Wednesday, October 27, 2021

Ki Aure Dattijo Dan Ki San Meke Faruwa bayan Kwana Biyu.......


Ki Aure Dattijo Dan Ki San Meke Faruwa  bayan Kwana Biyu.......

    Sirrin soyayyar aure da dattijon namiji shine mace ta san cewa zata yi kishi da matan da suka girmemata ne, wata kila kuma sun ma haifeta, irin wadannan mazan suna bukatar ganin mace da zasu aura tana mutunta matansa na gida musamman uwargidan kamin ta shiga da kuma bayan ta shiga. 

    Haka kuma duk da irin kaskantar da kansa da zai yi a gabanki ganin yana nemanki da aure kuma gashi zai iya kasancewa sa'an mahaifinki, yana da kyau ki mutuntashi kuma ki dauke shi da daraja ba wai kuma ki maidashi wani boyi-boyi ba saboda zai rufa miki asiri ya aureki a matsayinsa na tsoho. Hakan zai baki martaba da daraja wajen ya yansa da kuma abokansa dama wasu masu sanya idanuwa game da soyayyan naku.

    Irin wadannan mazan basu cika kawo sako da kansu ba, akasari suka samu wani da suka aminta da shi kokuma wani babba daga cikin yaran gidansu su rika aika ne wajen matan da suke so da aure. Anan sirrin maza irin wadannan dattijan shine ki tabbatar 'yan aikensu kina mutuntasu, haka kuma kada kiyi wani abu, ko ki fadi wata kalma ko aikata wata dabi'a da zai iya kawo shakku a idanuwan dan aiken ko cusa masa wani kokwanto a zuciya yadda zai yi tunanin cewa maigidansa, ko mahifinsa ko kakansa zai auro mace ballagaza. 

    Wanni sirrin irin wadannan mazan shine, suna da matukar yiwa macen da suke nema da aure hidima, hidimar da wani lokacin yana wuce hankali, koda suna da shi ko basu da shi, abunda irin wadannan mazan basu so shine suyi maki kyauta kike karba. Suna bukatar ganin duk wani kyautar da suka yiwa macen da suke nemanta da aure ta sa hannu biyu ta karba tare da da nuna farincikinta da annashuwa. 

    Sai dai kuma kada hakan ya baki damar yawan yi masa aike da bani-bani, ko kuma yawan gabatar masa da bukatunki dana kawaye ko iyayenki a duk lokacin daya zo wajenki. Duk da yake idan mai haline ba zai taba nuna miki gajiyawa ba ko kuma fushinsa a zahiri ba, sai dai kuma hakan yana iya zubar miki da mutunci a wajen na kusa da shi, shi kuma zai dauka cewa iyayenki ba dattawa bane, haka kuma irin wadannan mazan babu wanda yakaisu gori, kada kiyi mamakin idan watarana ya cemiki shi yake ciyar da gidanku.


    Da yake sun manyanta kuma sun saba da karabniya da 'ya'ya da jikoki, kuma dadewarsu a duniya yasa suka fahimce halaye na mata dai dai gwargwado, mazan da suka manyanta masu neman aure maza ne da suke sha'awan ganin macen da zasu aura kullum a cikin kwalliya, haka kuma suna son mace mai yawan shagwaba tabkar karamar yarinya ko kuma jika a gaban kakanta. 
    
Wani abun sha'awa da irin wadannan mazan shine yana da wuyar gaske su nemi macen da zasu aura da lalata koda kuwa suna da matsaniyar tsohuwar karuwace Kamar yadda kika yi hakuri a lokacin soyayyar neman aurenki da namijin daya manyanta haka zaki ci gaba da hakurin bayan kunyi auren. Munyi bayani a baya irin matsalolin dake tattarae da soyayya da namijin daya manyanta, hakama zaman aure dashi yake da nasa matsalolin.

    Akasarin dattijawan maza dai yana da matukar wahala a rasasu da mace a lokacin da suke neman wani auren, haka kuma ana iya samunsu da 'ya'ya manya wasu lokutanma har da jikoki. Don haka duk macen data zabawa kanta zaman aure da irin wadannan mazan dole ne sai ta hada da gagarumin hakuri ko tana gida daya da sauran matansa ko kuma kowacce da muhallinta.

