A Wata Masarauta (Kashi 1 Zuwa Kashi 10)
Zaune take tana kuka a gaban abbanta tana basa hakuri, Abba don Allah kayi hakuri kabarni nabar jaharnan natafi can inda ba a sanniba nayi karatu, Abba kataimakamu Sai a lokacin Abba yayi kyaran murya yace gimbiya bilkisu naji, bukatarki, meye dalilinki da ba kya son yin karatu a jaharku? Gimbiya bilkisu ta sunkuyar dakai kasa, tace Abba banason ace ni diyar sarkice, kona hada wani abu da masarauta, nisantana da masarautarmu shi zaibani kwanciyar hankali da kwarin gwaiwar yin karatuna.👤
Sai a lokacin Ammi tayi magana to memartaba kadiba abunda gimbiya bilkisu tace, kabarta tabar garin takoma can inda ba a santaba tayi karatun, tunda batason asan ko ita wacece Please Abba kamata abunda takeso kasan halin gimbiya bilkisu tun tana karama ra ayinta daban yake da yayan gidan nan, gimbiya bahijja ce take magana.
Sai a lokacin memartaba sarki yayi magana yace na yarda dake bilkisu, nayarda kije garin kano kiyi karatunki idon kuma bakyason kano to kije adamawa, Ta dago kanta daga sunkuye tana murmushi nanuna jindadinta, Abba garin kano zantafi domin a canne naji ance akwaisu da karama bako, Yace bamatsala Allah yayimki albarka ya tsareki a duk inda kike.💦
Gaba daya pallow ya amsa da amin kowa yana murmushin jindadi bayan kowa yamike zaitafi dakinsa sai sukaji , memartaba yace zakije tareda jakadiya domin ta kula da lafiyarki, Sai tabata fuska idanunta suka fara hawaye, Abba don kar asan koni wacece zanbar gombe zuwa kano karatu, kuma Abba sainaje da jakadiya Anty bahijja ce ta lakucemata hannu alamar ta yadda da abunda Abba yace, tace to Abba na yarda amma da sharadi ajawa jakadiya kunne idon mukatafi kada ta yarda tadinga sunkuyamun a gaban mutane, domin itace zata zama a matsayin ammi ta Sarki ne yayi murmushi tare da ammi sukace munji daina kukan, saitayi murmushi kowa yana murmushi sukatafi makwancinsu Memartaba yabada umurni a kiramasa jakadiya, waziri yatafi a guje yanakiran jakadiya, Jakadiya kuma kodataji kiran waziri gabanta yashiga faduwa domin idon taji waziri nayimata irin wannan kiran to tabbas tasan sakone daga wurin sarki, gabantane yashiga faduwa saicewa takeyi a zuciyarta to ita metayi? Dazaisanya memartaba ya aiko a kirata.💔
Waziri tagani yanafadamata sakon sarki, tashitayi tabi bayan waziri zuwa fadar memartaba sarki mai adalci, tanashiga fada jakadiya takai gaisuwa ga sarki fadawa saicewa suke sarki ya amsamki jakadiya amintanciya ga sarki, Sannan sarki yayi kyaran murya yafadamata dalilin dayasanya aka kirawota yanason takulamasa da gimbiya bilkisu domin za a turata karatu kano, kuma tare zasu tafi nan dai yafadata yanda sukayi da gimbiya bilkisu, jakadiya ta sunkuyar da kai kasa tace angama ranka ya Dade Allah yajadaran sarki mai adalci duk abunda kace haka za ayi ranka ya Dade, tatashi tafita Akabarshi da ammi suna tantauna maganar tafiyar gimbiya bilkisu Gimbiya bilkisu yace ga abdulrahaman, suna zaune a garin yola a wata masarauta mai adalci, sarki abdulrahaman yagaji sarautane a wurin mahaifinsa, masarautace wadda basu yarda da zulunciba, suna daraja talakawansu dabasu hakkinsu shiyasa yankin yola suke alfahari dashi fadawansa sukejidashi suna kuma ganin girmansa saboda yana adalci a tsakaninsu.💫
Sarki abdulrahaman yanada mata hudu, ta farkon sunanta sarauniya hadiza wadda takasance diyar sarkin zamfara ce, Allah ya albarkacesu da yaya uku danta na farko sunansa abdulrahaman wadda yaci sunan sarki, sai ta biyu gimbiya bahijja sai kuma ta uku itace gimbiya bilkisu, tun daga bilkisu sarauniya hadiza wato ammi bata kuma samun haihuwaba Sai hajiya zainab ita kuma yayanta duka matane, subiyar ta Haifa Sai halima ita kuma yayanta hudu duka mata.
Sai Aisha yayanta biyu mace da namiji Yayan sarki abdulrahaman goma sha hudune, mata sha biyu, maza biyu Shiyasa suka dauki tsanar duniyar nan suka dora a kan ammi saboda a ganinsukeyi da sarki yayi murabus to abdulrahaman zai mikawa sarautar domin shene babban dansa namiji, Acikin yayan sarki mata kuwa su goma sha biyyayan ammi sunfita daban da sauran, musaman gimbiya bilkusu, wadda gaba daya rayuwarta daya da sarki shiyasa yafisonta acikinsu domin gimbiya bilkisu akwai tausayin talakawa Motocine jere suna jiran fituwar gimbiya bilkisu domin rankiyarta makaranta, tafito tareda Abba da ammi da kuma bahijjah suna gaba sai ita da prince Adull suna daga baya suna magana, a can ta hango motoci sunyi layi duk ita suke jira, tana kawowa gafda motocin taja tatsaya tareda kallon maimartaba? Tace Abba tafiya zakayine? Naga duk anjeramaka motoci, Sai yayi murmushi yace duk yan rakiyarki ne gimbiya bilkisu, Nantake tabata fuska gaskiya ni Abba bazasu biniba, Abba inason inyi rayuwa irin yadda kowa keyi a makaranta Batare da ansan koni wacece ba, Abba don Allah kayi hakuri idon nabatamaka, Abba kace sutafiyarsu kawai banason rakiyar.💥
Sai a lokcin prince abdull yayi mgna, Abba kabani key din motar natafi na kaita da kaina, idon ka amince Ammi tace abdull tafiyarka batareda batakan tsaroba a kwai matsala, ammi ta hasala wai ita dolene sai anyimata yanda takeso. Bahijja tace ba haka za ayiba bilkisu kishiga kutafi idon akakusa kaiwa sai yaya abdull ya karbi key hannunsu sai yakarasa dake mkrantar shi kuma saisu jirasa, ko hakan meyimkiba.
