Monday, October 11, 2021

Menene Tarihin (Baiyajidda)




Tarihi ne gameda wayene (Baiyajjida) kuma,
Wayene Idi Aminu Dada

Muna baku ne tarihin game da wani babban bawan allha wanda aka fisanin sunansa"Bayajidda" wanda yakafa tarihi a kasar hausawa.

Wasu masana da suka yi bayani game da wannan bawan allah, Bayajidda wani babban gwarzo ne wanda yakafa tarihi ayankin hausawa ta wajen cingaba.

Bari muduba tayaya yayi rayuwarsa:-

    Shi wannan bawan Allah mai suna Bayajidda, babu wanda ya bada cikakken bayani game da shekarunsa ko mutuwarsa, a yadda tarihi ya nuna mutumin Bagadaza ne daga can kasar ta Iraki, ya biyo ne yashi kasar ta nigeria amma ta Maiduguri jahar Borno ta cenne ya shigo saga nan ne sai Yakoma zama a Daura cen jahar Katsina da zama.

MENENE TARIHINSA:

    Wasu suna cewa ne shi Bayajidda na daya daga cikin Karni ta 17 har zuwa 20 amma kasancewar hausa ta al'ada yanuna cewa Nacikin Karni ta 8 zuwa 11.

    Yadda tarihi yanuna akan cewa sunnansa "Abu Zaid" amma aka nadamasa sunan ta hausawa a matsayin "Bayajidda" wato dalilinda aka samasa wannan sunan shune, akan bayajin hausa, shiyasa aka samasa wannan sunan a matsayin bayajidda a yadda tarihi yanuna.

ME LABARI GAME DA (MACIJIYA)

    A yadda labari yanuna akan shi Bayajidda yayi kokari har yakashe wata (maciciyar) dake cen jar har Daura. It's wannan maciciyar da dame kowadake zama a wannan kauyan ta (Kusungu) duk wanda zai he wannan rijiyar dan neman ruwa to sai wannan maciciyar ta kireshi.

    Suna iya diban ruwa a wannan rijiya a mako daya kawai wato muna nufin ranar (Jumma'a) kawai amma shi Bayjidda sunbashi shawara akan karyaje kusa da wannan rijiyar in ba ranar (Jumma'a).

    Yakijin nasu sai yatafi ranar alhamis neman ruwa sai wannan maciciyar ta fito masa, sai da ikon allah ya baiwa wannan bawan allah dama ya pille ma wannan maciciyar kai da takobinsa inda yakara yinsuna inda jama'a suka fara samun daman zuwa diban ruwa a wannan rijiyar.

TAYAYA BAYAJIDDA YAYI (AURE)

    A wannan lokacinda suke fama da wannan maciciyar, ita Sarauniya Darma tayi alkawari akan duk wanda yakashe wannan maciciyar, to tayimasa alkawarin bada rabin wannan grain, sai ga Bayajidda kuma allah yabashi sa'an kashe wannan maciciyar.

    Sai dai kuma, shi Bayajidda bai amsa karbar wannan alkawarinda tayiba, shi yace bazai Karba ba sai dai yanaso zai aureta, amma a tarihi yanuna akan cewa Sarauniya bata yin sure sai gashi kuma ta aure Bayajidda. 

    Tarihi yanuna akan yadda Bayajidda yayi rayursa a wannan kauyen, kuma yashiga tarinda bai yaba faruwaba akan Daurama ta aure she dan tunda ana yin sarauta, mata ne kawai sune suke sarauta amma bayan sun yi aure da Daurama, a yau yaranda suka Haifa su suka gajeta.

Wannan shine iyakan tarinda muka samu game da (Bayajidda) daga daura jahar katsina.

GARURUWAN KASAR HAUSA.

    Shi wanda muke magana akan sa shi Bayajidda, ya Haiti yara guda (3) a cikin yaran nafarko sunansa Biram, wanda suka haifa da yar sarkin ta jahar Daular Borno, sai kuma a kwai Bawo, wanda suka samu da Sarauniya Daurama, na uku kuma sun haifa da wata kwarkwarra.

    Bawo ya haifi yara guda (6) shida, shikuma d a kawun nasu sun mulki garuruwan da dama wanda a yanzu ake kira "Hausa Bakwai" sune wato Daura, Katsina, Kanlo, da kuma Zaria da Gobir, sauran kuma sune Hadeja da Rano.

......................................................................................................................................................................