    Mafi yawan irin wadannan mazan da suka manyanta kuma suke bukatar aure, ba rashin jin dadin zama da tsoffin matansu bane basa yi, sai dai wasu loluta kamar yadda bincike ya tabbatar matan nasu na iya tsofar da bazasu iya gamsar dasu ba a lokutan jima'i. Haka kuma wasu tsofin magidanta giyar kudi ne ke dibarsu suji ko ba komai ai gara su samo wata mace mai dan galmi-galmi su aura domin su burge abokansu. Wasulokutan kuma abokai ne a tsakankaninsu suke yiwa tayi 'ya'yansu ga junansu.

    Koma dai da wace hujja ko dalili mace ta yanke shawarar auren namiji daya manyanta, babban sirrin zama da shi shine ta tabbatar da cewa bat nunawa matansa, 'ya'yansa, jikokinsa, 'yan uwansa da abokansa gadara da iyayin da zata iya fiskantar matsala dasu ba. Kamar yadda muka yi bayani a baya, a lokacin da dattijon na miji ya yanke shawarar auren mace, bai cika canza ra'ayi ba koda kuwa ya fahimci wani illa da macen da yake sonta da auren ba, haka kuma lokacin daya aure mace bai cika barin wani matsala a tsakaninsu yana bata masa rai ba ganin cewa yana da kwarewar zama da mata da kuma sanin irin matsalolin mata da hanyar warwaresu ganin shima ana kawo irin wannan gabansa na 'ya'yansa ko jikokinsa yana magacesu.

    Sai dai babban matsalar da macen data aure dattijon namiji zata iya fiskanta a zaman aurenta da mijin nata shine idan har ta sake wata matsala ya shiga tsakaninta da matan wannan mijin nata, ko kuma 'ya'yansa. Wanda irin gallazamata na karkashin kasa dana zahiri yana iya sanyawa ta gudu ta bar ladanta. Babban sirrin zama da irin wadannan magidanta shine ki tabbatar da cewa babu raini a tsakaninki da matansa duk da yake yanzu abunda suke ji wajen dattijon kema kina danawa, haka kuma a wannan lokacin idan matansa marasa fahimta ne da tsoron Allah zaki ga abubuwa da dama da cusa bakin ciki da takaici tumma ba ace kuna gida daya ba ganin su sun tasanma tsofa kekuma yanzu kike more mijin nasu dasu ci kurunciyan aure tare amma gashi yanzu sun zama 'yan kallo.

    Dole ki dauka cewa wannan matan da yanzu kike zaman kishiyoyi tare tamkar iyayen kine su, don haka duk wata bakar magana ko habaicin da zasu yada miki ki kauda kunnenki tamkar baki ji ba. Haka kuma kiyi kokakrin jawo wasu daga cikin 'ya'yansu ko kikokinsu da kika fahimci cewa masu saukin kaine da fahimta kusa dake domin kokarin nuna masu halin da kike ciki cikin hikima da dabara. Haka kuma ki tabbatar da cewa kin samu natsuwa sosai a duk lokacin da kika ga wani abu ba dai-dai ba a gidanki ganin zama da tsaffin mata a matsayin kishiyoyi, zama ne da mace take bukatr darasi a kansa ganin irin kissan da kisisina na gadar zare da irin wadannan matan zasu iya shirya mace ta fada idan bata yi hankali ba.

    Haka kuma wani sirrin da zaki iya dauke hankalin tsohon mijin nan naki dashi shine iya kwalliya da kuma tsaftace jiki da muhalli. Shi na miji ko kazami ne yana sha'awar ganin cewa yana zaune da mace mai tsaffta. Haka kuma irin wadannan mazan ko kura bai kaisu kwadayin nama ba idan masu lafiyan hakora ne, idan kuma ba masu shi bane kada a raba ki da shirya masa 'yar wata ferfesu na kaza ko na kifi a duk lokacin da zai shigo gidanki ko dakinki.

    Maza masu yawan shekaru sune mazan dasu kafi sha'awar ganin mace da manyan nonuwa ko kuma tsayayyun nonuwa, bincike ya tabbatar da cewa akasarin manyan maza masu shekaru da suke sha'awar kara aure babu abunda ke sasu hakan irin sha'awar ganin suna wasa da mikankun nonuwan budurwa ko karamar bazawara idan suka ga cewa matansu na gida sun tsufa.

    Don haka a duk lokacin da zaki yi kwalliyarki na jiran miji, ki tabbatar da cewa kin yi shigar da zasu fito da hantsarki sosai domin kwantar da hankalin dattijon mijinki. Haka kuma iya tafiyarki shi kansa wani sirri ne na zama da dattijon na miji, domin a lokacin daya kyalla idanuwa yaga cewa kina tafiya jikinki na kadawa nan take keji tsohuwar tsuminsa yana tashi.