Sai a lokacin tayi Murmushi ta rungume bahijja, shiyasa nakesonki Anty bahijja,kowa yayi dariya, sukashiga mota sai makaranta, garin kano tadabo dandin Hausa koda me kazo anfika Momy ce a bangaren prince adnan tana kokarin shiga dakin barcinsa, fadawa suka hanata shiga, yarima yabada umurni kar a bar kowa ya shigarmasa daki domin yanada bukatar hutu, Ummi ce tazo wucewa ta wurin, saitaji fadawa na gardama, saitadawo domin taji meke faruwa? Aikuwa taga Ashe momy ce fadawa suka hanata shiga dakin yarima Ummi ke tambayarta meyakawota sashen yarima adaidai wanan lokacin ? tunda tasan halin yarima sarai.💩
Momy na zubarda hawaye tanafadawa, ummi, wurin prince nazo shine yabada umurni kar a bar kowa yashigar masa daki, sabda yana bukatar hutu. Ummi tadafa kafadar momy tace tafiyarki barni nashiga dakin naga abunda yake tsinanawa da har zaisanya a hana mutane shiga, tana kaiwa wanan tawuce, basuyi yinkurin hanataba domin sunsan mahaifiyar sace. Kwance yake a kan makeken gadonsa, barci yakeyi cikin kwanciyar hankali, dakagansa kasan yaji dadin barcinsa, ummi CE tsaye a kansa tana kallonsa ta ynda yake barcinsa cikin kwaciyar hankali, ya manta lokcin makaranta ya kusa,bayan dazun yagama fadamata cewa yau sunada test a class dinsu Ummi takai dubanta a kan makeken agogon bangon dake like a dakin nasa, taga karfe 3:30pm bayan yafadamata cewa karfe 4:pm zasufara test din, nan tashiga tashinsa dakyar tasamu ya mafalka, da masifa bude idanunsa kenan saiyaga ummi a kansa yayi murmushin dole, Ummi yaushe kika shigo? Ya za ayi kasan shigowata kabude Baki da Hanci kana barci, Kaduba lokci kagani yanzun karfe nawa? Ba test naji kace ke garekuba? Yana diba lokaci yatashi da sauri yafada too let yayi wanka, koda yafito ummi ta tafiyarta tabashi wuri yashirya. Yana fitowa a gurguje ya shirya yasanya kananun kaya, sunyimasa kyau, ya dauki key din motarsa yafito domin tafiya makaranta, duk inda ya wurga bayi sai kaimasa gaisuwa sukeyi ko kallonsu bayayi, suma basudamu da hakanba domin idon da sabo sunsaba da halinsa. prince adnan kenan, Birnin kano garine mai yalwar mutane, acikin garin a kwai wata masarauta wadda sarki Bashir yake tsaye tsayendaka domin yaga ya amsarwa talakawansa hakkinsu.🙌
Sarki Bashir yanada mata biyu Matarsa ta farko hajia nafeesa haihuwarta daya namiji saidai bezo da raiba, tundaga lokcin ko batan wata bata kuma yiba, Mahaifiyar sarki ta matsamasa akan yakara aure, haka ya amince, ya aure diyar kaunarta maryam, ansha shagulgular biki amarya maryam Tatare a gdan sarauta, bikinsu da wata biyu tasamu ciki, sarki yayi murna da samun cikin maryam, ko ba komai zaisamu magajin sarautarsa, Baking ciki awurin hajiya mafeesa kuwa ba a magana, domin duk duniyar nan babu wadda ta tsana samada maryam da kuma Addah, domin cewa takeyi duk munafurcin Addah ne, datasanya sarki yayi aure.
Haihuwar maryam ta farko ta haifi danta namiji, Wanda yaci sunan fahad, yaro mai kama da mahaifinsa, kamarsu data da sarki, sarki ya dauki son duniyar nan yadorashi a kan fahad Fahad Nada shekara hudu, ta kuma samun wani cikin tahaifi adnan, sarki yayi murna da haihuwar adnan domin anyi shagulgular biki irin na gdan sarauta. Fahad da adnan suntaso cikin kulawa da gata domin sarki bayason abunda ya tabasu, Adnan shine karami, amma bayajin magana ga miskilanci da qasaita, da izzah, Takai takawo fahad shine babba amma kamar shine karami.💞
Yanada shekara shidda ta haifi yarta mace, taci sunan fareedah, tundaga lokacin bata kuma haihuwaba fareeda itace autar sarki Bashir, Motocine suka tsaitsaya nesa da makarantar, prince abdull da gimbiya bilkisu tareda jakadiya suka karasa makarantar, wurin shugaban mkrantar suka wuce dama yasan da zuwan nasu, maimartaba yayiwa shugaban makarantar bayin zuwan nasu. Domin maimartaba yaturawa shugaban makratar kudi yanemawa gimbiya bilkisu madaidaicin gida inda data zauna tare da jakadiya.
Prince abdull tareda bilkisu da shugaban makarantar suka fito daga office, zairakasu gdanda akasayawa bilkisu domin ta zauna tayi karatunta. Isarsu gidan kenan Prince abdull ya kalli gadan ya kuma kallon bilkisu yace mata, ke yanzun kinfison zama a irin wanan rayawar? Murmushi tayi tace yaya abdull a halin yanzun addu'arka nake nema Allah yabani abunda nafito nema, baice mata komaiba daga kafadarsa yayi alamar taji zata iyane yayimata sallama tare da fatan alkhairi yatafiyarsa, yabarta tare da jakadiya.
Prince adnan ne tareda yarima fahad yayansa, cikin mota direba na tukasu, tsaki kawai adnan keyi, yanayi biyu yana dibon agogon gwal dake sanye a hannunsa, yajuya ya kalle fahad dayake kallon kwalta, ynajinsa yana tsaki amma yakyalesa, Sai a adnan ne yajuyo da fuskarsa yana kallon fahad yace yaya nakusan latti fa, sai lokacin fahad ya kallesa yayi magana. Yace Kaine adnan bakajin magana, ai INA ganin kasanda zakuyi test din amma kashige daki kadinga barcika harda wani sanya fadawa sutsareka don kar a tasheka, Allah danice ummi bazan tashekaba kyaleka zanyi tunda bakada son karatu, banada ummi tatasheka dakayi loozing din test din gabadaya, niyan,un taimako daya zan iyayimaka shine dama direba ajiyeni zaiyi, nan gaba kadan, nashiga motata nakarasa inda zantafi, to amma kafini uzuri, idon mukazo kashiga motar tawa saika karasa makarantar yanda zakayi sauri. Murmushi yayi yace nagade big brother don hakan nakesonka, dariya fahad yayi, ddai nan direba yayi farking yafito, yashiga motar yayan nasa yajatada karfi sai mkranta.💗
Motocine na tsaitsaya a nesa da makarantar, prince abdull ne tareda gimbiya bilkisu da kuma jakadiya, suka fito, suka nufi mkrantar, kai tsaye offishin shugaban makaranta suka nufa, kasancewar prince abdull yasan offishin basu sha wahalar tmbyaba, kaitsaye sukayi sallama sukashiga, dama yasan da zuwan nasu, maimartaba yakirashi a waya yayimasa bayanin komai, ya kuma turamasa da kudi domin a sayawa gimbiya bilkisu gidanda zata zauna tare da jakadiya.
Nan suka kareyin komai, suka dunguma gaba dayansu, suka tafi gidanda gimbiya bilkisu zata zauna tareda jakadiya. Gidane karami nazaman mace daya madaidace, prince abdull yajuya ya kalli gimbiya bilkisu, sai ya merebaki, yace, yanzu kinfi bukatar zama a irin wnn raywar? Kina ganin gatane kikayiwa kanki dazaki zauna a irin wannan gidan, Kibaro masarautarku dagatanki da komai kidawo inda ba a sankiba, ba a san koke wacece ba kice anan zakiyi rayawa. Gimbiya bilkisu ta sunkuyar da kanta kasa, tace yaya katayani da addu'a Allah yabani abunda nafito nema, domin yanzun addu'arku nake nema.💅
Ya kada kafada, a lamar ita tasani, yayi mata sallama yatafiyarsa. A nan take jakadiya tanufota, tafadi kasa alamar girmamawa, tana fadin, Allah yajadaran gimbiya mekike bukata, a girka maki? Saita bata fuska, banaso, a matsayin ammi ta nadaukeki banason wasu sugane wani abu a taredamu, Jakadiya ta kuma runsunawa tana fadin ayi hakuri idon nabata ran gimbiya, Kinga irinta ko, ni kidaina cemun gimbiya, kikirani a bilkisu na, Jakadiya tace gaskiya ranki ya dade bazan iya kiran sunankiba, domin idon nayi hakan sainaga kamar nazubar da darajar masarauta, amma daga yanzun zandinga kiranki da diyata, Sai lokacin gimbiya tayi murmushi, tace bakomai na fahimceki jakadiya,ko hakan kika kiranidashi yayi. Nan tawuce daki domin tayi wanka, dakin ba laifin angyarashi kuma yayi kyau dai gwargwado, tafada toilet tayi wanka, koda tafito jakadiya hartakare masu abinci, nan tafaraci suna fira, tana kammalawa, ta haye gadonta takwanta, tareda tunanin gobe zatafara daukar darasi Gimbiya bilkisu ce cikin shirinta na zuwa makaranta, tasanya atamfarta pink and yellow, da hijabinta shima kalar pink tayi kyau, dama gata farar mace kuma kyankyawa.💋
Tafito ta iske jakadiya takaremasu abinci ta zauna taci, Saida ta koshi sannan tace jakadiya saina dawo, Jakadiya ta ajeye abunda takeyi tanufota tanafadin, Allah ya tsareki gimbiya takawarki lafiya yar sarki jikanyar sarki gaba sararauta gefinki mulki, Allah yadawo dake lafiy gimbiya. Bilkisu tayi dariya tace jakadiya bazaki dainaba kenan. Tafiya takeyi kamar batason taka kasa, waya ta takeyi da antynta bahijja tana fadamata yanada sukayi missing dinta a family nasu, bataji horn din motaba saidai jitayi anbugeta da ita har saida tafadi kasa, Saijitayi anja motar da karfi kowaye yayi tafiyarsa, saibiyar motar tayi da ido tana mamakin shi kuma wanan waye da zaibugeta da mota kuma yayi tafiyarsa, Safeena ce tazo wucewa ta wurin taga abunda ke faruwa, ta sauri ta karaso wurin takamata, ta Taiyida ita tsaye, tana kakkabe mata jikinta, sannu kinji, ina fatan bakiji ciyoba? Taiyi murmushi banji ciyoba yar'uwa nagode Safeena zata wuce kenan sai kuma tasawo tana tambayarta, don Allah yar'uwa meye sunanki? Bilkisu tayi murmushi tana kallonta, sunana bilkisu abdulrahaman yola.
