Tun Ina Karama_ 30 to 31
TUN INA KARAMA
Page 30
Tana fita dariya yayi sosai yace ai tunda kika riga nasan weeknest dinki yarinya zaki sha wahalata kafin ki bar gidan nan sai na nuna maki babu abun so a jikinki bare kiyi yanda kike so. Jawo bed drawer site din shi yayi ya balli maganinshi yasha don shima yana tare da feelings sosai amma bazai iya yin komi da jamila ba zaiyi hakuri har sai ya koma dakin Hawwa da haka bacci yayi gaba da shi.
Ita ko Jamila ranar ba bacci bata san haka ba da tasamu magani ta ajiye haka taita jin wani irin feelings tana ta matse cinyoyi tana zagin Yusuf da ya cuceta lokacin da bacci ya dauketa da yake tasa abun aranta haka tayi mafarki ta dan samu ta rage sha'awarta amma ba don ta gamsu ba don ba haka taso ba.
Bai dawo gidan ba sai 6:30 koda ya dawo Jamila bata tashi ba haka ya wuce part dinsa saboda yana so zaije kaduna yau zasuyi wani meeting haka ya wuce bathroom yayi wanka ya dawo ya shirya cikin wani suit abun gwanin ban sha'awa don Yusuf akwai kyau, ga haiba, ga kwarjini. Yana daya wannan shine jamila take fankama dashi awurin yusuf perfumes dinsa ya dauko yana fesawa , sallama hawwa tayi tare da shiga dakin. "amsawa yayi yana kallon kofar gani yayi tayi masa kyau sosai murmushi ya sakar mata itama ta sakar masa tare da isowa gabansa tana kokarin amsar agogon sha dayake kokarin daurawa ta kama hannun sa tana daura mashi " good morning dear "morning sweet heart ya jikin ki " am fine "good kin shirya ne? "Ye na shirya naga baka fito break bane jan hancinta yayi yace "kin manta yau ina azumi ne?" ayya na shafa 'a gaskiya ne litinin da alhamis yana azumi.takalman shi ta dauko masa ta goge ta tsugunna tana sanya masa kallonta yake yi cike da kauna yace"tanks littel" murmushi tayi tace aiki na ne." haka ta karasa shirya shi komi need. Sannan yake fada mata kaduna zashi meeting my be ya dawo yau ko kuma sai gobe saboda ya na so umar yaji to amma akwai wasu kaya da za'a kawo mana to dole saidai ni in tafi."yanzu yaya har sai ka kwana? shafa fuskarta yayi yace"littel ai kwana daya ne inma bamu gama ba ko kina so in biyo darene in dawo? in hakan yayi maki sai in dawo ya kalleta tare da dage mata gira daya yana murmushi. Turo baki tayi "nidai ban ce ba Allah ya kiyaye hanya adawo lafiya " "Ameen good wife."
PAGE 31
Kallonta yayi ya nunata da yatsa"wallahi kuskure na karshe da zaki aikata kenan kice zaki dora hannunki akan matata, kewai me yasa baki son zaman lafiya? Jamila zanyi maganin rashin kunyar nan taki! Kallon shi Hawwa tayi tace"Don Allah Dear kayi hakuri mu tafi kaga lkc na tafiya takara she magana cikin shagwaba. Jamila kasa magana tayi sbd mamaki yariyar takeyi sosai aranta kallon su kawai takeyi kamar status, wucewa yayi gaba Hawwa tabi bayansa da tafiya ta jan hankali Jamila kamar ta shaketa saboda takaici. Har yakai bakin kofa zai fita ya juyo yace"Kaduna zani kuma ba lallai bane in dawo yau dukkanku idan kuna bukatar wani abu ku nemi Umar, yana fadin haka ya fice daga gidan Hkenan.tabi shi, zamaJamila tayi akankujera ta fashe da kukan takaici. Suna fita Yusuf ya mikama Hawwa key ta bude mota tasanya masu kayan dake hannunta sannan ta shiga shima zama yayi Hawwa ta ja motar suka fita.
