Friday, September 17, 2021

Sako Ga Wanda Soyaiyarsa Ta Juyemasa Baya...


Daga cikin irin kalmomin da zaka dinga ji game da wanda aka karyawa soyaiyarsa. Wasu daga ciki sune kamar:-

1- Na dena soyaiya?

2- So ko wahala?

3- Bazan kara yin soyaiyaba?

4- Yin soyaiya ko yin bata lokaci?

   Mata Kuma Sai suna cewa

1- Maza mayaudara ne?

2- Namiji Ba Dan Goyo Bane?

3- Namiji Kanin Ajali?

4- Duk Wanda Ta rike Namiji Uba To zata Mutu Maraya?

    Maza Kuma Suce

1-  Mata Basu Da Alkawari?

2- mata mayaudara ne?

3- Mata Ba saYin Gaskiya?

A rayuwa zucia yakan sa mutum ya aikata abubuwanda ba da sonsa sai idan abin yafaru tukunna sai kaga yayi da nasani? Idan kayi zuciya da soyaiya to yakamata kayi zuciya da neman kudi ko cin abinci, kace ni daga yau bazan kara neman kudi ba ko ka ce ni daga yau bazan kara cin abinci ba amma ka iya ce ni bazan kara yin soyaiyaba har abada.

To inna da wata shawara ne game da wanda ransa ya bace game da soyaiya ko dayake ba musan me yake faruwaba game da budurwa da kuma saurayinta amma ga shawara kadan game dasu ko zai yi musu amfani garesu.

A kowane namiji yanaso yaga ya auri mace mai kew da kuma tana da ilimi kuma tazama ita yar masu kudi da kauna/ haka kuma itama mace tanaso taga ta samu namiji mai kew ga ilimi da kuma yana da kudi gaso ga kuma kauna a tsakaninsu dan soyiya tayi dadi.

Shi soyaiya zumace alokacin da ake yinta dan idan soyaiya tayi dadi to zumace take ta yawo a tsakanin su amma duk lokacin da daci yashiga sakanin zuma to kowa sai ka ga yana cewa shi daga yau bazai kara yin soyaiyaba har duniya ta tashi wato idan aka samu matsala kennan a sakaninsu su ma soyan kenan.

Shi wannan daci yakan faru ga wanda suka fara yin soyaiya ta farko dan idan aka samu masala sai kaga kowa zuciyarsa tazama taci kowa yana zagin juna a sakaninsu TO BA HAKABA ZAKUYI.

Mesa wai dan kawai kunsamu masala kadan kawai sai kayi zuciya ko kiyi zuciya to abin ba hakabane sai ka tambayi kanka in kayi maganan da bai kamata ba tan ta gayamaka kas kiya sai kayi zuciya ko kua kiyi zuciya to abin ba haka bane, bai kamataba kuyi haka a saka ninku ku masoya.

Idan zaka duba yaro ma wanda yakan soma sabon tafiya, zaka ga idan yafara tafiya ko idan yatashi sai kaga ya fadi amma duk da haka bazai kiba sai ka ga kuma zai kara tashi to wannan ma yaro kennan bai jada bayaba hakan kaima ba wai a lokaci daya kawai ba sai kiyi zuciya ko kayi zuci dan wani abu yafaru a sakaninku shiya na bada misali idan yaro yafar tafiya.

A wani yanayi zaka mutum yana yin kasuwanci sai kaga jarinsa yakarye amma sai kaga yaje kara nemi wani kudi sai yakara sawa a cikin kasuwancin nasa? to daga nan ne zaga ga ne cewa dan abu yafaru na farko bai kamata ba kayi ziciya sai kara kara gwadawa ka ga ni mai zafaru zuwa gaba.

Kuma zaga mai yin noma, idan wannan shekara bai samu komai ba zaka idan wani shekara yazo sai kaga bai damu da abin da yafaru shekaran da yawuceba, sai ka ga yakara yin wani noman inma bai da wani kudi sai kaga yaje ko ena ya nema kudi yakara sawa a noma.

Haka kuma masu rubutawa jarabawa ta makarantar sama da primary wato sakandare, zaka ga wani ya rubuta jarabawa sau uku amma bai zai ce ba zai kara rubutawa ba sai kaga yayi tayi har sai yayi nasara amma ba zai ce shi yagaji ba to wannan ma kayi alka'ari da wannan kasan ja da baya ba shawara bane.

Ko mai shiga jami'a ma sai kaga idan yagwada wannan shekara idan bai samu ba sai kaga yajira wani shekara idan yazo sai yagwada sai har anyi dace kamin kaga ya daina.

Wannan abubuwanda na lisafa muku dan kisani ko ka sani idan dan adam ka gwada abu guda daya ba ka ci nasaraba kar kayi zuciya kaitayi har sai ka sami sa'a, amma ya dangana game da abin da kakeso dan wani abu har iya rayuwarka bazakayi nasaraba.

Soyaiya yana daya daga cikin rayuwar mu a tayau? zaka ga wani ko da kudi sai yayi duk abin da yana dashi har sai yaga karshen, to wannan ma kasani soyaiya abu ne wanda bazamuce zamu jada bayaba dan yana daya daga cukin rayuwar mu a tayau.