    Haka kuma a duk lokacin daya shigo da abokansa wadanda suma watakila masu shekaru ne, to ki tabbatar da cewa kin karbesu hannu biyu-biyu, kuma ki nunawa mijin naki so a gaban wadannan abokan nasa har sai sun gamsu da cewa tabbas abokinsu yana cikin wani sabon rayuwa na zamantakewan aure, wanda hakan zai sasu suma suyi sha'awar idan suna da halin yi.

    Bafa ina nufin cewa ki kwanta a kansa ko ki sumbace shi a gabansu bafa, a'a, abun nufi shine ko ta hanyar hira ki tabbatar masu da cewa wannan mijin naki yafi saurayi dan shekaru 17 a wajenki. Da kuma nuna masu cewa baki bukatar jimawansa a waje da makamantar irin wadannan wasanni na baki wanda wasi sako ne da mai hankali yana iya fahimtar abunda ke dauke cikinsa.

    Sirrin zama da magidantan da suka tsofa shine, a kullum ki dauke shi tamkar kina auren saurayi ne, kada ki kyamace shi ganin akasarin manyan magidanta ana iya samunsu da wasu halaye irin na tsofa. Haka kuma ki tabbatar da cewa yadda zaki yi soyayyar zaman aure da na miji mai karancin shekaru haka shima zaki yi da shi. Haka kuma ki cire a ranki cewa kina zaman aure ne da dattijon daya yayi sa'ar mahaifinki, saki jiki ki wahala kiyi soyayayyar zaman aurenki da mijin naki.

    Sai dai kuma manyan matsalolin da mata suka fi fiskanta a lokacin zaman aure irin wannan shi ne na rashin samun haihuwa a wasu lokutan da kuma ishenshen kwaciya ta jima'i ga macen data ke da bukata da yawa.

MATAR DATTIJO:

A ranar baba ya tura aka aka kira masa dattijona, a soro nayi musu shimfida cike da ladabi ya samu guri ya zauna, kallona ya rika yi yana min murmushi tare da kashe min ido da alama dai so yake nayi masa magana, banza nayi da shi na wuce gida saboda ji nake gaba daya na tsane shi, tsakar gida na koma na barsu su yi magana da baba.

    Bayan sun gaisa baba ya fara yi masa bayanin makasudin haduwar su, gyara zama baba yayi sannan ya fara yimasa magana, nasan za kayi mamakin kiran da nayi maka Alhaji, kansa a sunkuye ya amsa kwarai kuwa baba, Allah yasa dai lafiya gyaran murya yayi sannan ya cigaba da cewa, zamu iya cewa lafiya amma ba lau ba.

    Cike da mamaki ya dago yana tambayar sa me kuma ya faru baba?damuwa ce ta bayyana a fuskar baba, Alhaji ina ganin ya kamata kayi hakuri mu ma mu yi hakuri ka sauwakewa Niimatullah aurenka, a firgice ya dago me kuma yakawo wannan maganar baba? girgiza kai yayi ba komai Alhaji kayi hakuri mu ma dole ce tasa zamu fasa amma mun san kana son yarinyar nan ita ma tana sonka, amma Niimatullah bata dace da kai ba, saboda kai mai kudi ne kuma mai ilimi kuma ka fito daga babban gida, ita kuwa yar talakawa ce kuma marainiya mara gata, ina jin tsoron barin Niimatullah ta aureka saboda furucin matarka a kanta kada ta hallaka mana ita wata rana saboda na fuskanci tana da kishi da yawa shi yasa na duba naga abinda ya fi alkhairi shi ne ta bar mata mijinta.

    Kaga a kullum karfin mukarewa yake kada a yi auren nan wani abu ya biyo baya, tunda Niimatullah yarinya ce karama har yanzu bata gama mallakar hankalin kanta ba gashi ba tada wayo ga rashin gata ko cutarta tayi ba mu da halin karbar mata hakkinta,dan haka nake rokonka dan girman Allah ka sauwake mata, saboda maganin a yi shi ne a bari, kusan zuwanta biyu gidan nan tana ci mana zarafi, har shake Niimatullah tayi har sai da ta kusa suma yanzu haka
wuyanta ciwo yake, don haka mu baza mu iya fada da abinda ya fi karfin mu ba don Allah ka saketa.