Safeena tace in kuma sunana safeena Ahmad Kano, dafatan zamu zama qawaye. Bilkisu tayi murmushi tace, ba matsala Allah yabarmu tare. Sukajera suka nufi makarantar, tareda ita da safeena Prince adnan ne a guje yashigo makarantar da motarsa yana sauri don kar yayi lorzing din test dinsa, besan da chabo gurinba kawai yabita cikinsa, Dayake lokacin damunane makarantar duk tayi chabo, tafiya sukeyi suna fira, saiji sukayi anwatsamasu chabo gaba daya jikinsu yalalace, musamman gimbiya bilkisu, da gaba daya kayan jikinta suka lalace, da chabon, Abokanin sa suna ganin haka, suka fashe da dariya, shi kuma duk beji ddin hakan da yaimataba, Yabude gabun motarsa yafito, tafiya yakeyi cikin qasaita da nuna isa, ya nufota domin yabata hakuri, saida yakawo daf da ita, daga kanta dazatayi sukayi ido biyu dashi, ranta a bace tadaga hannu ta wanke masa fuska damari, jikakeyi Tess,? Nan take wurin yayi tsit student kowa kallo yakeyi, domin sunsan halin yan group dinsu basajin mgna musamman prince adnan dakowa ke tsoronsa a makarantar, shiyasa suka sanyawa group din nasu mazaje group, Prince adnan dafe da kunci sai kallon bilkisu yakeyi, wadda taketa zuba masifa rai bace Kai wane irin dabbane wawa Wanda baya kallon gabansa, ba lantana bayansa, tun a baking get kakade ni a mota, kasanya kai kayi tafiyarka, duk hakan shekaba,sai daka biyoni har cikin makaranta, kai waye mekake takama dashine? Safeena ta Matso kusa da ita tarufe mata Baki, tayi shuru, domin safeena tasan halin mazaje group ba sauki ke garesuba hattada malamai shankansu suke.💜
Prince sai kallonta yakeyi yana tunanin wane irin hukunci zaiyimata, a rayuwarsa babu wadda yataba marinsa sai ita, ko ita din a gaban bainar jama'a ta maresa, harda zaginsa takeyi. Ya kuma matsowa kusa gareta yanamata kallon sama da kasa, yana fadin kicigaba dazagina mana meyasa kikayi shuru, yana fadin haka yana kara matsowa kusa gareta, Idon naci gaba mezakayi? Abunda zanyi kike tambaya ko? Budar bakinta zatayi magana saijitayi ya rungumeta yakai bakinsa cikin nata yana tsotsa student sai kuwa sukeyi suna fadin sai mazaje, tsawon minti 30 suka dauka a haka, sai kokarin kwace kanta takeyi amma yariketa tamau sai kiss yakeyimata, saida yagadama yasaketa, yadinga toshe hanci yana zubarda yawu, bakinta wari yakeyi, gaba daya student kowa ya dau kuwa yana tabi sai fadin sukeyi sai mazaje. Komawa yayi yashiga motarsa yabata wuta, yayi tafiyarsa, test dinda beyiba kenan.
A nan yabarta duke tana kuka, safeena ce tarike hannuta tamikar da ita tsaye tana sharemata hawayen fuskarta, taja hannunta suka karasa cikin hostel dayake safeena a hostel take zaune, shigarsu hostel keda wuya tazubamata ruwa ta wanke jikinta, ta kuma bata wasu kaya ta canza, tasamu gefin katika tazauna, idanunta suka cika da hawaye tana tuna irin cinmutunci da akayimata a gaban bainar jama'a.💝
Safeena ce ta matso kusa gareta tadafata, tace, bilkisu waini ko meye ya hadaki da wadan nan yan iskan? Duk makarantar nan sun ishikowa, basubar malamaiba bare dalibai, kowa ya shankarsu yakeyi saboda sunada daurin gindi a makarantar don haka suke taka kowa ynda sukaga dama. Wannan wadda kukayi fada dashi, yarima prince adnan kenan, dan sarkin garin nan ne, shiyasa komai yayi ba'a korarsa a makarantar sabda yanada daurin gindi. Shekaransa ta hudu kenan a makarantar nan duk yayi exams carry over yakesamu, kuma bawai don bayada ilimin ba a ah baya dai maida hankali a kan karatunsa, don haka kiyi hakuri da abunda yafaru dake, kuma kiyi taka tsan tsan da abunda kikasan zai kuma hadaki dashi, don ba mutunci ke garesaba.
