Ina Hujjar Take Kashi Nafarko...... NI Da Dalibata...
DUNIYAR MARUBUTA KUNNENKU NAWA INA HUJJAR TAKE.......
Ina Hujjar Take:...
Idanunta sun yi jawur kamar jan gauta saboda tsabar kukan da ta sha, kana kallonta ka san tana cikin rashin nutsuwa. Yanayin fatarta ma ya nuna ba haka asalin haskenta ya ke ba. Tana girgiza kai ta dubi Hajiya Naja'atu da 'yarta Shafa'u da ke zaune a gefenta, ta ce. "Mummy, rayuwata tana cikin garari, ku tausaya min ku ba ni kariya, idan ba haka ba, wallahi gab na ke da tarwatsewa.
"SHIMFI'DA"
Muhammad, "SHIMFI'DA" Idanunta sun yi jawur kamar jan gauta saboda tsabar kukan da ta sha, kana kallonta ka san tana cikin rashin nutsuwa. Yanayin fatarta ma ya nuna ba haka asalin haskenta ya ke ba. Tana girgiza kai ta dubi Hajiya Naja'atu da 'yarta Shafa'u da ke zaune a gefenta, ta ce. "Mummy, rayuwata tana cikin garari, ku tausaya min ku ba ni kariya, idan ba haka ba, wallahi gab na ke da tarwatsewa." Hajiya Naja'atu ta girgiza kai cikin jimami, sannan ta ce. "Yi shiru haka nan Fulani, duk wanda ya sanki a da, idan ya ganki yanzu ya san kina bukatar taimako. Amma matsalar ita ce, tun d'azun da kika iso gidan nan mun tambaye ki me ya faru kin 'ki sanar da mu, sai kira kike mu tausaya miki. Tausayi ai dama ya zama dole ga dukkan musulmi matsawar yana da karfin imani.
Shin yaushe kika baro Egypt, Kuma mene ne ya hana ki je gidanku" Wasu hawayen suka 'kara zubo mata, tana girgiza kai ta ce. "Mummy dubi yadda na koma, na rasa gata a duniya, ina zan saka kaina" Shafa'atu ta dube ta, ta ce. "Don Allah Fulani ki nutsu ki bamu amsa, don musan yadda zamu hudowa lamarin." Shiru bata amsa ba, sai da taci kukanta, sannan ta fyace majina ta ce.
BIYU. "mummy, ina ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta ke" Gaba dayansu suka fito da idanu cike da tsananin tsoro, Hajiya Naja'atu ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me ya yi zafi haka Fulani" Wa za ki kai 'kara" Kai tsaye ta amsa mata. "Daddyna zan kai 'kara"Zumbur suka mike a matu'kar razane, Shafa'atu ta ce.
Kina da hankali kuwa Fulani" Mahaifinki za ki kai 'kara a hukumar kare hakkin dan Adam"" Fulani ta mi'ke ita ma, ta ce. "Wallahi Mummy, sai na kai Daddy 'kara ga hukumar kare ha'k'kin dan Adam, ko da kuwa hakan zai yi sanadin 'karewar numfashina a duniya" Wannan karon ma idanu suka sake fitowa waje, Hajiya Naja'atu ta shiga sallallami. "Yau na shiga uku ni Naja'atu, anya kuwa Fulani kina cikin hayyacinki? Ko kin fara shaye shaye ne" Me kike so duniya ta dauke ki, mahaifinki za ki yiwa wannan tozarcin.
Haba. " Fulani ta katse ta da fad'in. "Wallahi Mummy ina cikin hayyacina, tun da nake rayuwata ban taba shan kayan maye ba. Kuma Daddy shi ya tozarta kanshi ba ni ba." Kuka ya sake kwace mata. Hajiya Naja'atu ta tsura mata idanu kawai ta kasa cewa komai, haka Shafa'atu sai girgiza kai ta ke kamar 'kadangaruwa. Cikin kukan Fulani ta ce. "Wallahi ba zan taba yafewa Daddy tozarta min rayuwar da ya yi ba, kuma sai na bi duk hanyar da zan bi na fitar mana da ha'k'kinmu a kansa.
Hajiya Naja'atu ta ce mata. "To na ji, zauna sai mu san abin yi." Ba musu Fulani ta koma ta zauna tana share hawaye. Shiru na tsayin mintuna goma sannan Hajiya Naja'atu ta ce. Fulani, bari na yi miki matashiya akan matsayin mahaifa ga 'ya'yansu. Iyaye su ne 'kashin bayan duk wani d'a da suka haifa, Allah Ya wajabta yin biyayya a gare su matsawar biyayyar ba ta sabawa addini ba.
