wani tausayin sa da kaunar sa tana kara shiga cikin ranta tana ganin soyayya amma soyayyar yusuf da hawwa Tun tuni yayi mata wuri na musamman arayuwa gaba dayansu birgeni sukeyi kuma yusuf yana son hawwa fiye da tunanin mai karatu haka itama hawwa anata haukan na kuriciya kawai yan uwan taka ne, cikin karfin hali mami tace my own son ina son kazama namiji tsayayye bana son ka kara zubar da hawayenka akan matarka wadda itace zabinka bazan so inga mace tana sanya yarona kuka ba gaskiya bazan lamunta ba saboda haka kada in kara ganin haka my son.
Kallon ikon Allah umar yakeyi masa tare da tausaya abokin nasa don ya daina bashi mamaki tausayi yake bashi wanda tun tuni ya fada tarkon son hawwa amma yanayi da irin taurin kai irin na abokin nasa yasa yakasa tantance hakan, duba da yanda yanmata ke bibiyarsa amma yana avoiding dinsu lallai so daban ne Allah bamu masoyan gaskiya Amin, mami ce ta ka tse masu shirun su wanda kowa da abunda yake kitsawa karka damu yusuf ummanka tafi kowa son zamanka da hawwa don na tabbatar babu wanda zata sallama ma kowa hawwa idan ba kai ba don haka ka kwantar da hankalinka babu wata matsala insha Allahu umar ya nisa "yace hakane mami nima abunda nake nuna masa abi komi a hankali haka dai suka ci gaba da maganganunsu da mami da cewar sun bar mata komi tayi masu jagora daga karshe suka tashi suka nufi part din yusuf da yake mallakinsa ne a gidan.
Saboda shima dan gidan ne suna shiga ko ina a gyare tsab ga kamshi yana tashi ko ina na kusuwar dakin saboda mami ba daga baya ba wurin tsabta koda yusuf ba zaune yake ba amma kullum cikin gyaran shi take ko ta gyara da kanta ko kuma su fatima su gyara sbd tace a koda yaushe yana iya shigowa suna shiga umar ya wuce bedroom bai tsaya yin komai ba ya fada toleit yayi wanka yana fitowa kwanciya yayi akan gadon dakin don ya gaji bai dade kwance ba bacci yayi gaba da shi, shi ko yusuf dama bai shiga ba pallow ya tsaya ya zauna kan kujera sai yanzu ya tuna cewa ya kashe masu wayoyinsu cikin hanzari ya yasa hannunshi aljihun suit dinshi ya dauko wayoyin ya kunna don yasan rigima na can sunayi ita da umma kuka kam ya tabbatar ta sha shi har sai ta ba umma haushi kuma sai yaji ba dadi bai kyauta ba bari ya kunna wayar ya kirata ko kara zolayarta yayi.
Cikin fushi umar yace walhi yusuf baka da tausayi saida ka kara sanya mata wata damuwa wai kai wane irin mutum ne? kullum a irin damuwar sanya ta ciki to ni gaskiya bazan yarda ba arinka yin wannan dani ba.
Wallahi kuma wannan izzar dake bisa kanka garaka sauketa ka tarairayi abunda tuntuni shine zabinka to kana ji kana gani zakayi asara ka daina ganina kowa yana bayanka haka umar ya gama shiri ya yana bambamin fada shidai yusuf bai kara cewa komi ba tunda dai yasan bai kyauta ba umar nagama sanya kayansa yace ma yusuf bani wayata mika mashi yayi batare da yayi mgn ba yace daga yau kada ka kara yi mani irin haka yanzu ummah cewa zatayi hada baki mukayi yana gama fadin haka ya fita yusuf tashi yayi yabi bayansa ya rufe part din aranshi ya ce dole in lallabaka umar suna fitowa part din mami suka shiga suka sameta a falo ita da fatima da ta dawo daga school kenan cikin kulawa tace a'a har angama hutawar ne mami ta tambayan su.
Ta cigaba da cewa dama yanzu ummi take tmbayar big bros nace kuna ciki kuna hutawa ban ma san yanzu zaku fito ba ko ta karashe magana tana dariya, umar ne yayi saurin cewa mami wani aiki ne ya taso mana yanzu ake neman mu a company baki zamuyi shine muke son juyawa insha Allahu yusuf baiyi zaton abunda umar zaice kenan ba kallonsa kawai yakeyi ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da hamdala tunda dai umar bai tona masa asiriba wurin mami fatima ce ta gaishe su tare da cewa nidai banji dadi ba wallahi cikin damuwa ta kara she magana.
To haka nan zan makale ko ajikin tayar motar yusuf ne nima in bishi katsina gidan ummah don nasan akwai rigima kwance mai zuwa ya biyoni......?
Page 14
Koda suka kama hanya babu mai maganan cikin su kowa da nasa tunanin arai umar tuki yakeyi amma zuciyarsa fa da tausayin dan uwansa kuma amininsa gaskiya ne yusuf yana tsananin son littile amma ya kamata ya nuna mata ita ce abokiyar rayuwarsa ta har abada amma ba komi zai kara ankarar da shi batare da wata matsalaba, yusuf kuwa irin tashin hankalin da zai tarar yake tunanin fuskanta a haka har suka kusa shiga katsina wajan karfe 8:30 na dare suka shiga cikin katsina umar ne yace to kadai tanaji amsar da zaka ba ummah ko.