Bilkisu dake zubarda hawaye tadago da kanta daga sunkuye ta kalli safeena tace nagode safeena, kuma in Allah ya yarda zankiyaye, Safeena tayi murmushi tarike hannuta suka fita, suka nufi class domin daukar karatu, Bilkisu CE tayi kwalliya cikin wani Jan matiriyal, tayi kyau sosai, saitakira safeena tafito suhadu a bakin titi, zasutafi super market siyanyar kayan kwaliya, tafiya sukayi bamai nisaba takaisu wurin, atare suka shiga wurin kowa yana zabar abunda yake bukata, sai sukaji sanarwa duk wadda yake cikin super market din yafito waje yarima adnan zaiyi siyayya, nan take kowa yashiga hada kayansa domin yafita yabashi wuri yashigo, amma banda bilkisu daci gaba da daukar kayan datake bukata.💨
Shinfidar capet akayimasa a inda zai taka kafarsa, mai dauke da tambarin sunan prince adnan, takawa yakeyi cikin qasaita da isa, fadawa sai kirari sukeyimasa suntakemasa baya. Adai dai lkcin bilkisu takare siyayyar kayanta zata fito, nantake sukaci karo da juna, sai kallon kallon sukeyiwa junansu, shiyana kallon Dan karamin bakinta, ita kuma tanayimasa kallon sama da kasa Taja dogon tsaki zatawuce, saiji tayi madawa nakiran karya kikeyi yar matsiyata duka kinemi gafara a wurin yarima, shi kuma wani murmushi yakeyi najin dadi yanajiran ta durkusa tabashi hakuri Ta kuma matsawa kusa garesa saiji yayi tawatsa masa miyau (yawu) a fuska Bakayi martabar da zan baka hakuriba, taja hannun safeena sukafito, fadawa sukayi yunkurin tareta, ya tsayar dasu, siyayyar da baiyiba kenan Yajuya yashiga mota direba yajashi sai GDA A fusace yakoma gida, duk inda ransa yake yabaci, fadawa sai kwasar gaisuwa sukeyi amma baya kulasu, Dakinsa yafada kai tsaye, a kan makeken gadonsa ya kwanta sai faman ajiyar zuciya yakeyi, zumut yamike tsaye kamar wadda wani abu tsunkulesa, sai safa da marwa yakeyi, yana tunanin irin abunda bilkisu tayi masa, a rayuwarsa babu wani wadda yatabayimasa irin wulakancin da bilkisu tayimasa, tabbas zan dauki mataki a kanki zan nunamaki cewa kin tabo jinin sarauta, domin sarauta bawasa bace, Tafe take cikin farin ciki da annashawa, sai murna takeyi domin rayuwarta tayimata dadi, domin tarama wulakancin da prince yayi mata sai bawa safeena labari takeyi tana dariya.💘
Saiji tayi anjanye mata mayafi a bayanta wai gawatayi a fusace, sai ganin fadawa tayi kowanensu da katuwar bulalarsu a hannunsu, suna kallonta yarima yace azomasa dake yar matsiyata. Kallo tabisu dashi cikin mamaki, batada alamar motsawa daga inda take, ganin batada alamar tafiya suka suma yunkurin daukarta. Wata irin tsawa takatsamasu wadda kowane daga cikinsu saida yashiga hankalinsa, domin suma sun fahimci wani abu atareda ita, Kallonsu takeyi sama da kasa, duk wanda ya kuskura yataba mun jiki to wallahi kusani duk sai kungane kurenku, ta kuma dallamasu harara Duk abun nan dayake faruwa a kan idon yarima, shima mamaki tabashi, ta yanda take iya katsawa fadawa tsawa, shidai a iya saninsa duk wadda yayi ido biyu da fadawa sai hankalinsa yatashi musamman idon ba'a gidan sarauta yakeba, shiyasa yaturomata su domin sutafi da ita, mamaki yakeyi to ita wacece? A fusace yafito motar yaja hannunta da karfi tana kokarin kwacewa amma takasa, ya bude murfin motar ya turata ciki yamayar yarufe yazagaya mazaunin direba yashiga yaja motar da kafi yabar makarantar da ita.
Tafiya sukeyi mainisa, babu wadda ya kula dan uwansa, prince sai huci yakeyi kamar wani zaki, tuki yakeyi kamar zaitashi sama Ganin bayada niyar tsayawa, gudu yakeyi sosai, duk tsoro ya lunlube bilkisu, juyawa tayi ta kallesa idanunta cike da hawaye, Cikin yanayin kuka take magana, malam wai ina zaka kaini ne? Menatare maka a rayuwa kakeson kaga kamusgunawa rayuwata? Mekake takama dashine? To wallahi kasani duk abunda yasameni kaima baza a barkaba, Kuma saikayi dakasani a rayuwarka, idon sarauta kake takama da ita, sarautar wata masarautar tafi sarautar ku, ina mai tabbatar maka da kajuya da akalar motarka kamayardani a inda kadaukeni, Duk masifar da takeyi be kulataba be kuma fasa gudun dayakeyiba, idanunsa sunkade suyi jajer, duk maganganun da takeyi jiyakeyi kamar tana watsamasa ruwan zafi a jiki, musamman da takecewa Sarautar wata masarautar tafi sarautarsu.💚
Metasani a sarauta, datake fadamasa haka, tabbas zan nunamata kalar tamu sarautar, domin ta tabbatarda babu wata sarautar da tafi tamu masarautar mulki. Wani dogon burki yaja a dai dai wani katafaren gida, megadi yafito yabude masa get, yashigar da motarsa a guje yanufi farking space, yaja wani dogon burki wadda saida bilkisu tarufe idonta saboda tsoro, tashiga zubar da hawaye, tana maiyi masa Allah yasa a zuciyarta, Fadawan dake gadin gdan saida shiguwarsa a guje tabasu tsoro, kasancewa kuma basusan dazuwansaba, domin idon zaizo yakan kirasu a waya yashedamasu da zuwan nasa domin a share masa gdan ka kankabemasa kura.
Suna sa makin zuwansa domin ba a dai dai wanan lokacin yake zuwa gidan shakatawar nasa ba Ganin tsayuwarsa lafiy yasa suka runtumo a guje sunka sunkuya alamar girmamawa suna gaidasa tareda yimasa kirari, Allah yataimaki yarima, Allah tsare gabanka ya kuma tsare bayanka, Dan sarki jikan sarki, sarauta gabanka da bayanka, Kaine zaka kaji mahaifinka, yarima mejiran gado, Allah ya taimakeka bamusan da zuwankaba, zagayemasa mota sukayi sunatayimasa kirari shikuwa, saiji yakeyi da qasaita da mulki, kasa fitowa yayi saida ya dauki minti 30 sannan yabude murfin motar ya fito, Duk abun nan da akeyi bilkisu kallonsa takeyi, tana mamaki a zuciyarta ta yanda yakeji da mulki da isa Da kuma miskilanci.💃
Koda yafito fadawa nabiye dashi, zagayawa yayi dai dai wurin zamanta, yabudemata murfin motar, beyi mata maganaba ita kuma batayimasa, bata kuma fito a motarba, Ya dauki minti 10 a haka, sannan ya maida kallonsa gareta, yace idon bazaki fitoba zansanya fadawa su daukomun ke akai, sushigomun dake, Yana kaiwa nan yajuya yayi tafiyarsa, ganin yasoma tafiya yasanyata fitowa domin yana iya sanyawa a dauketa din tunda ba imani ke garesaba, Tafiya yakeyi tana biye dashi.
Domin ita koda za'a kasheta batasan a inda takeba, Wata kofa yanufa,tana biyedashi shiganta kofarke dawuya taganta cikin wani katafaren pallow na alfarma pallow yayi kyau sosai amma duk da kyau pallow bazai rudetaba domin tasaba ganin fiye da irin wanan Tsaye tayi abakin kofar taki Shiga ciki, Shima tsaye yayi yana kallonta, beyi mata maganaba, saifama yakeyi da mulki, sunshafe kusan minti 30 a hakan, sannan daga karshe yabude baki yayi magana, idon bazaki shigoba zansanya a fadawa su daukomun ke, Domin yanzun kinshigo fadata, zannuna maki sarauta da mulki ba abun wasabane, zan mulkeki yanda rai keso, domin na fahimci a gda ba'a koyamaki yanda zaki daraja masautaba, basu kuma koyamaki yanda zakibawa yayan sarauta girma ba, Domin zan a zabtar dake yanda kikasan ake azabtarda tsintantun bayi, zaki zama baiwata, kuma kiyimun aiki irin na bauta, har sai kin fahimci cewa kintaba yayan gidan sarauta, Murmushi tayimasa tareda karasa shiga daga cikin pallon, karasawa tayi kusa garesa tana maiyin murmushin a fuskarta zagayesa tashigayi tanayimasa kallon sama da kasa, sai daga karshe tabudemaki tayi magana, Adnan kake kowaye? Baka isa nayimaka bautaba, kuma bakayi martabar da zan zamemaka baiwa ba, Dame kake takane? Kalmarka dayace kace mulki, to kai ba yarima bane face bawa, ba kuma bawan kowabane face bawana ni bilkisu ta nuna kanta Ko kamanta lokacinda kabudemun murfin mota nafito, to kasanya a ranka tun daga lokacin kasoma yimun aikin bauta, Writing by Ummu safwan.😛
Magana takeyi amma idanun yarima sunkade sunyi jajir, gaba daya kansa ya daumasa zafi, Tsawa ya daka mata, wadda ita kanta saida ta firgita, amma bata nunamasa hakan ba, Karya kikeyi wallahi ke wacece? Da har zaki kirani bawanki? Lallai yau saina sanya a ladabtar dake, sai Sanya anhoraki horo mai tsanani, horonda saikinyi dakinsani dabaki zo duniyaba, Kallon sa tadingayi sama da kasa, kaima Dame kake takama bayan sarauta, har sarauta kakeyi? Ina Mai tabbatar maka da idon kaga mulkin wata masarauta to zakasan kai yarima adnan ba sarauta kakeyiva, sonkai kakeyi da nuna isa.