Haka kuma babu iyayen da za su haifi d'a su so jefa shi hanyar da zai muzanta, sai dai idan iyayen ba na 'kwarai ba ne. Wannan na yarda za su iya abin da ya fi haka ma. Akwai ha'k'kok'i masu dama da suka wajabta ga 'ya'ya da iyaye, wanda a fahimtar da na yiwa rayuwarki mahaifinki bai gaza da sauke wad'annan hakkoki a gare ki ba. Koda ma ya gaza abin da kike shirin yi sam bai dace ba, domin ya halatta idan d'a ya ga mahaifansa sun yi wani abu da bai dace da addini ba ya nusar da su.
Ga dukkan alamu kuma ke ba ki yi haka ba, don me za ki bar wa shaid'an linzamin zuciyarki?" Ta tsagaita tana duban Fulani, yayin da Fulanin ta yi murmushin takaici, ta ce. "Mummy idan da akwai yiwuwar hakan ba zan ce zan kai Daddy ga hukuma ba.
Abin da Daddy ya yi min ya sa6awa addini, domin ya keta min HADDI" Jin ta ambaci haka Hajiya Naja'atu ta san lamarin ya munana, munin da bai kamata ta tauye Fulanin ba, don haka ta ja numfashi, ta ce. UKU. Jin ta ambaci haka Hajiya Naja'atu ta san lamarin ya munana, munin da bai kamata ta tauye Fulanin ba, don haka ta ja numfashi, ta ce. "Shi ke nan, akwai wata aminiyata Hajiya Rashiga Usman Gidad'o da ke aiki a hukumar kare hakkin dan Adam da ke Abuja, kin ci sa'a ta zo garin nan shekaran jiya zasu yi bikin 'kaninta, don haka ki yi hakuri yanzu dai dare ya yi, ki kwanta ki huta, inyaso gobe da safe sai mu je gurinta." Fulani ta goge hawayenta, ta ce.
Shi ke nan Mummy, na kuma gode." Misalin karfe goma na dare Fulani da Shafa'atu na kwance akan gado, Shafa'atu ta dan juyo ta dubi Fulani tare da ambatar sunanta. Fulani ta amsa ita ma ta juyo ta dube ta, Shafa'atu ta ce. "Ina kika baro Juwairiyya?" Ta ce, "Tana gurin mahaifinta."
Shafa'atu ta girgiza kai, ta ce. "Kin yi kuskure da kika baro ta, a ganina a matsayin Juwairiyya na 'karamar yarinya 'yar shekaru biyu bai kamata ki barota uwa duniya haka ba. A tunanina laifin wani ba ya shafar wani, tunda ba mahaifinta ne ya bata miki rai ba, bai dace ki barshi da Juwairiyya ba. A tunaninki wane hali za su shiga su duka biyun yayin da suka rasa ki" Fulani ta cije lebe cike da takaici, ta ce.
Wallahi ba ni sonta, Don Allah mu rufe shafin hirar nan, zuciyata na tu'ku'ki." Shafa'atu ta yi shiru ba ta kuma magana ba gudun kar ta kuma sanya Fulanin a wata damuwar. Washegari da safe sun gama 'breakfast' karin kumallo har maigidan Alhaji Nura, sannan Hajiya Naja'atu ta umarci Fulani da su shirya. Ba su bata lokaci ba suka gama komai, suka fita a motar Hajiya Naja'atun.
Tafiyar mintuna arba'in da uku ta sada su da Zawachiki Haousin Estate, sun tarar da Hajiya Rashida a gidanta ba ta tafi gurin hidimar bikin da suke ba. Kallo d'aya Fulani ta yiwa matar ta nutsu da yanayinta, ta kuma tabbatar zata iya taimaka mata.
Bayan sun gama gaisawa, Hajiya Naja'atu ta yi mata bayanin abin da yake tafe da su. Shiru na wani lokaci Hajiya Rashida ta yi tana nazari, sannan daga bisani ta dire kallonta ga Fulani, ta ce. "INA HUJJAR TA KE na kai mahaifinki ga hukuma da kike yun'kurin yi" Fulani ta yi shieu kamar ba ta ce ba, sai kuma ta ga wannan ita ce fa damar da zata yi amfani da ita ta ceto rayuwarta daga tarkon da ta ke ciki, don haka ta ce.
"INA DA HUJJA mai 'karfi da ta sa ni wannan yun'kurin." Hajiya Rashida na kallonta, ta ce. To zan so jin HUJJAR kafin na amince miki aiwatar da wannan yunkuri." Ranar wanka aka ce ba a boyen cibi, haka Fulani ta ambata a ranta, tukunna ta gyara zamanta tana duban Hajiya Rashida ta soma da cewa.
