Monday, November 15, 2021

Wani Babban Labarine Ga Wasu Guda Biyu (Khalifa & Khalifa)



😍Khalifa & Khalifa😍


Masoyane Abin Abin Gwanin Ban sha'awa Da fari sun kasance Suna Matukar so da kaunar junan su tsawon Shekaru kusan (3) Suna Tare kwatsam watarana Sai Allah ya Jarabci khalifa saurayin Hafsat da Rashin lafiya Takai ta kawo Har Jarinsa Ya Kare na kasuwanci akan neman magani domin ko tashi baya iya yi sai an kwantar sai An tayar 'yan Uwansa wasu Har Sun Gaji Da Dawainiya Dashi Yarinyar nan Hafsat Amma Kullum Tana cigaba Da Rike Soyayyarsu ta kasa Rabuwa dashi tana iya bakin Kokarinta domin Bicike akan maganin rashin lafiyarshi kullum bata da Zance sai nashi ta Nace Dole Sai Shi 'yan Uwanta Suka fara tsangwamarta akan cewa ta fito da miji ta rabu dashi Tunda tana da manema ga 'yan uwanta Na jini Samari.πŸ’

Amma Taki Kula kowa rannan kwatsam tana bibiyar Kafofin Sada Zumunta Sai taci karo da wani Bawan Allah Yana Mika Sakon godiya Ga wadanda Sukayi dawainiya dashi Har ya samu lafiya wanda shima Irin wannan Rashin Lafiyar ta taba faruwa dashi wanda ya bayyana Cewa A Indiya ya samu Maganin Cutar da Take damunshi Hafsat Batayi Kasa A guiwa Ba ta tutubi bawan Allannan ya bayyana mata yanda Za'ayi Saurayinta Insha Allahu Zai samu lafiya Kai tsaye batayi kasa a guiwa ba Taje ta samu Mahaifinta Ta Rokeshi Akan Tunda Suna Da Hali ya taimakawa Saurayinnan Nata A kaishi Indiya Shima Ko Zai samu sauki Haka Kuwa Akayi Mahaifinta Alhaji Naseer da yake yana Matukar son Abinda Take so.πŸ’•

Sai ya Amince Aka biyawa khalifa Saurayin nata Kudi Zuwa Wani Asibiti A Indiya bayan an kaishi Indiya Cikin Ikon Allah a cikin Watanni Shida zuwa bakwai Sai Allah ya Bashi Lafiya Ashe Lokacin Da yake Jinya kafin ya Karasa Samun Lafiya A Sallameshi Soyayya Ta shiga tsakaninshi da Wata daga cikin Masu Kula dashi wata Baiwar Allah Likata Nurse ce Safeenat Wacce Asalin Iyayenta 'yan Nigeria ne Amma Mazauna Indiya Ita Haifaffiyar Indiya ce Soyayya Tayi nisa A Tsakanin Khalifa da Safeenat.πŸ’—

Sai ya bayyana Mata gaskiyar cewa Shifa bashi Da komai a yanzu Amma yana Sonta taya Za'ayi Aure ya tabbata A Tsakaninsu? Safeenat Likitannan Tace Ba komai indai wannan ne zata bashi Kudi Masu Yawa Wadanda Zai ja Jari amma A kasar indiya take so su zauna Idan har ya Amince To? Sai Ya tabbatar mata cewa ya yarda ya Amince cewa Idan An sallameshi Zai dawo yayi sallama Da iyeyenshi tare da Sanar musu, Haka kuwa Akayi bayan an sallameshi Ta bashi Kudi masu yawa dazaiyi kasuwanci.πŸ’ž

Bayan ya dawo Nigeria da yake Ba State dinsu daya da shi da Hafsat ba ita 'yar Katsina ce shi kumaKhalifa Dan Kano sai ya kasance Bata san Cewa ya dawo Nigeria bama Daga Karshe Hafsat Sai Labarin Bikinshi Taji Wallahi Abokina ne Sosai Da Sosai so tight Ni kuma Bansan Me yake faruwa ba Domin tun lokacin da yake Jinya A Nigeria Ni kuma Na samu Scholarship Na Tafi sudan karin Karatu sai Da Ina Sudan ne ma Na Samu Labarin Cewa An kaishi India kafin ya dawo daga India ni kuma Na dawo Nigeria Hutu har bayan Dawowarshi nima bansan ya dawo ba kwatsam Sai dai naga Kiran Hafsat jiki a sanyaye cikin sanyin murya kalar tausayi tana kuka Cewa Wai Ance Za'ayi Bikin Abokina amma Bazamu iya fada mata me yake faruwa ba Dan Allah da gaskene Abinnan Ko karyane wai taji cewa shi da wata 'yar India zasu yi Aure.πŸ’”

