Shawara Ga Mallami Na Addini Game Da Ciwon Da Yaki Warkewa Bayan Anyi Na Asibiti
Cutukar Game Da Jikin Dan Adam
A rayuwa a yadda rayuwan al'uma yanuna, tawanci jama'a suna fama da yawan ciwon kai, sai dai ko da yake ciwon kai ya banbanta kala kala, wani yakan zama idan yagaji kokuma yayi yawo a rana, wani kuma ciwon kai nasa a cikin jini ne. To ga hanyar da zaka yi insha allah zaka yi mamaki dan kowane ciwo da allah yayi a duniya a kai maganinsa in har ka hada da addu'a zaka samu sauki in allah yayarda.
Daya daga ciki shine ka karanta "SURATUL FATIHA" har idan duk lokacin da har idan kanka yafara maka ciwo ka kama dai dai inda kanka yana yimaka ciwo sai ka karanta "Fatiha Kafa Daya" kafa daya in allah yayar lokaci kadan zakaga kanka ya daina maka ciwo insha alllah.
Har ida mai dena yimaka ciwoba, kakara karanta kafa Biyu in kakaranta bai dena ba ka karanta kafa bakwai in sha allah zai dena nan take ba da jimawa ba, shi adu'a yana da mahimmanci sosai.
Na biyu kuma shine, zaka iya amfani da wata mai da ake kira "HABBATUS SAUDA" zaka iya kane meshi amma ka tabbatar cewa ka samu wanda yana da kew, sai kasamu Garwashin Wuta sai ka ringa subawa kadan kadan zai fara hayaki sai ka dinga "SHEKA" a hankali hankali insha allah zai dauke nan ba da jimawaba.
Ta uku kuma zaka iya amfani da man " TAFARNUWA" sai ka dinga shafawa a goshinka kokuma inda yake yima ciwo insha allah za a samu waraka. Alla yasa Mu Dace Ameen.
Shi wannan ciwon ta kai yakan kama dan adam kamar yadda mukayi bayani bisa sama ga da yadda yake kama an adam. Shi wannan ciwon ta kai ya kasu kala kala, wani yakan yimasa a Goshinsa, Wani kuma yakan yimasa a bayan kansa, shiwanna na bayan kai yawanci yana damun masu hawanjini har idan jininsu ya dan hau kadan ko ya dan sauka sai sufaraji ta bayan kansu, amma wani lokacin koda jinin bai hauba, kuma bai saukaba zai nuna musu allama ta bayan kansu yan yi musu ciwo ta da allama jini yana kokarin hawa ko yana neman ya sauka. Har illa kuma zakaga wani ciwon yana yimasa a fuskansa ta gefa daya wanda aka fisani da (Migrain) a turance kenan, wani kuma zakaga gefen idanunsa ne yana yimasa ciwo ammam ba wai idon ne yake yimasa ciwo ba.
Shi wannan ciwon ta kai na gefe daya shine wanda mukayi bayani bisa sama wato (migrine) shi wannan ciwonkai ta gefe da yane a yadda mukayi bayani, shi wannan ciwon kai ya bambanta da kowane ciwon kai, dan har idan yatashi maka zakaji kamar gefen kanka zai fita ko da ka sunkuya za kaji kamar idonka zai fita, kuma wannan ciwon ta gefe daya baya warkewa dan a yadda likitoci sun yi bayani, basu taba ji wai wanda yana da ciwon kai na gefe daya ya warke ba, sai dai idan ya tashimaka sai kaje asibitin wanda sun kware da "kai" dan su baka magani, Kuma in har yatashi maka, shan su kamar "paracetamol" ba zai yi maka komaiba dan shi wannan ciwon ba karramin ba gani za kasha ba kamin kasamu sauki.
Wannan ciwon ta migrine sai dai ka dinga shan magani a kunlum duk lokacin da ya tashimaka dan kasamu sauki amma ba wai kamar sau ran maganin ciwonkai ba idan kasha zai dauke gaba daya sai ya dauki wani lokaci da dama kami kafarji.
Ita kuma ciwon kai ta kan"Hanci" shikuma wannan ciwon kai yafi kama wanda suke da "Mura" yakan damunsu. Wasu ciwon kai din yakan kawo wa ne ta wanjen abinda muke ci kokuma abinda muke sha da kuma in zazzabi yakamaka sai yanuna maka allama da sauransu.
Wata mai suna Habiba Tana mai cewa " ida wani yabata mata rai ko wani abu yasa meta na da muwa to ranar zata kwana ko ta wuni ta na fama da ciwon kai a yadda ta ce.
Wani likita yana cewa ga Habiba yace wannan shine ciwon kai na damuwa amma har idan kin samu kwanciyen hankali kadan zai sauka amma har idan kina yawan damuwa, kuma yana yawan damunki idan har kinshiga wani damuwa to yakan iya yakawo miki hawanjini sai kiyi kokari ki kai ziciya nesa dan kar kishi masala a yadda likitan ya gayamata.