INAHUJJAR TA KE? "ba ni mantawa da ranar wata laraba, duk da a lokacin ina da karancin shekaru, domin ban haurawa shekaru sha biyu ba, amma kaifin hankali da wayon da nake da su a lokacin zan iya tunawa da duk wani al'amari da ya gudana a gareni. Misalin 'karfe goma na dare ne, mun gama daukar karatu daga Malam Sunusi Mustapha Isah wanda ya ke koya mana ilimin addini, gab na ke da soma bacci, don kanwata Murjanatu mai shekaru hudu tuni ta yi bacci.
Bazato ba tsammani UMMI ta shigo dakin da sautin kuka, ga kuma hawaye da ta ke sharewa a fuskarta. Kai tsaye ta fada saman gado yayin da na matsa kusa da ita ina fadin. "Ummi me ya faru" Ba ta iya ba ni amsa ba, illa ci gaba da kukanta da ta yi. Abin da ya sa nima na fashe da nawa kukan ke nan.
Haka Ummi ta rungume ni muna ta kuka ni da ita babu mai rarrashin wani, har tsayin lokaci sannan na yi lamo akan gado hawaye na shatato min babu sautin kuka, sai ajiyar zuciya. Ita kuwa Ummi sam ba ta tsagaita da kukanta ba, zan iya cewa wani ne ma ke korar wani. Ko da na ji an turo kyaure ban daga kai ba, domin ba 'karamin kuka na sha ba. Muryar Daddy da naji yana kiran.
"HALIMATU" Na tabbatar shi ne ya shigo. Sanin da na yi da tsare gida, wato ba ya saurarawa kowa cikin 'ya'yansa ya sa na 'ki dago kai, shesshek'ar kuka da ajiyar zuciya ma da nake yi, na yi kokarin tsayar da su. A kalla ya kira sunan Ummi ya fi sau uku ban ji ta amsa ko d'aya ba, hakan ya sa na gane kukanta yana da nasaba da shi ne.
Ji na yi ya ci gaba da cewa. "Don Allah Halimatu ki rufa min asiri, wallahi ba halina ba ne, ko nawa ne zan ba ki matsawar za ki rufe sirrina." Wannan karon na jiyo ta ce. "Kana tunanin akwai amfanin da 'kazamar dukiyarka zata yi min. Ai wallahi AHMAD ka ba ni mamaki da kunya, ban taba tunanin zan same ka da zamba cikin aminci ba. " Ya katse ta da cewa. "Na ro'ke ki da wanda ya busa mana numfashi ki yi hakuri, ki kuma rufa min asiri.
Wallahi kin ji na rantse na daina har abad. " Ita ma ta katse shi cikin raunanniyar murya, ta ce. "Ka daina hada ni da Allah, asirinka kam a rufe yake kamar yadda ka rufe shi, sai dai ka sani idan Ubangiji Ya yi nufin tona maka asiri, ni da kai da abin da ka mallaka ba mu isa rufe shi ba. Ni dai da bakina babu wanda zan iya fadawa, sai dai ka sani tsalle daya zaka yi ka fada rijiya, ma'ana muddin ba ka sauwa'ke wa aurena ba, to a sauyawar zamana da kai kadai zai iya sanya wa a asirinka ya tonu." Muryarsa a sanyaye ya ce mata. "Wannan hukuncin ya yi min tsauri Halima.
Ta katse shi tun kafin ya karasa. "Ashe kuwa ba ka fatan asirinka ya rufu" Wallahi ka ji na rantse da girman Ubangiji, muddin ba ka sake ni ba, komai zai iya faruwa." Shiru na 'yan mintoci, sannan na ji ya ce. "Na ji zan sake ki, amma sai kin yi alkawarin ba za ki fadawa kowa ba har abada." Murmushin takaici na ji ta yi, ta dora da fadin.
"Na yi alkawari, sai dai Ubangiji na kallonaka, zai kuma fidda hakkin duk wanda ka zalunta." Ya ce, "Eh na ji, tunda kin yi alkawari na gode, ki ba ni kwana hudu insha Allah zan sauwake miki.
Ta ce, "Ina jira, idan kuma ka rushe hakan ina mai yi maka albishir da kwana hudu ba zasu maimaituwa ba da izinin Ubangiji sai ka ga abin da ranka ba zai so ba." Ya ce, "Ka da ki damu." Ina jiyo takunsa har ya fice daga dakin, yayin da Ummi ta sake fashewa da wani sabon kukan. Karancin shekaruna bai hana ni fahimtar wani gagarumin laifi Daddy ya aikata wanda ba ya son fallasuwarsa, sai dai na kasa cankowa a lokacin, domin ban san hanyar da zan canko din ba.
Washegari sam ban ga walwalar Ummi ba, domin yini ta yi a daki, su Googgo Zulai dama ba shigowa suke dakin ba, saboda mummunar akidar zafin kishi da suka sanya wa ransu. Don haka babu wadda ta damu da rashin ganin Ummi na zirga-zirga a gidan, musamman da ya kasance yau kwanakin girkin Ummin ya kare, Inna Amina ta karba. Ni ma hakan ce ta faru da ni, ko da na je makaranta ma ban sami nutsuwa ba, har malamai na tambayar ko ba ni da lafiya ne. Da "Eh" na ke bin su, domin a hakika ma ba ni da wadatar lafiyar.
