Meyasa Maza Suke Yaudaran Mace? Da Kuma Meyake Sa Baki Yayi Wari

   



Abubuwa Guda Biyu Zamuyi Bayani Shine:-
Mekesa Maza Suke Yaudaran Mata
Mekesa Baki Yayi Wari

A rayuwan mu na yau, neman aure yazama abune wanda take da wahalla har ida baka samu mace nagari ba? wasu suna mantawa da allah har idan suka sa wani abu a ransu har idan abi bai yi ba sai kahada da rokan allah yabaka sa'a game da abin da kake nema.

    Har idan kana neman aure, sai kayi kokari kane ma kayi (instingifari) allah yazaba maka nagari dan komai a rayuwan mu nayu sai ka hada da allah har idan bakaso kasamu cikas a ciki.

    Sai yayi "Raka'at guda biyu" kamar yadda hadisi ya rawaito "Jabir dan  Abdullahi daga riwayar bukhari (1166) bayan yayi sallama wasu malamai, wasu mallamai suna ganin za a iya yin wannan addu'a kafin sallama, kamar Shekkhul Islam Ibn Taimiyya, sai yakaranta wannan addu'a ta neman zabi daga Allah.

Na biyu shine kane mi shawara ga mallaman addini da kuma masana subashi shawara game da bukatarshin da yagaya musu, duk wanda yakan nema shawara game da wani abinda ya damesa, to zai yi nasara game da duk wani abin da yasa a rayuwarsa.

    Ta uku kuma har idan namiji ko mace yana neman aure to ayi kokari a cire son zuciya game da neman aure, dan a rayuwar mu ta yanzu samun mace nagari ko namiji nagari yana da wa hala? zamaninmu na yanzu mata masu kew basu da yawa, sai kaga ga mace bata da kew amma ga addini, wata kuma ga kew amma bata da hali, sai kaga namiji hankalinsa yarabu kashi biyu.





















Manzon allah yace namiji yakan aure mace ta hanya guda 4, zaka iya auran mace da addinta, ko kewnta, ko arzikinta, ko matsayinta, Daga Bukhari 5090. Daga Abu Hurairah RA. Wannan abubuwan guda hudu da muka lisafasu, zaka iya samun mace wanda tana da wannan abin dukka, wasu matan kuma suna da guda uku, wasu suna da guda biyu, wata kuma daya ne allah yabata.

Wacce mace wanda tafi? duk wanda tana da wannan suffofin guda hudu? amma ga wasu da muka lisafa shine:-

  1. Mai kew, mai kudi, mai addini, dukan wannan guda hudun tana da shi.
  2. Mai addin da kew.
  3. Mai matsayi da kuma kudi babu amma babu kew da kuma addini.
  4. Mai addini amma babu kudi.
  5. Tana da kew amma babu tarbiya da addinni.
  6. Mace kuma wanda tana da abubuwa na Boye, kamar, hakuri, iya zaman aure,.
  7. Mace wanda tana da shi kuma a fili shine kamar, tsayinta haskenta, da sauransu.
    Mafin yawa a yanzu mutane suna son suga sunnemi mace mai kwe, amma dazaran sun dauki shekaru, wannann kewn nata yatafi sai kaga anfara samun matsala game da abinda yasa ya aureta yatafi. Yawancin maza suna samun matsala ne yawancin idan ka aure mace dan kewn ta sai kaga suna ba wa mazn wahalla dan tasan dan kewnta ne ka aureta shiyasa zata dinga yimaka abinda tana so.

    A kwai wasu abubuwa da dama wandda maza ko mata suna so suga tana da shi, ko yana da shi, amma hakan bashi da kew fa musulinci, wani zakaga yana son yarinya doguwa, kofara, ko siririya, ko wanda tana da jiki, amma hausawa sunce kewn wani munini wani, zakaga wani yana yabon wana dan tana da kew amma wani kuma yana yimata ganin ita mumunane.

    Ya tabbata da wani Hadisi daga Maa'kalu dan yasar yace: Wani mutum yazo wajen Manzon allah SAW, sai yace Na same wata mata zan aura tana da matsayi kuma mai kyau ce, na iya auranta? sai yace masa a'a. bayan wani lokaci kadan kuma yakara zuwa yakara tambayansa yace masa zan iya auranta, yakara ce masa a'a. Yakara zuwa na uku yakara cemasa zan iya auranta: sai yace masa ku auri mace mai iya soyaiya, kuma mai haihuwa domin zan yawaici al'umma da ku. (Abu Dauda 2050. Nasaiy 3227. Silsila Na Albaniy. 2373.

