Tun Ina Karama 26 to 27
TUN INA KARAMA
Page 26
Ganin ya kashe wayar ne tayi sauri ta zira jallabiya da hijabi ta shiga bathroom ta wanke jinin da ya bata mata jiki ta fito da sauri rike da wayarta da tashi daidai shigowar umar shima nufarsa yayi inda yake kwance cikin jini don ya bugu sosai ca kumarsa yayi bai damu da jinin jikinsa ba yana girgiza shi yana cewa "brother wallahi idan har wani abu ya sameka bazan bar jamila ba haka ya sungumi dan uwansa hankali tashe ya fito dashi zuwa mota itama hawwa ganin haka yasa ta bishi da gudu ta shiga motar gudu umar yakeyi har ya kawo Alheri hospital wanda dama shine asibitin families dinsu haka ya isa cikin tashin hankali dama yayi waya da doctor din yana isa suka nufi kansa suka dauke shi sai emagency nan da nan likitan yashiga duba shi tare sauran nurse din hakayayi nasarar cire masa kwalbar da tashige masa a goshi tare dayi masa dinki saboda ta huda shi wurin har yayi rami.
Ita ko hawwa banda tunanin irin hali irin na jamila babu abunda takeyi, haka likitan yace su bari sai nan da 1hrs zai sallame su daga nan ya rubuta maganin yace umar yaje ya nemo su haka suka tafi da hawwa tare da kwantar mata da hankali.
Bayan sun gama komi doctor ya sallamesu tare cewa nan da kwana uku su dawo, haka sukayi masa godiya suka tafi. Gaba daya motar babu mai magana saboda kowa da irin tunaninsa akan jamila haka suka isa gida mai gadi ya bude masu kofa tare dayi ma maigidan nasa Allah ya kyauta don yaji komi kuma shima yayi tir da halin jamila.
Suna yin parking hawwa ta fito ta bude masu gidan shi kuma umar ya kama yusuf suka shiga ciki yakai shi har part din hawwa sannan ya nuna ma hawwa yanda maganin yake sannan yace shi zai koma sai da safe dare yayi sosai "yusuf yace bros nagode Allah yabar zumunci." ba komi umar yace Allah ya baka lafiya sai na dawo da safen haka sukayi ban kwana hawwa ta biyo shi ta rufe gidan shi kuma ya shiga mota ya nufi gida cike da takaici aransa.
Hawwa na dawowa wurin yusuf ta zauna tace" yaya bari in hada maka tea kasha kafin kasha magani ko, ta tambaye shi cikin damuwa tausayinta na fa aranshi yarinya karama amma ana sanya mata damuwa da yawa why ya tambaya a zuciyarsa, azahiri kuma murmushi yayi yace"duk yanda kike so sweet heat zanyi, murmushi tayi tace to hak ya kamata tashi tayi ta wuce kitchen ta sanya mashi ruwan zafi tare da warming din kazar da suka zo dashi don su duka babu wanda yaci komi in banda cinye juna da sukayi wanda yasa har jamila tayi masu wannan rashin mutunci.
Haka tayi komi ta dawo ta zauna kusa dashi tana bashi tea din yana sha ita kuma tana ci kadan don ita kanta komi ya fita aranta amma bata so taga yanada damuwa aransa ita dai fatan ta Allah ya bashi lafiya kafin tace komi. Bayan ta gama ne ta taimaka mashi ya shiga bathroom yayi wanka tare suka gama komi suka fito haka ta shirya shi cikin kayan baccinsa saida ta tabbatar ya kwanta sannan itama ta hau bisa gadon ta kwanta tare da rungume shi ta baya juyowa yayi yana mamakin yanda ta canza duk wannan kunyar ta ta ta cireta shima murmushin jin dadi yayi ya kara rungume abinsa ko ba komi ya samu natsuwa aransa, sai muce Asuba ta gari masoyan juna.
Basu dade ba umar ya shigo duba shi hawwa bayan sun gaisa ne ta tashi taje ta kawo ma shi lemu da ruwa, yusuf ne yace" freind ina so ka rakani in maido da jamila, cikin razana umar ya mike tsaye yana nuna shi da ya tsa zaiyi magana sukaji faduwar tiren da hawwa ta dauko da lemu da glass cup din data dauko suka fadi kasa suka fashe saboda jin furucin da hawwa taji yusuf yayi na zuwa dawo da jamila, gaba daya suka juya tare da ganin hawwa bata tsaya ba sauraren komi ba ta juya da gudu tana kuka.
Page 27
Tana shiga daki tasa key ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yusuf binta yayi a kidime yana kiran sunanta amma yana isa kofar yaji ta sanya key, komawa yayi wurin umar wanda tunda yazama kamar an dasa shi saboda mamaki yazama kamar status.
Kaga irin abunda nake nuna maka yusuf, yanzu ace kai bazaka iya hakuri da jamila ba saboda sun gama dakai sun maida ka wani wawa saboda da Allah kanayi ma yarinyar nan adalci kuwa? gaskiya yusuf zan fidda hannuna akan wannan badakala taku don bazai yiwu ba kullum problem's yaki karewa tsakaninku kai kuma kullum kalmarka bata wuce revenge zakayi taking ba kuma har yanzu kaki gamawa da al'amarin ba.
Koda umar ya kira nabila ya fadi mata ga abunda yake so tayi ta amsa da to kuma bata kawo komi aranta ba sannan yace mata bai so abarta ita kadaine tunda zasu fita da yusuf ne, koda nabila ta fada ma umma sakon umar na zuwanta gidan hawwa bata hanata ba don itama tasan hawwa tana bukatar wani kusa da ita tunda jiya ta koma, umma tace ma nabila idan kin shirya ki tafi a motar hawwa saboda abar mata abunta can nasan ai kun kusa komawa school"haka ne umma zan tafi da ita dama key din yana hannuna. To shikenan agaisheta amma kada kiyi dare umar ya maido ki gida "to umma ngd.kiran hawwa tayi kamar yadda umar yace ta sanar mata zuwanta hawwa tana da son boye tsakaninta da yusuf shiyasa koda nabila ta kirata bata daga ba saida ta saita kanta sosai sannan ta kirata kuma ita kanta nabila bata fahimci komi ba.
Suna gama samun mafita umar yace su fita kada ma tasame su haka suka fito shi yusuf ga plastar agoshi gidan su umar suka wuce direct suka nufi sashin umar batare da sun yarda Ammi ta gansu ba bare ta tambaya me yasamu yusuf din.
Ita ko jamila tana gida gabanta na faduwa tana tunanin ya zatayi idan kuma an samu wata matsala tsakaninsu amma tayi mamakin yanda har yanzu bataji wani feed back ba kuma tayi tunanin ko hawwa zata fadi ma umar komi kuma shima tasan daya sani da yanzu yazo yayi mata hauka amma bari takara sauraren su iyaka kawai tace masu bada niyya tayi ba tsautsayine kawai tana wannan tunanin ne mummy ta shigo dakin suka ci gaba da kullawa suna kwance wa.
Nabila data zo wurin hawwa bata fahimci komi ba don bata son daga dawowarta tace ga matsala tana so ta fahimci abunda yusuf yake nufi da zaman su, haka suka sha firarsu kamar bata da wata damuwa koda nabila ta tmby ta aunty jamila cewa tayi ta fita hospital tunda ta na tunanin kamar afternoon takeyi haka suka bar maganar batare da tunanin komi ba azuciyar nabila.
contact-form
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home