Matan mahaifina guda uku ne a Goggo Zulai mai yaya uku ita ce uwargida, Yaya Hisham da ke karatu a Malaysia shi ne babban danta kuma babba gaba dya a gidan, sai A-Asiya ke bi masa, sai A-Mardiya. Mahaifiyata ita ce mata ta biyu a gurin mahaifinmu, sunanta Halimatu wadda muke kira Ummi, ita ma mu uku ta haifa, Yaya Usman da Ke karatu a Florida shi ne babba a dakinmu, sai ni SAFINATU da nake binsa ana kirana da FULANI, shekaru kusan goma tsakanina da shi.
Mahaifiyarmu ta sake haihuwa abin da ta haifa baizo da rai ba. Sannnan ta sake 6arin wata biyar. Bata sake samun ciki ba, sai da na shekara takwas, sannan ta sami cikin Murjanatu.
Inna Amina ita ce mata ta uku a gurin Mahaifina Ahmad Lere, an aurota ne gab da za a haifi Murjanu, a yanzu haka tana da danta namiji guda daya mai suna Hamza, jimillar yaran gidan mun tashi bakwai. Ummi tana da hakuri, sai dai yawan tashin hankulan su Goggo Zulai ya sa ta zabure tana maida raddin wasu abubuwan da suke mata.
Ni Da Dalibata
Yah salam kawai yake maimaitawa azuciyarsa" ganin yadda Hafsat ke kuka,hannunsa yasa yadago kanta yasa yatsansa yatsare mata hawayen,tared a kok'arin rabata da jikin sa amma tasak e manne masa tana kukan shagwaba. dama tarasa wazatayi mawa ,sai gashi yazo",cikin kasalallar murya yace yi shiru kinji Hafsat d'ina kidawo nan gun,yanuna mata gefensa. Tare da cewa kinga in baba yasamemu ahaka bazaiji dadiba mutuncina zai xube agunsa.ai da sauri tabar jikin sa tadawo gefensa tana cigaba da kuka "cikin damuwa yace me kikewa kuka waye yasaminke kuka yanzun yakarbi mummunan hukunci aguna "cikin kuka tace babane.
"Da sauri ya maimata Kalmar babane"
D'aga kanta tayi tareda cewa yaya dan Allah katemakeni baba zaimun aure yarinya dani! Wani irin bugawa yaji xuciyarsa tayi hade da jin jiri da wani mugun ciwon kai,murya asarke yace aure kuma Hafsat wa baba zai auramiki?,yafada had'e da kafeta da jajayen idanunsa. Cikin kuka tace wlh bansanshiba nima please kaje ka rokesa yyi hkuri wlh banason auren da kuma Wanda zai auramun ta fada hade da sakin sabon kukan.
"Cikin wani yanayi yace ke wa kikeso"
K'uri yayi mata yana jiran tace k'ila koshi takeso, sai yaji tace bbu koma nidai kawai banson auren. Tsakin dabesan yyiba yaja ,hade da tamke fuska yace k'ila dakin gayamun Wanda kikeso to danayiwa baba magana ,sai a auramiki shi"amma innace abarki kada ayi auren ,yace waKikeso ?nace masa me. Da sauri tace amma yaya kag, da sauri yace ki koma ciki anjima zamuyi waya bance kije ko inaba kina jina, kallonsa tayi hawaye na zuba tace gidansu Fatima zanje",cikin isa yace nace bazakiba yafad'a had'e da dafa bango saboda jirin dayakeji had'e da kunar zuci dan ji yake damuwarsa ta nunku akan wadda yake ciki,saidai wani gefen na zucoyarsa na tahumarsa dalilin damuwarsa dan ance Hafsat zatayi aure.
"Kallonsa tayi ganin yyshiru,tace natafi"
Cikin damuwa sir Aliyu yace dan Allah Hafsat dina kidena kukannan haka,nima wallahi ina cikin damuwa yau ,zanyimana addu a kinji kema kiyimana. Daga masa kai tayi hade da shigewa gida ",dan intayi magana kukane zaizomata. Shikuwa sir Aliyu da sauri yafito dg gidan,kallo daya zaka masa kasan yanacikin tashin hankali da damuwa.idanunsa sunyi jajir ,jijiyoyin kansa duk sun tashi ga jiri na d'ibarsa,da sauri yabud'e mota yashiga ya aza kansa kan sitiyarin motar."
