TUN INA KARAMA
Page 26
Hankali tashe ta nufi yusuf! cikin hanzari ta isa garesa yana dafe da inda jinin yake zuba. ita ko jamila na ganin hawwa ta taho da gudu yasa tayi saurin tsallake sa ta murda key din kofar ta fita a firgice ta fada mota ta bar gidan gabanta na faduwa tana cewa Allah yasa dai ba mugun ciwo ta ji masa ba.
Hawwa naganin halin da yusuf yake ciki ta kara fashewa da kuka ta tsugunna ta rungume shi tana kuka ko ba ba'a sanar mata ba tasan aikin jamila ne ganin jinin bai tsaya ba yasa ta tashi da gudu ta koma part dinta ta dauki wayarta ta kira umar bugu daya ya daga jin muryarta yasan ba lafiya "natsu kiyi mani bayani little waye ba lafiya? cikin kuka tace" yayane jamila ta fasa ma kai gashi nan kwance jini na zuba. What, jamila kashe wayar yayi kawai ya nufi gidan yusuf dama yana hanya ne zaije kai wani sako da daddy ya aike shi.
Ganin ya kashe wayar ne tayi sauri ta zira jallabiya da hijabi ta shiga bathroom ta wanke jinin da ya bata mata jiki ta fito da sauri rike da wayarta da tashi daidai shigowar umar shima nufarsa yayi inda yake kwance cikin jini don ya bugu sosai ca kumarsa yayi bai damu da jinin jikinsa ba yana girgiza shi yana cewa "brother wallahi idan har wani abu ya sameka bazan bar jamila ba haka ya sungumi dan uwansa hankali tashe ya fito dashi zuwa mota itama hawwa ganin haka yasa ta bishi da gudu ta shiga motar gudu umar yakeyi har ya kawo Alheri hospital wanda dama shine asibitin families dinsu haka ya isa cikin tashin hankali dama yayi waya da doctor din yana isa suka nufi kansa suka dauke shi sai emagency nan da nan likitan yashiga duba shi tare sauran nurse din hakayayi nasarar cire masa kwalbar da tashige masa a goshi tare dayi masa dinki saboda ta huda shi wurin har yayi rami.
Haka dai aka gama mashi komi aka kaishi dakin hutu, likitan na fita su umar suka tashi suka nufo shi " umar yace yaya doctor? murmushi yayi ya dafa kafadarsa yace" babu damuwa umar muje office haka suka bi doctor har office suna shiga ya nuna masu wurin zama suka zauna sannan doctor yace"bakomi umar yayi sa'a wuri dayane kwalbar ta shige sosai kuma an cireta anyi masa diki wanda dole ne yasamu hutu na wani lokaci koda na sallameku kuma akwai magungunan da za'a nema zan rubuta maka su yanzu kuma idan yayi 3 days zan kwance masa dinkin ana dressing din wurin, amma wai umar sister dinku kuwa she is very stupid tayaya zakiyi ma mijinki haka yanzu da da tsautsayi fa ta fasa mas kai ya mutu fa? umar ji yayi kar zuciyarsa zata fashe sbd takaici amma wallahi idan zai ganta yanzu sai ya canza mata kamanni.
Murmushin yake yayi yace"nidai fatana kada wani abu yasamu brother"ba komi insha Allahu amma you better ku dauki mataki don ba'a san abunda gaba zatayi ba, Allah ya kyauta Amin umar yace.
Ita ko hawwa banda tunanin irin hali irin na jamila babu abunda takeyi, haka likitan yace su bari sai nan da 1hrs zai sallame su daga nan ya rubuta maganin yace umar yaje ya nemo su haka suka tafi da hawwa tare da kwantar mata da hankali.
Bayan sun gama komi doctor ya sallamesu tare cewa nan da kwana uku su dawo, haka sukayi masa godiya suka tafi. Gaba daya motar babu mai magana saboda kowa da irin tunaninsa akan jamila haka suka isa gida mai gadi ya bude masu kofa tare dayi ma maigidan nasa Allah ya kyauta don yaji komi kuma shima yayi tir da halin jamila.
Suna yin parking hawwa ta fito ta bude masu gidan shi kuma umar ya kama yusuf suka shiga ciki yakai shi har part din hawwa sannan ya nuna ma hawwa yanda maganin yake sannan yace shi zai koma sai da safe dare yayi sosai "yusuf yace bros nagode Allah yabar zumunci." ba komi umar yace Allah ya baka lafiya sai na dawo da safen haka sukayi ban kwana hawwa ta biyo shi ta rufe gidan shi kuma ya shiga mota ya nufi gida cike da takaici aransa.