Ta kuma yin murmushi tana kallonsa, inason kafadamun a wace masarauta akace bafade ko bawa ya dau mace? A tunanina idon kana takama da mulki ko sarauta bata haka yadace ka bulloba, Kataba ganin anyi Prince kazami, dubeka wallahi a wata marautar ko waziri baza'a bakaba bare a baka prince mai jiran gado, don hakan nace ba sarauta kakeyiba illah hauka don haka nace kaje wata masarautar koda za'a nunamaka yanda ake gudanar da mulki da sarauta, Taku takeyi dai2 a cikin pallon, sauda tazo gabdashi tashiga zagayashi tana kallonsa sama da kasa Kallonta kawai yakeyi yana tunanin irin hukuncin da zaimata Sai dai yaji ta kyalkyale da dariya, daga bayansa, juyawarda zaiyi sai yaga tana nunashi da hannu tana dariya Nan yashiga kallon kansa sama da kasa, yana tunanin meye a jikunsa wadda take kallo yake bata dariya.👏
Gashi tafadamasa maganganu masu zafi, wadanda yake tunaninsu, wace kazanta yakeyi wadda har zata kallesa tace masa qazami? Duk jiyojin kansa sun firfito sbda bacin rai, Besan lokacinda ya doka mata tsawa, had saida takusan faduwa zaune saboda tsoron da tajiya, da kuma yanayin da taga ya chanza, Yanunata da yatsa, kiyimin shuru, Ke wacece? Me kike takama dashi? Waye ubanki a garin nan? Da har zakizo masarauta ta, fadata, kina fadamun maganganu, Kallonsa takeyi cike da tsoro amma ta dake a zuciyarta, domin batason yagane tafarajin tsoronsa, domin yaji ddin yimata wulakanci, Ido tabisa dashi tana hararansa, Ubana ba wanibane, kuma be zama dole kasan koshi wayeba, Kuma babu abunda nake takama dashi face darajata da martabata ta ya mace.
Kuma ni mutum ce mai rai da numfashi kamar kowa, kuma kamarka kodayake gani kakeyi a tunaninka kamar kafi kowa, Da kuma kace na iskoka fadarka, masautarka, a tunanina a gaban bainar jama'a kasatoni, kuma wallah saikayi danasanin abunda kayi domin ni bana barin ayi zalunci bareni bilkisu a zalunta, Mekike iyayi? Mezakiyimun? Ke harkinada matsayinda harzakice zaki iya ramuwar abunda nayimaki? Nan yayi murmushin mugunta, ya jefar da wayarsa a kan kujera, ya zauna yana kallonta A gogon dake makale a hannunta na gwal, tadiba 12:pm ta maida kallonta garesa, shima ita yake kallo domin yaga agogon dake saye a hannunta, saida ya firgita da ganinsa, domin yasan tabbas a kwai wani abu datake boyewa a kanta, Saiji yayi tana mgna, prince ne sunanka ko yarima ne ko adnan.
Lokacin cin abincina yayi, ina bukatar a maidani gda, domin nasan bakada abunda kake iya ciyardani, zumur yamike tsaye yashiga kwalawa fadawa kira A guje fadawa suka fito, kowane daga cikinsu, kansa a sunkuye alamar girmamawa, Allah ya taimaki yarima gamu, kallo yabisu dashi ya kuma mayarda kallonsa zuwa gareta Yana murmushin mugunta, yacewa fadawan suyi tafiyarsu, Yace daya daga cikin abunda zan azabtar dake dashi kenan yunwa, zan horaki, horo mafitsanani, domin sai kinyi danasanin taba yayan sarauta, Kisani babu wani abu dazaki nema kirasa a gdan, babu bawanki dakika ajiye dazaki sanya aiki da harkika iya bude baki kinafadin lokacin cin abinci yayi Mekikasani najin dadin rayuwa? Da harzaki iya bude baki kifadi hakan.👾
Tokisani abinci bazaki cishiba har sai lkcinda naga dama Murmushi tayi tana kallonsa, tadaga masa hannu ya isah, yarima, kasani bakowane irin kazamin abinci nakeciba, musamman wadda yafito ta hannunka, Nafadamaka lokcin cin abincinane yayi ina bukatar a maidani gda, Kallonta kawai yakeyi, bayada niyar motsawa daga Inda yake, Ganin hakan yasa itama tanemi wuri a kan kujera ta zauna,tashiga dan ne Dan nen, wayarta dake hannunta, Can dai yaga zaman baya masa, tashi yayi, yafada dakin barcinsa a kan makeken gadonsa yayi kwancensa yana waya, da abokaninsa yan group dinsu mazaje garap yanadariya, Bayan yakare wayar,da abokanensa, sai yayi kwance rubuda ciki, yana murmushi koba komai yasan yau ya rama abunda bilkisu tayimasa, koda yunwar da yabarta yasan tahoru, Tsayin minti 30 yana kwance, ko meyatuna? oho zumut yamike daga kwaciyar, yanufo pallon inda bilkisu take zaune rayuwarta a bace, domin yanzun 12:30pm lokacin tashinsu daga makaranta yayi, Jakadiya zatayi sauraren dawowarta makarata Ta kallesa sama da kasa daniyar tayi magana, amma kuma tafasa, Kallonta yakeyi yana murmushin mugunta, nufota yayi yana kallonta, malam kitashi mutafi.
Kallonsa tayi da niyar tayimasa magana, amma kuma tafasa, takara dibun agogon hannunta taga 1:00pm hankalita yatashi domin tasan jakadiya zata shiga damuwa, narashin dawuwarta, Batayi masa maganaba bata kuma kallesaba, domin zaran tabudi bki tayi mgna kukane zai biyo baya.💬
Mikewa tayi, tabi bayansa suka nufi mota, A bakin mota taja tayi tsaya, shikuwa har yazauna a maxaunin direba, yana jiran tashigo sutafi, taja tayi tsaye, ta dauki tsawon munti10 a hakaa, ganin batada niyar shigowa tanason batamasa lokaci, yabude murfin motar da karfi yafito, Don Allah malama idon bazaki tafiba kijaye kibawani hanya na wuce, tunda ke bakitashi tafiyaba, ni inada abunyi, Kyalesa tayi kuma bata matsa daga inda takeba Kallonta yaci gaba dayi, yace kodayake gdan ne bakyason fita, saboda kinga gda mai kyau, kuma kinsha esee ko.
To saikinbar gdan nan koda ranki bayaso. Fisgar hannunta yayi da karfi yabude murfin motar ya jefata ciki Ya mayar da murfin yarufe Ya zagaya yashiga mazauninsa ya tada motar yajata da karfi suka fita gdan. Tafiya sukeyi bata kulashiba harsuka kusan zuwa makaranta, gabda zai shiga makaranta sanan tabude baki tace ajiyeni nan Da karfi tayi mgnar yaja wani burki da karfi ya tsaya domin saida tabashi tsoro Mude murfin mutar tayi tafita, sanan ta sunkuya tayimasa magana, Nagode da bin umurnina da kayi na ajiyeni a nan, amma kasani bana barin bashi, Mukama da kai wani likacin Yanayin marecene mai hade lumshi da iska mai dadi.💨
Bilkisu ce tareda da safeenat, tafiya sukeyi cikin farin da annashawa, fira sukeyi suna dariya alamar yanayin garin yayimasu dadi, Sautin dariya sukadinga ji a gefensu yanatashi, waigawarda bilkisu zatayi, saitaga majalisace ta mazaje group zanzaune, suna kallonsu suna dariya, ido biyu tayi da prince sai yakuma barkewa da dariya tareda mukarabansa suna nunata da yatsa, Batabi takansuba, domin tasan abunda tashirya masa, saidai taja hannun sakeenat subar gurin da saurinsu, Yau ranar alhamis CE takasance ga daliban makarantar suke halarta a wani resturent dake makarantar domin shakatawa musamman idon marece yayi Bilkisu ce tareda safeena suka nufo wurin shakatawar, kowace taja kujera ta zauna, bilkisu tabada umurni da akawo masu abun motsa baki, Koda aka kawomasu, sunfara sha kenan, sai bilkisu ta kalli safeenat tace don Allah sister danjirani naje can nadawo, bata kawo komai a rantaba, tace OK sister amma karki dade, tace karkidamu yanzun zandawo.