"Yaya Ahmed dake tafe a mota yahangi sir Aliyu cikin wannan yanayi atake yasan babu lafiya"
Da sauri yayi parking ya fito yana kiransa be jiba yashige motarsa" da sauri yy Ahmed yabisa.yabud'e gaban motar yashiga yasamesa kansa duk'e.da sauri Ahmed yace friend lafiya meke faruwa ne "cikin damuwa sir Aliyu yadago,saida yaya Ahmed yatsorata da yanda yaganshi." Cinkin damuwa ya sanarda shi halin da yake ciki. Ahmad yayi ajiyar zuciya yace wannan ne abin damuwa, Aini nan banga abun damuwaba,tunda kak'i kayi aure ai gara suyima.tsaki sir Aliyu yaja hade da cewa ,aibansone shiyasa ,itama Hafsat dina ,za 'amata auren dole yafada kamar zai yi kuka.
Yaya Ahmed yace banganeba, nan yabashi labarin itama Hafsat auren dole za'a mata.murmushi Ahmed yaya yace tokai meye damuwarka, Wata harara sir Aliyu ya bankawa Ahmed yace ,my Hafsat ta na cikin damuwa ya za ai hankalina yakwanta. "Girgiza kai Ahmed yaya yace wlh ko kaso ko ,kada kaso kanason Hafsat so mai tsanani Wanda ko a idonka gashina kwance had'e da tsantsar kishinta".
Wallahi kama farka in bacci kake tun kan sonta yayimaka illah ko lahani kasani ka bayyana mata.amma wannan ai kishinta kake,wallahi duk wanda yasan so,indai yyi zaman minti biyar daku zai gane kana ma Hafsat wani irin zazzafan so hade da kishinta me tsanani ,nagane hakan tun a hidimar biki na,kuma nayiwa Fatima tambayoyi ta bani amsa anan na kara tabbatar wa kaina kanasonta,inhar baka zameta ba ko mai zai iya faruwa. Nan dai Ahmed yayita masa bayani hade da ankarar dashi cewa yyi zurfi ason Hafsat dakuma tamvayarsa kanajin kaza inka ganta ko kaganta da wani, me kakeji intana cikin damuwa ko Bacin rai?nan yacigaba da cewa zakaji kaza da kaza inkiuna tare kobakwa tare ko in kun gamu ko kaganta da wani nmji.
doguwar ajiyar zuciya sir Aliyu yayi hade da cewa na yadda abokina da maganarka dan duk abubuwan daka lissafamin irinsu nakeji game da ita. Nayarda indai hakan shine so to lallai son Hafsat yamun illah ,muddin bansametaba komai zai iya faruwa dani yafad'a cikin damuwa. A hankali Ahmed yace friend kayi hkuri kaji kayi biyayya ga daddy sannan kayita adduar ai nmj mijin mace hudu (4) ne daga baya saika auri Hafsat din inrabonkace.
"Batare da sir Aliyu yyi magana ba yatada motar"
Da sauri Ahmed yace wait,nan yakira driver na gidansu yace yazo yamayar masa da motarsa gida.kallon sir Aliyu yyi yace nizan kaika gida bazan bari katafi kai dayaba komai zai iya faruwa. Babu musu sir Aliyu yafita Ahmed yazauna amazaunin driver yajasu suka dauki hanyar gidansu sir Aliyu. Bayan sunyi parking ko sallama sir Aliyu bebari sunyi ba yafito arikice yayi cikin gidan.
"Shikuwa Ahmed ya fito dg motar yyi waje,had'e da yiwa abokinsa adduar samun sassauci"
Yana shiga bbu ko sallama yanufi gun mommy dake zaune akushin kusada su sa'ada da kabeer,kamar wani yaro haka yafad'a kan cinyarta,yana Sabbatu cikin tashin hankali. Mommy kuwa naganinsa tasan dama hakan zai faru tunda daddy yace zai sanar dashi maganar aurenshi. Cikin tausayinsa tace baba na meke faruwa ne kke cikin wannan yanayi.
Arikice hade da rik'e mata hannuwa yace please mommy kitaimakeni zanrasa Hafsat dina mommy itace bugun zuciyata mommy can iya rasa raina inbansametaba,mommy baban ta zai mata auren dole zai aura mata wani ba niba. Wallahi matata ce duk Wanda yayi yunk'urin auranmun mata wallahi zanyi ajalinsa domin dan ni akayita dani ta dace hafsat pleas e mommy kada kibari arabani da matata wallahi zan iyayin komai akan hakan bazan sau, da sauri mommy ta rufe masa baki hade da cewa ya isa haka.
"Waya jamaka"
Kai kajawa kanka gudun hakan yasa na tambayi meke tsakanunku ?amma sai kacemun ai dalibarkace. Sai yanzun dakaji za'amata aure zakace kanasonta. Sukuwa su sa'ada da kabeer mamakin sir Aliyu suke dan tunda suke dashi yaune sukaji yace yanason wata mace. Shikuwa kabeer azuciyarsa yace madallah anzo gurin ai dama duk masu cika bakin basayin soyayya duk ran da takamasu hmm basuji da daddy ji dai yaya ko ina ya aje miskilancin nasa duk yake wannan haukan akan mace.