    Tunda dattijo ya sunkuya bai dago ba wani gumi ne ya rika yanko masa ta ko'ina,nan da nan idanunsa suka yi jawur saboda takaici, bai san ya xai yi ba idan aka ce ya rabu da Niimatullah ba, cikin rawar murya yake wa baba magana, kayi min arziki baba wlh bazan iya sakin Niimatullah ba, dan Allah a yi hakuri zan tsawatar mata wallahi ban san tana zuwa tayi muku haka ba, dafa kafadar shi baba yayi ka kwantar da hankalinka Alhaji wannan duk ba wani abin tayar da hankali bane, abu ne da muke so a yi maslaha saboda Allah ya sani amanar Niimatullah a hannuna take, duk wani abu da ya sameta muna da alhaki a kai kuma sai Allah ya tambaye mu wannan dalilin yasa dole a warware auren nan saboda gudun bacin rai.

    Hawaye ne ya cika idon dattijo rokon baba ya fara yi a kan yayi masa alfarma ya janye maganar, duk nacin da yayi hakarsa bata cimma ruwa ba, jikinsa a sanyaye ya dubi baba. dan Allah ina so xan yi magana da Niimatullah, cikin sakin fuska baba ya bashi amsa ba komai Alhaji ai bazan hanaka magana da iyalinka ba tunda har yanzu a karkashin ikonka take.

    kirana baba yayi cike da ladabi na tsugunnah tare da cewa gani baba, cikin kulawa yace mijinki ne yake son magana da ke yana gama fada ya bamu guri, kan shimfidar da aka yi masa na zauna, sunkuyar da kaina nayi saboda yadda na ganshi yana cikin tashin hankali da damuwa karasowa yayi ya zauna kusa da ni, fadawa jikina yayi yana Hawaye tare da tallafo fuskata Niimatullah me nayi miki kike neman yanke alaka da ni? me yasa kike son na sake ki alhalin kinsan zuciyata baza ta iya jure hakan ba, ke kika fadawa baba kina son na sake ki? sunkuyar da kaina nayi tare da cewa.

    Eh na zabi hakan ne saboda hankalina zai fi kwanciya dama na dade ina tunanin hakan saboda cin kashin da matarka take mana ya fara yawa, na yanke shawarar hakura da kai indai hakan zai yi sanadiyyar farin cikina dan allah ka sake ni ko zan huta da wulakancin da matarka take mana.

    Kallona yayi da jajayen idanunsa lallai baki san adadin yadda nake sonki ba Niimatullah, ke yanzu a tunaninki zan iya rabuwa da ke wallahi son rayuwata nake miki bazan iya hakura da ke ba saboda ina matukar sonki, a halin yanzu kawai kina ganin kaso ne mafi kankanta daga cikin irin son da nake maki, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna miki tsantsar soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure.  

    Ba zan taba mantawa da sadaukarwar da kika min ba, kina yarinya kika aure ni a matsayina na dattijo, kina tunanin zan manta da wannan sadaukarwar? don haka babu macen da zata samu gurbin soyayyar da kika samu a zuciyata, kisa a ranki bazan iya rabuwa da ke ba,ya zan yi da rayuwata idan na wayi gari bakya tare da ni, ki tuna a wajenki kawai nake samun farin ciki, yana karasa maganar ya fashe da kuka.

    Nima kukan na rika ni kaina nasan ina son dattijona amma hangen abinda xai je ya dawo nake yi, cikin kukan nake masa magana nasan kana sona amma dan allah ka duba halin da zan fada ka sake ni, matarka bata kaunata tana zagina ta zagi innata me zan je gidanka nayi, ni tuni na bawa xuciyata hakuri a kan rabuwa da kai kuma ta hakura da kai.

    Kamo ni yayi hada da kirjinsa yana rarrashina, me yasa zaki min haka Niimatullah, kin san irin kaunar da nake miki da zaki ce sai na sake ki, indai aka takura na sake ki wallahi nasan sai na rasa raina, saboda soyayyar ki ta gama yi min illah. Zame jikina nayi na nufi bakin kofar shiga gida ina share Hawaye, hada kansa yayi da bango yana ta kuka kamar karamin yaro, bazan iya jure ganin shi yana kuka ba wannan dalilin yasa na shige gida gudun kada zuciyata ta buga saboda bacin rai.

    A soron na barshi ya fi kusan minti talatin yana kuka cikin kukan yake kiran sunana, Niimatullah ki tausayawa rayuwata ki aure ni, ki tuna irin yadda nake sonki da kaunar Ki,tun lokacin da na fara ganinki, kika shiga raina kin samu gurin da baza ki taba fita ba har abada. ke ta daban ce Niimatullah, kina da wata baiwa wadda ba kowace mace Allah ya bawa ba, ina samun nutsuwa idan ina tare da ke,kada ki guje ni Niimatullah ki kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskar ki,zan yi kokarin wadata ki da jin dadi daga cikin nau’ikan ababen jin dadin rayuwar duniya. 