Gaskiya ne umar yusuf ya fada tare da cewa insha Allahu zanbi shawarar ka nagode da kauna, kafadar shi umar yadan buga yace kai mal meye na godiya bayan biyana zakayi gaba daya suka sa dariya dai dai lokacin suka iso get din gidan su yusuf sunayin horn baba mai gadi ya bude suka shiga ciki tare da gaishe shi ya amsa cikin mutunci suna isa wurin parking sukayi suka fito gaba daya kamar basu da wata damuwa ledar da mami ta basu suba umma ce umar ya dauka tare da cewa to ango shiga gaba cikin zolaya "a a yusuf yace saidai mu jera ka idan ummat ta tashi maido mu sai ta maido mu tare ko haka suka shiga falon gidan tare da sallama Asabe ce cikin falon tana ta faman yima nabila tsiya wai bata da aiki sai nemo girke girken zamani awaya tace suma sai sunyi irin shi maimakon ta nemo na gargajiya, amsa sallamar sukayi tare da yi masu sannu da zuwa kaka Asabe hira kukeyi hakane? yusuf ya tambaya yes wallahi tabashi amsa Allah karami ya hanya ya kuka baro su mamin kaduna.
Kwance take ta juya bayanta in banda hawaye babu abunda ke zuba a idanuwanta wanda sun maki tsayawa sallamar nabila ce tasa ta tasake lafewa agadon jin muryar umar ne da ya kira sunanta little baki da lafiya ne ya tambaya tare isa gaban gadon yasa ta juyo sukayi ido hudu da yusuf dake bayansu cikin azama ta tashi da sauri tayo kan yusuf kallonta umar da nabila sukeyi cikin mamaki ta tana zuwa ta fada jikinshi ta fashe da kuka mai cin ran mai saurare baiyi yunkurin hanata ba ya riketa shima ji yake kamar ya kurma ihu saboda tausayinta "umar ne ya girgiza kai ya kalli nabila allamar su basu wuri ya raba ta gefensu ya fita itama nabila ta bi bayan shi tare da jin dadin samu farin cikin kawarta bayan fitar sune yusuf ya dago ta yace my dear wife, gabanta ne ya fadi cikin sauri ta dago kai ta kalle shi daga mata gira yayi tare da murmushin sa mai tsada ya ce to be insha Allah kuka ta sake fashewa dashi hankicib ya ciro a aljihunsa ya cigaba da goge mata hawayen dake zuba little ya kirata yace ko baki auren yayanki.
Cikin jin kunya ta juya zata bar wurin saurin riketa yayi kinga shikenan duk inda zani sai mu tafi tare babu mai hanamu ko? ya tambaya ta rufe fuska tayi tace bacewa kayi baka kara dawowa gidan nan ba haba little ni na isa wasa fa nayi maki turo baki tayi tace shine kasa har ummah ta mareni ta karashe magana hawaye na zubar mata kuma har yanzu fushi takeyi dani matsawa yayi ya zaunar da ita kan gado shima ya zauna yana jin wani yanayi na da ban dan gane da ita shiyasa yayi dabarar raba jikinsu ya zaunar da ita cikin kulawa yace babu abunda zai rabani dake hawwa kuma me yasa kika ce ma ummah bata son ki? ai kinga dole ranta y baci don haka mu duka munyi laifi ya kamata muba umma hakuri kuma koda wasa kada ki kara fadar haka kinji ko? yanzu kinga da Abba ya dawo maganar auren mu za ayi kinga ai gidana zankai ki saidai ki rinka zuwa kina gaisheta ko? cikin jin kunya nace kullum ko.
Tana cikin wannan tunanin ne suka fito gaba daya cikin jin dadin ganinsu "ummah tace to uban yan rashin kunya kaje ka taho da ita ko? ai ganin yanayin ummah yasan ta sako baiyai wata wata ba yaje gabanta yana kwasan gaisuwa da tuba haka su Asabe da umar nabila sukaita dariya niko inda nake tsaye ban kara motsi ba jinayi ummah tace auta duk da yayan naki ya dawo fushi kike dani kuma? rufe fuskata nayi na karaso wurinta na kwantar da kaina a cinyarta nace umma nima na tuba bazan kara ba shit naga ta dora hannunta abakina tace kada in karajin haka ya wuce ta kalli yusuf ta dungure shi tace tashi kabani wuri ja iri mara kunya haka ya tashi yana sosa keya umar yayi ma su umma sallama don dare ya farayi kuma yace ma yusuf dama gida zai wuce haka suka fita suna dariya, bayan sun fita ne umar yace to mun godema Allah da komi yazo cikin sauki haka ya rakashi yace saidai ya dauki mota shi bazai raka shi ba don ya gaji dariya umar yayi a amshi key din ya shiga ya daga masa hannu ya fita ya wuce gida.
Yusuf na komawa ciki yasamu falon ba kowa sai TV shi kadai yana ta yi murmushi yayi yaje ya kashe tv ya kashe wutar falon shima ya wuce part din shi cike da farin ciki da jin dadi aransa...?
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home