Sir Aliyu ne yatashi dafe da xuciyarsa yana kiran Hafsat !Hafsat!! Hafsat!! Yana dafe bango dan gaba daya ya haukace musu,sai surutai yake musu,basu auneba sukaga ya fad'i kasa su mamme. Da sauri mommy ta yi gunsa tana salati,sa'ada kuwa kuka ta saka "Kabeer ne yyi hanzarin dakko swan mai sanyi yadunga kwaraya masa ,cikin ikon Allah yasa ki ajiyar zuciya hade da bude idonsa.
"Sannu kawai su mommy ke masa da su sa'ada"
Ahankali yatashi zaune ya karbi sauran swan din yashanye sannan yatashi batare da yayi magana ba yayi part dinsa. Kabeer ne yayi saurin cewa momm yako maje hospital adubasa dan Allah. Wani mugun kallo sir Aliyu yajuyo ya aikowa kabeer hade da cewa kai yaushe nafara wasa dakai. Sunkuyadda kai kabeer yayi yace yi hakuri yaya. "Tsaki sir Aliyu yayi yabar gun", mommy kuwa hararan kabeer tayi hade da nufa part dinta. Tana zuwa ta bincikowa sir Aliyu magunguna harda na bacci sannan ta wuce kitchen ya had'a masa tea mai kauri ta nufi part dinsa.
"Shikuwa sir Aliyu kwance yake kan bed yyi rigingine idanunsa alumshe yana tunanin Hafsat dinsa mommy ta sh igo d'akin"
Saida tayi sallama sau uku (3) tukum ya amsa yana dan Sosa kansa."ahankali mommy ta ce tashi zaune babana. Babu musu yatashi ta bashi tea din ,bayan yasha tabasa magani ,hade' da yimai nasiha yayi biyayya ga daddynsa kuma yyita addua. Bajimaba da shan tea din bacci mai nauyi yyi gaba dashi.mommy ta kallesa cike da tasayi tabar dakin. Hafsat kuwa tun bayan Sir Aliyu yatafi takoma dakinta ta cigaba da aikinta wato kuka.
Domin itadai kowama zata aura walahi tana tsoron sex dan tanaji in mate dinsu na bada labari in sun karanta a littafi ,cewa da wahala sosai,saitaji duk ta tsorata da aure to Balle batasan wanne marar imanin zaa aura mata ba.tana kukan da tunane tunane had'e da fushi da sir Aliyu bacci yayi gaba da ita, bata farkaba sai gab da sallar la'asar bayan tayi sallah ,tajima tana adduar allah yazaba mata abinda yafi alkhairi yakuma baiyana mata mahaifiyarta.
Cikin ikon Allah saitaji damuwarta ta rage ,nan taje tayi wankanta ta wuce islamiya kasa.cewar yanzun hadda take,amma fa tayi fushi da sir Aliyu sosai. Bangaren sir Aliyu kuwa shima sai bayan laa'asar yatashi ,yayi wanka hade da sallah.
Cikin ikon Allah yaji duk wani k'unci da damuwarsa sun rage. Neman guri yayi ya zauna yafara tunani n Hafsat dinsa." mur mushi yayi daya tuna duk abinda yakeso matar dazai aura takasance dasu Hafsat tanadasu du ka.nafarko ya. Yana son wacce zai aura takasance yarinya danya sharaf,yadda zai raineta da kansa zai koya mata sonsa da kula da yaransu su zauna lfy.sannan kuma mai kunya ilimin addini da tarbiyyamai son danginsa,sai yaduba yaga Hafsat duk ta had'a wa inna abubuwan. Wata zuciyar ta ce kanada tabbas din zaka mallaketa.
Tunawa yayi kilama har yanzun batadena kukaba da sauri yazaro wayarsa yakira baba. babu bata lokaci baba yadaga had'e da sallama,Hafsat dke gefensa cikin sanyin muryarta tace baba waye yakiraka.
"Baba dake cewa lafiya lau aliyu ya gida"
Atake Hafsat ta gane cewa da sir Aliyu baba keyin waya,aisaita kwanta ta rufe ido kamar me bacci. Shikuwa sir Aliyu tun sadda Hafsat ke tambayar baba yaji muryarta,dama dan ita yakira yanaso suyi magana "can yace baba ko Hafsat na kusa mu gaisa, "Kallonta baba yayi ,yace aiko kamar tayi bacci Bari natasheta.