Likitan yakan karacewa dalilinda yasa muke yin rubunda kowa bazi iya ganewaba sai ankai wa likita shi zai gane me aka rubuta, dalilinda yasa muke yin wannan rubutun haka da kar a gane wani idan yasani zai mayar dashi kayan maye, kokuma yaje yayi amfani da shi ta wajen mugunta. Tana kara mecewa idan aka kai takardan wajen mai sayar da magani sai yace bai ganeba abinda aka rubuta, sai likita yabata amsa yace ai idan likita yayi miki bayani ko yayi maka bayani ga sunnan maganin da kuma yadda zakayi amafani da ai shikkena magana yakare tun da anyimaka bayani yadda zaka yi amfani da shi.
Wani yana tambayan liki akan yana da ciwon siga kuma yana bin ka'ida yadda likita yace nabi, amma ina yin fisari sosai kuma sai yinjiki nakeyi, me shawara likita? Sai aka abashi ammsa akan yayi kokari yaje asibitinda aka rubuta mishi maganin sai yayi ea likita bayani ko kayi kuskure ta wajen yin amfani da wannan maganin ko ba ka shansu bisa ka'ida.
Wani kuma mai suna Nuhu yake tamyan game da wai wani abu ne ya fitomasa a wuya ta baya amma baya yimasa kaikayi kuma baya yimasa zafi ko wani abu? Sai aka bashi amsa akan yayi kokari ya tuntube likita, dan irin wannan masalar yawanci "Jifan Dajine" dan shi idan yashafe jikin dan adam to baya yin zafi sai dai kaga yana ta cin jikin dan adam. To sai kayi kokari kaje wuirin likita dan kasamu bayanai sosai game da wannan larural.
Wani kuma yakan tambaya ne game da wai, hakorinsa ta gefe daya ta karshe yana yimasa ciwo amma yayi shwara akan yana so yacire shi amma wasu sunce idan yacire zai kama na kusa da shi ko hakan gaskiya ne shiya sa nayi tambaya. Sai yace masa a'a wannan bahaka bane barin hakori wanda yana da susan yakan iya kama sauran har idan yagama da wanda yakama sai ya koma kan dayan, amma sha wara mai sauki shine, zaka iya zuwa asibiti har idan bakas ka cire to za a cika wannan raminda yayi da wata garin siminti na podar hakori amma cin kashi zai baka wahala, in kuma kana so a cire shi sai a chire ka huta gaba daya.
Wani kuma yake tambaya wai game da har idan ya samu masal game da jo idan yana yankan farcensa har idan reza ta yankeshi sai yafara ji kamar zai fadai sai hajijiya ya kamashi wani lokacima sai har yane mi waje ya zauna kamin hankalina yazo, to menene mafita? Amsan da yasamu shine, yawan hajijiya har idan mutum yanayi yawancin har idan mutu yazubar da jini sosai yakan iya samunsa, wani kuma idan kawai yaga jini ko a kasa ko a jiki wani ballema wai yaga a jikinsa sai hajiji ya yakamashi, hajijiya yawancin yana zuwa ne game da zubar da jini a jikin dan adam in har ba wai rashin lafiya ce ta sameshi ba.
MENENE MAGANIN CIWON BAYA KUMA DA MAGANIN CIWON JIKI.
Wani bawan Allah ne yakewa wani mallami tambaya gabe da yana fama da ciwon baya yana mecewa ga wannan mallam bayansa ne yana yimasa ciwo, yake gurin likita anyimasa gone gone amma har yanzu bai Nina allama ta wani ciwo ba, amma ni dai nasan abinda yake damuna har ma wani lokaci Nana iya sunkuyawa, kuma yana yawan sani yin fisari da kuma yin iska, haka zalika idan har yatashi mini zafin nan sosai yake yimini kuma ina da"Basir" narasa abinda zanyi tunda name asibiti basuce sunga wani ciwoba ko wani abu ba.
AMSA DA WANI BABBAN MALAMI YA BAIYANA.
Mallamin yana maicewa, mu mallamai ana tunawa da mu ne idan har mitum wani ciwo ta sameshi ko wani larura to ana za a nememu. To akai wasu hanyar da zakabi ko kuma wasu abubuwanda zan lisafamaka said nayi amfani da su kaga me zai biyo bays. Kane mi wannan abubuwan shine:-
- Man zai tun.
- Man Habba da kuma.
- Man tafarnuwa.
- Zayi Fatiha kafa bakwa 7 zama daya.
- Zaka karanta Ayatur Kursiyu kafa 11.
- Zaka karanta Suratul Yasin Kafa 1.
- Suratul Milk shima kafa 1.
- Suratul feel Shima kafa 5.
- Suratul Shitta'i Shima kafa 5.
- Suratul Iklas ma kafa 3.
- Suratul Falaq ma kafa 3.
- Suratul Nas Shima kafa 3
Kuma yakan cewa zaka iya shafawa ta ko ina a jikinka a duk inda yana yimaka ciwo insha allahu zakaga abin mamaki sai ka samu sauki in har kabi yadda nacemaka.
Dangane da Basir da kace yana damunka, sai kanemi:-
- Kannemi Garin Ganyen Magaraya
- Garin Ganyen Sabara.
Kowannensu zaka FIBA cokali 7 Sai ka hada da Garin Tafarnuwa cokali 3. Sai ka hada da Zuma mekew ka ringa sha, in Allah yayarda zaka samu sauki bi izninla.
contact-form
Labels: Lafiya
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home