Gashi Ko ta kirashi bata samunshi ya Canza Layima Kwata kwata Nace Bansani ba Wallahi tabbas Nima bana samunshi a waya Amma Zan Bincika Mata Inji bayan Da nayi kokari na Sameshi na tambayeshi Sai ya tabbatar min Da hakane Gaskiya Banji dadi ba wallahi Saida Nayi hawaye Domin Daga shi har iyayenshi Basu kyautawa Hafsat da iyayenta ba Ko dayake ba Lallai iyayenshi sunsan Me yake faruwa ba, Da kyar Na Iya Kiran Hafsat Ina ta zullum akan maganar haka dai na dage na kirata na fada mata cewa Maganar nan Da Gaskece fa saura wata Biyu za a yi Bikinsu a yanzu haka, amma wallahi nima bansani ba kafin in gama magana sai naji shiru Wallahi Yarinyar nan Ashe a take Ta Fadi Sumammiya Sai Asibiti.πŸ’“

Bayan haka Da na sameshi na sanar dashi Halin Da Hafsat Take Ciki Karshe ma Tashi yayi ya bani guri Yace min Idan Sonta nakeyi Inje Inyi Jinyarta mana Gaskiya maganar nan Batamin dadi ba Tsawon kwana uku ina fama Dashi Sai ya daina Yaddama kwata kwata mu hadu Bayan sati guda Na Shirya Naje Katsina domin In duba Yarinyar nan Allah sarki tana Gadon Asibiti Ko magana Da Kyar take iyayi na tausaya mata A haka naci gaba da Jerangiya zuwa katsina, hanyar Katsina Ta zamo kamar Titin Unguwarmu Har Allah ya baiwa Hafsat Lafiya domin ko ba komai tare ta sanmu kuma idan Abokina yaci Amanarta Tamkar nima naci Amanarta ne iyayenta Da har Sunce Zasu Dauki mataki Amma daga baya Sukace ko dayake da Ai sunyi sunyi da ita akan ta rabu dashi amma Sai ta nuna taurin kai taki yadda wai dama mazan kano Ance ba abin yadda bane dan Haka Yanzu babu ruwansu bazasu yi mishi komai ba.πŸ’ž

Yaje shi Da Allah Kwatsam ana haka Saboda yawan Tuna Abinda Khalifa Abokina yayiwa Yarinyar nan Da tunawa akan kudin goro da yasa aka yiwa mazan kano ana kallon bamu da Amana Abin baimin dadi ba da kuma Tausaya matan da nakeyi a duk sanda na tuna ko bacci wallahi bana iyayi sai naji Na kamu da son yarinyar nan Banyi kasa a guiwa ba kuwa sai na kirata a waya Na sanar mata cewa Ina Sonta amma dai dan Allah kar tayi tunanin wani abu ta fara yin shawara tukunna Daga baya zan bayyana mata dalilaina akan Sonta ba kuma dama can ina sonta bane wallahi yanzu ne Allah ya jarabceni da sonta amma tayi tunani ai kuwa babu jima A ranar da yamma ta sanar dani in fada mata dalilina amma dai ta amince kafin ma taji dalilu sai na kwashe na fada mata dalilaina akan sonta saidai wani hanzari ba gudu ba amma Gasikya a yanzu bani da Halin Aurenta domin Karatu nakeyi amma Dai idan ta Amince Da Zarar Na Kammala Karatu saura Shekara daya sai Muyi Aure Idan Allah ya nufa Haka kuwa Akayi.πŸ’•

