Meyasa Ana Samun Mutuwar Aure A Cikin Lokuta Kadan
Mekesa Ana Samun Mutuwar Aure Da Wuri
Assallamu alaiku yan uwa jama'a, muna so ne muyi bayani game da yadda mutane suke magana game da, meyasa mata aurensu yakan mutuwa da wuri. Wasu matan sunce mazan ne basu da hakuri, ta wani wajen kuma mazan sunce matan ne basu da hakuri, to bari mugani ta wane bangare ne aka fisamun matsala kota wajen matane ko ta wajen mazane da kuma tayaya zamu magance wannan matsalar.
Zakaga masoya suna yin soyaiyarsu kamar har idan rana daya nasu hadu sunga juna ba sai kaga kamar zasu mutu, zakaga za a wuni ana ta yin chatting ko ta facebook ko ta whatsapp, in allah yakawo dare kuma sai a hadu ido da ido a cigaba da hira kuma kowa baya so yarabu da juna dan zunzurutun son da kowa yake wa junansu har lokacinda zakaga anyi aure, bayan aure kuma kowa yagaji da ganin juna bayan lokaci kadan kuma sai kaga anfara samun matsala da kadan kadan sai kaga abin yayi zafi in har ba a sa hakuri a ciki ba sai kaga saki yashiga aure ko wata biyar baiyiba aure yamutu.
To wannan al'ammarin bamusan ko me yake faruwa ba, yadda yanzu mata zawara suka yawa a yanzu, sai kaga mace taje gidan rediyo tana magana dan ita bazawara sai kaga kunya yafita a idanunta tana gaya wa duniya akan duk wanda yana sonta da gaske tafito yanuna kansa har idan dagaskiya yake yi sai suyi aure. Ita kuma bata tunane akan zuwanda tayi gidan rediyo za a fasarata ta hanya da dama.
A yadda mukayi bincike namu game da yadda aure yake mutuwa bawai yana da ga bangare daya kawai ba, ko wanne yana da na shi a ciki.
Wasu da ga cikin abubuwanda yakan iya jawo aure ya mutu shine, zaka namiji yana neman yarinya dan wani abinda yaga kamar tana da shi, sai kaga sonta yashiga ransa amma wannan son da yake yimata ba wai son na allah da annabi bane kokuma zance bai gina wannan auren dan allah ba kawai yana duban tana da wani abune wanda yaso kuma yashiga ransa, bayan anyi wannan auren yazo yagani abin kuma ba haka ba, sai kaga yafara wasu hallinda ita matar baza ta gane metayi masa ba, zata ta fara ganin wulakanci da dama iri iri sai kaga yana allah allah tayi wani abinda zai sa ya saketa.
Wani dalilain kuma zakaga mace bata son wani, amma iyayenta suna sonshi badan komai ba dan arzikin da yake hannunsa, sai kaga yarinyar tace bata so amma iayen sai sufi karfinta sai ta aureshi dan suma sudinga lasa abida yake dashi. Sai kaga bayan anyi aure yasanu abinda yakeso daga nan zata fara ganin abubuwa masu banhaushi dan yasan ta aureshi ne dan abin hannunsa a shiyasa zai fara yimata abinda har zai jawo dalilinda har idan ta nuna bacin ranta sai yasamu hanyar da zai saketa.
Zakagani wani lokaci namiji yana son yarinya amaimakon yafito mata a yadda yake da kuma yadda allah ya ajiyeshi, sai yafito mata da karya dan kawai yasamu yadda zai jayo hankalinta, bayan yasameta yayi nasaran aureta, sai kaga bata gani abinda take zaton za ta samu ba. Da ga nan ne sai idan basu sa hakuri a cikin zuciyarsu ba, sai saki ya shiga tsakaninsu dan auren karya bai da amfani fadin gaskiya shine mafin'alheri ga masoya in ana so ayi zaman lafiya.