Da sauri sir Aliyu yace ah ah baba rabu da ita tayi baccinta.nandai sukayi sallamada baba,sir Aliyu kuwa yasan sarai Hafsat ba bacci takeba kwaidai fushi take dashi. Murmushi yayi yace oh Hafsat akwai rigima da shagwaba ,nasan haka zanta fama da rigimarta inmukayi aur, da sauri yayi shiru sakamakon tunawa da yyi Hafsat wani za'a aurama ita "cikin jin haushi hade da wani kishi da yataso masa yatashi yafita dan zuwa masjid.
Koda dare Hafsat da sir Aliyu bbu Wanda yyi baccin kirki duk da damuwa suka kwana ,kowa na tunanin dan uwansa. Washe gari haka sir Aliyu yatashi duk yad'an fad'a saidai fuskarsa tayi fiyau da shi,ko break beyiba yanufi gidansu hafsat ,dan hankalinsa yak'i kwanciya Hafsat tana fushi dashi. Yana isa yayi parking yafito kaitsaye yakutsa kai cikin gidan ,asoro yasami Hafsat tana sharewa kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.
"Ai tana ganinsa tasaki tsuntsiyar tayi cikin gidan aguje."
Murmushi sir Aliyu yyi dan yalura har yanzun fushi take dashi,dan haka shima yasaka kai cikin gidan, "Yana shiga yasami babu kowa tsakar gidan", kallon wani d'aki yyi yaga yan takalmi bakin k'ofar dakin atake jikin sa yabasa nan Hafsat ta shiga. Beyi wata watab a yashiga had'e da sallama, da sauri Hafsat ta d'ago dan batayi tunanin zai biyota ." nan ta ammasa sallamar".
Ta juya masa baya batace komaiba,aha nkali yace my Hafsat duk fushinne har haka ,bazaki tausayamunba ki barni najida abinke damuna,sai kin karamun wata damuwar, "yakikeso nayi da raina "Ahankali tace nidai yaya katafi ni bazan hakuraba, Allah kuwa. Shiru yayi yana tunani,can yace my Hafsat gidanku fa nazo,shine zakimun haka.Kallonsa ta d'ago tayi hade da murguda baki tace eh din tun, shiru tayi ganin Laure a k'ofar dakin.ckin masifa tace keko?kinanan kuna aikata masha,arku har cikin gd ko to asirinku yatonu wlh oh da rana Kiri k'iri bbu tsoron Allah ai.. Wata rikitacciyar tsawa sir Aliyu yadaka mata had'e da cewa ya isa haka wallahi kinci darajar baba da wlh yau kinyi nadamar kalamanki,amma ko yanzun zan had'a ki da k'ananun yan sanda,yafad'a tareda da Jan doguwar tsuka yabar gidan.
Hafsat kuwa shiru tayi kamar andasata agun tanajin ciwon maganganun Laure da haushin tafiyarda sir Aliyu yayi. "Laure kuwa jiki amace ta nufi d'akinta".dan ta tsorata da maganar sir Aliyu. Shikuwa sir Aliyu gida yanufa yanajin haushin kintsayawa da yayi ya rarrashi Hafsat.
"Bayan kwana biyu"
Sir Aliyu ne zaune kan bed duk yayi yar fuska ga sajen fuskarsa yyi yawa baya gyarawa kwana biyu (2) saboda hankalinsa ba kwance ba sai Karen hancinsa dayyi siriri ya k'ara fito da ramarsa,sai tunani yake can wata dubara ta fad'o mishi da sauri yakira mommy yace ta turo masa sa'ada yanzun .Babu jimawa sa'ada ta shigo dakin ,bayan ta zauna ,cikin sakin fuska sir Aliyu yace y'ar autarmu wani aiki zakimun kinji ko?
"Ahankali tace wanne aiki"
Kallonta yayi yace matso kiji babu musu. Tamatsa kusa dashi yarad'a mata wata magana Shewa sa'ada ta yi had'e da cewa to yaya bara najira kashirya danni ashirye nake. Murmushi yayi yace ammafa inaso abun yazama sirri kada ki nuna mata cewa inasonta,kin fahimta?
"D'aga kai tayi alamar eh"
Bece komai ba yashige bathroom itakuma sa'ada ta fito daga dakin. Bayan yagama shiryawa sai wani fitinannan k'amshi yakeyi ya kalli kansa a mirror, yaga duk k'simba ta cika masa fuska.
Murmushi yayi daya tuna Hafsat ta tab'a cemasa yafi mata kyau inya gyara sajensa na fuska ai da sauri ya jawo wata lokar yafito da kayan gyarawar ya gyara abinsa yaya kyau sosai,nan yasami mommy da sa'ada a waiting parlour a zaune. Kallon sa'ada yayi yace Auta muje,na musu ta mik'e hade da kallon mommy ta ce muntafi da yaya zaimun shopping. Murmushi mommy ta yi dan tasan bbu wani shopping dazasu.