    Wannan hadisi yazo da siffofi guda biyu  sune soyaiya da haihuwa, yaya za a yi zaman soyaiya, kuma ku haifi yara wanda zakuyi musu tarbiya bisa yadda addinin musulunci yace. Zamu kara wasu suffofi guda 11 . A kwai wani hadisi da ga Abdullahi dan (Amri) yace Manzon Allah SAW yace: samun mace ta gari a wata riwayar da Tirmiziy ya ruwaito da siffofi guda biyar, wacce idan ka kalle ta za ta faranta maka rai, idan ka bata  umarni za ta yi maka biyayya, idan kayi mata rantsuwa ko kashedi ba za ta saba maka ba, idan ba kanan ko kayi tafiya za ta kiyaye maka dukiyar ka da mutuncin ta. Idan muka kalli wadannan hadisi guda uku za mu ga sun zo da siffofi guda goma sha daya kenan sune:-

  • Mai addini.
  • Mai kudi.
  • Mai kyau.
  • Mai matsayi.
  • Mai soyaiya.
  • Mai haihuwa.
  • Mai faranta rai.
  • Mai biyayya.
  • Mai daukar tsawa da kashedi.
  • Mai kiyaye dukiya.
  • Mai kiyaye mutuncin ta.
    Wannan sune suffifin da mika sa mu daga manzon allah SAW wanda irin matar da yakamata ka aura, amma irin wannan mace wanda take da wannan abubuwanda muka lisafa, samun irinsu yana da wa halla, amma har idan kasamu mace mai wannan duk a binda muka lisafa to kagama more aure har a bada.

ME KE SA MAZA SUKE YAUDARANSU

Dalilina shina, kashi cikin 75% namata ke sa maza su yaudaresu, Sai kaga mace wai dan namiji yazo wurinta yace yana sonta sai tayi amfani da wannan damar dan akan wai shi yakawo kansa yace yana sonta sai ta fara yimasa jan'aji, wai dan kar ace yasameta da sauki sai kaga idan yazo yana jiranta a waje sai lokacinda ta gadama zata fita , kokuma tace masa yaje yadawo anjima tana yin waniabu tukunnan yanzu.




















Daga nan ne sai kaga namiji yace zai yi hakuri yabita da duk abinda zata yimasa har sai yayi kokarinda zai gani yashawo hankanlita, bayan yagama saci zuciyarta tazama tana mutuear sonsa, sai yayi kokarinda zai ga yarabuda ita, sai kaji tana cewa ai munafikine ya yaudareni allah ya'isa, amma baza ta tuna abinda tayimasa a baya ba.

Yawancin matan yanzu idan baka zomusu da karyaba, to baza ku zauna lafiya ba, shiyasa maza yanzu sai idan suka yiwa yarinya magana sunga ta ida ta dosa, sai su bita a yadda take so, nan bada jimawaba idan yanemi hanyar gujeta sai tace ya yaudareni amma baza ta tuna akan ita yar karyane ba.

Zakaga namiji idan yazo wa mace yace yana sonta ko da bai je ta wurin iyayenta ba, sai kaga ta meyar dashi kamar Bank, ko da yaushe idan zai zo wurinta sai ta ce masa kasayamin (ice cream) ko kuma wani abu dai na marmari, to kagani wannan ba yi bane har idan namiji yace yanasonki ba zancen kashe miki kudi batare da ansan shi a gidanku ba, kuma dik namijin da yake kashe miki kudi to kisani sai kinbiya ta wani hanyar, amma mace ta gari zata ta ce masa yaje gidansu su sanshi to kagani wannan shine hanya mai kyau, dan a gidansu ansa waye ne yake nemanta ko da yakashe mata kudi yasan ko zaiiya aureta ko ba zai iya aureta ba.

Har idan namiji yana kashe miki kudi haka kawai, to kisani ba zai kashe miki a banza ba sai sai yane mi wani abu a wurinki, har idan yasamu abinda yake bukata, to zai yi kokari yaga yayi awungaba kayansa, dan yasan kinsoshine dan abin hannunsa ba wai an allah da annabi bane, sai kaji ta ya yaudareni. To Allah ya kewta.

A wani lokaci zakaga mace tana soyaiya da wani wanda shi yasan bazai iya aureta ba, kuma ko da tace masa yafito sai yadinga yimata hanyar da ba zai fitoba, kuma sai kaga ta kori duk wanda take tare da shi akan tasamu wanda takeso alhali kuma ba auran ta zai yiba dan idan yace ba zai aureta ba, zatace ai ashe baya sonta dama, sai kaga suna ta soyaiya sama da shekaru bayan tayi, tayi yafita, yakifita har idan yaga abin zai yi tsanani to anan ne zai nemi hanyar sa da zai gudu, kuma tasan wannan ba iya aureta zai yiba dan aikinda yake dashi tasan ba zai iya riketa ba sai kaji tan cewa ya yaudareta. To Allah ya kyauta. 