wani dalilain shi ne rashin kulawa da juna ko ta wajen mace ko ta wajen namiji, dalilin da yasa nace haka, zaka ga mace bayan tayi aure ko bayan sun samu yara sai kaga ta fara yimasa rashin kulawa kamar misali bazata ta na kulawa dashiba dan tana gani sunriga sunyi aure kuma sunsamu yara a tsakaninsu ko tafara rashi tsafta wani lokaci zakaga idan kazo gida kamar da yamma sai katarar kwanon da aka ci abinci har zuwa yamma bata wanke ba ko sharan gidan ma zakaga batayiba, da kuma rashi kwalliya da sauransu. Ko kuma yakan faruwa daga shi namijin ta wajen rashin kulawa da ita bayan sun dauki lokaci ko shekaru bayan tafita akansa duk abinda yakeso yayi da ita sai kaga yafara mata wulakanci daga nan kuma wani namijin sai yafara neman matan banza a waje to kagani baza ta yarda ba dole ne tafara nuna rashin jindadin abinda kake yi har idan baka dena ba dolene har idan tagaji zata nuna maka abubuwa da dama na bacinrai har wanda zai kawo sanadiyar saki a tsakaninku.
Sha'anin aure abune wanda yakamata mu dinga kulawa, kuma abune wanda har idan munbi yada allah yafada abune wanda yakesa mutum yasamu aljannah har idan ma'auratan biyu kowa yabi abinda ubangiji yace game da aure. Kuma Allah (SAT) yana maicewa, har idan ka sake matarka Al'arshin Ubangiji yana kadawa, shi saki a musulunci hallal ne amma ba ace a rika yinsa wanda ba bisa ka'ida ba, sakin aure ana yinsa ne bisa yadda addinin musulnci yace ba wai kawai dan wani karamar matsala yashi ga a tsakaninku ba sai kace mata na sake a'a bahakabane, dan wasu mallaman addini sunce har idan wata matsala yashiga tsakaninka da matarka wanda har yakawo kun samu tsappani, kayi kokari kafita ko kaje kasamu wani abokinka kuyi hira nan da lokaci kadan zaka ga hankalinka ya kwanta itama sai kaga tayi sauki wani lokacinma in har kadawo gida sai kayi mamaki yadda zata karbeka.
wannan shine abubuwanda suke jawo aure yakan mutuwa da sauri dan idan za abi yadda shari'a yafada to akan samu sauki sosai ba wai yadda a yanzu muke sakin mata kamar yadda muke yin nunfashi ba, ko da kake so ka sake matarka kabi yadda addini yace to zaka samu sauki har idan ita matarka din taki tayi hakuri a sasanta to sakin yafi alheri amma kawai kwasam ka sake mace ba wai tayi maka na kirkiba dan kunjima kuna zaman uare ta ita ka gaji da ita sai ka nemi abinda zai kawo muku matsala dan ka saketa.
A wani lokaci kuma mata susuke kawo matsala gameda wasu matan bayan anyi aure an samu dan shekaru ana zama, sai kaga anfara yin kawance da wasu matan da ba na kirkiba sai kaga sun sata cikin wani rayuwa wanda har zata fara raina mijinta sai tana ganinsa kamar ba mutum bane halayenta zai canja dan tahadu da matanda sun bude mata idanunta wanda sun fi karfin mijinsu sai abinda suka ce a gidansu, to kagani wannan ma har idan mijinta yayi daidain karfinsa har idan abin yagagara dolene kaga saki yashiga tsakaninsu.
Yawancin matsalar da ake samu cikin kashi (100) ana samun kashi (70) na laifi daga wajen namiji, dan shine allah yabashi ikon tsakanin ma aurata shi yake da izini yasaketa, muji tsoro allah zakaga mace tana tafiya amma jikinta yana wani waje dan rashi zaman lafian da bata da shi tare da mijinta, wata idan tayi maka bayani abina yake faruwa da ita in kaji na watanku sai kaga gwara na wancan dan mu mazan muke fara kawo matsala a tsakaninmu da matanmu sai mu mayar da su kamar bayi dan kai ne allah yabaka izzinin aiwatar da komai ko wani idan yaga tafito daga gidan da iyayenta basu da karfi sai yamayer da ita kamar baiwa a gidansa hakan baya da kew, ka guji hukuncin allah dan lokacinda hukuncinsa ya haukanka zaka yi kuka wanda kana neman hawaye ma ya sauka bazai sauka ba.