Wata hanya tabi wadda zata sadata da wurinda aka ajiye wasu fararen kujeru guda 4 kallon kujerin tashigayi daya bayan daya, idonta yakai a dayar da akasanyawa tambarin Prince adnan, saitayi murmushi cikin farin cikin, takarasa kusa da kujeran, saida tafaqaici idon mutane yanda ba mai kallonta, snn taciro wani abu a jakarta mai kamar allura tasonsoka a kan kujeran, idon ba lura kayiba bazaka gane ansoka wani abun a kaiba tana karewa tayi saurin barin wurin, ta koma wurin zamanta, Labari sukeyi da safeenat amma hankalinta naga prince domin tana dibon shiguwarsa A can ta hango prince yashigo yana wani kasaita da mulki da miskilanci, fadawa abunkaninsa suntake masa baya, shikuwa harwani kankabe jiki yakeyi da hankicif, yana wani yauki da jinkai, bai tsaya a ko inaba sai a wurin zamansa, domin yasan a nan kawai yake zama, Saida abokaninsa suka zauna snn shima ya zauna zaunawarsa keda wuya, mezayaji saiji yayi wani abu ya tsikaresa a duwawu, wata irin wahalanliyar kara yasaki, harsai da hankalin mutanen wurin gaba daya yadawo kansa, Nan take kallo yadawo kansa, kowa mamaki yakeyi meyasami prince yake kuwa haka Nan take maza da mata kowa yayo kansa ganin yakasa tashi, daga zaunen, dayake, amma banda bilkisu, kuma ta hana sakeenat zuwa, Kowa tambayarsa yakeyi prince lafiy.👤
Meke faruwa? amma yakasayin mgna, sai zufa ke tsantsafosa ta ko ina idanunsa sunkade sunyi jajir alamar rayuwarsa tabaci Ganin bayada niyar magana kuma yakasa tashi, sai abokaninsa suka dau wayarsa, suka kiramasa fadawansa dake can waje sunayimasa tsaron motarsa, Ganin kiran yarima fadawa suka nufo wurin a guje, suna Allah ya taimakeka Allah yakaremaka lafyarka yarima gamu, be kallesuba sai yayi masu nuni da sudagashi, basu gane abunda yake nufiba, saida abunkaninsa suka fadamasu abunda ke faruwa, Batare da bata lokaciba suka kankaresa yanda babu mai ganinsa Daya daga cikin fadawan ya kamasa ya mikar dashi tsaye, saiji sukayi ya kuma sakin kara wadda bemasan yayitaba, fadawa saicewa sukeyi Allah yataimakeka hakuri zakayi.
Bilkisu dakecan gefi tana dariya, domin duk abunda yakeyi a kan idonta, dariya takeyi tana nunawa safeenat, Safeenat itama abun dariya yabata, tace sis ba dai dasa hanunki a cikin abunda yafaru da prince ba? Dariya ta kuma yi banada lakacin yimaki bayani yanzun bari sai munhadu a gda, Mikewa sukayi gaba dayansu.
Zasu tafi, bilkisu taja hannun safeena sis muleka wurin can muga abundant ke going a wajen prince Safeenat binta tayi tana murmushi Haka suka isa wajen, a dai dai lokacin fadawa narike dashi zasu wucewa dashi, tafiya yakeyi kamar Wanda akayiwa kaciya, Bilkisu mexatayi inba dariyaba, Shan gabansa tayi tana dariya Tace hi....yarima kowa kallo yabita dashi, shikuma yaja ya tsaya kasa tafiyar, Taku takeyi cikeda kasaita, gabansa tazo ta tsaya, ta kallesa sama da kasa, can kuma ta kuma tuntsirewa da dariya, saida tagama dariyarta mai isarta, harda dafe ciki Shikuwa ya kulu don ya fahimci babu wadda yasherya masa wannan abun sai ita, jiyayi kamar ya shaketa ta mutu yakeji Saida tagama dariya mai isarta, sannan ta kallesa tace yarima kake Ko prince? Yau ina sarautarka take be? Ina mulkinka? Sannan ina qasaitarka? Ashe kai ba namiji bane? Hakan kakeson zama sarki.
Waima na tambayeka a wace masarautar akace irinka yana iya mulkin mutane? A wace masarautar akace mutuminda ba jarumiba yana zama sarki? Shi sarki a duk inda yashiga sai a angane yashiga wajen, saboda kwarjininsa da iya takunsa na sarauta, Amma kaifa? meka iya bayan girman kai, da miskilanci dason girma, Kataba ganin inda sarki talakawansa kejin tsorunsa.,? Taja wani dugun tsaki, jikake kacap, zata wuce kenan , taji fadawa na fadin, karya kike yar matsiyata babu Wanda yadace yazama sarki sai yarima adnan, don haka zubarda yawun bakinki.
Tamaida kallonta ga fadawa, tayi masu kallon sama da kasa, Idon babba na magana ya kamata kudinga bashi respect, bai dace ina mgna da shuganku kusanya mun baki, Yakama kuje kukuyi yanada ake daraja babba, Kodayake bnga laifinkuba, shugaban naku besan yanda ake mulki ko saurataba bare Ku yan kuransa, Yunkurawa sukayi da niyar ladabtar da ita prince ne ya daga masu hannu, da karfi yace Ku kyaleta Kamasa sukayi, suka sanyashi a mota, suka nufi gida dashi, A bakin get direba yayi horn, maigadi ya budemasu get, suka shigar da motar sannu a hankali saboda kar yarima yaji ciyo, parking space suka nufa suka'ajiye motar, fadawa suka nufosa, suka kankamasa sai sannu suketa yimasa.😇
Nuni yayi da hannu, alamar susakesa. sakinsa sukayi, sai sannu sukeyimasa. " tafiya yakeyi kamar wadda akayiwa kaciya, domin shi kadai yasan abunda yakeji a jikinsa. Dakyar yasamu ya shiga gida. Baby takan kowaba, kai tsaye sakinsa ya nufa, yafada a kan makeken gadonsa, ya kwanta rumda ciki, Sai a lokacin yakejin wasu hawayen wahala nafitomasa, Tunani yakeyi, irin hukuncin da zaiyimata, tabbas zan hukuntaki, hukunci mai tsanani, zan ladab"tardake, wadda ko makiyinki sai ya tausayamki, zanunamki cewa babu wadda ya isa yataba, "yayan sarauta ya kuma zauna lafiy, Shikadai yake surutunsa, kamar wani zautance, Bilkisu kuwa yana barin wurin, taja hannun safeenat suna dariya, tana fadamata yanda abun yafaru, sai dariya sukeyi, "Mutane kowa fadin albarkacin bakinsu sukeyi, wa "dansu na jinjina mata, wa "dansuwa na ginta, Mafiyawan masu zagin nata duka matane, wa "danda suka mutu a kan son sa.