Jamila ko na fita bata zame ko ina ba sai gidansu tana shiga tayi parking ta fito ta shiga cikin gidan bata zame ko ina ba sai part din hajiya mariya tana shiga ta sameta sai hada mata magungunan takeyi cikin tashin hankali tace mummy na pasa masa kai.
cikin tsoro tace"garin yaya jamila! zakiyi wannan danyen aikin? wallahi mummy hanani fitowa yayi shine nima na aikata hakan, "kash! amma ke banza ce to yanzu ai kin lalata komi sai ki zauna mu nemi mafita zuwa safe, " ai dole mummy daddy dai bashi nan ko? don shima yanzu naga kamar ya fara bin bayansu Abban yusuf."ke don Allah kyale shi can da munafurcin su kije ki kwanta bashi gari "to mum nagode.
Hawwa na dawowa wurin yusuf ta zauna tace" yaya bari in hada maka tea kasha kafin kasha magani ko, ta tambaye shi cikin damuwa tausayinta na fa aranshi yarinya karama amma ana sanya mata damuwa da yawa why ya tambaya a zuciyarsa, azahiri kuma murmushi yayi yace"duk yanda kike so sweet heat zanyi, murmushi tayi tace to hak ya kamata tashi tayi ta wuce kitchen ta sanya mashi ruwan zafi tare da warming din kazar da suka zo dashi don su duka babu wanda yaci komi in banda cinye juna da sukayi wanda yasa har jamila tayi masu wannan rashin mutunci.
Haka tayi komi ta dawo ta zauna kusa dashi tana bashi tea din yana sha ita kuma tana ci kadan don ita kanta komi ya fita aranta amma bata so taga yanada damuwa aransa ita dai fatan ta Allah ya bashi lafiya kafin tace komi. Bayan ta gama ne ta taimaka mashi ya shiga bathroom yayi wanka tare suka gama komi suka fito haka ta shirya shi cikin kayan baccinsa saida ta tabbatar ya kwanta sannan itama ta hau bisa gadon ta kwanta tare da rungume shi ta baya juyowa yayi yana mamakin yanda ta canza duk wannan kunyar ta ta ta cireta shima murmushin jin dadi yayi ya kara rungume abinsa ko ba komi ya samu natsuwa aransa, sai muce Asuba ta gari masoyan juna.
Washegari da safe bayan sun gama komi ta bashi magani suna zaune a pallor tayi pillow da cinyarsa shi kuma yana wasa da kalabar dake kanta shi kansa wani dadi yakeji aransa yanda yaga bata damu da abunda ya faru ba bare ta tambaye sa me ya faru tsakaninsa da matarsa. Ba zato taji yace"little amma ina fatan babu wanda yasan me ya faru ina nufin su umma.
ariya tayi tace"babu wanda yasani, "good house wife haka ake so mace ta rinka rike sirrin cikin gidanta kuma kada ki damu da abinda jamila takeyi with time kinji ko?" Naji yayana kuma insha Allahu zanyi yanda kace"Allah yayi maki Albarka "Amin dear ta amsa masa tare da kara shigewa jikinsa.
Basu dade ba umar ya shigo duba shi hawwa bayan sun gaisa ne ta tashi taje ta kawo ma shi lemu da ruwa, yusuf ne yace" freind ina so ka rakani in maido da jamila, cikin razana umar ya mike tsaye yana nuna shi da ya tsa zaiyi magana sukaji faduwar tiren da hawwa ta dauko da lemu da glass cup din data dauko suka fadi kasa suka fashe saboda jin furucin da hawwa taji yusuf yayi na zuwa dawo da jamila, gaba daya suka juya tare da ganin hawwa bata tsaya ba sauraren komi ba ta juya da gudu tana kuka.
Page 27
Tana shiga daki tasa key ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yusuf binta yayi a kidime yana kiran sunanta amma yana isa kofar yaji ta sanya key, komawa yayi wurin umar wanda tunda yazama kamar an dasa shi saboda mamaki yazama kamar status.
Kaga irin abunda nake nuna maka yusuf, yanzu ace kai bazaka iya hakuri da jamila ba saboda sun gama dakai sun maida ka wani wawa saboda da Allah kanayi ma yarinyar nan adalci kuwa? gaskiya yusuf zan fidda hannuna akan wannan badakala taku don bazai yiwu ba kullum problem's yaki karewa tsakaninku kai kuma kullum kalmarka bata wuce revenge zakayi taking ba kuma har yanzu kaki gamawa da al'amarin ba.
Umar kasan bazan boye maka komi ba arayuwata ba to wallahi ban taba son jamila koda da second daya ne idan ba don asiri ba kuma gaba daya mun san haka to jamila tayi mani abubuwa da yawa arayuwa infact ma ince maka ban taba samun mutumin da ya musguna mani ba arayuwa irin jamila idan har na rabu da jamila salun alun to gaskiya banyi abunda ya dace ba amma ina so in nuna ma jamila ita bata isa ba arayuwa duk abunda take takama da shi ina so in raba ta dashi in nuna mata ita bata isa ba kuma bazata iya samun digo araina ba na soyayyarta kuma ina so duniya tayi mata kunci, ina so in azabtar da rayuwarta har sai ta wulakanta sannan inyi mata mai gaba daya zan dasa mata ciwo a zuciyarta wanda har ta mutu bazata daina jin sa ba.