    Ina tsanin sonki babyna bazan iya barin ki ba ya karasa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani, cikin gida na shiga ina zuwa na fada gado ina kuka, ban san halin da zan tsinci kaina ba idan aka raba ni da shi, shine mutum na farko da ya fara koyar da ni soyayya, a kullum burinsa ya tarairayi jaririyar zuciyata wacce bata san komai ba sai soyayyarsa da karfi na rika fadar hakan ina cigaba da kukana, innata ce ta shigo inda nake saboda taji sambatun da nake yi dafa kafadata tayi tana rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah indai Alhaji rabonki ne zaki aure shi,mu dai fatan mu ya yiwa tufka hanci wannan matar tasa ta daina zuwa tana ci mana mutunci, nasan Malam zai sakko saboda yana son abinda kike so, a ranar cikin damuwa na wuni.

    A bangaren dattijo kuwa yana komawa ya tarar da gidansa ba kowa, kwafa yayi ya samu kujera ya zauna a falo yana jiran dawowar matarsa, tunanin Niimatullah ya shiga yi da yadda zai shawo kan baba ya kyale shi ya tare da matarsa, baya jin xai iya rabuwa da ita saboda duk wani farin cikinsa ya hango shi tare da ita, yana cikin tunanin yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa, hannu yasa ya share gani yayi an tsaya a kansa, a hankali ya dago, matarsa ya gani tsaye tana yi masa wani kallo a fusace ya mike yana nuna ta da hannu, ji yayi bakinsa na rawa saboda takaicin da ya cika zuciyarsa kasa ce mata komai yayi.

    Cike da gadara take masa magana, naje na lalata auren yar iskar yarinyar da kake so, saboda bazan taba iya sharing dinka da wannan kazamar yarinyar ba, kuma wallahi ka sani na rika yi maka haka kenan Har abada ba kai ba kara aure, duk inda kaje neman aure sai na rika zuwa ina ci musu nutunci a haka har su yi zuciya a fasa auren, mutumin banza kawai mara alkawari, a fusace ya dubeta. ni kike kira da mutumin banza Hajiya Maryam? tsare shi tayi da ido tana harararsa na fada duk abinda za kayi sai dai kayi, karya nayi maka ba mutumin banzan bane kana tsoho ka auro yar cikinka saboda son zuciya da kwadayi an girma ba a san an girma ba, lalata aure yanzu na fara idan zaka nemi yan mata dari ni kuma sai na lalata auren har sai ka hakura ka daina.

    Komawa yayi ya xauna saboda idan ya cigaba da tsayawa tsaf zai fadi wani bakin ciki ne ya cika zuciyarsa cike da fushi ya mayar mata da amsa wlh ba dan arzikin yayan da kika haifa ba da zamana ya kare da ke yau,a matsayina na uban yayanki kike kirana da mutumin banza saboda ba ki da hankali, auren Niimatullah ne bakya so kuma kisa aranki kamar amarya ta tare a dakinta ne, kuma ki shirya ganin wulakanci kala-kala Allah dai ya kawota da alkhairi, da sannu sai na ganar da ke kuskurenki sai kin yi nadamar kirana da mutumin banza shashasha mara amfani, sai kin zama tamkar shara a gidan nan dama ba ki da wani amfani a wajena banda bata min rai babu abinda kike yi mahaukaciya kawai, yana gama fada mata ya wuce dakinsa.

    Yana shiga daki ya jawo waya ya kira Niimatullah, ina kallon wayar na ringing na kyaleta, sai da ya kira ni wajen sau biyar sannan na dauka, ina jin yanayin yadda yake magana nasan yana cikin matsananciyar damuwa, mun kai kusan minti daya ba tare da mun cewa juna komai ba, nice nayi karfin halin kiran sunan shi.

    Dattijona! cike da damuwa ya amsa min da na'am my Niimatullah, cike da damuwa nake masa magana, idan har akwai wani abu da zan roka a wajenka bai wuce na rokeka a kan, ka amince mu kasance tare ba har abada, domin tabbatuwar mafarkin da ya jima yana bayyana a cikin baccina, ina sonka amma dole na barka tunda iyayena sun hango min matsala a tare da Kai.