Soyaiya tana da dadi ko da yaro nema yasan yin soyaiya abu ne mai dadi, wasu abinda yasa suke fada haka dan yafaru dasune a baya shiyasa suke gani kamar ko yaushe idan sun kara yin soyaiya hakan zai kara faruwa da su? to kar suyi wannan tunanen komai yakan canjawa babu kamar ma soyaiya har ida kafara da wata sai ka manta ma katabayin soyaiya da wata.

Inna kara maicewa yawanci soyaiya ga wanda suka fara na farko zakaga suna jin dadi dan basu sani wani lokaci soyaiya ta na da daciba, idan yafaru dasu sai kaga kamar zasu mutu dan tashin hankali. To dan allah duk wanda yasan yafara yin soyaya ce na farko sai yayi la'akari a irin wannan yakan iya faruwa dashi a ko da yaushe na bacinrai sai ya danne zuciyarsa ko zuciyarki komai zai zama daidai in allah ya yarda.

Har idan kasan wata ko wani baya sonki ko bata sonka sai kaga yana so yayi kokari yaga yaja hankalinta ko hankalisa in har kasan batasonka to maza kayi hakuri muddin tasan ita ba ta sonka ko baya sonki abin yazam da dole, to dan allah kuyi hakuri da juna dan abin da zai biyyo baya bashida kew.

A wani lokaci zakaga idan soyaiya tazam wani iri kamr shekarunku yazam daban wannan ma yakan zama masal game da masoya, wannan ma sai ku duba yana daya daga cikin kawo masala game da soyaiya.

A kwai wani abinda yakamata muyi alka'ari dashi zaga wani bai da sana'ar da yana yi sai ka ga wai yana neman wata shi kuma baiyi kokarin yayi tunani yaje yane mi sana'a ba sai idan ta samu wani ai kaga wai yana cewa ai ta yaudareshi ko ta ga da bai da komai shiyasa ta kishi? kasan mata da maza da banne zaka iya zama sama da shekara gumasha amma na mace baza ta iya ba dan suna da lokaci amma kai baza ka duba ba sai ka ce wai sai kasamu sana'a kamin kayi aure bayan ba a san lokacin ba kuma sai kaga baya sa na'ar komai wai yana nemanta sai tayi tajiransa har kaga tagaji dashi, in ta samu wani wanda yanada sana'ar a yakeyi idan yafar nemanta sai kaga wai yana cewa allah ya isana kin cuceni dan kingani banda kudi a hannuna.

Zaka ga wani yana soyaiya da wata yar mai kudi sosai amma sai kaga shi dan talaka? a rayuwa soyaiya ba ruwansa da kudi amma ka dauki yarinya daga gidan mai kudi tana shan ASSI si ka kaita gida haya kai ma kasan in ba tana sonka sosaiba bazata yarda ba daga gidan dadi zuwa gidan haya kaima kasan a kwai masalan fa himtawa ga wanda bai sani ba.

Akwai wani babban abu wanda mu maza ko mat wanda mukayi kuma munsan illar a karshe shine kamar:-

in kasan kana neman mace ba na aureba kawai na yin soyaiya ne to kar ka fara, dan idan ta yaudareka kar kaga laifinta kace wai ta yaudareka idan ta samu wani wanda yana sonta zai aureta. Dan yin haka yana da hasari game da wanda ba nemanta na gaskiya yake yiba, shiyasa kanemi na aure dan kar bacin zuciya ya sameka zuwa gaba.

Amma idan kaga kana neman yarinya amm tana da rawan ido sai kayi kokari ka kai kayan sadaki dan idan wani yanemi yazo wurinta sai iyayenta sun sani, shiyasa akeso kayi binchike iyayenta kamin kafara neman yarinya, idan har kagane iyayenta masu neman duniya ne sai kasan me zakayi tun kafin kafar nemanta, kasan wasu iyayen suna son duniya koda kai kakawo kudin sadaki idan wani wanda yafika yazo sai su mikamaka kudinka suce zatyi makaranta ashe kuma ba haka bane.

Har idan kaga idan kana neman mace har idan kaga tafaramaka jan baya ko yin wayar da kukeyi yajabaya ko yin haduwan da kuke yi ba kamar na da ba kuma bata yawan kula ka kamar na da, to kasani a kwai wani abu a kasa da yake tafiya ko ta samu wani sabon saurayi sai kaga komai ya canja a sakaninku kamar bada ita kake soyaiyaba.

Idan hakan kaga yafaru dakai sai kayi kokari kayi bincike kaga me yake faruwa idan har kagagar ganewa sai kadena yimata magana ko kiranta kar kayi kamar na sati biyu, har idan ba ta damu da kaiba tanemeka to kasani ta samu wani wanda tafara soyaiya da shi, to kasani ta daina sonka sai kasan mezakayi, karma ka dame kanka katozarta mata maiyasa ta canjamaka dan ranka zai bace sosai dan zata gayamaka abinda zai da meka dan karkakar yimata magana.

Magan ta karsh da zan fada shine, har idan kasan kana soyaiya har mace ta bata maka rai sai kayi hakuri ko kiyi hakuri ka ba wa kanka hutu na wani lokaci idan ka huce sai ka koma yin soyaiyarka da budurwarka.

Hakuri shine maganin zaman lafiya, kar abi wa zuciya daga baya kuma ayi da nasani. Wannan shine bayanin da zan iya yimuku game da yin zuciya sakanin mace da saurayinta.


contact-form


Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home