Sunday, September 26, 2021

Bayanai Game Da LIttafin Soyaiya Ta Hausa, Ko Me Yake Ciki....

 


Menene Akece Littafin Soyaiya, Kuma Yaya Ake ji Idan Aka Karantashi

    Bayanai yana zuwa muku ne domin game da yadda mata da za suke yin karanta takardun hausan ko zan ce littafin soyaiya za a ce.? Maganganu da da ma suna zuwa ne game da cecekuce akan yin karanta littafin ta soyayai ga jama'a, babau ma kamar ma mutanen ta Nigeria suna son karanta littafin soyaiya babu ma kamar matan aure har idan basu da abin yi sai su dauki littafin na hausa su fara karantawa amma yanzu zuwa finafinan hausa yaragesu da yin amfani da littafin soyaiya ko karanta shi.  

2.  A yanayin yadda abin yanuna, yawanchi littafin yakan badab labarine game da zamantakewa da kuma yin soyaiya kokuma yin al'ada ta hausawa kokuma yanayin rayuwa ta duniya da sauransu. A kwai wata bangare a kano wanda ake kiranta wato'Dabino" a hausance wannan wurin ya kunshi littafin ta karatun hausa da dama bamu ma kamar ta yin soyaiya dan sauransu, kuma yawancin takarda mata ke sarrafasu kokuma zance mata ke rubutasu, jama'a da dama suna zuwa su saya yanmata da kuma matan aure ma suna zuwa su saya.












3.   Wata baiwar allah tana mecewa, ita a kunlum tana karanta wannan littafin ta soyaiya ba don komai bane dan takare kanata da kuma tazama bai bada shawara gameda wani abin idan yafaru gameda masoya biyu sai tazama mai bada shawara, tace karanta wannan takardan ta littafin soyaiya yana da mahimmanci sosai ga masoya dan zai nunamaka yadda zaka bi idan ranka yabace sakaninka da budurwarka kuma da yadda zaku sasanta a sakaninku da masoyarka ko masoyinki a yadda ta fada.

 4.   Tana kara mecewa akawai wata littafin da a ka yita wato wanna littafin yana nunawa game da ranar da mace zata shiga dakin mijinta a ranar aure to wannan takardar ta samu shiga sosai ga wa matan aure da kuma matan da basu yi aure ba. Kuma tana kara mecewa a kunlum sai mata sma da goma sunzo sunsayi wannan takardan, dan mai sayar da wannan takardan shi yayantane zai chika a cikin jakar sa amma kafin ya iso kasuwa sai yasayar sama da goma a hanya kamin ya'iso shagonsa.












5.   Kuma yawancin wannan littafin yana da bayanai dayawa a ciki dan bazaka ga ana maganar a fili ba amma har ida kafara karanta wannan littafin ta soyaiya, zaka ga abubuwa da dama sai kaga kamar ma kana kallon fim ne bakaso yakare sai kaga karshensa, kuma yana da abubuwa kamar yadda zaka tafi da rayuwarka a sauwake ta hanyar soyaiya tare da masoyarka ko masoyinki batare da ansamu masalaba.

 6.  Wannam littafin hausa ta soyaiya yana bawa jama'a masu neman aure dakuma wanda sunriga sunyi aure in har kin cuce mijinki ko kai kincuce mijinki ko saurayinki ko budurwarka zakaga sakamakonsa a karshen abinda zai faru da kai ko da ke, dan ya kunshi masaloli ta wajen yin soyaiya da mace ko soyaiyar bayan ancika alkawari anyi aure yana runuce yadda zakibi da mujinki a ko da yaushe yana tunanenki ba wai kawai kina gani dan kunyi aure ba sai ki kwanta ki mika kafan ki dan wasu basu iya soyaiya ba amma muddin kina karanta wannan littafin zakiga ashe kin bata lokacinki da jimawa dan mata dayawa sun koyi yin soyaiya ta wajen karanta wannan littafin.

 7.   A kawi ta baiwar allah wanda ake ki ra sunanta Fatima Sulaiman? ta baiyana cewa tasamu alhairi sosai game da sarraf littafin ta soyaiya da kuma wayar da mutane ta wajen ilimi da zamantakewa ta wajaen aure. Tace ta rubuta wannan littafin sama da 21 kuma har yanzu tana rubutawa da bata da wani abinyi ko wani sana'ar sai rubuta littafi sai ta sayar kuma har yau ba wanda yace mata littafin ta bai da kew da yayana nuna yadda zakayi rawura a ka idancen bida musulunci ko babu ma kamr tawajen yin soyaiya amma yawanci mata ne suka fi sayar wannan litafin dan yawanci yakunshi mata ne ba maza ba.

8.    It wannana baiwar allahj maisuma "Fatima Sulaiman akwai wasu takardan ta rubutashi guda shida amma guda hudu dagaciki sun samu nasarar shiga finanfinan ta hausa, wato takardan ne ta kunshi wani abu ne wanda yashafi wata mata da tana da bakin zuciya game da kishi wanda tayikokarinta taga ta hana mijinta yin aure harma tayi kokarin ta ga ta hallakashi amma abin abiyuba. To daga nan ne suka duba wannan littafin ita yadace su yi fim din hausa akan sa dan yana da mahimmanci sosai ga al'umma dik wanda yagani zai yi tunani abin da zai faru zuwa gaba shiya aka yi kokari akayi fim na hausan sa a ciki.