.....................................................................................................................................

MEYAKE SA BAKI YAYI WARI

    Shi ciwon ta masalar ta warin baki abune wanda da zaran mutum yabude bakinsa, to baza ka iya jan nunfashiba da warin da zai fito daga bakinsa kamar wani warin mushe ko kamar bakin shadda. Wannan ciwo ta warin baki ba wai wani abune wanda baza'a iya maganceshi ba, abune akwai hanya da dama wanda ake magance sai kaji kamar baka taba yin warin bakiba.

    Zakaga kuma shiwanda yake da wannan warin bakin sai kaga idan yana magan she bazai ji wannan warin  bakinsa ba sai dai wanad yake kusa da shi shine zai ji wannan warin bakin na sa.

    Akwai wata cibiya kiwon lafiya wanda aka fisaninta da mujallar ta (Medicine News Today) ta wallafa hanyar da za a magance wannan wanda suke fama da wannan ciwon ta warin baki. Shi wannan ciwon ta warin baki yazama ciwon dare ga jama'a a yanzu, dan mutane da dama suna zuwa wajen likita game da wannan ciwon dan neman magani sabo da rashin sakewa a cikin jama'a.

    Dazaran mutum mai warin baki ya bude bakinsa tundaga nesa nasawon kamar mita uku 3 sai anji warin bakin nasa har idan yagane ana jin wannan warin na bakin nasa sai kaga baya zuwa kusa da mtane sosai dan zai zamamasa abin kunya.

MEYAKE JANWOWA

    Yawancin abinda yakan kawo warin baki shine, rashin tsafta ta wajen wanke baki, wani kuma sai kaga idan yasamu wani rashi ta lafiya sai kaga yasamu wannan larural ta warin bakai.

    Akwai wasu kuma tawajen cin abincine ko zance abincin da muke ci shi yakan jawo wannann warin baki. kokuma abubuwnda muke sha ayau da kunlum wani abin har da bakinsa bai dace da wannan abinba to yakan iya samun wannan ta warin baki.















  1. Rashin wanke baki ko tsaftar baki.
  2. Barin abinci a baki idan angama cin abinci
  3. Ba wanke baki bayan anga ma shan kayan zaki.
  4. Hakorin ka ya rube daga can karshe.
  5. Bakin ka ya bushe garam.
  6. Shan kayan maye kamar su wiwi da sauransu.
  7. Akwai wasu magungunan da likita in yarubuta maka kana sha, shima yakan jawo warin baki, amma har idan lokacin da andena shan wannan maganin to bakin zai iya dena wari.
  8. Wani bakin kuma dalilin wasu kwayoyin cutar da suka taru a hanci ko wuya suma suna iya jawo warin baki.
  9. Abinci kamar cinsu tafarnuwa da cin albasa shima yakan iya jawo warin baki sosai har idan ba'a wanke baki sosai ba dan albasa yana da wari sosai da shi da tafarnuwa.
TAYAYA ZAMU KAUDA WANNAN CUTAR TA WARIN BAKI.

    Shine wanke baki da brush har idan duk lokacin da aka ci abinci, kokuma goge baki da Aswaki a duk lokacinda aka sha wani abu ko naci akmin a kwanta. Amma wasu likitan sunce kar kayi amfani da abin wanke baki kala guda daya, ka dinga canja wa shi yafi.

  1.     Ana so a dinga zuwa wurin likita dan yaduba abinda yake faruwa game da wannan warin baki, dan su zasu gane har idan a kwai wani hakorinda yasamu matsala ko ya lalace kokuma wani cutar ce tasameka su zasu gane in nayin maganine zasu baka magani har idan na bada shawar ne kuma zasu baka sahwara.
  2. Zaka iya wanke bakinka da ruwan zafi amma a sa gishiri a ciki dan yana kau da duk wani kwayoyin cutar a baki.
  3.  Adin yin amfani da wata sunsiya ko makamancisa dan a cire duk wani abincin da ya makale a sakanin hakoranka.
  4. Har idan zaka wanke baki da brush naka sai ka goge harcenka sosai, dan shima dattin abinda kaci yana daskarewa akan harcenka.
  5. Aguji shan taba da kayan maye ko naruwa ko naci.
  6. Adinga cin cingam wanda bai da zaki dan shima yana sa baki yayi haske dan duk abinda kaci har idan kaci cingam zai cire duk abinda yamakale a hako rinka.




Post a Comment

Previous Post Next Post