Zakaga namiji yamayer da saki kamar wani abin wasa, sai kaga yau ya aure wata bayan wani lokaci kadan sai kaga yasaketa kuma yakar auran wata bayan yasamu abinda yakeso sai kaga kuma yakara saketa duk bawani dalilin da har yakai wanda zai saketa, to irin wannan bashi da kew dan lokacinda allah yakamaka, har kamutu rayuwarka ba zai yimaka kew ba har idan baka tuba ka koma ga allah ba.
Shi a rayuwar mu na yau game da matan aure da mijinta ba wanda zai samu natsuwa ga juna sai da mijinta, shima mijin ba zai samu natsuwaba sai da matarsa, wannan allah ne yashiyar mace bazata iya rayuwaba sai da namiji, kuma namijima bazi iya rayuwa ba sai da mace, tu a zamani annabawa sunyi bayani game da mace abune kamar zinariya, ko wane irin kudin da allah ya baka zakaga mace tana juyashi tana zoliyarsa kamar yaro karami ba komai bane kawai allah ya dauramusu abu ne wanda yana jikinsu har idan akwai soyaiya a tsakaninsu na aure.
Zakaga wani yana neman wani abu a wajen wani sai kaga yagagara samu, amma idan har yabi ta wajen matarsa sai kaga anyidace, to mata abune wanda allah ya basu wani abu ajikinsu wanda zakaga namiji zai mayar da kanasa kamar yaro karami.
To dan allah aji tsoron allah adena yin sakin mace kamar wata dabba, dan a lokacin su kakkanninmu sunci nasara ba dan komai bane da hakurin da sukayi na zaman aure shiyasa suka ci ribar aurensu ba dan komai bane dan sunbi yadda shari'a yace, amma mu yanzu sai kaga kunlum namji yane cewa mace sai na sakeki ai' kunlum zakaga yana furtawa a bakinsa to hakan ba dai dai bane abi shari'a a zauna lafiya a cin ribar aure.
A dinga daraja mata har idan sunyi laifi kayi musu nasiha kuma ka dinga yaba mata shi arayuwa soyaiya bata tsufa sai dai masoya su sufa, kulawa da juna ga maurata yakan kara soyaiya a tsakaninku, amma sai kaga mace idan tayi wani laifi kadan sai kaga namiji yafar mata tsawa kamar ita ba mutum bane, har idan matanka tayilaifi kokuma tanayin wani abu ka hanata ta takiji sai kace mata taje gidansu ta zauna wani lokaci ita da kanta zata yi nazari akan laifinda tayi, wata har idan tana da imani zata baka hakuri akan laifinda tayimaka to dole ne tasan tayi kuskure zakaga baza ta karayiba.
Kuma mata kuna da naku laifi, wata idan taji mijinta zai karamat kishiya sai kaga tafara daga hankalinta kuma allah ya hallatta namiji yakan iya kara mace biyu har zuwa hudu. Dan annanbi (SAW) yace mata zasu shiga wuta dan tawajen bijirewar dan mijinta zai karata kishiya wanna shurmen banzane dan allah yariga ya hallatta in har kinnuna bacin ranki, to kina jajjawa da abinda allah yafada. Muji tsoron allah a dinga yin hakuri, Annabi (SAW) duk macenta ta kafircewa mijinta zata shiga wuta "Bukhari".
Mata dan allah ku rika yin tsafta dan idan mijinki yashigo gida ganin farkon da zai fara yimiki daga sama har zuwa kasa, har idan tayi kwalliya zai yi sha'awa ko su rungume juna, amma har idan kina nan kwasap ba dankwali, kai a tsefe, kinannan kamar wani namiji to hakan bai da kew, yakan sa namiji yafar neman mace a waje. Har idan aka bi wannan abinda muka fada to za'a samu sauki game da mutuwar aure da yake faruwa.
Ina yin fatan alheri ga muji soron allah a duk macenda aurenta yamutu har yayi sanadiyar tazama bazawara, sai ta kama kanta, tarike mutuncinta allah zai bata mafita har idan ta kama kanta. Allah yabamu dama kuma yaganar da mu a duk wata hanyar da ta sabawa shari'a. Assallamu Allaiku.
Hakika ina jin takaicin a yadda yau aka wayi gari mace-macen aure ya yi yawa musamman a kasarmu ta Hausawa ko in ce matanmu na Hausawa, musamman idan ina kallon sauran yarurruka a fili ko a fim.