    Cikin sanyin murya yake min magana yanzu baza ki tausayawa mijinki ba niima, ina cikin damuwa ko abinci na kasa ci, yanzu babu taimakon da zaki neman mana a wajen baba ya taimaka ya kyale mu muyi rayuwar farin ciki da juna,shikenan duk ginin da muka yi a baya ya rushe my Niimatullah, ki duba halin da zan shiga ki tallafi rayuwata, ji nayi hawaye sun fara zubo min hannu nasa na goge.

    Ina sonka dattijona amma bazan iya aurenka ba saboda mugun halin matarka saurin dakatar da ni yayi, tsaya Niimatullah bana son kina kawo tunanin wannan matar a ranki, babu abinda ta isa ta hana game da auren mu rayuwa mai dadi za kiyi da mijinki, ki tallafi rayuwata ki shawo min kan innah da baba su yarda da ni, a sanyaye na amsa da to zan yi insha Allah sallama muka yi da shi ya kashe wayar.

    Ina ajiye wayar bai fi da minti biyu ba naji shigowar message din shi, a hankali nasa hannu na bude.

Ina fatan zuwan ranar da zan kasance shinfide a saman kafadun ki na kwana a cikin dakin Ki, na kasance a tallafe bisa hannuwan ki,wato ranar da za a kirani da angon ki. Ki duba kaunar da nake miki ki shawo min kan baba, ina sonki ki huta abar alfaharina. Ina gama karantawa naji wani hawaye ya xubo min na tabbatar da cewa mijina yana sona idan na bar shi ban yimasa adalci ba.

    Wajen innata na koma fadawa nayi jikinta ina kuka, cike da tausayawa ta dube ni, me ke faruwa da ke Niimatullahcikin kuka na amsa mata da dattijona innah kada ya mutu ta sanadina na samu alhaki, yana cikin damuwa yace na roke ku, ku janye maganar nan dan Allah.

    Cikin kulawa inna ta dube ni tare da girgiza kanta, kiyi hakuri Niimatullah zan samu malam nayi masa magana nasan zai janye idan yaga halin da kuke ciki,ni kaina bana son auren nan ya tarwatse saboda Alhaji mutumin kirki ne kuma tsakani da Allah yake sonki kiyi hakuri Insha Allah zai sakko, rarrashina ta rika yi har sai da hankalina ya kwanta.

    Wayar da ke gefen mu ce tayi ringing, hannu innah tasa ta dauka,sallama tayi cikin kulawa aka amsa mata tare da cewa dan Allah ina neman Niimatullah ne, da sauri innah ta miko min wayar na kara a kunnena tare da yin sallama muryar matar da take min gyaran jiki naji cikin ladabi na gaida ta, tambayata dalilin da yasa kwana biyu banzo makaranta ba ta fara yi, muryata na hardewa na bata amsa saboda bakin cikin da ke cike a raina, an fasa auren shi yasa na daina zuwa.

    A razane ta tambaye ni me kike fada min haka Niimatullah bana son shirme fa, ina innar ki?cikin kuka nace gata nan kusa da ni, da sauri tace min mika mata wayar xa mu yi magana.

    Cikin girmamawa take wa innah magana, sannu baba ya gida ya yara, nice matar da nake gyarawa Niimatullah jiki naga kwana biyu bata zo ba shi yasa na kira nasan jiki da jini, sai kuma yanzu da na tambayeta dalilin rashin zuwanta naji tana min wata magana wai an fasa auren nata menene gaskiyar abinda take fada min baba? kana ganin Innata zaka gane tana cikin damuwa don damuwar har a maganarta ta bayyana, bayani ta fara yi mata ba karya Niimatullah ta fada miki ba gaskiya ne abinda ta fada, cike da mamaki take tambayar innata, to menene dalilin
hakan baba.

    Sauke numfashi Innah tayi mun fasa ne saboda muna ganin hakan shi ne abinda zai fi zama Alkhairi a gare mu dakuma ita, mijin Niimatullah yana sonta nasan kema kin san haka, amma kishiyarta ce ba tada kirki zuwanta biyu gidan nan tana ci mana mutunci har tana ikirarin zata hallaka Niimatullah wannan dalilin yasa muka fasa.