Yau gidan cike yake da yan"uwa da abokanin arziki, Domin uwar"gida sarautar mata, wato hajiya nafeesa, ciki kegareta, wata bakwai, amma babu wadda yasani, Domin tana ganin kamar rashin haihuwarta yanada nasaba, ga hajia maryam mahaifiyar adnan. Gashi tadau burin duniya ta daurashi a cikin, lokacinda ta fahimci tana da cikin,sai ta tsiri tafiya garinsu, bata dawoba saida cikin yakai wata bakwai, don haka ko sarki, bata fadama tanada cikiba, sai yau dayakai wata bakwai, Sarki yayi murna sosai, don haka ya gayyato "yan'uwa da abokanen ar'ziki, domin atayashi murna.💛
Ba sarki ba, har maman su adnan tayi murna da samun cikinta, Amma duk da hakan. hajia nafeesa, cewa takeyi, duk munafurci ne, ba"kin ciki takeyi, da cikin. Ita dai batabi takantaba bare tabiye mata. Shine fa, taga shiguwar, Prince cikin fushi, yana tafiya kamar wadda kwai yafashema a ciki, Ai kuwa babu abunda tashiga fadi, sai dan "bakin ciki, mai irin rayuwar uwarsa, yaji labarin inada ciki, shine ya shigo rai "bace, To komai ba"kin cikinka, sai na haifi muslimu a gidan nan, domin shima ya hau karagar mulki, Masifa taketayi ita daya, kamar wata zaranriya, Shi dai prince yana dakinsa, duk abun duniya ya damesa, saboda bakin ciki ko kayan jikinsa be cireba, Sai maganar zuci yakeyi, Kamar ni prince d'an d'an sarki a'ce, wata "yar matsiyata take yiwa abunda taga dama.
Zunbur ya mike tsaye, kamar wadda wani abu ya tsikara, sai safa marwa yakeyi, Yana tunanin, ita wace ce? Dame take ta'kama? Waye ubanta a garin nan? Dolene nayi bin cike a kanta, domin na tabbatar da ko ita wace ce, Koma yayi ya kwanta, rumda ciki, idanunsa sun rikede sunyi jajir , sai tunani yakeyi, ta ina Zaifara bincin. Sannan idon yagano asalinta wane hukunci zaiyi mata? Wadda saitayi dana sanin, saninsa, a' rayuwa Tunda daga lokacin, Bilkisu basu kuma haduwa, da prince Adnan ba. "Itama hakan yayi mata dad'i, domin tasamu kwanciyar hankalin ga karatunta, Amma duk da hakan, kwana biyu da bata sanyashi a ido ba tajita duk ba dad'e, sai tunani takeyi, "ko lfy ya daina zuwa makaranta.🍳
Wata zuciyar kuma nafada mata, kudai abunda taimasa ne, yasanya shi rashin lafiy, harya daina zuwa makaranta, "zaune take ita d'aya tana tunanin prince. gani take kamar abunda taimasa bata kyauta masa ba. Kwance tashi bawuya a wurin Allah. Bilkisu harsun kammala jarabawarsu lafiy, kuma suna saran, ayimasu hutu, ranar friday, amma har yanzun bata sanya Prince a i'donta ba, Yau juma'a takasance ranar hutu, Bilkusu da jakadiya suna har had'e kayansu domin tafiya gida, suna kammala had'a kayansu kenan sai Safeenat ta shigo domin suyi bankwana da Bilkisu, Bankwana sukeyi amma kowan censu kuka takeyi, basa sun rabuwa da junansu, "Jakadiya tsaye tayi tana kallonsu, domin kuwa itama sai da suka bata tausayi,kukan da sukeyi na rabuwa da juna, sannan tayi karfin halin yimasu mgna "Kuyi hakuri safeena, ai hutun ba mutuwa bane, kamar gobe ne zakuga kundawo.
Haka suka 'kare kuke kukensu nazasuyi missing din junansu. Jakadiya ce taja a kwatin kayansu suka nufi tasha, domin shiga motar da zata kaisu yola. Tareda Safeena suka nufo tashar, saida taga tashin motarsu, suna dagawa junansu hanntu, sannan tajuya tanufi gida, ido cike da hawaye, tana mai kewar Bilkisu, Motarsu na dagawa, takira maimartaba ta sheda masa da cewa gasu nan, sun taso yanzun. "Maimartaba murna ya shigayi, yatura a kiramasa Ammi mahaifiyar Bilkisu, Shiguwar Ammi keda wuya, yashiga fadamata gimbiya Bilkisu tayomasa waya motarsu ta taso, gata nan isuwa, don haka a shirya mata, duk wani abu da akasan tana bukata, kuma a sanya masu kula da dakinta, su kakkab'e mata kura, a gyaramata shi, Ammi murmushi tayi, "Tace angama ranka ya dad'e yadda kace haka za'ayi.💎
Murmushi yayi ya kalli matar tasa cikin so da kauna, yace don hka nkesonki Ammin yara, domin kinabin umurnina koda kuwa hakan beyimki dadi ba Itama murmushi tayi. tace dole ne nabi umurninka mijina,domin samun farin cikin ka, koda kowa hkan shi zaisanya rugujewar nawa farin cikin, Maimartaba kallonta yakeyi cikin so da kauna , sai jawota yayi a jikinsa, yana sunsunar duk ilahirin jukinta da sha humra mai Kamshi, yasanya bakinsa a nata yashiga tsotsar lamb'anta, yana shafata tako ina a jikinta, bakinsa cikin nata, yake cewa wai meyasa Ammin yara bakya tsofa? kullum sai yarinya nake ganin kina k'ara komawa. " Janye jikinta tayi a hakanli daga nasa, tana kallonsa da murmushi a fuskarta, tace ai kaine baka tsufa, ranka ya dad'e, kullum yaro kake komawa.
ko da yaushe dawata salon sabuwar soyayya kake zomun mai rikitani, wai meye sirin? Ranka ya dad'e? Kara jawota yyi a jikinsa yana fadin tafo nafadamki sirrin. kokarin zarcewa,naga sunayi a guje ni Ummu Safwan nabarmasu d'akin don karnaga abunda yafi karfin idona, maimartaba da Ammi ba'a tsufa.
Gimbiya Bilkisu sun sauka lafiya, saukarsu kenan, takira maimartaba tasheda masa da sunsauka, Ai kuwa nan take yakira direba yabada umurni da aje da sauri a d'aukota a tasha, Motocine tare da fadawa suka tafo daukarta, ganinta tsaye cikin tasha, saida tabawa fadawan mamaki, lallai samun irin gimbiya Bilkisu sai antona A nan take suka nufota suna kwasar gaisuwa, "Ita kuwa hannu ta daga masu, alamar sutashi batason hakan. Mota tanufa suka bude mata kofa tashiga tareda jakadiya, suka nufa gida.
Da i'sarsu gida, fadawa sai kwasar gaisuwa sukeyi, wasunsu kuwa sai bangajiya sukeyi mata, wasu nayimata kirari. "Allah yatsare mana ke kinbiya, ya tsare gabanki ya kuma tsare bayanki, barka da zuwa sarauniyar mata Gimbiya Bilkisu mai gadon zinari. Shigarta pallon kenan ta hango, Ammi da Bahijja da kuma prince abdull, sai kallonta sukeyi cikin murna da farin cikin dawowarta, kallo tabi kowa dashi tana murmushi, kowa sai tunani yake a wurinsa zata fara zuwa. Ita kuwa tayi tsaye, taki karasa shiga cikin pallon, bata fuska tayi tana kallon kowa, "Suma ita suke kallo suga a wajen waye zata fara zuwa. A can ta hango maimartaba na sakkuwa. ai kuwa a guje tanufesa tana dariya da murna tanufesa, ta rungomesa. Shima sai dariya yakeyi cike da murnar ganinta. Kowa sai mamaki yakeyi, musamman Prince Abdull dayasan tafi shakuwa dashi a kan kowa a gdan.📢
Kowa kallon mamaki yabita dashi, musamman prince Abdull, da ya sheryamata kwarya kwaryar walimar dawowarta. A nan me martaba yabada umurni da akawowa Gimbiya Bilkisu, Abubuwan motsa baki, a nan take a kacikawa gimbiya gabanta da abubuwan ciye ciye. Gaba dayansu sarki yabada umurnin duk su sauko a'ci abinci gaba d'aya. Kowa ya sauko, a ka zunzuba abincin, kowa ya faraci, amma banda gimbiya Bilkisu, Maimartaba ya maida kallonsa gareta. "Yace gimbiya meke faruwa ne? Ko abincin ne bakyaso? Yanzun nasanya akawomki wadda kike bukata. "Turo Baki tayi, tana shagwaba, ni Abba lokacin cin abincina baiyi ba, tadiba agogon dake daure a hannunta na gwal, a shagwab'e tace Abba dibafa kagani yanzun 6:30 kuma Abba kasan sai 7:00 nakecin abinci. Maimartaba yayi murmushin jin dadi, " yace tabbas gimbiya hakane. na manta,Allah yayimaki Albarka. tayi dariya tace amin Abba. Ta maida kallonta ga Bahijja "tace Anty Bahijja dake da yaya Abdull naga kunyimun k'iba dayawa, gaba dayansu suka sanya dariya.