              WAYENE IDI AMUNU DADA

    A yadda tarihi yanuna game da Idi Amuni Dada, shi aminu dada babban jarimi wanda yayi gogar maya a lokacin da yake mulki. Shi Idi Aminu marigayin sofon shugaban kar ta"Uganda" She anhaife shi ne a shekara tsakanin 1923 to 1929 an haifeshi a wata kauyen kabilar ta "Kakwa dake kusa da bakin wata rafi, wato kusa da bakin ruwa a kasar ta uganda.

    Shi marigayi Aminu yayi mulki ne daga shekara "1972 har zuwa 1979. a wanan lokacin she Idi Amin yayi wata shugabanci ne na gaba wanda har idan baka kabilarsa to kana cikin wahala, yakashe mutane da dama daga dubu "1000 har zuwa 3500" a lokacinda yake mulkinsa a yuganda.

    Shugaba idi amin yayimakarantarsa ne na horar da sojoji a can kasa ta burtania, kuma da aga nanne har yasamu girmar ta "lutanant".

    Daganan sai ita kasar ta Uganda ta samu yancin kanta a shekara ta "1964" inda aka nada wani mai suna Milton Obote, a matsayin fraiminista inda yai kokarin ya kara wa shi Idi Amin girma har zuwa Kaftin dalilinsa da biyaiyan da yayimasa shiyasa ya daukakashi.

    Idi Aminu Dada yazo yazama babban dan jagoran ta Comandan sojoji. Idi Amin da Obote an zargesu da laifin fasa karsan Gold da Coffee dakuma hauran ta giwa na democradiya a kasar ta "Congo" da ga nan kuma sai aka kafa wata komitin bincike game da wannan abinda yafaru. Daga nan ne sai wani sakri dake kasar ta Uganda mai suna "Buganada" a '1962' daga nan ne sai kara masa makami yazama babban genera na sojoji daga nan kuma sai Idi Amin yayi kokari kame wasu ministoci guda biya da wasu kanan ma'aikata, kuma sai yamayar da kansa shiga bankasar ta Uganda.

    Daga nan ne kuma shi wannan sarki Buganada abin har yafi karfinsa yanema gudun hijira da gaggawa zuwa Britania yane ma mafaka daga can ne har allah ya dauki ransa a shekara "1969" a can ta birnin Birtania.

    Shi wato marigayi Idi Amin tunda ya hau wannan mulkin ba abinda yayi sai kabilunsa yake dauka wa a shigar soja, daga nan ne sai Obote wato farko frimminista ya mayar da martani akan wannan abinda yakeyi, sai yayi kokarin ba da umurni da akama shi Idi Amin a daureshi kamar yadda ake daure talaka, sanadiyar wannan ne yakawo gaba tsakaninsu da shi Idi Amin.

    Da ga nan ne sai da Idi Amin yaga haka, sai yayi amfani da makaminsa na janaral yayi juyin mulki a lokacinda Obote yana halarta wata taronda akayi ta Commonwealth daga can kasar ta Singapore.

    Bayan yazama shigaban kasa daga nan ne komai ya chanja a kasar har yasoma kiran kansa Fil'mashal har zuwa tsawon rayuwarsa.

Marigayi Aminu Dada, yana da babbar allaka da mutanen palastinawa.

    Alokacinda da Idi Dada yana mulkinsa, mutane akkala daga 1000 har zuwa dubu 6000 ne suka rasa rayukansu sakamako mulkinda yake yimusu. Sai daganan sauran kasashen duniya suka juyew gomnatin Uganda baya game da mulkin Idi Aminu Dada.

    A lokacinda shekara ta 1979 ne Shigaba Idi Amin, yayi kokari yaga ya mamaye kasar ta Tanzania amma sai Shugaba "Julius" yafikarfinsa da yayi amfani da yen ta adda na Uganda daga nan ne yasamu dama "Obote" yakoma zuwa kan mukaminsa.

    Sai daga nan ne "Idi Aminu Dada" yaga abin yafi karfinsa, sai yayi gudun hijira zuwa can kasar saudia yasamu mafaka, kuma yana da mata hudu 4, daga bisani sai wani ciwon rashin lafiya yakamashi sai aka kaishi babbar asibbintin da ake ji dashi na sarkin makka wato "Faisal" dake saudiya.

    Idi Amin sai jikinsa din yayi tsanani, sai babbar matarsa ta nema afuwa ga wanda yake shugabancin kasar wato "Yoweri" tana mecewa dan allah yayi hakuri Idi Aminu Dada yazo gida dan ya mutu a can, sai yace mata a'a.