    Cikin nutsuwa malama ta fara yiwa Innah bayani, ina ganin ba haka ya kamata a yi ba baba, tufkar kawai za a yi hanci, amma batun a fasa ma bai taso ba, saboda za a cutar da zuciyoyi biyu da suka dade suna son juna, tunda matsalar nan ba daga wajen bawan Allahn take ba bai kamata a fasa ba, saboda idan aka fasa an ji tsoro kuma an bata damar ta cigaba da yin haka nan gaba, ita wacece da zata ce ita kadai xata rayu da mijinta,tunda Allah yabashi dama kuma yana da ra'ayin kara aure dole yayi, bazai yiwu a ce duk gyaran da muka yi ya tashi a banza ba baba, gobe insha Allah zan zo tare da Alhajin duk inda matsalar nan take sai an warwareta, godiya Innah tayi mata sannan suka yi sallama. 

    Ba karamin dadi naji ba da jin kalaman malama nasan tana zuwa komai ya zo karshe insha Allah. Baba na dawowa innata ta sanar da shi yadda suka yi da malama, shiru yayi na wani dan lokaci yana nazarin maganarta a hankali ya dago da kansa yana duban mu ni da innah, ni kuwa gabana sai faduwa yake saboda ban san irin amsar da zata fito daga bakin sa ba, cikin nutsuwa ya fara yi mana magana.

    Ina so ku fahimci wani abu ko kadan ban taba jin na tsani auren Niimatullah da Alhaji ba, hasali ma zan fi kowa farin ciki idan aka ce sun yi aure saboda nasan kyakkyawan hannu na kai ta, baza mu taba yin da na sani ba, amma abinda za a duba matsalar matar nan da irin furucin da take yi a kanta, nasan irin wadannan matan ba tun yanzu ba idan suka yi yaki da baki suka ga bai ci ba komawa suke su bi mutum ta kasa, shi yasa bana son abinda zai zo ya tayar mana da hankali muna cikin zaman mu lafiya.

    Ji nayi kamar nayi kuka wata sabuwar soyayyar Dattijona ce take dada bijiro min ban ki a ce na tashi na komagidansa da rayuwa ba, duk wata matsala da baba yake hango min ni a yanzu bana ganinta, saboda ko kadan Allah ya cire min tsoron matarsa kuma ina jin zan iya yin fito na fito da ita ba tare da wata fargaba ba, nasan nayi nisa a zuciyar mijina wanda bata isa ta kamo ko rabin son da yake min ba, kaina a kasa na fara yiwa baba magana.

    Ni dai baba idan da yadda za a yi dan Allah ka bari na aure shi wallahi ina son mijina, cike da mamaki innah ta dube ni, inye Niimatullahi har kin san dadin mijinki, lallai yaran zamani sai dai a barku kawai, shi kuwa baba kallona kawai yake y rike baki Innah ce take ta bayani.

    Malam tunda har Niimatullah ta furta mana tana son mijinta ina ganin ba mu da wani zabi wanda ya wuce mu tattara ta mu kai ta dakinsa, girgiza kai baba yayi, nima tunanin da nake yi kenan shi yasa kika ga na kasa magana, amma zan nemi Alhaji yazo ya tattara ta su tafi kuka na fara yi cike da shagwaba nake magana a tattara ni fa kace baba sai kace wata kayan wanki ni Allah sai ma na fasa auren, murmushi baba yayi ko kin fasa sai an kai ki tunda ina yi miki gata har kina cewa kina son mijinki ni ba ruwana dole sai kin tare, kuka na fara yi a kan ni bazan tare ba na fasa tashi baba yayi ya bar mana wajen, kan cinyar innah na fada ina cigaba da kukana.

    Washe gari Dattijo da malamar mu suka iso gidan mu a tsakar gida suka same ni ina hada kwanuka, sauri nayi na sanya hijabina saboda bazan iya jure kallon da yake bina da shi ba, a dakin innah nayi musu shimfida, shiga malama tayi ta zauna shi kuwa dattijona a tsakar gida ya tsaya yana cigaba da kare min kallo, cike da tsiwa nake masa magana.

    Menene ka tsura min ido kamar baka saba ganina ba, murmushi yayi tare da matsowa daf da ni riko hannuna yayi cikin sigar shagwaba yake min magana shi ne don kin ganni kike wani saka hijabi ko,naga dai komai na jikin ki mallakina ne to me zaki boye min.