Iyayenta ma Suka Amince Ganin Yanda Nayita dawainiya da bata da lafiya Kusan Kullum sai naje. Ana Haka Sai Saura kwana tara (9)   bikin Abokina Da Safeenat 'yar India zata je Bikin Birthday na wasu kawayenta su biyu Dake (Mumbai) tayi Accident Akan hanyarta ta zuwa kafin aje Asibiti rai yayi halinsa ta Rasu Bayan An kammala Jana'iza da kusan Sati biyu sai Ya dawo daga India kai tsaye yazo ya Sameni cewa Shifa wallahi Yanzu yana son Budurwarsa ni kuwa ban nuna masa Cewa soyayya mukeyi ba. Sai nace masa yaje ya sameta ai ba wani Abu bane Sai yake cewa Dani amma yana Tunanin Da wuya Ta Hakura Akan abinda ya faru shifa dama wallahi Yana Sonta kawai dai Kaddarace Ta riga fata bazai Iya Dakatar da zuciyarshi akan soyayyar Marigayiya bane Sai Nace Hakane Ai ina jin ba matsala yaje ya Sameta sai yace to inzo in rakashi nace masa bazan iya ba Da can kullum ai ba dani yake zuwa gurinta ba bayan haka ta faru bawan Allahnnan yaje ya sameta Ita kuma bata ji kunyar fitowa ta bayyana masa komai ba Domin Jin kunyar mara kunya Ai Asarane Ta nuna masa Cewa ita fa Yanzu Ni take so kuma Soyayya muke haka suka rabu babu dadi.πŸ’˜

Bayan ya dawo Wai Shine Yake cewa dani wai Naci Amanarsa Kuma Munafiki Ne ni Dan Kuka haka ya karemin Zagi bance dashi komai ba karshe dai yanzu Akan Abin Ya sami iyaye na Shine Mahaifina Yake cewa dani Bai kamata wannan ya Raba tsakaninmu ba Kawai in hakura in bar masa Akwai mata da yawa a duniya Ni kuma Duk Duniya Ita nake so wallahi Ba dan wani Abu nake sonta Tausayinta yasa Na sota domin In saka mata Da Alkhairin Abinda Abokina yayi mata kuma A Zahirance Ina Sonta So Bilhakki da Gaskiya domin Allah har Cikin Raina. Wai Shin mutane me yasa Muke manta Wanda yayi mana Alkhairi kafin mu zama wani Abu amma da zarar mun zama wani Abu Mun samu rayuwar da tafi ta baya sai Mu manta da Alkhairi Allah yasa Mu gane.πŸ’—

Dan Allah Jama'a wai shin Menene Mafita kuma Wai shin dama Haka Cin Amana Yake.πŸ’—

Kayi Comment πŸ‘‡


contact-form


SO NE KO YAUDARA?


Duk wani abu da ake yi wa ’ya mace na kyautatawa wanda zai kara so da kauna da aminc ida yarda, bakin gwargwadon iya karfina ina yi mata su.

Kallon satar zuciya da bayanai masu sanyaya rai da zuciya yadda za su kwanta kamar tsumma a randa, ina yi mata su, har wayar salula nake kokarin in saya mata, amma ina dar-dar, don gudun kada in saya mata lasisin da zai dada bayar da damar yin shakwalatin bangaro da batuna, sannan kuma na dada bude mata hanyar Magana da wasu samari, dama ga shi har yanzu na kasa gane a babin da nake ciki.😁

Wai a yadda nake jin labari, idan ba na nan tana maganata, wasu kawayenta har suna kiranta da sunana amma idan mun hadu da ita babu alamun haka daga gare ta, to yaya za a yi in tabbatar da wancan labari gaskiya ne? Shi dai kare da aka ce ana yin biki a gidansu cewa ya yi mu gani a kasa.πŸ˜‡

Wani abu kuma da na lura da shi shi ne, abubuwan da masana soyayya suka alakanta su da so, ban ga tana nuna min su ba, domin sau da yawa abin da masoyinka yake so kakan so shi, amma ita ba haka take ba, ba ta iya daurewa, ko da ina son abu ita ba ta damuwa da shi, kawai abin da take so shi ne daidai kuma shi zan bi, ba ta daure zuciyarta ko alkunya ta yi, ta nuna abin da na damu da shi ita ma ta damu da shi.πŸ˜ƒ

Lokacin duk da muka hadu nakan nuna mata so na a fili amma ita ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, kuma ba ta san ana yi ba harara a duhu. Idan muna hira da ita ba na kosawa, amma ita sai kaga tana hamma, wato tana nuna min alamar barci take ji. Da ta fara hamma sai in fara hada karena, domin wannan hammar ita ce agogonta na jin barci ko kuma kammala hirarmu. Da na tambayeta abin da ya sa take yi min haka, sai ta ce β€œBa ka san kunyar ka nake ji ba.πŸ˜‚

Wannan lamari yana ba ni mamaki da kuma sa ni cikin tunani, kuma ina tambayar kaina da kaina, mene ne wannan, So ne Ko Kuma Yaudara.πŸ˜†

Kayi Comment πŸ‘‡

contact-form



Labels: ,

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home