"Ahankali tace kudawo lfy", sa'ada ta ce ameen hade da fita ta bisa"
Sa'ada da sir Aliyu bazu tsaya ko inaba sai gidansu Hafsat.nan sa'ada ta kalli sir Aliyu dke nuna mata gidan da hannu yace ga gidansu can yi gaba zan biyoki intsaya a soro sai kifitomun da ita. Babu musu sa'ada ta fito dg motar tayi cikin gidan,tana shiga tayi sallama Hafsat dake daki tanasaka kaya dan fitowarta kenan daga wanka,tanajin muryar sa'ada ta fito da gudu suka rungume juna ,cikin farin ciki Hafsat tace yau inada babbar bakuwa nan tajata dakinta. Bayan tasaka kaya,suka dan fara fira Hafsat nason ta tambayi sir Aliyu amma tanajin nauyi,fan kwana biyu nan dabata gansaba adaddafe tayisu.
" Sa'ada ce takatse mata tunani gun cewa pls muje gidansu Fatima naga tanada kirki"
Hafsat tace ok muje nan tasaka hijab suka fito,suna isowa asoro taji kamshin sir Aliyu da sauri ta d'ago kanta caraf suka yi shekara hudu (4) dashi. Sa'ada naganin haka ta maiza tayi tafiyarta gidansu Fatima dan dama haka suka tsara da sir Aliyu. "Kallonta yayi yace my Hafsat kin huce ne" Shiru tayi sai tura baki gaba take. Murmushi yayi yace duk Dan sabida kiyi farin cikin nakawo miki sa'ada ,kuma inji kindena fushin dani. Cikin shagwaba ta ce ai yanzun na hakura ,amma pls kayimun murmushi yaufa kusan kwana hudu (4) rabon da inga murmushinka.
"Ahankali yakalleta yace nima haka Nayi missing smile naki amma kalleni,tsurrawa juna ido sukayi kowa na mamakin ramar da d'an uwansa yayi. Sir Aliyu ne yafara mata murmushi itama tamaida masa,ahankali yace kinyi kyau bana gajiya da kallon wannan kyakkyawar furkar taki. Murmushi tasake cikin yar shagwaba a hade da yarinta tace kaima yaya kayi kyau banason in rabu dakai pls ta fad'a kamar zatayi kuka. Kallonta yayi yace dakinyi kuka zamu bata ,mudage da addua kinji ko.
"To tace."
Ahankali yace abinda nibaki tab'a cewa ma Nayi kyauba kuma wannan gyaran fuskar danayi danke nayisa. Da sauri ta kallesa azuciyarta tace kodai yana sona shima "Afili saitace Allah yaya kanamun kyau sosai ayanzun nikayiwa wannan kwalliyr taka. Kafin yace wani abu sa'ada ta shigo tace yaya muje dan Allah marece ayyi bata jira amsarsaba tayi gaba.
Kallon Hafsat yayi yace my Hafsat zamu tafi,turbune fuska tayi kamar zatayi kuka ,cikin shagwaba ta ce nibanyardaba daga zuwa sai tafiya. Cikin rarrashi yace to ai gobe zanzo muje na kaiki amiki steaming kinjik, shiru yayi gani yadda take ta dire dire da bubbuga kafa kasa ita bata yardaba. Lumshe idanunsa yayi dan in Hafsat ta yin irin wannan rigimar tata yana shiga wani yanayi. Matsawa yayi gab da ita ,murya na rawa yace gayamun me kikeso kike wannan rigimar.
Cikin kukan shagwaba ta ce nibanason katafi kabarni dan bangaji da ganinkaba. Murmushi yayi dan jin dadin kalamanta ya yadda kobata sonsa to tadamu dashi. Rarrashinta yayitayi abu ga masoya saigashi yashawo kanta,hartahakura tamasa rakkiya hade da cewa sa'ada ta gaidamata mommy. Sannan yaja motar suka bar anguwar.
Washe gari da misalin karfe 10:am sir Aliyu zaune kan carpet gaban daddy yazo gaidashi.bayan sun gaisa daddy yace kaga lokacin bikin nan yadan matso tunda saura sati uku (3) yau zanje Dubai da mommy nku muhad'a lefe daganan muje Egypt mutaho da marar lafiyar nan a maodota gidan nan akwai wani doctor da zaizo yasake bincika rta. Shine nikeso ko inmuntafi ko bayan mundawo kaje gidansu yarinyar nan kuga juna kakuma gaida mahaifinta.
Wani fad'uwar gaba sir Aliyu yaji da Bacin rai jin maganar auran nan na nandai.
Jin yayi shiru daddy yace ina sauraronka ,inmuntafi zakaje ko kuwa sai bayan mundawo daga Dubai.
contact-form
Labels: Soyaiya
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home