 9.   Wasu littafin ta ya kunshi abubuwa da dama kamar wanda suna da mataye sama da daya ko kuma masu guda hudu, Kuma wasu sashin daga cikin takardun ya yayi maganane akan yadda iyaye suke yiwa yaransu aure tun suna kananansu amma kuma ya wancin yaran suna so suga sunyi auren har ma ida sunyi makaranta a yadda ra'ayin su yake.

10.    Wani bawan allah mai suna Sani Yakubu yana maicewa, wannan littafin ta hausa yakunshi abubuwa da dama game da hausawa da kuma yanayin rayuwa ta duniya, kuma yana kara de maicewa wannan littafin bai wai kawai a Nigeria ce ake yin amfani da ita ba, yace harma kasase ta ketare suna sayen wannan littafin sukai zuwa kasarsu suma su sayerdashi dan suma suna amfana dashi ta wajen fahimtar rayuwa inji mallam "Sani Yakubu.

 11.  Mallam yakubu yana maicewa, a kowane mako muna samun sabon littafi guda ta kwas wanda aka kirkro kuma kowanne a muna sayar dashi akan naira 250 zuwa 300 amma idan har sabone  yakan kai naira 350 wani lokaci ya dangana a yadda kasu wannan littafin in har yazo maka da sauki zaka sayar dashi da sauki amma idan yazo maka da sada kaima zaka sayar da sada, hakkan muke jiyawa a hankali hankali.

 12.   Yan akar maicewa, a shekarun baya da suka wuce jama'a da dama suna zagin wannan littafin suna ga kamar bata lokacine, amma yanzu su da kansu suna mecewa ai wannan littafin ashe yana da kew dan yakan nuna al,adu da kuma sauransu game da rayuwar dan adam wanda har ma idan kafar karantashi ba kasoma yakare sai kaji wanni iri.

13.    Yakan kara cewa zakaga yara da dama sunzo sunsaya wannan littafin iyayensu ne suke aikoso su sayo musu dan su karanta dan baza su samu sufitoba dalilin zaman aure. A kunlum sai kaga yaro yazo dashi a rubuce dan ba zai iya rikewa ba sai su rubuta mishi akan wata takarda, muna samun irin wannan sama da ashirin a yini har idan ansan kanada isheshen littafin a wajenka.

14.    Sani Yakubu yakara cewa zakaga mata sun zo sun saya samada 50 idan sunje anguwa sai su dinga bada haya dan suma su samu wani abu a ciki dan wasu masu da lokacin da zasuzo kasuwa dan neman littafi amma idan ankawo musu zuwa gida yafi musu sauki sai su bada mai rahusa bayan sun karanta sai su maiyar wa maishi kuma su kara daukan wani.

15.    Kuma wanna littafi ba wai kawai a gidane kawai ake karantawa ba, harma gidan FM ma suna gabatarwa a kowan litinin da alhamis na safe kuma jama'a da dama suna jiran wannan lokaci dan sauraron wannan littafi ta sawon miti gomasha biyar a kowace littinin da alhamis.

16.   Wani mallami da yacw a lokacin da yake koyarwa kamin yayi ritaya, yace mata dalibai suna zuwa da wannan littafin ta hausa suna boyewa a cikin rigarsu dan idan sunsa a cikin himar nasu za a gane sai suna karantawa a boye dan kar malam yagani harma idan suna tafiya zakaga suna karantawa har a kai wani lokacinda wata karamar yarinya tana tafiya sai tana karanta wannan littafin ta hausa har mashin ya kadeta hannunta yakarye, kaga wannan littafi yana da abubuwa da dama wanda har idan kafar karantawa baza ka jidadi idan yakareba sai kaga tuni sun gudu kasuwa sun saya wani littafin.

17.    Amma wasu mallan addini sun tayi korafi game da wannan littafi akan hakan ba daidai bane ya lalata yara.

18.   A kwai wata shekaran da ta wuci wanda jama'a suka kai kukansu zuwa ga gomnatin kasar game da wannan littafin ta soyaiwa harma sanadiyar wannan karan da aka kai, aka bada umurni abi kowane makarantar a tara wannan takardun a samasa wuta gaba daya, yaza kowane makarantar dake cikin kano an kwashe wannan littafin gabadaya an samusu wuta.

19.    Bayan haka sai jami'an gonati suka ce duk wani littafin da aka bugashi sai ankai zuwa jamiyar ta illimi an tantance kamin a fitar zuwa kasuwa ko zuwa makarantu.

20.    Amma wannan dokar bai jima ba dan masu shirya wannan takarda sun kai kara zuwa kotu sun ci nasara game da kotu ta basu sufada albarkacin bakinsu a yadda suka buge wannan dokar ta hanna biga littafin soyaiya.




contact-form


Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home