Amma hakan bazata samu ba har sai mun zama clothenings da ita don haka ina so ku bani lokacin ku fahimce ni babu komi araina intentionally nayi maganar nan dama ina so hawwa taji don inga reaction dinta kuma nagani zanyi handle din komi ya kara she mgn yana kallon umar sosai.
Ajiyar zuciya umar ya sauke tare da jinjina kai alamar gamsuwa "to amma yusuf taya ita hawwa zata tabbatar ba sonta kake ba?" Yes ina so hawwa ta kwaci kanta wurin jamila tacire tsoron da takeyi mata arai kamar yadda nabila ta bata shawara kuma naga ta dau hanyar yin hakan, kuma ina so ita jamila tasan hawwa ita kadaice macen da nake so a zuciyata duk da ta kasa gane hakan har yanzu zan bita akan asirinta na ta siri har sai nakai inada zamu fara game din daga nan zata fadi kasa warwars daga ita har uwarta."to shikenan amma you have very careful about her "insha Allahu freind." Amma ba yau ba kaje ka lallashi littel.
Yes wallahi umar tunda ta kulle daki bazata saurareni yanzu ba "to yanzu kasan ya zamuyi?" Ban sani ba umar."nabila zan kira tace mata zata zo yanzu na tabbatar bazata cigaba da fushin ba har kasamu ka fahimtar da ita komi cikin hikima."gud idea freind.
Koda umar ya kira nabila ya fadi mata ga abunda yake so tayi ta amsa da to kuma bata kawo komi aranta ba sannan yace mata bai so abarta ita kadaine tunda zasu fita da yusuf ne, koda nabila ta fada ma umma sakon umar na zuwanta gidan hawwa bata hanata ba don itama tasan hawwa tana bukatar wani kusa da ita tunda jiya ta koma, umma tace ma nabila idan kin shirya ki tafi a motar hawwa saboda abar mata abunta can nasan ai kun kusa komawa school"haka ne umma zan tafi da ita dama key din yana hannuna. To shikenan agaisheta amma kada kiyi dare umar ya maido ki gida "to umma ngd.kiran hawwa tayi kamar yadda umar yace ta sanar mata zuwanta hawwa tana da son boye tsakaninta da yusuf shiyasa koda nabila ta kirata bata daga ba saida ta saita kanta sosai sannan ta kirata kuma ita kanta nabila bata fahimci komi ba.
Suna gama samun mafita umar yace su fita kada ma tasame su haka suka fito shi yusuf ga plastar agoshi gidan su umar suka wuce direct suka nufi sashin umar batare da sun yarda Ammi ta gansu ba bare ta tambaya me yasamu yusuf din.
Ita ko jamila tana gida gabanta na faduwa tana tunanin ya zatayi idan kuma an samu wata matsala tsakaninsu amma tayi mamakin yanda har yanzu bataji wani feed back ba kuma tayi tunanin ko hawwa zata fadi ma umar komi kuma shima tasan daya sani da yanzu yazo yayi mata hauka amma bari takara sauraren su iyaka kawai tace masu bada niyya tayi ba tsautsayine kawai tana wannan tunanin ne mummy ta shigo dakin suka ci gaba da kullawa suna kwance wa.
Nabila data zo wurin hawwa bata fahimci komi ba don bata son daga dawowarta tace ga matsala tana so ta fahimci abunda yusuf yake nufi da zaman su, haka suka sha firarsu kamar bata da wata damuwa koda nabila ta tmby ta aunty jamila cewa tayi ta fita hospital tunda ta na tunanin kamar afternoon takeyi haka suka bar maganar batare da tunanin komi ba azuciyar nabila.
Su umar basu dawo ba sai karfe 4:30 suna zuwa suka iske hawwa kamar ba abunda ya faru tsakaninsu koda nabila ta tambayai hawwa me yasamu yaya a goshi cewa tayi koface ta buge shi yayi rauni Allah ma ya kiyaye, umar najin yanda hawwa take kare mijinta azuciyarsa yace lallai yusuf Allah ya baka yar aljannar mata haka nabila ta jajanta masu sukayi sallama suka rako su har bakin mota suka tafi wurin motar ta ta wuce inda nabila tayi mata parking.
binta yayi da kallo don ita ko sake kallonshi batayi ba tunda su nabila suka fita budewa tayi ta dauki abunda zata dauka ta rufe bata saurare shi ba ta nufi hanyar shiga cikin gidan binta yayi abaya tana shiga tayi hanyar part dinta cikin sauri ya isa gareta ya rike mata hannu juyowa tayi kafin yayi mgn ta daga masa hannu dakata yusuf! cikin razana ya bita da kallo don ko da wasa bai taba jin ta kira shi agaban shi ba kai tsaye....
contact-form
Labels: Hausa Novel