- Abu na farko da na nazarta shi ne kwata-kwata auren ba a gina shi domin Allah ba. Wasu sun gina shi akan karya, wasu kwadayi wasu kuma domin wasu abubuwa da yake hange a tattare da macen wanda suke burge shi wanda da zarar an yi auren ya ga ba yadda ya zata ba, to sai ta fi ta daga ransa sai ya fara yi mata wulakanci daganan ya saketa. Wannan maganar da na fada ba ina nufin kowa ba, ina magana akan mafi yawancin mutane.
- Sannan abu na biyu wanda shi ma yake taka rawar gani wajen mutuwar aure shi ne kwadayayyun iyaye. Sai ka ga mai kudi yana neman auran yarinya ko ba ta so iyayenta za su tursasa mata sai ta aure shi saboda kwadayin abin hannunsa, ba za a tsaya a yi kyakyawan bincike ba saboda yanad a kudi, sai a dauki yarinya a aura masa, wanda a karshe sai irin wannan aure ya zama na nadama. Da ta shiga gidansa sai ya fara gwada masa irin halayensa na cin mutunci daga nan kuma sai saki ya biyo baya.
- Abu uku kuma shi ne karya. Namiji zeai je ya yi ta yi wa mace karya, ya rudeta ta don ta aure shi wanda da zarar an yi auran sai ta tarar da sabanin abin da yake mata karyarsa daga nan sai ka ga an fara samun matsala, daga nan sai saki.
- Abu na hudu shi ne rashin hakuri tsakanin ma’aurata, shi ma yana taka muhimmiyar ruwa.
- Abu na biyar shi ne rashin iya rike juna da amana da tattala juna da nuna wa juna soyayya daga dukkan bangarorin biyu. Sannan kazanta tana taka rawar gani wajen mutuwar aure, musamman daga bangaren mace. Akwai abubuwa da yawa wanda yakamata mu lura da su domin magance wadannan matsaloli na mutuwar aure.
Hakika aure wata hanya ce wadda ake samun aljanna a cikin sauki a cikinta sai dai ya danganta yadda ma’aurata biyu suka tafiyar da auren cikin tsoron Allah. Haka nan saki shi ma halal ne amma ba a son yinsa a addinance domin Allah (SWT) ba ya son a yi saki domin duk lokacin da aka yi saki sai Al’arshin Ubangiji ta girgiza.
To da wannan dalilai ya sa saki ya zama abin ki wanda ba a son sa sai ya zama dole domin akwai matakan da shari’a ta ajiye yadda za ka bi da mace wanda har in ta bijire to sai a saketa. Amma ba yadda ake yin saki birjik a halin yanzu ba, babu wata hujja mai karfi.
A nan nake kira ga maza su ji tsoran Allah domin su ne suke yin saki domin mace bat a sakin kanta sai dai namiji ya saketa. ’Yan uwana Musulmi maza ku sani cewa mata ba abun wulakantawa ba ne kamar yadda kuka mayar da su a yau. Kowace mace idan ka yi hira da ita za ka ji irin izayar da take ciki a wurin mijinta, idan ka ji na wannan, sai ka ji ai na waccan ya fi muni.
An wayi gari mata a wulakance wasu mazan sun maid a mata tamkar riga idan ya sa waccan, ya sa waccan. Wallahi wannan musiba ce kuke jawo wa kanku don wannan ba burgewa ba ce. Kamar yadda Manzon Allah (SAW), yake fada a hadubarsa ta ban-kwana ina imuku wasicci da alkairi gamata. To ku ji ’yan uwa yanzu tun da Annabinmu ya fadi wannan, mata yakamata su zamo abun wulakantawa? .
Annabinmu mu ne fa ya fadi wannan! Kuma kar ku manta duk rintsi mata ne suka haifeku. Ina nasiha akan masu wannan dabi’a ta wulakanta mata akan su daina. Mace tana da daraja, kalmar mace tamkar zinariya take wajen yin walkiya a kowane lokaci. Mata suna da sinadarai wadanda suke da tasiri, a cikin al’umma wanda har ta kai sun samu matsayi babba. Mata suna da wani launi mai juya mazaje tamkar linzamin doki, komai matsayin mai mulki ko kudi ko sarauta.
Labels: Soyaiya
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home