Kiran wayar mummy tayi bugu biyu ta daga wayar cikin kuka Jamila tace"mummy Yusuf ya canza gaba daya na shiga uku mummy! cikin tashin hankali mummy tace "me kuma ya faru Jamila? bata boye mata komi ba tun dawowarta ta sanar mata abunda ya faru." Kwantar da hankalinki kada ki kara damuwa zan nemi hajiya Lami zamu san abunyi ki kyalesu kawai, cikin jin dadi tace"nagode mummy haka sukayi sallama dacewar sai taji daga gareta ita mummy din, amma fa duk bayanin da Jamila tayi ma mummy batace Yusuf ya marita ba nan ta tashi itam ta tafi ta shirya don zuwa hospital.
Duk abunda sukeyi Umar na kallonsu ta window tun zuwansu dariya kawai yakeyi masu, sanin dama Umar na ciki yasa yayi knocking "yes come in budewa yayi yashiga dagowa yayi yana son gane wani abu amma sai ya fuske " morning Mr lover dftn dai kasha zumar sosai ya karashe mgn yana guntse dariyarsa. Kallonsa yayi yace ni matsalata dakai sanya ido akan abunda babu ruwanka yana magana yana kokarin kwashe takardun gaban Umar daya sanya ya hada masa"nifa inace ma tare zaku tafi?wani irin kallo yayi masa yace"bazan iya talla da matata ba only one day, dariya yayi yace "nidai nagama komi zanje inci gaba da aikina ya tashi yana kokarin fita, kallonsa Yusuf yayi yace" ina so ka kula da gidana ka kuma sanya ido in dawo don yanzu nan saida na ci uban Jamila kafin mu fito wai zata mari Hawwa, don ta ganmu tare zamu fito. Dawowa Umar yayi yazo kusa dashi ya dafa kafadarsa yace"Ina ftn dai bata taba mani kanwata ba ko? his seriously yake maganar "Kaima kasan ba zan bata wannan damar ba don haka ka kula dasu." Insha Allahu bros, sallama sukayi yayi masa ftn Alkairi sannab suka rabu.
Hawwa na shiga school ta wuce lectures dinta. Bayan sun fito ne suka hadu da nabila inda suke zama suka wuce suka zauna, nabila tace"wai Hawwa ya akayi naganki da motar yaya Yusuf ko taki tasamu matsala ne? dariya tayi tare da zama tace "ai kedai bari yau dana sha mari wurin aunty Jamila saboda tahowa da motar nan ta karashe mgn tana dariya." Ban fahimce ki ba?"eh to zamu fita dashi tace ban isaba ai ranar girkinta ne shine zata gaya nani magana nikuma na rama shine fa wai zata mareni shi kuma yaya ni banma luraba kawai ya kwasheta da mari nikaina saida na tsorata."yes wayyo cikina Allah na gode maka amma fa yau naji dadin labarin nan ashe zanga wannan lokacin?"Amma nabila baki da dama wai wannan abun kikema dariya haka? ni kinsan Allah nayi mamaki."wallahi daba da mota nazo ba ai da sai na biki inga irin zanar da zaki sha tunda yaya bashi gari. Yes"ai ni na fita harkarta dama dazun ma don ganin idonsa ne."yes matsoraciya.
Hajiya lami ta kira ta shedamata komi cewa tayi kawai su shirya su koma wurin bokan wannan ba abun abari bane gara su koma koma mi za'ayi ayi shi kawai. Koda nagama lectures sallama mukayi da nabila tare da bani kwarin gwiwar kada inji tsoronta nima gida nane. Nabila har ta dau hanyar gida sai kuma wata zuciyar tace mata taje gidansu ta gani ko daddy ya dawo haka ta karkata motarta don zuwa gidan, koda ta shiga ba wanda ya sani don bata shiga da mota ba bakin get ta ajiye ta haka suka gaisa da mai gadi ta shiga ta bayan lambun gidan ta shiga amma abunda kunnenta suka jiyemata ne mummy na fada ma Aunty jamila yasa takasa gaba ta kasa baya saboda razana datayi........?
Labels: Hausa Novel
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home