Sannan tamike tace "Ammi bara nayi wanka kafun nashirya lokcin cin abincin nawa yayi. Gaba dayansu, Kallo suka bita dashi, suna mamakin tafiyarta makaranta be canza mata rayuwa ba. Kai tsaye d'akinta tanufa, mamaki tashiga yi, ganin ancanza mata komai na dakin, murna tashigayi a Zuciyarta tana godewa maimartaba domin tasan shine yasanya ai'mata komai, domin yafison a koda yaushe yasanyata farin ciki. K'arewarta wanka keda wuya, yayi dai dai da lokacin cin abincin nata, a gurguje ta shirya cikin wani matirial, pink and blue. Yaimata kyau sosai.
Sankowa takeyi sannu a hankali kan bene, domin ta halarci wurin cin abinci, ta taran da Bahijja, da kuma maimartaba zaifita fada, Kallonsu tayi gaba dayansu tayi murmushin jin dadi da farin ciki, yau gata a gida, a gaban iyayenta da kuma 'yan uwanta. Maimarta ne yayi gyaran murya yace "gimbiya Bilkisu anfito? Murmushi tayi, ta sunkuyar da kanta k'asa, tace Allah yakara maka lafiy, nafito domin naci abinci, na huta, Ganin fitowarta yasanya maimarta komawa ya zauna, yafasa fita fada. Sai kallon gimbiya yakeyi yana murmushi, domin duk a cikin 'ya 'yansa Allah yafi d'ora masa son gimbiya Bilkisu, ga biyayya, ga kuma kyauta, bata kyamatar talakawanta.👭
Bahijja tayi kyaran murya, tace "yauwa Bilkisu, jiya a masarautar kano sun aikowa da Abba sa'ko, akan cewa matar sarki Bashir, tanada ciki har natsawon wata bakwai. Bilkisu batace komaiba, face ya mutsa fuska da tayi. tace "mamansu fadila? Ko kuwa wannan jarabanbar matar tashi? Gimbiya Bahijja ta kalleta tayi murmushi, tace "ba mamnsu Fadila ba. d'ayar. "Kice jarabanbar kenan. Ita dai gimbiya Bahijja komai batace ba, domin idon da sabo, tasaba jin irin wad'an magan ganu, a bakin gimbiya Bilkisu. domin tuntana k'arama, idon sukatafi da ita can, kusan kullum saitasha doka a wurin Hajia Nafeesat, tana dukanta tana zaginta, tana cema mai bak'in hali irin na mahaifiyarta.
Shine mafarin tsanarda tayiwa Hajiya nafeesat. dalilin da yasa batason zuwa gidan kenan. Don ita harga Allah ta manta dasu. Koda taje kano karatu gaba d'aya ta manta da sunada wata alak'a a tsanin masarautarsu. Gimbiya Bahijja tace "har Abba nafad'in muje tare dake, kinga Idon hutu ya kare, kinfuta da zuwa da jakadiya sai dai kawai ki zauna can gidan. Tunkafin tarufe baki tace. Allah ya kiyaye ni. Tana fadin hakan, kamar tayi kuka, a nan kowa yasanya dariya harda maimarta, yace karkiyi kuka gimbiya babu wadda zai tilasta maki abunda bakiso, Karkiyi kuka share hawayenki.
Murnushi tayi tace "nagode Abba nah Dariya tabawa kowa, daga nan kowan nensu yatashi yanufi d'akin barcinsa. Kwance tashi asaran mai rai. Gimbiya Bilkisu har ta kammala hutun ta. Shiri takeyi domin komawarta makaranta. Maimartaba ne ya aiko kiranta. Ajiye kayan sake han nunta tayi, tanufi wurin maimartaba, domin jin kiran dayake mata. Gurfane take gabansa ta sunkuyar da kanta, kasa "Allah yataima keka, Allah yak'ara maka lafiy gani, naji ance kana nemana.
Maimartaba yayi kyaran murya, yace "Gimbiya Bilkisu nakiraki ne domin na shaida maki cewa, tareda Antynki Bahijja zaku tafi. domin zataje tadiba lafiyar Hajia Nafeesat, sbda kinsa zumuntar dake tsakanin mu da sarki Bashir. Ta d'ago kanta cikin biyayyah ta kalli maimartaba "Abba ba wai zank'ibin umurninka bane a'a ba hakan nake nufiba. sai dai Abba kasan a motar haya zan koma, kuma ita Anty Bahijja bata shiga motar haya Abba, Banason mutafi tare da ita a motar gida. yin hakan shi zaisanya agane koni wacece,kuma banason abunda zaisanya a gane ko ni wacece Abba kadiba mgnata. Ta kuma durk'usawa, "tuba nakeyi Abba idon nab'ata maka rayuwa kayi hkri.
Kallonta yakeyi, yana murmushi jina jinjinawa hali irin na Bilkisu, Yace "karki damu 'yata. Nasan bakifad'i hakanba domin kin batamin rayuwaba. Tashi kitafi Allah yayimki Albarka. Tace " Amin Abba. Ta koma taci gaba da shirinta domin komawa makaranta Sarki Bashir mahaifinsu Adnan, da Ammi mahaifiyarsu Bilkisu uwa d'aya Uba d'aya ne," Kada ku manta da Ammi mahaifiyarsu bilkisu 'yar sarki ce," da masarautar kano. da masarautar yola. suna da kyan kyawar fahimta." da sarki Abdulraham, da Sarki Bashir abokanen junane." don haka sarki Bashir yabawa sarki Abdulraham Auren k'auwarsa Ammi," Kunji alak'ar zuwan Bahijja garin kano," Amma Bilkisu da Adnan babu wadda yasan juna a tsakaninsu. sabda tuntana k'arama tadaina zuwa gidansu saboda jininsu be had'u da hajia Nafeesa ba.
Motocine birjik harabar gidan, za'ayiwa gimbiy Bahijja rakiya, kwaliya tayi kalar ta gidan sarauta." tasanya alkimba, sai tafiya takeyi cikin k'asaita da mulki," Fadawa kuwa sai zuba mata kirari sukeyi," Ammi ce a gefenta, tarakota,sai jamata kunne takeyi, tace "Bahijja kikula da kanki, kiyi taka tsantsan da mutanen gidan, domin kinsan zaman da sukeyi da hajiya nafeesa, kiguje abunda zai kai ya komo a gidan," sannan kizama maiyiwa kowa biyayya, musamman hajiya nafeesa dazaki tafi wurinta," Bahijja tayi murmushi, tace "Ammi kada kidamu insha Allah babu abunda zaifaru. kinsan tsuhuwa mai ran karfe Adda tana nan bata mutuba. don haka bazan..........?
contact-form
Labels: Hausa Novel