TUN INA KARAMA
Page 28
Mamaki ne ya hana yusuf magana sbd yanda yaga tashin hankali a fuskar hawwa karara, juyawa tayi ta barshi wurin yana tsaye haka ya ganta ta shige part dinta ta rufe. Murmushi yayi cikin ransa yace hawwa a hankali zaki fahimceni zakuma ki san ke kadaice araina, azahiri kuma girgiza kai kawai yayi ya shige part din shi shima batare da ya kara binta ba.
Hawwa na shiga daki fashewa tayi da kuka tana cewa meyasa nayi sabo da soyayyarsa dama abunda umma ke gani kenan taso rabamu? gaskiya bazan iya ganin wannan rashin hankalin ba ace wai mace ta so hallaka ka amma kana cewa zakaje ka dawo da ita alhali ita ko bin ta kanka batayi ba anya akwai adalci cikin wannan rayuwa kuma kace wai kada afada ma kowa, to me kake nufi ne.
Haka tai tayin tunaninta wanda babu amsa cikinsa hardai ta tashi tayi wanka tayi sallah. Bata iya cin komi shiyasa ta dan sha tea kawai ta kwanta shima sakamakon tana da ulcer kada ta samu matsala yasa ta sha.
A bangaren yusuf kuma shima hakan take saida ya gama komi zai kwanta ya tuna da umar cewa yayi bazasu je gidan su jamila ba yadai kirata awaya yace ta dawo, haka ya dauki waya bayan ya gama komi ya kira jamila, zaune take tana chatting awaya kiran shi ya shigo wayarta cikin tsoro da fargaba take kallon kiran har ya katse. Tsaki yayi ya kara kira har ta kusa katsewa ta daga cikin karfin hali,"hello tace kafin ta kara magana yace"come back our home right now! kafin ta sake magana taji dif ya kashe wayarsa, cikin mamaki da jin dadi tayi ihu wanda har saida mummy tayo dakin da gudu tana fadin "lafiya jamila.
Mummy yusuf ne ya kirani wai in dawo gidan yanzu ta fada tare da rungume mummy cikin jin dadi mummy tace "amma fa ya shammace mu amma ba komi tunda dama mun gama komi kawai ki maza ki shirya ki tafi kinsan ance da zafizafi akan bugi karfe " gaskiya ne mummy bari kawai in tashi to yi sauri kinga 8:30 tayi kije can ki kara shiryawa kinde ji bayanin danayi maki ko? yes! mummy naji amma kinsan nayi mamakin da abunda nayi masa kuma banji ya fada mani komi ba harda wannan dan kazagin nashi banji komi ba.
Ke wai an gaya maki mu na wasa ne har yanzu ke yarinya ce ai an riga angama komi ke dai tashi dama inata tunanin munyi waya da daddy dinki yace gobe zai dawo dama kada ya dawo ya sameki kuma ya fara fada amma naji dadi tunda anyi haka kuma koda kinje ki kwantar da hankalinki ki bashi hakuri kinga dai alamar yana sonki ko?"gaskiya ne mummy bari ki gani"tasahi tayi ta shiga cikin bathroom ita kuma mummy ta fita don ta fiddo mata komi cikin sauri ta gama komi ta fito ta shiga part din mummy haka suka fito mummy tayi mata rakiya har gaban motarta tare da fada mata yanda ya kamata tayi komi haka ta tashi motarta mai gadi naganin haka yace"ga matsiyaciyar nan bari in bude kafin tayi mani rashin mutunci haka ya wangale mata get. Ita kuma dari da tamanin ta fita gidan batare da tunanin komi ba.
Tunda ya kirata bai sake sukuni ba haka ya zauna zaman jiranta, cikin awa daya ta iso gidan shima mai gadin gidan naga ninta ranshi ya baci haka ya bude mata get din ta shiga cikin izza da rashin hankali parking lot ta isa tayi parking ganin duk motocin gidan na nan yasa tayi ajiyar zuciya tace"shegiya neman wurin zama har an dauko mota hmm zanyi maganinki. Bude kofar motar tayi ta dauko abunda tazo dashi ta fito ta kulle motar bakin kofar ta isa bell din kofa ta taba sau biyu.
Tasowa yayi ya bude mata dama tunda yaji zuwanta yana bude mata yaja ya tsaya, ita kuma kakarin shiga takeyi tana tafiya tana cewa yagida ya jikinka"binta yayi da kallon mamaki cikin takaici yace"normal direct part dinta ta wuce batare da ta saurare shi ba.
Shima rufe gidan yayi ya wuce part din shi tare da tunanin hali irin na jamila wato bata ma iya gaishe shi sai wani izza take nunawa lallai jamila kinyi kuskure yanzu za'a fara game din murmushi yayi tare da shafa kanshi ya kara yin balance a kujerar da yake zaune, tabbas kinyi abubuwan daza su sanya in rabu dake amma da sauran lokaci.
Ita ko hawwa bata ma ji dawowar jamila ba ta riga har tayi bacci, jamila ko na shiga sashenta ta ajiye magungunanta tayi amfani da wanda zatayi ta boye sauran, tayi imani dama ba zuwa zaiyi ba tashi tayi ta kulle part dinta ta nufi nashi. Dai dai falo suka hadu da hawwa ta taso zataje part din shi itama saboda ulcer ta ta tashi kuma maganinta yana part dinsa ka cibus sukayi dai dai kofar shi kalan kallo suka tsaya yi da mamkin juna itadai hawwa bata san ta dawo ba ita kuma jamila tana ganin mai hawwa zatayi dakin sa bayan yasan tana gidan.....?
