Zaka Iya Duba Bayanai Wanda Likita Suka Baiyana Game Da Wasu Cutuka Kamar Su Ulcer...
Bayanai Game Da Cutuka A Jikin Dan Adam Bisa Kasa
A yadda bayani yanu cewa, wani bawan allah ne yayi tambaya game da wani masala da yasamesa ta hanyar wata karamar hannunsa yana yi masa ciwo, a awani lokacima wai sai kaji kamar ba jikinsa ba kuma yana yawan damunsa kamar yasa hannaunsa a kankara hakan yake, yana tunani ko yasar ciwon sanyi da a ka sani ko shine ya kamashi, shiyasa yanemi tambaya game da wannan ciwo zuwa ga likita.
Wani babban likita dake zama a birnin lagos wadda aka fisani da "SHAZALI".
Shi ciwon sanyi bawai shan ruwan kankara ne yakan kawo shiba, kokuma a lokacin sanyi sai kaga wai mutane suna cewa kar ciwon sanyi yakamasu, ba wai haka bane shi ciwon sanyi anna iya kamashi ko ta wajen saduwa da mace ko kuma idan kun hada jiki da namiji ko na mace ana iya kamawa ba wai shan kayan sanyi ne yakan jawo waba a yadda likitan yace.
Yan dada kara mai cewa ciwon ita na sanyi da ban take, kuma ita ciwon ta kashi shima daban yake, chiwon ita wato ta sanyin kashi anna samunta ne ta wajen abubuwanda muke hadiyewa ko kuma muna ci a cikin abinci daga ciki ne yakan taruwa a jikin mutum yazo har yataru a sauran gabobi na dan adam a cikin sakanin gaba ko kashin kafansa shiyakan kawo ace masa ciwon sanyi, idan har yataru ga sakanin kafanka ko sakiyar kashi sai yadinga damunka, dan taruwanda yayi a kafanka sai idan kataka sai ya dinga damunka, shiyasa wasu suke ce ai ciwon sanyi ya kamani.
Shi wannan ciwon yawanci anfisamu tawajen manya maza da kuma mata da shike shekaru yaja, amma yara kuma baya kamsu dan sunyi kanana, har idan kaga wani yaro karami kafarsa yanuna alaman kun buri to ba ciwon sanyi bana allama yana nunawa yana da ciwon ta sikila ce ba sanyi bana. Kuma kasani har idan iyayenka suna da wani ciwo na kakkanni to kai ma kasani zaka iya samun wannan ciwo dan ana gada.
Munyi wasu bayanai bisa sama akan wato aka ciwon sanyi? a wani lokaci zaka ga mutu yana yawan samun damuwa a kafansa, zaka ga yana kumbori, sai suna cewa ciwon sanyi ne to ba hakabane, wato ana samun wannan ciwo ne ta wajen idan har mutum yana yawan cin nama dayawa to akwai wani sinadari ne dake jikin dan adam wanda har idan yana yawan cin nama sai kaga kafansa yana kumburi ba komai bane illa wani ciwo ne wanda ake kirarta "Uric Acid" a turance kenan, sai kaga mutane suna cewa sanyi yakamasu to ba wai hakan bane yawan cin nama ne yakan kawo haka.
Kuma dole ne kaje zuwa asibiti dan a gwadaka dan a san abunda yake damunka, yakan zama ba "Uric Acid" ne yakan damunka ba zai yazama wani larurane daban yake damunka, shiyasa muke so mutum yaje asibiti dan tabbatarwa kasan me yake damunka akan kana cewa a'a sanyin kashine yake damuna amma she ba hakan bane.
Dokta Ina yawan ciwon kai kuma yadade yana damuna kuma koyaushe idan yafara damuna sai kaga narasa abinda yakan yimini dadi.
Sakon Amsawa Daga Likita:-
Shi ciwon kai a yadda kafa abune karami kuma tawani bangare abune babba" yadda kace yana damunka sama da shekara hudu? to kaga wannan shekara hudu da kace ma shima wani abu ne daga ciki. Ciwon kai a yadda kafada ba abune wanda zancemaka ba a lokaci daya, dan abune wanda yakanso a samu lokaci da likita su bincika yadda abin yafara damunka, kuma yakan faruwa ne a wani lokaci kokuma yana yimaka wani lokaci, lokaci, kasan shi ciwon kai yakan faruwa har idan mutu yagaji kokuma yayi yawo a rana sai kaga yafara damunsa amma wanilokaci idan yasamu hutu kadan sai kaga yasamu sauki kokuma yanemi magani na ciwon idan har yasha sai kaga yasamu sauki.
Nabiyu kuma shine a kai wani babban ciwon kai wanda ake kiransa "Migrain" a turance, shi wannan ciwon kai yana da balla'in zafi ta gefe daya na kai na dan adam, zakaga ma idan har yafara, baka isa ba ka sunkuyar da kanka dan zaka ji kamar kanka zai fadi zuwa kasa, kuma shi wanan ciwon kai yakan dauka lokaci har sai ma kadage da neman magani kamin kafara jin saukinsa
ME YAKE KAWO FISARIN JINI
Amsawa daga Tujudden:-
A yawanci anna samun masala ne game da wasu kwayoyin cutuka da yake taruwa a mattattaran fisari sai kaga dan adam a wani lokaci sai kaga yafara yin fisarin jini kokuma ida yafara fisarin in yazo karshe sai kaga jini yazo a karshe to sai yayi maza ya ziyarci asibiti dan ganin likita kar abin yazam sanani.
Likita, Wai Dagaske Ne Maganin Sauro Har idan a ka shafeshi a jikin dan adam wai yana da masala?
Amsa Daga Malumfashi:-
Lalle kam yawanci mutane suna amfani da maganin sauro na shafawa zuwajikinsu amma bisa ga yadda fatar mutum yake, wani baya karbar jukinsa, kuma zakaga wani jikinsa wato fatar zai fara tashiwa ko yafara yimasa kaikayi, to bazaka shafa kawai a jikin kaba sai kasamu wani gefe ka gwada ka kagani idan har bai yimaka wani illa ba na zuwa wani lokaci to da allama ya kar be jikinka to zaka iya shafawa zuwa jikinka gaba daya, amma kawai sai kafara shafawa zuwa jikinka to zaka iya jawowa kanka masala sosai dan wani magani sai da gwadawa ko jikinka yazo daidai da maganin.
IDAN MUTU YASHA LEMON KWALBA KO KAYAN GONGONI NA GAS, YANA KAWO ILLANE.
Amsawa Daga Likita Sulaiman:-
Shan kayan kwalba wanda yakan dauke da gas a yadda ma'aikatn kula da lafiya suka baiyana cewa, shi gas na kwalba ko kayan ta gongoni bai da wata illa dan anyi bincike sosai akan wannan gas ta kowane kayan kwalba ko na cikin leda basu da wani illa a yadda bincike yanuna.
Shwara ga kowane al'umma har idan kasamu wata masala dan allah kayi kokari kaje ka ga likita dan barin ciwo a jikin ka yakan sama wani abu daban ajiki, kamar yadda mukayi magana a sama ta farko akan ciwon sanyi amma ashe ciwon "Uric Acid" ne yakan damunka, wato ciwon da ake samu tawajen cin nama.
contact-form
Labels: Hausa
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home