    Harar shi nayi tabdi wallahi ba mallakinka bane nawa ne ko innah za a tambaya tasan da haka, murmushi yayi gami da jan kumatuna kina da dabaru na sanya ni murmushi my Niimatullah ko da a ce ina cikin fushi idan kika yi magana sai naji wni snyi a raina,kin zamo wata ta daban a gare ni, shi yasa ina ganin ki dukkan shaukina yake tashi,bana gane cewa ni namiji ne sai ina tare da ke, don haka ki daina tuhumata idan ina kallon ki, tunda kina sona ko matar dattijo. 

    hankali na gyada kaina alamar eh, murmushi yayi sannan ya cigaba da magana nasan da cewa tunanin ki a kullum bai wuce neman hanyar da zaki inganta rayuwata ba ki bani farin ciki mara misaltuwa,wannan dalilin yasa na sadaukar miki da soyayyata kuma nake fatan kasancewa da ke har abada my Ni'ima, bazan iya daina kallonki da begenki ba har sai ranar da numfashina ya kare duk maganganun nan da yake yi kaina na kasa saboda kunyarsa gaba daya ta kama ni,maganar da innah tayi masa ne yasa ya dawo hankalinsa, a sanyaye ya cika ni tare da sumbatar hannuna, sai na fito my Niimatullah na sake ki ne ba dan na koshi da ke ba,sai dan zuwa na samo mana mafitar yadda zamu rayu da juna har abada, sakina yayi na koma gefe na zauna.

    Tattaunawa suka fara yi a kan maganar tarewa ta a gidan dattijo, kwala min kira innah tayi da hanzari na karasa dakin cikin ladabi na tsugunna tare da cewa gani innah, cike da kulawa ta dube ni kira mana malam a waje, takalmana na saka ina fita naci sa'a na same shi, yana shigowa malama ta fara magana.

    Mun xo ne baba a kan maganar tarewar yarinyar nan, naji ana cewa kun fasa shi ne nazo na baku hakuri a kan bai dace a yi saurin yanke hukunci haka ba,tunda dai suna son junansu, kuma maganar kishiya baza ta tsoratar da mu ba tunda yarinyar nan mijinta na sonta duk wani abu da zai cutar da ita zai yi kokarin kawar mata da shi.

    Gyara zama baba yayi, ni dama ban zafafa ba Hajiya fatana dama yazo ya fada mana irin matakin dazai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda zai je ya dawo ko ba haka ba. Gyara xama baba yayi, ni dama ban zafafa ba Hajiya fatana dama yazo ya fada mana irin matakin da zai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda xai je ya dawo ko ba haka ba.

    Cike da zumudi dattijo ya fara magana, wallahi baba babu wata matsala da za a samu duk wani matakin da ya kamata na dauka naje na dauka, na yi mata magana a kan ba ita ba Niimatullah idan kuma ta cigaba xa tayi a bakin aurenta.

    Saurin dakatar da shi baba yayi, a'a ba a haka Alhaji kada auren nan yayi sanadin rabuwar ka da uwar yayanka idan kayi haka baka yi adalci ba sannan duniya zata zage ka mu ma zata zage ma, a zaci don ka auri jikar mu ne kayi mata wannan wulakancin, baza a duba girman laifin da tayi ba namu za a gani, don haka kada ka fara aikata haka, kawai kai dai kayi niyyar tsayar da adalci a gidanka sai kaga Allah ya taimake ka amma batun kace zaka saketa ma bai taso ba.

    Cike da ladabi dattijo ya amsa da insha Allah zan kokarta baba, na gode da wannan shawarar da ka bani, haka suka cigaba da tattaunawa daga karshe aka tsayar da lokacin tarewar mu nan da sati biyu masu zuwa, ba karamin dadi dattijo yaji ba, nima farin cikin ne ya kama ni saboda duk kusan hirar da suke yi a kunnena ake yinta.

    Tashi suka yi zasu tafi, a tsakar gida dai suka kara tarar da ni, kirana malama tayi ta fara yi min nasiha. Kinga yanzu tarewar ki ta matso don haka gyaran jiki zamu rika yinsa ba dare ba rana idan kuma baki tsaya an gyara ki ba kin zauna kina gaddama kishiya ta raina ki,ni ba ruwana don haka yanzu duk abubuwan da na baki ki mayar da hankali ki shanye, idan kin zo gobe zan baki wasu ki kara sha,so nake ki rikita mijin nan naki ya kasa gane hanyar garin su, dariya muka yi gaba daya har mun yi sallama ta tafi ta dawo ta kira ni, kije mijinki na son magana da ke, makale kafada nayi ni Allah bana son zuwa, hararata tayi kinga irin abinda yake hada ni da ke ko wuce mu je nace miki.

    Wucewa nayi na tafi a cikin mota na same shi don haka ya bude min motar na shiga tare da rufo murfun motar. Wannan kenan.


contact-form




Labels:

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home