Page 29
Tsaki jamila tayi, ta shige itama hawwa tabe baki tayi tabi bayanta, knocking tayi "yace mata " yes come in budewa tayi ta shiga cikin sakin fuska ba kamar dazun ba.
Sallama hawwa tayi da mamaki ya amsa mata sallama shiga tayi"am kuyi hakuri na shigo maku ba lokacin daya dace ba tana magana tana nufar inda ta ajiye maganin ta juya zata fita, tashi yayi zai bita don yasan tunda har ta fito neman maganinta awannan lokaci yasan ulcer dinta ce ta tashi.
Lokacin da ya fito har ta kusa shigewa part dinta kiran sunanta yayi "hawwa juyowa tayi tana kallon kara sowarsa yana zuwa hannun ta ya kama suka wuce tare.
Jamila kuwa sakin baki tayi tana kallon su yanda har ya bita baima kula da ita ba ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa zanyi maganinku indai nice badai kin iya kilbibi ba, too zan kamaki yarinya ko tare aka haifeku sai kin bar mani yusuf.
Koda suka isa part dinta zaunar da ita yayi akan kujera falo yace" hawwa wai me yasa kike son yin wauta da lafiyarki ni na tabbata yau baki ci abinci ba kuma kinsan kina da larura so kike ki jawo mana wata wahalar little baza ki gane abunda ke zuciyata bane game dake nasan damuwarki to amma ki fahimce ni littel wallahi bana yin wani abunda zan cutar dake kuma bazan bari wani ya cutar dake ba amma ina so ki dauka jamila itace kaddaramu ta rayuwa ba kuma zamu iya kauce mata ba to ina so ki tayani neman mafita wurin Allah insha Allahu zamu samu don Allah ki kwantar da hankalinki ki dawo mani da natsuwata ki saurareni ki daina nisanta kaina dake you are my best friend sweet heart , jinjina kai tayi tace"ba laifina bane zuciyata ce ta kasa cire damuwar dake damuna game dakai ina so nima in saba da rashinka kusa dani saboda nasan ba ni kadai bace awurinka amma na kasa wannan hakuri meyasa bazaka ga laifin "so" ba.
Ni nasan zuciyata tayi rauni akan soyayyarka yaya amm zanyi kokarin danne zuciyata akan komi ta karashe magana cikin rauni irin nata.
Tausayinta pal aranshi, jawota yayi ajikinsa ya rungume yana jin kamar ya maidata cikin jikinsa "kada ki damu lokaci ne zai zo ya wuce zamuyi rayuwar farin ciki ta har abada don haka yusuf ur own babu wadda zata shiga fadarki our only one in my heart, " nagode tace tare da share hawayen da suka zubo mata "me kika ci yanzu?" Na sha tea."ok ina zuwa tashi yayi yaje wurin fridge
ya dauko mata fresh milk ya dauko cup ya zo wurinta ya bude ya tsiyaya mata ya jawota jikinsa ya samata cup din abakinta bata musaba ta bude bakinta tana sha har ta shanye sannan ya ajiye cup din ya dauko maganin sannan ya bata tasha ya kama hannunta ya mikar da ita hanyar bedroom dinta ya bi da ita suna shiga bathroom suka wuce ta wanke bakinta sannan suka fito ya kama hijabin dake jikinta ta ya cire ya zaunar da ita kan gadon shima zama yayi yace"yakamata ki kwanta saboda nasan zaki school gobe daga masa kai tayi "gud to kwanta, gyarawa tayi ta hau gadon sosai ta kwanta tashi yayi daidai kanta ya shafa kanta tare da yi mata light kiss agoshinta sannan yace" have a nice bed rest my own , murmushi tayi tace"tanks. Kashe mata wutar dakin yayi sannan ya fito ya rufe mata dakin yazo falo nan ma ya kashe mata komi sannan ya fita ya kulle part din ya nufi part dinsa cike da soyayyar matarsa arai yama manta ya bar wata jamila adakinsa.
Haka yasamu jamila tana ta cika tana batsewa kallo daya yayi mata ya wuce bathroom jamila tana son yi mashi rashin mutunci amma babu hali saboda tana son cimma burinta haka ta cije ta daure ta basar, yana fitowa ya shirya cikin kayan baccin sa yazo ya kashe wutar dakin ya hau gadon ya kwanta yana kwanciya itama ta kwanta batare data ce masa komi ba.
kowa da abunda ya ke sakawa a zuciyarsa can dai taga shirun tayi yawa kuma tasan ba bacci yakeyi ba haka nan ta share ta matsa kusa da shi ta rungumesa ta baya jinta haka yasa ya juyo shima ya rungumeta sauke ajiyar zuciya tayi da alama tayi missing din shi cikin jin dadi ta cigaba da aika masa da sako shima yana maida mata haka suka cigaba da romancing din juna kamar zasu cinye juna sai da ya tabbatar ta kamu sosai babu abunda take jira sai sex takai karshe so take kawai taji shi cikinta amma ya tsaya bata lokaci. Murmushin mugunta yayi sannan ya tamke fuska ya kunna wutar dakin yace"mata tashi ki bar mani daki cikin razana ta juyo tace "what!!!!.
contact-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home