Daga nan ne marigayi Idi Dada allah ya dauki ransa a shekara ta "2003" ga watan 16 ga ogosta.

Idi Aminu Dada, yazama babban jarimi alokacin shekara "1960" a lokacinda yake mulkin kasar ta Uganda.




      WANENE AKE KIRA (Kharl Marx)

    Tari hi ne muke da shi game da wani bawan allah wanda aka fisaninsa da (Kharl Marx) shi wannan bawan allah yayi gogor maya game da neman yanchin mutane da kuma fahimtar da jama'a game da yanayin rayuwa. Kuma a lokachinda yake jagoransa ta (Philisopha) yaza duk abinda yafada ana amfani dashi, kuma akan rubuta shi a matsayin babbar wata mujalla ce ga dunuya gaba daya.

    Shi kuma wannan bawan allah nan da ake kira Kharl Marx yayi rayuwarsa ne daga shekara (1818 zuwa 1883) a duniya, kuma yabar littatafe da dama wanda duk jami'ar da kaje a  duniyan nan, sai kaje katarar da abinda yarubuta game da rayuwa da sauransu.

    Shi wannan bawan allah Kharl Marx shi cikakken dan jarida ne, kuma babban dan siyasa be wanda yafada aji. Shi kharl marx yayi rayuwarsa a kasashe da dama kuma allah ya dauki ransa a watan sha hudu ga watan March 1883 daga can birnin ta Lodon kasar ingila.

    Shi Kharl Marx a rayuwansa yayi kokarin karantarwa game da duk wani tattalin arziki nakasa yadda za a sarafasu game da al'umma ta duniya gaba daya. Kuma shi ne yakirkiro yanayin rayu yadda al'umma sukeyi wato (Socialism) kuma shine yakirkiro yarenda yawancin loyoyi keyi wanda aka fisani da (Marxism) da kuma inda kir'kiro bayanai game da rayuwa da kuma zamantakewa wanda aka fisani da (Communist). Dakuma tsarin tattalin arziki ga al'umma tsarin yadda jama'a zasuyi amfani game da yanayin rayuwa.

    Shi Khar Marx yanada iyayi suna koyar da yaren juwish a lokacin "1824" daga bisani sai iyayensa suka bar koyarwa, sai Shi Karl Marx lokacinda yana karami yanada shekara (6) a duniya da haifuwa sai ya ziyarci zuwa makaranta da ma haifinsa yake koyar wa daga bisani kuma sai yayi wasi da makarantar sai yabar duk wani addinin da yakeyi akan yana fada wai iat "Duniyarma ba wanda yayisa, dakuma wai duk hallitan da kaga a duniya, wai shiyayi kansa" Shi Kharl Marx yayi rayuwansa ne bai yarda da allah ba, kuma yaki duk wani addini a duniya akan bai yarda da allah ba.

    Kharl Marx ya ziyarci wata makarantar mai babban tari mai suna (Friedrich Wilhelm Gyamnasi'um) a garinsa na "Tier" yayi shekaru (5) inda yayi kokarin kammala karatun nasa a (1835) a lokancin yanada shekara (17) da hai fuwa a duniya. Kuma wannan makarantar tana koyar da harcina da dama, kamar su latin? kuma shi Kharl Marx yayi nisa a yaren ta latin da wasu yaruka inda yakan karantawa dakuma fasarata batare da an samu matsalaba.

    Daga nan ne kuma yanema ya kure da wasu harcina kamarsu, latin, jamusanci, faransa da sauransu, amma yafi kurancewa da (Jamusanci) dan idan yafar magan da wannan harcen, baya samu matsala ta wajen fahimtar da magana.

    Saboda haka, ma haifinsa yana so yaga Marx ya karanta harkan Lauyanci amma shi a nasa shawara yafiso yakaranta harkan profesa akan na shari'a. Yayi kokarin yaga yazama mawaki a lokacinda yana saurayinsa, amma bai samu daman yin wannan yin wakar ba, saboda karatunda yasa a gaba. Wannan takardan wakokin da yarubuta, sai yazama masa abintunawa a lokacinda yazama babba, har wa yau wannan takardan da yarubuta na wannan kar, sun zama abin tarihi a wasu kasashen nahiyar turawa.

    Daga nan ne sai yaje kara karatunsa a birnin "Balin" inda kuma sai yahadu da wasu wanda suna da irin a kidarsa na neman ilimi ta wajen yadda addini yake tafiya a duniya da kuma yadda al'umma suke rayuwa a dunuya daga bisani sai yakammala karatunsa yazama "Dukta" a (1841). Daga nan ne yayi kokari ya bude wata shfir ta kwakwalwa har inda yayi kokarin zama mai rubuce rubuce ta aikin jarida.

    Daga nan sai Marx yabude wajen sashin kwakwalwa da rubuce da rubuce wanda har yasa shi yashiga harkar gidan jarida, wato yazam a editor nagudan jaridar (Cologne Rheinische) a (1842) sai dai daga baya ita gomnatin ta (Balin) ta rufe wannan gidar jaridar har na tsawon shekara biyu(2).

    Daga nan ne sai ita gomnatin ta faransa ta ko ri Marx daga kasarta, sai yakoma can kasar Brazil da zama inda yabude Jam'iyar ta siyasa ta (Comunist) da kun rubuta ma'anoninta.

    Anan ma sai gomnatin Brazil ta ko reshi daga kasar, sai yakoma (Cologne) sai yakoma editan jaridar (Neue Rheinische) a cikin watan June (1848) dagan shima bayan shekara daya sai ita gomnatin (Prussia) tacemasa ya bar yanki da zama, daga nan ne kuma Marx ya koma can birnin faris ta faransa da zama, bayan lokuta kadan, sai itama gomnatin ta koreshi daga kasar, sai yakoma kasar London da zama.

    Da yakoma kasar Landan dazama, Marx sai ya mayar da hankalinsa akan rubuce rubu a fannin ta jarida da harcen ta (englishi da kuma jamusanci). A cikin watan ta ogos, Kharl Marx yaza babban wakilin gidan jaridar (New York Daily Tribune) a "1862".

    A shekara 1864 Marx yabada gudumawar ta kasa da kasa a birnin ta London. Daga nan ne sai sauran kasashen duniya suka fara nemansa game da abubuwanda yayi na cingaba na wayar da al'umma ta wajen siyasa da sauransu.

    A lokacin 19 gawatan june 1845 Marx ya aura wata yarinyar da duk a kauyen garinsu na Tigre ba wanda yana da Kew na wannan baiwar allah sunanta ( Jenny Von Westphalen) kuma allah ya dauki ranta ne shekaran biyu 2 ga watan ta Decemba 1881 sanadiyar kamuwa da cutar ta Cansa.

    Muwar wannan baiwar allah yasa Marx cikin wata rayuwan wanda haryasa game da wasu binciken da yasa a gaba tawajen fahimtar da jama'a yasamu Marsala, har yaza baya yiwa kowa magana a lokacinda matarsa ta mutu.

    Shi Kharl Marx yawancin rayuwansa akan rubuce rubucene na harkar jarida, baya da lokaci da kowa sai yarubuta kuma yakaranta abinda yarubuta.

    Marx a rayuwars yana shan taba sosai wanda har shine sanadiyar da yakawo masa illa har ajalinsa dan baya wasa da duk wani kayan maye kamar su Giya da sauransu.

    Kami. Marx yarasu, yayi kokarin cinma burinsa game da yadda kasar Rasha ke yin mulki a 1917-1921, inda talakawa masu karamin karfi suka kayar da mulkin sama da (300) da masu bin bayansu dune (Soviet Union) suka kada mulkin kama karaya.

    Daga nanne masu karamin a fada aji, suma suka soma yin shugabanci. Ayau Marx yayi wani abu a duniya inda har yau ana amfani da duk wani takardun da yarubuta ta wajen wayer da jama'a ko ta fannin kimiya da fasaha, ko ta ina yayi magana akai.

    Shi Marx yayi wata rayuwane wanda ake ce (Kore) shi wannan akidarsa ne wanda bai yarda da Allah ba, yace duk wani abinda kaga yana yawo a sama ko kasa har idan na hallitta ne to ba wanda yayishi akan shiyayi kansa ba wai wani ne yayiba, dan shi baiyarda da Allah ba.

    Kuma shine yayi kokarin rubuta littafin ta zamantakewa wanda har ko ina aduniya ana amfani dashi.

    Marx a rayuwarsa ya bata lokacinsa ne ta wajen rubucen rubucen takardan jarida, inda yakeso yaga a ko'ina al'umma suna amfani da wannan yanayin rayuwanmu ana yau.


contact-form


 

Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home